Showing 24001 words to 27000 words out of 512766 words

Chapter 9 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1544

suna zaune aka fara kiran sallar la'asar, bin shi tay da ido har ya kusa kai bakin kopar ta ga ya d'aga hannunshi na dama ya had'e yatsunshi biyu suka d'an yi sauti nan take ta gane mi hakan ke nufi wato yasan kallon shi take, murmushi tay ta jingina da kujera komae na shi mai burgewa ne Allah ne shaidar ta tana tsananin son shi saidae ba yadda zatai k'addara ta riga fata, ganin zuciyarta na kokarin maida ta ruwa don har k'walla sun fara taran mata a idanu yasa tay saurin kawar da tunanin ta yunk'ura ta mik'e itama, d'akin Saude ta nufa lokacin data shiga Sauden ta fito daga toilet da alamu Alwala tayi tana ganinta ta washe baki tace "Fateema yan Makaranta an dawo" itama murmushi take mata tace "Eh Aunty Saude kin dawo lafiya" ta amsa mata da lafiya lou Fatun tace mata zata yi salla ne ta amsa da to ta nufi Toilet, bayan tayo Alwalar a kusa da Sauden ta shimfid'a abun salla ta kabbara, saida suka gama sannan Saude tayi mata Maganar Aurenta da aka fasa tace d'azun da gwaggo ta shigo take fad'a masu taji mata dad'i Allah yasa haka yafi zama Alkhairi Fatuu ta amsa da Amin can wayarta ta fara ringing ta kai hannu gefen Katifa ta d'aukko sunan Ya Haisam ta gani hakan yasa ba tay picking ba ta yunk'ura tay ma Saude Sallama ta fice,

