Showing 480001 words to 483000 words out of 512766 words

Chapter 161 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

2419

damunshi shine a wane hali take ciki hakan har kuka yake saka shi, bin juna sukai da wani irin kallo mai nuni da tsantsar ƙaunar da suke ma juna can Farhar ta furta "I love so much Kamal, pls dont turn your back on me",

"I will never do that to you, My Love, i'm very grateful for accepting me for who i am, ban ta6a tunanin zaki so ni haka ba saboda tazarar dake tsakanin mu ajin ki ya wuce na ki soni shiyasa koda kika nemi da muyi ƙawance saida na jinjina abun sosae yanzu gashi kin za6i ma in zama abokin rayuwarki, i can't thank you enough, but, i give you all my heart in return" wani kalan murmushin daɗi tay ta faɗa jikinshi tare da lumshe ido yay shiru ƙirjin shi na bugawa don hakan abu ne da bai ta6a faruwa dashi ba ya haɗa jikin shi da mace koda kuwa yar'uwarshi tun bayan daya balaga duk da su a al'adarsu hakan ba wani abu bane amman su da yake suna da ilimin addini sun san hakan haramun ne shiyasa bai ta6a kowacce mace, hannu ya kai ya ɗagota suka haɗa ido tana ɗan murmushi ta furta yayi haƙuri taji daɗin Maganarshi ne, dama tun ba yanzu ba da suna ƙawance tana yawan ta6a shi tun yana sharewa ganin abun na yin yawa yace mata ta bar ta6a shi ba kyau kada su rinƙa samun zunubi, ce mashi tayi yazo suje ya gaida Mom ɗin ta ya ɗan waro ido tare da buɗa baki yace ba matsala kuwa tay yar dariya tace mashi he should be a man ba abund zai faru shima yay dariya yace to ko ta jirashi a falon Gwaggo ko Aunty Haulat ya shirya tace Ok ta juya tana faɗin yayi kyau sosae yace to, shiryawa yay cikin ƙananun kaya baƙin jeans da jar t-shirt anyi bakin rubutu a gabanta ƙafafunshi yasa baƙaƙen takalma sai agogo itama baƙa sumar nan tashi tubarkalla dama koda yaushe a kwance take ya ƙara gyarata sai salƙi take ya feshe jikinshi da turare ko maƙiyinshi sai dai don ƙiyayya yace bai yi kyau ba, lokacin da suka fito Amadu na shago yaje yace mashi zai je gaida surukarshi yay mashi Addu'a yay Maganar yana dariya shima Amadun dariyar yayi yace to Allah yasa a wanye lafiya in sun ji shiru kuma zasu zo beli Kamal ɗin yay dariya, tunda suka shigo harabar gidan gabanshi ke ɗan faɗuwa hakanan ya daure, lokacin da suka shigo cikin parlon ba kowa su Husnarh na Kitchen don rana tayi ta nufi bedroom ɗin Hajiya tare dashi, ita ta fara shiga shi kuma yay tsaye saida ta kalli cikin ɗakin taga yadda suke sannan ta juyo tace mashi ya shigo mana, ƙasa ƙasa da murya yace ta fara faɗi masu mana Hajiya dake kishingiɗe akan lallausan carpet ɗin gaban gado ta tada kai da tuntun ta ɗan ɗaga murya tace ita da waye anan ta maido kanta cikin ɗakin tana murmushi tace Kamal ne, tashi zaune sosae Hajiyar tayi tana faɗin to ya shigo mana shida ɗakin matarshi, tare suka shiga yay sallama ta amsa tana murmushi lokacin da idanunshi suka sauka akan Hajiya Maryam dake kwance saman gado ta rufe odo ƙananun kitson kanta sun bayyana sai da gabanshi ya buga sosae da sauri ya kauda idon, nuna mashi wuri Hajiya tay gefenta tace ya zauna Farha ma ta zauna cikin muryarshi mai daɗi ta bafullatanin daya ji hausa ya gaishe da Hajiya ta amsa tare da yi mashi ya jiki tace ai tukur ya faɗi mata yana can yana zazza6i Masoyiyarshi ta 6ace, da sauri ya sunnar da kan shi don wata irin kunya ce ta rufe shi data yi maganar Farha dake murmushi tace ko School baya zuwa,

