Showing 195001 words to 198000 words out of 512766 words

Chapter 66 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1615

gari Lahadi da Yamma Senator ya koma Abuja bayan ya k'ara zuwa wurin Hajiya sun tattauna game da Auran tace mashi yay k'ok'arin fahimtar da matan shi yace in sha Allah, anan ya iske Fatuu suka k'ara gaisawa har yana tambayar ta in tana son wani abu tana murmushi tace ba abunda take so yace mata ta dage da karatu, da daddare bayan sun gama cin Abinci ya buk'aci ganin matan nashi a part d'in shi, bayan sun zo a nutse ya fara masu bayanin dalilin kiran nasu da Hajiya tay, gaba d'ayan su sun ji Al'ajabin Maganar ba ma kamar Mahaifiyar Haisam d'in, bazaka gane yadda ta d'auki Al'amarin ba daga yanayin Fuskarta ta tambaye shi mi Hajiya Maryam tace game da hakan, bai 6oye mata komai ba game da yadda ta ji zafin abun dama abunda tay tunani kenan a cikin ranta dole tasan baza su ji dad'in abun ba, ba kamar da taji yarinyar har ta samu ciki, jin tayi shiru yasa shi ce mata bata ce komai ba ta d'an watsa hannu tace to ita mi zata ce kawai dae Haisam bai kyauta ba ya zaiyi abu irin wannan ba tare da neman shawara ba tun farko gashi yanzu rayuka na neman 6aci na Hajiya Maryam aka gani ina ga ita Fanan d'in, nunawa tayi ita tana ganin gara a raba su kawae zai fi da azo asamu rashin Fahimta,

Aunty tace "Gaskiya ni ina ganin in aka ce a raba su ba'ai ma Yarinyar Adalci ba kaman yadda Hajiya tace tunda shi ya fara sanin ta yanzu in aka raba auren dole sunanta zai canza zuwa bazawara, kuma ni ina ganin yana son ta ne shiyasa tun farko ma ya auretan ko kuma daga baya ya fara sonta shiyasa har abu ya shiga tsakanin su, haka da bai son ta sai inga kaman bazai yarda yaci gaba da zama da ita ba" d'an jimm Mom d'in shi tay alamar tunani kafin tace "zai iya auren ta don ya taimaka mata kawae and zai iya cigaba da zama da ita tunda Hajiya na son hakan koda bai son ta" gyad'a kai Aunty tay "hakane, nasan halin shi sarae zai iya kasancewa hakan, amman dai kamar yadda Hajiya tace ina ganin muyi masu Fatan Alkhairi kawae don ni ina ganin dama can Allah ya k'addaro matar shi ce shiyasa ma har suka san juna" jinjina kai Senator yayi Mom d'in Haisam da yanayin fuskar ta ya sauya tace basu ganin Hajiya Maryam zata ga suna supporting d'in shi Saboda d'an su ne basu damu da halin da Fanan zata iya shiga ba, Senator ne yace to tunda Hajiya haka take so ai dole su bi abunda take son sannan yasan damuwarta Saboda tunanin halin da Fanan zata shiga ne idan Allah yasa bata tashi hankalin ta kamar yadda take tunani ba yana ganin komai zai daidaita, cigaba da tattaunawa sukai daga baya suka bar part d'in nashi,