Zaune a Dining area ta hango shi ta nufi can yana ta lallatsa wayar shi ganin haka yasa ta fara k'ok'arin serving nashi ta tambaye shi mi zai ci yace mata abunda ya kamata d'an murmushi kawae tay ta fara zuba mashi gaba d'aya sanyayyan k'amshin da jikinta ke saki ya cika mashi hanci saidae bazaka ta6a gane yanayin shi ba lokacin idon shi na akan wayar hannun shi baya ta gama ne tace "Ya Haisam bismilla" Slowly ya d'ago ya kalli Abincin da ta zuba mashi shak'e da plate kafin ya d'aga idon ya kalleta ta nufi d'ayan bangaren ta zauna opposite dashi ganin kallon da yake mata ta kuma san dalili yasa ta yin yar dariya tace "ai nasan yanzu kana cin Abinci sosae shiyasa na zuba maka haka" d'an murmushin da iyakar shi lips d'inshi yay kafin yace "Who told u?" tura baki tay tace "Ba kayi aure ba" wani kalan kallo yake mata har saida tasha jinin jikinta a d'an rud'e tace "dama na ta6a ji Ya Abbas yace in kayi aure zaka rink'a cin Abinci hannu baka hannu kwarya lokacin daka fara kaini gidan shiyasa nace haka" ta k'arasa had'i da sunnar da kai still kallonta yake ya kuma tuna da lokacin da Abbas d'in yay Maganar kusan 4yrs yanzu amman bata manta ba, hannu ya kai ya d'auki spoon ya fara cin Abincin a nutse itama ta fara kokarin zubawa saidae kaman rabin nashi ta zuba tana yi tana satar kallonshi yay kaman bai ganin mi take yi, tana fara ci ya dakata yace "how can u eat comfortably da wannan" yay Maganar yana mata nuni da kan shi ta gane Hijab d'in jikinta yake nufi hakan yasa ta kai hannu ta cire ta dama yar k'arama ce saidae kuma kanta ba kallabi sai tulin gashita dake fake ganin bai kamata ta zauna ba kallabi ba kuma ana cin Abinci yasa ta ninka Hijab din tay irin d'aurin ture kaga tsiyar nan taci gaba da cin Abincin, wohoho maza masu abun ban mamaki wai kuma sai yadda d'aurin yay mata yay mashi kyau ba kamar yadda tulin gashin ya fito waje ko don matarshi ba irin gashin gareta ba kuma ita ta saba sakin shi oho dae shi yasan dalili, duk in ta d'ago sai sun had'a ido yana kallonta sai ta d'an mashi murmushi abun mamaki saiga Haisam ya take Abinci ba tare daya ankare ba abun shima ya matuk'ar bashi mamaki Fatuu kuwa ta hau yi mashi dariya tana fad'in ashe Ya Abbas da gaske yake saidae kawae yay mata murmushi, kusan a tare suka gama Fatuu ta kwashe kayan da sukayi amfani dasu takai kitchen saida ta wanke su sannan ta fito ta maida hijab d'inta lokacin shi har ya koma cikin parlon hakan yasa ta nufi can tana zuwa a gefen shi ta tsaya tace zata wuce gida d'an shiru yay yana kallonta sai kuma ya mik'e yace suje zai bata abu yay gaba tabi bayan shi, hanyar part d'in shi ya nufa hakan yasa tabi shi lokacin da ta shiga Falon har bata san sadda ta saki murmushi ba bata yi zaton zata k'ara shigowa cikin shi ba duk da tasan dama dole zai rink'a zuwa to amman a tunanin ta zai rink'a zuwa da Matar shine, ce mata yay ta zauna shi kuma ya nufi hanyar Bedroom ta ci gaba da k'are ma parlon kallo tamkar yau ta fara shigowa kuma yana nan yadda yake ba abunda ya canza sai gyara da yasha k'amshi na tashi, bayan wani lokaci ya fito hannun shi ruke da abu da bata gane ko minene ba a gefenta ya ajiye sai lokacin ta gane sabuwar Laptop ce ya koma daga can gefe ya zauna ganin ta bishi da ido yasa a hankali yace tata ce tayi amfani da ita d'an waro ido tay sai kuma tay murmushi tace mashi ta gode Allah ya saka da Alkhairi ya k'ara bud'i ya jinjina mata kai can kuma sai ta d'an kwa6e fuska ganin haka yace "What?" A shagwa6e tace "ban wani iya amfani da ita ba" still yay yana kallonta kafin yace a Secondary school ba'a koya masu ba ne tace "an koya mana amman ai duk theory ake duka bai fi sau a k'irga ba aka kaimu Lab yin practical kuma mudae in munje game d'in jirgi dana had'a bangarorin jikin mutum muke" yadda tay Maganar sai kace wata k'aramar yarinya yasa shi yin dariya batare da ya shirya ba ta zuba mashi ido tana kallon tsantsar kyau bayan ya dakata ya d'age mata gira yace "shikenan ai sai kici gaba da game d'in jirgin" tura mashi baki tay tana yamutsa fuska ganin haka yasa shi mik'a dogon yatsan shi ta kalli tissue box d'in da yake nuna mata sai kuma ta kalleshi cikin rashin fahimta yace mata in ta fara kuka sai ta yaga ta goge tunda kuka bai mata wuya sai lokacin ta fahimci abunda yake nufi tay dariya sigh yay yace taje da daddare zai zo ya koya mata abunda ya kamata tace to ta d'auki laptop d'in had'i da mik'ewa tace mashi sai anjima ya jinjina mata kai kawae ta nufi hanyar fita, bayan ta fice d'age kan shi yay yayin da a ranshi ya fara tunanin wani abu da shi kadae yasan minene, ya dan d'auki lokaci a haka kafin ya yunk'ura ya mik'e duk jin jikinshi yake wani iri hakan yasa shi yin tunanin tafiya Gym ya nufi Bedroom don ya shirya. Cike da farinciki Fatuu take nuna ma gwaggo Laptop d'in itama sai washe baki take tana saka Albarka kamar yasan Fatun dama ta fara Maganar siyan computer d'in har tambayarta gwaggo tayi ko ita tace ma shi tana buk'atar ta ne da sauri tace mata a'a wllh da kan shi ya kawo mata tace yayi kyau bata son ta rink'a tambayarshi abu ta bari sai in shi ya tambayeta sannan Fatun tace mata to dama ita bata hakan kokarin tashi ta fara yi don taje tayi wanka, bayan ta gama ta shiryawa da doguwar riga mai gajeran hannu gwaggo ta shigo cikin d'akin Fatuu ta kalleta da murmushi ta nufi bakin gado ta zauna itama Fatuu zama tay gwaggon tace har ta gama shiryawa tace eh, shiru ta d'an yi sai kuma tace "da nace wai tunda Abinci tazarce muka yi ko za'a had'a mashi wani abu maras nauyi haka?" Fatuu dake kallonta tace "wai Ya Haisam" tace "Eh ba kince zai zo koya maki Computer d'in ba?" d'aga kai tay tace "Eh haka yace, to mi za'a had'a?" d'an shiru gwaggo tay alamar tunani kafin tace "ko ayi mashi fatan dankalin turawa yaji Alaiyahu" Fatuu tace "eh kuma kinga ba Abinci bane mai nauyi dama asa harda kifi" yar dariya gwaggo tay tace to bari sai a siyo gasasshen kifi tarwad'a ayi amfani dashi ta tambayeta da ta wuto shagon Amadu yana ciki tace