"To ai yanzu sai kaci gaba da zuwa tunda gata ta bayyana" ta faɗa tana yar dariya shima murmushi yake bai ce komai ba, juyawa tay kan Hajiya Maryam tace tayi bacci ne ga ɗanta yazo su gaisa shiru bata motsa ba Hajiyar tace ƙilan tayi bacci dama bayan ta gama cin abinci tace bacci take ji, miƙewa Farha tay ta rankwafa saman gadon ta shiga ɗan bubbugata, buɗe ido tay da alamu baccin ne ya ɗauketa fuska a yamutse tace lafiya ta tashe ta nuna mata saitin Kamal tayi tace dama shine yazo gaidata ta wurga mata wani kallo mai kamar harara, har zata faɗi wata magana sai kuma tayi shiru ta maida idonta kan Kamal Farha tace mashi su gaisa ya ɗago ido ya kalli Hajiya Maryam ɗin cikin faɗuwar gaba yace mata ina wuni kamar bazata amsa ba sai kuma ta ɗaga mashi kai ya ƙara cewa an zo lafiya kamar wadda akai ma dole tace lafiya daga haka ta maida idanunta ta rufe, cigaba da jan shi da magana Hajiya tayi har tana tambayar yanayin karatunshi yana dai maida hankali ko yace mata eh, bayan wani ɗan lokaci yay mata sallama ya miƙe Farha ma ta miƙe Hajiya ta kalleta tana murmushi tace Juliet za'a raka Romeo tayi dariya, buɗe ido Hajiya Maryam tayi tabi Kamal ɗin da kallo har suka fita Hajiya data lura da tana kallon Kamal ɗin bayan fitar su tana murmushi tace to ya taga surukin nata tayi shiru bata ce komai ba,

"Inda zaki ɗauki shawarata kija yaron nan a jiki ki gina rayuwar shi sai yafi ma ruƙe maki ɗiyar taki da daraja" shiru Hajiya Maryam ɗin tay saida Hajiya tace bata jita bane sannan ta ɗan ta6e baki tace nawa akai ma haka amman suka butulce da sauri Hajiya tace sai dai dama can in butulun ne amman tana da yaƙinin zuri'ar Dije ba butulu bane Hajiya Maryam ɗin tay shiru bata ce komai ba can Hajiyar ta ƙara cewa "bari in maku da yaren daku yan siyasa kuka fi ganewa, yanzu aji kinja shi a jiki kin ginashi sannan kin ɗauki ɗiyarki kin bashi wane irin farin jini kike tunanin zaki a wurin mutane ta yadda koda nan gaba kin fito takara hakan zai iya saka mutane su za6e ki don ansan baki ƙyamar talaka kuma su naki ne, yanzu kamar yaron nan Sameer yadda ya auri ƙawar ita Fateema akai ta jinjina abun yanzu bashi ba ko mahaifinshi ya fito wata takara mutane da dama sai sun za6e shi dalilin haka, amman kawai misali ne na baki kan amfanin taimakon talaka a wurin ku yan siyasa nafi son komai zaki mashi kiyi mashi don Allah, ɗan jimm tayi kamar bazata tanka ba can ta tambayi Hajiyar mi yake karanta ta ɗan yi shiru alamar tunani kafin ta faɗi mata,

"Yanzu kenan ita Farhar zatayi ta zaman jiranshi har ya gama karatun?" ta tambaya idonta akan Hajiya tace mata to yanzu duka ba saura shekara ukku ba ganin lokacin ne mai wuya ai amman yadda yanzu shekara ta zama kamar wata ai kaman gobe ne zai gama in kuma zasu bashi yana karatun to sai a kawota nan Katsina shi yana karatunshi Hajiya Maryam ɗin ta ɗan ta6e baki bata ce komai ba, tambayarta Hajiya tayi yaushe zata koma tace tana tunanin ko zuwa anjima Hajiyar tace ta bari sai gobe mana tana kallonta tace to dama ba dalilin Farhar yasa ta kirata ba Hajiya tana murmushi tace "Eh, amman ban gaji da ganin yar autar tawa ba" ba shiri Hajia Maryam ɗin tayi murmushi,