Bayan Mahaifiyar Haisam ta koma Bedroom d'in ta, a gefen tanfatsetsen gadon ta daya sha k'ayataccen bedsheet ta zauna tay shiru tana kallon wuri guda da alama zurfin tunani ta shiga, sam ta kasa gane mi take ji game da Al'amarin, wayarta ta d'ago ta fara k'ok'arin kiran Haisam, bayan ta fara ringing ya d'aga suka gaisa tace mashi taji abunda ya aikata ba tare da sanin su ba batare da kuma yayi zurfin tunani ba mi zai sa yayi Aure da sunan taimako bazai yi amfani da wata hanyar ba, hak'uri itama ya bata tace tunda yaje yayi gaban kan shi ai dole suyi hak'uri amman yasan yadda zai yi ya fad'i ma Fanan ba tare da ta tada hankalin ta ba yace zai yi hakan in sha Allah cikin nuna k'auna yay mata Sallama tace Uhmm kawai, bayan sun gama wayar d'an jimm tayi sai kuma ta fara k'ara yin kira, Jidderh ta kirawo tace tazo d'akinta tana son ganinta, after few minutes ta shigo tana sanye da doguwar riga kanta ba kallabi sai bak'ar sumar ta wuluk da ta faka hannunta ruk'e da wayarta ta nufo gefen gadon ta zauna tace gata,

"Akwai wani yarinya Neighbor d'in Hajiya I can't remember her name amman sun saba da Hajiya sosae...." Katseta Jidderh tay da fad'in "Sis Fatuu?" d'an d'age ido tay alamar tunani tace ta dai manta sunan k'ilan itace da sauri Jidderh tace bari ta nuna mata picture d'in ta ta gani in itace, shiga cikin gallery d'in wayarta tayi ta bud'o hoton Fatuu ta nuna mata tana gani ta shaida Fuskarta tace mata itace, tambayar ta Jidderh tayi miya faru da ita da d'an alamun rudu Mom d'in nasu tay d'an guntun murmushi tace ba komai she just wants know about her, cikin rashin fahimta Jidderh tace mi take son sani game da itan, tana d'an yarfa hannu tace kaman ya halayyarta take da mu'amalarta da Mutane haka, Murmushi Jidderh tayi harda gyara zama don tana bala'en k'aunar Fatuu nan ta shiga fad'i mata halayenta tace tana da kirki sosae ga faran faran ga son mutane gashi tana da dad'in zama bata da wuyar sabo kuma daka zauna da ita sai kaji ta burge ka, nan ta fad'i mata farkon saninta da ita lokacin data dawo daga Yola tazo gidan Hajiya da kayan Fulani har hoton da suka yi ranar ta bud'o mata da tasa Haisam ya turo mata don ta rasa shi, labarin tsakaninta da Ya Haisam abunda ta sani da wanda Hajiya ta basu labari ta shiga bata, tace mata yanzu haka suna gaisawa don ta zama kamar k'awarta ma, tambayar ta tayi zasu yi shekaru d'aya tace "No na girme ta da kusan 3 years ma, kawai dai she has a good shape kinga hips d'in ta kuwa Mom wllh kyace ba nata bane in kin ganta sun yi haka..." ta mik'e tana gwada ma uwar yadda hips d'in Fatuu suke ita dai sai murmushi take, komawa Jidderh tay ta zauna tace mata wai miyasa take son sanin abubuwa game da ita ne, shiru ta d'anyi tana rolling eyes ta kalleta da murmushi tace "Now she's part of this Family" waro ido Jidderh tay baki bud'e alamar mamaki cikin daurewar kai tace bata gane ba, ce mata tay Yayan su ya Aureta cikin rashin fahimta ta d'an waro ido tace Ya Nameer, yar harara ta wurga mata tace Nameer d'in da bai a K'asar Big bro d'in su take nufi, k'ara waro idanu waje tay tana kallon Mom d'in nasu da itama take kallonta ta d'an ta6e baki da d'an murmushi, cike da Al'ajabi ta tambaye ta yadda akai ta zama Matar Ya Haisam d'in nan ta fad'i mata, aikuwa ta washe baki cike da Murna tace "Oh my God! am so Happy to hear that Mom, wllh na dad'e ina masu sha'awar auran juna don sun dace sosae ba K'aramin fahimtar juna zasu samu ba, kaman fa shi ya raine ta Mom, bai son 6acin ranta bata son 6acin ran shi itama, sosae jinin su ya had'u baki ga yanda suke kulawa da juna ba, tun bayan dana santa dashi naga sun bala'en yin matching saidae kuma nasan ba zai aureta ba Saboda Maganar auren su da Aunty Fanan kuma lokacin tayi k'arama ma, daga bayan nan data girma inta ji inama suyi aure, ashe da rabon zasu yi d'in" cike da Farinciki take Maganar sai faman washe baki take, d'an d'aure Fuska Mom d'in tayi tace ai raba Auran za'ai nan da nan murnarta ta koma ciki tay mata wani kallo kaman zatai kuka tace "but why Mom, Don Allah kar a raba su" d'an ta6e baki tay tace Auren na son kawo rashin fahimta don Momy d'in su ta Lagos ta d'auki zafi sosae sannan Fanan ma tasan in taji za'a iya samun matsala, Fuska a yamutse Jidderh tace ai dama dole hakan ya faru Saboda kishi amman daga baya tasan komai zai daidaita zasu yi hak'uri ita dae don Allah kar su raba Auran, yar harararta Mom d'in tayi tace da yake ba ita akai ma kishiyar ba a shagwa6e ta kama hannun Momyn tana mata Magiya, ganin tana murmushi yasa ta gane wasa take cike da zumud'i tace bari ta kira mata Fatun su gaisa, har ta d'ago wayar ta dakatar da ita tace ba yanzu ba ta bari aga komai ya daidaita itama kar ta fad'i ma kowa cikin yan uwanta tace to, ce mata tay zata iya tafiya ta mik'e tana fad'in zatai ta yin Addu'a Allah yasa komai ya daidaita da wuri su sha shagali don duk abunda akai a bikin Aunty Fanan itama sai anyi Momyn tace Uhmm kawai ta nufi kopar fita tana ta murna ta fice.............