mata a'a a rufe yake tace to bari ta kira taji k'ilan ma kasuwa ya wuce daga Makaranta in yana can ma sai ya siyo komae daga haka ta mik'e ta nufi hanyar fita, bayan ta koma d'aki ta kira Amadun cikin sa'a kuwa yace mata yana kasuwa taji dad'in haka nan ta bashi saftun duk abunda take so, gab da Magrib Amadu ya dawo ya siyo komai Gwaggo ta kira Fatuu tazo ta fara feraye dankalin ita kuma gwaggo ta fara gyara kifin zuwa bayan Magrib sun kammala komae gwaggo tace ma Fatuu sai taje tayi wanka kada taje wurin mutane tana k'arnin kifi duk da ba ita ta gyara ba amman yana iya kama mata jiki tace to, tana fitowa daga wanka tayi Alwala bayan ta shiga d'aki ta tsaya gaban wardrobe tana tunanin kayan da zata saka can ta fiddo wasu light blue riga da skirt yan kanti kayan na da d'an k'auri amman roba ne ta saka sun mata kyau sosae shape d'inta ya fita har ba'a Magana tasa bak'ar hula a kanta bayan ta gama ta kabbara sallar isha, ana gama salla sai gashi yazo lokacin itama Fatuu bata dad'e da gamawa ba ta jiyo cool voice d'in shi yana sallama mik'ewa tay tasa hannu ta cire hijabin ta aje bakin gado sannan ta fito lokacin yana tsaye gefen Parlor jikin shi sanye da k'ananan kaya da murmushi ta isa gabanshi shima ya d'an yi mata tace ya shigo mana tay gaba ya bi bayanta, a saman 3 seater ya zauna tana tsaye sai kuma ta juya ta nufi Freezer don d'aukko mashi lemu da ruwa yabi bayanta da kallo har ta bud'e ta d'aukko yana ganin zata juyo ya kauda idon shi kanshi baisan miyasa yake yawan kallonta ba abunda ba halinshi bane, a saman Carpet ta ajiye su ta bud'e Coke d'in ta tsiyaya mashi a cikin glass cup kafin ta mik'e still da murmushin ta d'an rankwafa tana mik'a mashi yana kokarin kallonta idanunshi suka sauka akan saman boobs d'inta da suka d'an bayyana sakamakon duk'awar da tay da sauri ya kawar da idanun shi had'i da amsar cup d'in ya furta thanks ta koma gefe ta zauna kan kujera one seater kamar sau ukku yay sipping ya ajiye bayan ya d'ago suka had'a ido Calmly yace "go and bring d Laptop" tace to ta mik'e still dae kallon yabi ta da shi har ta fita, tana fita gwaggo ta shigo da fara'a ta zauna suka shiga gaisawa ta k'ara mashi ya gajiya don d'azun sun gaisa da taje gidan, godiyar Laptop tay mashi yace ba wani abu ta k'ara mashi godiya da Addu'oi yana amsawa a hankali daga baya ta mik'e ta fita Fatuu ta shigo ta mik'a mashi ya amsa ya gyara zama yana kokarin bud'e ta ita kuma ta sake juyawa ta fita, kayan Abincin taje ta kawo ta tambaye shi ta zuba mashi yanzu ya d'an d'aga mata hannu alamar a'a idon shi akan Screen hakan yasa ta mik'e tana kokarin komawa inda ta tashi ta zauna ya dakatar da ita ta hanyar nuna mata gefen shi alamar ta zauna nan bayan ta zaunan ganin ya d'aura laptop d'in akan laps d'in shi yasa tace ko ta daukko d'an table ya d'aga mata kai alamar eh, bada jimawa ba ta dawo ta aje a gabanshi ya d'aura laptop d'in a sama daga haka ya fara nuna mata abubuwan da yakamata ta iya dama duk ya tura mata Apps ba laifi kuma tana catching yafi koya mata Ms-Word inda zatayi typing duk in yayi abu sai itama tayi abunda yafi bata wahala in tazo yin highlighting dasu dragging sai ya rik'a kubce mata dama sun fi sauk'i yi inda mouse ne tana cikin yi taji ya kawo hannunshi ya kama hannun nata da sauri ta d'an kalleshi ganin bai ko kalleta ba yasa ta maida idon kan screen d'in yana ruk'e da hannun ya rink'a koya mata tun tana jin wani iri hardae ta saki jiki saidae gaba d'aya kamshin jikinshi wani irin narkar mata da zuciya yake sakamakon kusancin da suke dashi a zaunen,sosae ta koyi abubuwa harda yadda zata tura abu a turo mata da yarda in kamar zasu yi online class da dae sauransu lokacin da suka gama kusan goma saura ganin yana niyyar ta shi yasa a shagwabe tace to Abincin fa still yay yana bin ta da kallo kafin yace bai son Abinci mai nauyi da daddare da sauri ta sauka ta fara bud'ewa tana fad'in ai tasani ya gani ba mai nauyi bane light food ne wani irin daddad'an kamshi ne ya buge parlon ganin baice komai ba yasa kawae ta fara zuba mashi kaman d'azun ta shak'e mashi plate tana yi tana kallon shi tana yar dariya ganin tana kokarin d'aura mashi saman table d'in ya dakatar da ita yace zai ci a kan carpet ta aje a nutse ya sauko ya mik'ar da k'afaffun shi ta yadda Abincin ke a gefen shi ya kalleta yace ta d'aukko wani spoon d'in tace to bayan ta dawo ta mik'a mashi da kai yay mata alamar ta ci ta langa6ar da kai tana fad'in nashi ne ai bin ta yay da wani irin kallo hakan yasa ta matsa gaban Abincin suka fara ci a nutse, sosae Abincin yay ma Haisam dad'i can sun yi nisa Fatuu ta d'ago da d'an murmushi suka had'a ido ta d'age mashi gira tace "da dad'i?" murmushin gefen baki yay bai ce komae ba, ba laifi sosae suka ci Abincin don har k'ara masu Fatuu tay saida suka gama ya kalleta cikin ido yace "Yayi dad'i da yake bake kika yi ba" waro ido tay sai kuma ta fara rantsuwar ita tayi abu kad'an gwaggo tayi still yay yana ta kallonta fuskar shi a sake sai faman rantsuwa take a shagwa6e tana fad'in ai shima dae yasan ta iya girki ko can Calmly ya furta "Ok kin yi kokari" tace ta gode sannan ta mik'e ta kwashe kayan ta kai kitchen, lokacin da ta dawo har ya mik'e zai tafi ta tsaya gabanshi suna Facing juna tace tafiya zai yi ya d'aga mata kai tace suje to ta raka shi ta fara K'ok'arin juyawa kawae sai taji ya kamo hannunta cak ta tsaya ta zaro ido kafin slowly ta juyo still yana ruk'e da hannun suka zuba ma juna ido kan Fatuu ya gama d'aurewa gaba d'aya ganin shi take tamkar bashi ba Saboda bak'in abubuwan da yake mata wanda ko ada can da bai da aure bai mata hakan ya lura da irin kallon da take mashi hakan yasa a hankali ya saki hannun kafin Slowly ya furta "It's already late ba sai kin raka ni ba" tamkar yar k'adangaruwa ta jinjina mashi kai kawai don gaba d'aya jin ta take wani iri don kallon da yake mata bai saba yi mata shi ba, kokarin bi ta gefenta ya fara da sauri taja gefe tana ci gaba da kallon shi har ya fice .............