"Kina yarinya Haƙuri ne dake sosae ba wanda zai ce in kin girma zaki zama rigimamma" tana murmushin tace mata ita ai bata rigima sai akan abunda take ganin shine daidai Hajiya na dariya tace haka dai tace,

"Yanzu da Farhar zaki tafi ne?" Hajiya ta tambaya tace mata eh saboda su Abraham suna zaune gida su kaɗai Hajiya ta jinjina kai kafin tace yakamata ma su koma gabanta can Abujar tace eh tana shirin yin hakan sai kuma Hajiya ta sake cewa to shi Dr ɗin sai a barshi a Lagos shi kaɗai Hajiya Maryam tace to tunda can yake aiki dole can zai zauna sai su rinƙa zuwa mashi Weekend ko kuma shi yaje Abujar in anyi hutun School ma sai yaran suje mashi hutu,

"To ki bashshi kawai ya ƙara aure mana" wani kallo tay ma Hajiyar sai kuma tayi ɗan murmushi tace ashe bata sonta har haka Hajiyar tayi dariya tace miye abun rashin so daga ta bata shawara yadda zata yi ma Dr adalci tace ai bata mashi rashin adalci tana kamantawa kuma itama ai bata rayu da kishiya ba ko, Hajiyar tace ai ita shine ke tafiya can aikin sojan shi ya barta ba itace ke barin shi ba kamar ita, Hajiya Maryam ɗin tace ai koda take barin shi bai zarta ƙa'ida ba da har zai sashi ƙara wani aure, ruƙe ha6a Hajiya tayi tace oh kowa gudun kishiya ita ko da ba'a yi mata ba General ɗin ne bai ra'ayi ba wai ita ta hanashi ba, Hajiya Maryam dake ɗan murmushi tace ai ba abun daɗi bace ita ko sunanta ma bata son ana faɗa,

"anya Maryam, adai rage zafin kishi tunda ba'asan abunda Allah ya ƙaddaro ba" da sauri tace "in dai ta wannan bangaren ne ba abunda ya ƙaddaro in sha Allah auren zobe mukai da shi" dariya Hajiya tayi tace banda wanda aka ɗaura masu a Masallaci kenan wani suka ƙara ɗaurawa tsakaninsu Hajiya Maryam ɗin na murmushi tace mata eh, haka suka cigaba da yin hira sama sama har baccin ya sake ɗaukar Hajiya Maryam.

Washe gari da safe ta koma tare da Farhar, sosae Dr Mahaifin Farha yay farincikin amincewar da Hajiya Maryam ɗin tayi, bayan dawowarta ne Dr ɗin yasa suka zauna don yin shawara game da Kamal yadda zasu inganta rayuwar shi nan ya bada shawarar su fitar dashi ƙasar waje yayi karatu a can ita kuma Farha sai taci gaba da yin Master's degree ɗinta ta amince da hakan, Hajiya ta kira ta sanar da ita suna son fitar da Kamalun waje tace ta sanar da dangin shi, Gwaggo ta kira ta sanar mawa koda Amadu yaji zancen bai goyi baya ba haka da aka sanar ma Fatuu cewa tayi gaskiya kada a amince a ƙyale shi yaci gaba da karatun shi anan salon nan gaba ayi mashi gorin an ɗauki nauyin karatun shi Gwaggo tace to ai ba roƙonsu akai ba su suka yanke hakan Fatun tace ita dai gaskiya bata goyon bayan hakan tunda ai karatun nan ma lafiya lou zai yi ya kuma samu aiki mai kyau, Gwaggo tace itama in son samu ne tafi son a ƙyale shi tunda ma har ya fara yin nisa saidai kuma bata son Hajiya taga anyi masu ba daidai ba, Amadu yace ai Maganar bata Hajiya bace ita da saƙo aka bata yasan zata fahimce su in aka nuna mata tunda ya riga ya fara anan har ya shiga shekara ta biyu a barshi ya ƙarasa, Gwaggo da kanta taje wurin Hajiyar cikin fahimta tayi mata bayanin da Amadun yayi tace itama saida tayi tunanin hakan to amman tunda saƙo ne aka bata shiyasa ta isar, kamar yadda sukai da Gwaggon haka Hajiya ta sanar ma Hajiya Maryam hakan yasa ta fara tabbatar da su bama su Kwaɗayi bane sanin da wuya ai ma wani tayin karatu a ƙasar waje amman ya maida, Soyayya sosae su Farhar suke sha ita da Kamalu don sun samu yanci daga baya ta fara shirye shiryen fara cigaba da karatunta.