_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:29] +234 901 700 4868: * ASM 071*


~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~



*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*



.........A nutse ta fara karanta sak'on wanda ke bayyana sirrin zuciyar wadda ta turo wato Zarah, bayanin tun lokacin da Allah ya jarabeta da son shi da irin wahalar da ta sha hakane ma yasa ta amince ai mata Aure Saboda ta rasa shi har Allah ya juya Al'amarin ya aureta, Hak'uri ta bashi kan zargin shi da tayi ta nuna bata san akwai Aure ba a tsakanin su kuma Saboda son da take mashi ne yasa taji zafin abun sosae hakane ma yasa data samu ciki tak'i saurarar shi harta 6arar don kuma bata son girman shi ya zube a idon mutane duk don k'aunar shi da take, a k'arshe ta nuna mashi tana cikin mawuyacin hali Saboda canza mata da yayi a yanzu da burinta ya cika ta zama Matar shi, Hak'uri ta k'ara bashi tace in don cikin da ta 6arar ne yake nuna mata halin ko in kula in sha Allah zata biya shi fin shi ma amman tana a cikin matsananciyar damuwa da har tana son shafar karatun ta........., Tun Fanan na karantawa lafiya lau har ta kai yanayin Fuskar ta ya fara sauyawa, lokacin data gama karantawa d'agowa tay da yanayin d'aurewar kai ta kallo hanyar Kitchen da Haisam ke ciki, k'ara maida idonta tayi akan Screen d'in tana sake biya sak'on lokaci guda hannuwanta suka fara yin kerma ta zuro da fararen k'afafuwan ta k'asa, Slowly ta mik'e har lokacin tana cikin k'ara karanta sak'on, saida ta karanta shi sau ukku tamkar mai yin hadda, gaba d'aya ta kasa gasgata abunda take karantawa gani take kamar ba daidai take karatun ba ko kuma ba sak'on Haisam d'in bane hakan yasa sai k'ara maida idonta take tana k'ara karantawa, zuciyar ta ce ta shiga gasgata mata sak'on shi ne in ba haka ba mizai sa ta turo mashi kuma ga alamu nan a bayyane har sunanta an ambata a ciki kan ciwon da ta yi lokacin da Fanan d'in tazo......."Kenan Auran Zarah ya yi a 6oye???" ta fad'a acikin ran ta, wani irin bugu zuciyarta ta shiga yi mata ta fara numfashi da k'arfi har saida ta d'an bud'e baki jin numfashin na neman yi mata wuyar fitarwa, tana haka Haisam ya shigo cikin parlon yana sanye da wando 3 quarter da armless hannuwan shi duka biyun ruk'e da mug d'an tiriri na fitowa alamar abun ciki mai zafi ne, wani irin kallon tashin hankali ta shiga bin shi da shi hakan yasa shi dakatawa daga d'an gabanta yana kallon ta shima har saida gaban shi ya d'an fad'i ganin yanayinta da kuma wayar shi dake hannunta don yanayin kallon da take mashi na tuhuma ne, nufo shi tay a fujajen tana zuwa fuska a hautsine ta d'aga mashi wayar shi dake hannunta daidai kan sak'on a kid'ime tace "Don't tell me dis message is for you!!!" maida idon shi yay akan Screen d'in ya gane Zarah ce ta turo saidai bai fahimci miye akace a sak'on ba, wucewa yay yaje ya aje mugs d'in akan c-table ya juyo lokacin itama ta juyo tana kallon shi, hannu ya kai ya amshi wayar ya fara karanta message d'in a nutse har ya gama, d'agowa yay ya kalleta ta kafe shi da idanunta da ta zaro Fuskarta har ta fara yin ja alamar motsuwar