Mun gama Sabon salo da An yanka ta tashi yanzu mun shiga WASA FARIN GIRKI😂




_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2036*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*






.........Sosae Fatuu ta dage da karatu ita da Fauzy don seat d'in su guda a hankali suka zama abokai sosae duk da ita Fatun Day take yi tare suke yin break wani lokacin daga gida tana kai mata abubuwan ci, Bayan wata ukku sukayi jarabawar pre intro wadda daga ita bayan wasu wata ukun zasu yi intro exam d'in wadda itace yar bala'en wadda kowa ke tsoro don mutane sosae ake zubar wa, cikin Nasara ita da Fauzy sun ci pre intro din wad'anda basu ci ba kuma aka rink'a karfafa masu guiwa don su dage kafin ai d'ayar. A bangaren Khalid yana can yana fama da ciwon so don tun bayan da aka fasa Auran su Allah ya jarabe shi da tsananin son Fatuu gashi yasan ya rasata kenan har Abada don mahaifin shi kaifi dayane kuma ita kanta Fatun ta rufe duk wata kafa da zai samu yin Magana da ita gaba d'aya ya zama salihin k'arfi da yaji ga Dad d'in shi bai kula shi sosae bai dae yi fushi da shi ba amman bai shiga har kar shi Mom ce kawae ke kula shi ta damu sosae da halin da yake ciki haka Sadeeya ma da tuni ta koma school tana yawan kiran shi don jin yadda yake da kuma k'arfafa mashi gwuiwa kan ya daina damuwa, har Abokan aikin shi wasu sun fahimci yana cikin damuwa, Ciwon so ba dad'i Khalid ma an d'and'ana Allah ya bada lafiya.

Zaune suke a cikin d'akin su na Hostel da yake Saboda jarabawar dake gaban su yasa Fatuu ta dawo cikin Makarantar kamar yadda sukae da gwaggo don itama tasan had'arin dake tattare da ita shiyasa ta barta ta dawo don yin karatu sosae duk ranar Monday in tazo sai juma'a da an tashi take komawa gida, gado biyu ne acikin d'akin nasu d'aya a 6angare dama d'aya kuma a hagu, d'akin baida girma sosae sun gyara shi komae tsab, Fatuu na zaune saman gadon dake hagu tana facing Fauzy dake zaune a saman na dama kowannen su ruk'e da littafi suna karatu akai akai suke tambayar juna abu, can bayan wani lokaci Fatuu ta d'ago da niyyar yi mata magana sai taga ta kife fuskarta akan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login