Bayan sabuwar Gwamnati ta fara ayyuka sosae Haisam ya tuntubi Alhaji lawal kan buƙatar ayi ma garin su Fatuu hanya a kuma gyara masu wutar lantarki kasantuwar shine ɗan majalissarsu na tarayya ya bashi tabbacin za'ayi masu, tuni aikin ginin Kamfanin Haisam wanda ƙwararran kuma sanannen Companyn gini anan Abujar keyi ya kankama, a yadda aka tsara zuwa nan da shekara guda za'a gama, tuni Al'umma sun fara sheda cewa sabuwar Gwamnati data hau ta aiki ce don kuwa anfara gudanar da ayyuka gadan gadan a faɗin ƙasa bayan hawan ta mulki ciki harda shirye shiryen da zasu tallafa ma talaka ya dogara da kan shi da yake ba laifi mai girma shugaban ƙasa ya samu abokan tafiya da shawara na ƙwarae masu tausayin talakawa, Kawu Mani har Abuja ya fara zuwa da Gwaggo acan ya samu inda ya kaita aka fara koya mata turanci don ta iya karatu, kan kace mi Gwaggo ta canza ta ƙara murmurewa duk alamun tsofanta daya bayyana yanzu babu sosae farinta ya ƙara fitowa tayi dumurmur abunta dama gata doguwar mace abun dai saidai ace tubarkallah, a bangaren First Lady kuwa wato Mahaifiyar su Haisam abun ba'a magana yanzu jin daɗi ya ninninku ta ƙara wani irin kyau Jama'a kowa yabon kyaunta da kuma kirkinta ake don mace ce mai sauƙin kai wadda kowa nata ne mutane har so suke a nunota tana jawabi don ta iya magana ba ƙaɗan ba, a yadda mutane keta faɗa ba'a ta6a First Lady kamarta ba wadda ta ko ina tayi, su Fatuu da Mino ana can America Mino ta maida hankali tanata karatu haka Nameer ma.

Lokacin da za'ayi bikin cikar President shekara ɗaya a kan kujerar mulki aka shirya buɗe Companyn Haisam, da lokacin Hajji yayi gaba ɗayansu suka je harda shi shugaban ƙasan da Hajiya dasu Mom suma su Fatuu da Mino da Fanan da Haisam da Nameer nan Nigeria suka zo suka tafi tare harda Aunty Laila da Mijinta harda Jidderh ma duk wanda suka isa aikin Hajji a Familyn shugaban ƙasan saida suka je haka bangaren Minister Hajiya Maryam taje ita da Mijinta da Farha, sosae sukai ma shugaban ƙasa Addu'oi kan Allah ya tallafa mashi ya taya shi sauke nauyin dake kan shi kamar yadda ya roƙesu kan suyi mashi Addu'oin, Haisam ma sunyi mashi Addu'oin Allah yasa ya buɗe Companyn shi a sa'a, bayan gama aikin Hajjin suka dawo gida Nigeria, abun na Allah ne su Fatuu an zama Hajiya harda haƙorin Makka tasa haka ma Mino kuma sosae yay masu kyau, bayan dawowar su sun ɗan zauna a Nigeria Haisam ya duba ginin nashi wanda tuni yayi nisa lokacin Fatuu da Mino suka tafi Katsina Hajiya dai President ya ruƙeta kan sai ta ƙara hutawa sosae ita Hajiya Maryam ma cewa tayi kada ta koma Katsina ta dawo nan da zama kawai shima President ɗin dasu Mom suka nuna goyon bayan hakan Hajiyar ta nuna tafi son zama a can don ta saba da mutane kuma bai kamata ace duk sun baro can ba tunda nan ne tushen su, bayan zuwan su Fatuu Katsina har gidan Aunty Mareeya da Feenah taje ta kai masu tsaraba harda Abdul ɗan gidanta shima yasha tsaraba haka Aminiyarta ma Haulat tayo mata tsaraba kullum tana a gidan Gwaggo anan ma take kwana tunda shi Haisam na Abuja, bayan sati biyu suka koma America, bayan komawarsu ne Haisam yaba Fatuu da Fanan damar za6a ma Companyn suna yace yana son duk sunayen su ya fito a ciki nan suka shiga haɗa sunaye ita Fatuu tace ko asa HAIFAN ita kuma Fanan tace HAIFAT zai fi, ƙarshe dai HAIFAT TechWorld aka yanke saka ma Companyn.