jini, shiru yay kawai yana kallonta yama rasa mi zai ce mata don komai sak'on ya bayyana, girgiza kai ta shiga yi tana fitar da numfashi da k'arfi cikin d'an k'araji tace "so it's true, You married Zarah without my knowledge!" still bai ce mata komai ba aikuwa ta daka mashi tsawa a gigice tace "tell me! is she ur Wife??" d'an cize lip d'in shi yay na k'asa Slowly ya lumshe mata ido nan take ta gane mi hakan ke nufi, cikin fitar hayyaci ta fara ja da baya tana cigaba da girgiza mashi kai, bin ta ya fara yi yana ce mata "I can explain myself..." a haka har ta dangane da kujera kawai sai ta haye saman ta gudun kada ta yi ma kanta wani abu yasa shi kai hannu zai kamo ta ai kuwa ta tafi gaba d'aya ta wuntsila bayan kujerar ta fad'a saman tiles daga jin k'arar ba K'aramin bugawa tay ba, juyawa yay da sauri ya zagaya lokacin har ta mik'e tana k'ok'arin rugawa d'aki cikin zafin nama ya kamota ta fara kokowar kwacewa cikin k'araji fuskarta da idanunta sunyi jawur take fad'in "Leave me alone! Ya Haisam u'r a betrayer! u betrayed my trust, u broke the promise u have made to me! U deceived me....!" Gaba d'aya bata a cikin hayyacin ta idanunta sun jik'e da k'walla fatar k'asan idon tayi wani irin ja kamar jini, sai kiciniyar k'wace kanta take ta kansa sai rarrashinta yake yana ta tsaya zai mata bayanin yadda hakan ta faru amman ina tak'i sauraren shi fad'i take ba abunda zai fad'i mata ta san don ance tana da matsala shiyasa yayi tunanin bazata haihu ba yaje ya auri Zarah gashi nan har yayi mata ciki duk da Alk'awarin da yayi mata, abu fa ya ture gaba d'aya Fanan ta burkice mashi duk ta rud'a shi har fuskar shi ta bayyana, da dai taga ta kasa kwacewa kawae sai ta kai bakinta a jikin damtsen shi dake a bayyane ta daddage ta gartsa mashi cizo aikuwa ba Arzik'i ya saketa Saboda rad'ad'in Azabar da ya ratsa shi wurin har ya fashe nan da nan jini ya fara zubowa, ai yana sakinta ta watsa a guje hanyar Bedroom yana ganin haka shima ya bita don ya fahimci abunda take son aikatawa haka take da ranta ya 6aci sai ta ruga ta kulle kanta a cikin d'aki, ko kafin ya cimmata tuni ta shige lokacin daya kai hannu cikin zafin nama zai bud'e kopar data turo tuni har tasa Key, bugun k'opar ya fara yi da d'aga Murya yana kiran sunanta yana ta bud'e karta yi ma kanta illa, tana shiga d'akin a haukace ta nufi bango ta fara kai mashi bugu tana wani irin kuka na fitar hayyaci, har saida knuckles d'inta suka fara fitar da jini sannan ta daina ta nufi gado ta zauna dabar tana cigaba da kukan, a ranta ta fara tariyo sak'on aikuwa ta k'ara tsananta kukan ta fara sambatu tana fad'in Ya Haisam da Zarah sun ci amanarta, tunowa da Maganar ciki da ta samu tasa ta kai hannu ta fara bugun Katifar hakan bai sa ta samu sassaucin abunda take ji ba acikin zuciyarta sai ma k'ari nan fa ta mik'e ta fara wurgi da abubuwa abun har ya kai da fashe fashe, gaba d'aya hankalin Haisam ya gama tashi sai faman bugun k'opar yake da k'arfi yana kiran sunanta yana fad'in kada tayi ma kanta wani abu ta bud'e kopar, har ta kai ya fara mata Magiya ko tana jin shi ma oho ba dai alamun zata bud'e,