A kwana a tashi ba wuya har gashi shekara guda da hawan su President Ali Washegarin da akayi bikin murnar cika shekarar aka buɗe katafaren Companyn Haisam wato HAIFAT TechWorld, Kamfani ne da zai rinƙa ƙera kwanfutoci da saida bangarorinta da building softwares products da kuma Internet services daban daban da Online Services tare da kuma Consulting Services, sosae ginin kamfanin ya ƙeru yana da bangarori daban daban harda elevator ke akwae da zai kai mutum can sama abun sai dai ace Ma sha Allah, Mutane da dama ne suka halarci bikin buɗe shi ciki harda Mahaifin Haisam ɗin da manyan ƙososhin Gwamnati harda na wasu ƙasashen makwabta sannan ta bangaren danginsu kowa yazo har su Gwaggo harda Baffan Fatuu da Yadikko haka yan uwansu yan Ethiopia su Hajiya Zainab da Sameer harda Fauzy tare da twins ɗinsu da suka girma abun sai dai ace tubarkallah, abokan aikin Haisam ma turawa duk sun zo ciki harda waɗanda ya ɗauka zasu yi aiki tare gaba ɗaya duk wani masoyin Haisam da Abokan shi suna a wurin harda su Abbas da Najeeb da Saleem, ba ƙaramin mutane aka haɗa ba kowa yayi shiga ta alfarma kar ma su Mom suji su Fatuu ma ansha rantsattsan leshi iri ɗaya ita da Fanan wuya da hannu sun sha danƙararrun gold Haisam ma yasha bugaggun fararen suit sai necktie baƙi haka ƙafafunshi na sanye da dakakkun baƙaƙen cover suma abokan aikin nashi duk suit ne a jikinsu, yaran su gwanin burgewa duk sun girma su Twins yanzu shekararsu ukku da watanni amman sai kace sun fi hakan don suna da tsawo da kuma kauri suma suna sanye da suit na yara Esha kuma shekarunta biyu itama tana sanye da ƙananun kaya riga da wando an raba mata baƙar sumarta biyu ta saukko har ta wuce kafaɗarta kunnanta na sanye da barimar diamond da yan hannu ba ƙaramin kyau yaran sukai ba duk wanda ya kallesu sai ya ƙara yan jarida duk sun zagaye wurin suna ta aikin ɗaukar rahoto, bayan jin bayanai da suka danganci sabon kamfanin daga bakunan wasu masu ruwa da tsaki a kamfanin ciki harda Chief Executive Officer (CEO) wato Haisam da Mr President da wasu turawa a tare Haisam ɗin da Fatuu da Fanan suka yanka ribbon ɗin da aka zagaye ƙopar shiga cikin kamfanin mutane suka sa tafi ji kake "raf...raf...raf...) wasu suka shiga faɗin "Behind every Sucessiful Man there is woman or women" duk akasa dariya kafin akai bismillah suka sa kai, ginin bene ne hawa ukku akwae Ofisoshi daban daban da bangarorin gudanar da aikin kamfanin ko ina an zuba nagartattun furniture da suka dace da wurin wani abun ma sai Office ɗin Haisam wata daula ce guda akwae kuma ɗakin taro wanda aka sa haɗaɗɗan zunguren tebur aka kewaye shi da kujeru mahaɗin shi, haka akai ta zagayawa wurare ana ɗaukar hotuna da Vedios Mutane sai yabo

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login