sintiri ya shiga yi tsakanin Window wadda itama take a kulle da kuma kopar yana tunanin Mafita, zuciyar shi ce ta bashi ya fara bugun kopar k'ilan yaci sa'a ta bud'e duk da yasan mawuyacin abu ne don dakakkar k'opa ce, ba irin bugun da bai ma kopar ba iyakar k'arfin shi amman ba alamun zata bud'e dole ya dakata don shi kan shi ya gaji, Hajiya ce ta fad'o mashi a rai a rud'e ya nufi cikin parlon inda Fanan ta jefar da wayar ya nufa ya d'auka, tana fara yin ringing Hajiyar ta d'auka ko gaida ita bai yi ba ya shiga fad'i mata abunda ke faruwa itama rud'ewa tay ta shiga tambayar shi dama bai sanar mata ba duk da tasan inda ya sanar mata zata ji kawai ta rud'e ne, ce mata yay eh ya bari yayi 2 Months da dawowa sai ya d'auki hutun da basai an rink'a biyan shi ba su taho nan Nigeria su kwana biyu lokacin sai ya sanar mata dama irin haka yake gudu shiyasa, tambayar shi tayi to yanzu ya akai ta sanin yay d'an jimm hakanan sai yaji baison fad'i mata zancen sak'on da Zarah ta turo sai yace mata kawai a Wayar shi ta gane, ce mashi tay to yayi k'ok'ari ya 6alle kopar mana yace mata ba irin k'ok'arin da bai yi ba tak'i bud'ewa, tambayar shi tayi anan ba masu aikin 6alle k'opa ne sai lokacin ya tuna da sauri yace mata ba'a rasawa tace to yay hanzari don Allah ya kira azo a bud'e kar wani abu ya sameta ta razana ne sosae ba ta haka yakamata ta sani ba.

Bai san ina zai samo wanda zai 6alle kopar ba amman da yake yana a K'asar da aka cigaba ne komai k'ank'antar sana'ar mutum zaka samu ya d'aura a internet, yana yin searching sai gashi ya samu, kiran su yay a waya ya fad'a masu aikin da yake so ayi mashi da Address d'in gidan, bayan sun gama komawa yay wurin d'akin yana cigaba da knocking wai ko zata bud'e amman shiru abunda ma ya k'ara tayar mashi da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login