Showing 492001 words to 495000 words out of 512766 words

Chapter 165 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1656

dashi ya amsa a hankali da sauri itama Esha tace "Good Evening My Daddy" wani kallo yay mata mai kaman harara ba tare daya amsa ba nan take ta gane da ita yake fushi ta shiga kikkafta idanu tana motsa baki, ba tare daya saukko daga saman kujerar ba still fuskar shi a ɗaure take ya fara magana cikin cool voice ɗinshi da har yanzu bata canza ba idon shi akan Esha yace dama duk faɗan da ake mata kan ta daina rashin ji bata ɗauka, da sauri tace mashi ta bari Allah,

"Kin bari shine kika fasa ma classmate ɗinki baki?" ya faɗa tare da ƙara ɗaure fuska ta ɗan waro ido jin abunda yace don tunda take rashin ji a School ba'a ta6a yi mata maganar ba a gida, cikin ɗan tura baki tare da yamutsa fuska tace ai itace ta karya mata colour ko, aikuwa a ɗan fusace Haisam yace miye colour da don ta karya zata kama bugunta har ta fasa mata baki kuma ai ba shine rashin ji na farko ba da take a School ɗin dama ance ta saba bugun students kan ƙaramin abu kuma wani lokacin ita take fara jan su sannan tana ma malamai rashin kunya, tana jin abunda yace ta fara ta6e baki tana ɗan nishi idanunta suka ciko da ƙwalla cikin muryar kuka ta fara faɗin Allah karya ake mata ita bata rashin ji kuma duk wanda ta buga shi ya fara jan ta kawai dai teachers ɗin nasu sun tsaneta shiyasa za'a yi mata sharri, shiru Haisam yayi yana kallonta kawai don komai take yi ƙuruciyar Fatuu take tuna mashi yasan gaba ɗaya halinta ne na yarinta ta gado shiyasa bai cika damuwa da rashin jin ta ba don yasan zata daina, sai faman rantse rantse take tana faɗin karya malaman ke mata Haisam ɗin dai bai ce mata komai ba idon shi na kanta, yadda take faɗin malaman su ƙarya suke mata sun tsaneta sai ta tuna mashi da can baya lokacin ƙuruciyar Fatuu ta ta6a faɗi mashi magana makamanciyar wannan, ba tare daya saki fuskar shi ba ya katseta ta hanyar faɗin Teachers ɗin nasu take ce ma suna ƙarya idanunta sharkaf da ƙwalla tace to ai ita bata rashin jin da aka faɗi mashi, juyawa yay ya kalli su Twins dake ta bin su da ido sai kace an aje photocopy ɗin Haisam don sak fuskar su irin tashi ce komai da komai, tambayar su yay abunda aka faɗa game da Esha ɗin gaskiya ne Abie yay shiru don shi magana wuya take mashi Adam ne yace eh gaskiya ne bata jin magana taita bugun Students kuma tana ma Teachers rashin kunya har suma da suke Yayyenta ta raina su tana masu rashin kunya kuma har bugunsu take aikuwa yana rufe baki tai kukan kura ta nufe shi, da sauri Adam ɗin yace ma Haisam ya gani ko gashi nan zata bugeshin aikuwa a fusace ya daka mata tsawa ta hanyar kiran sunanta yace in ta sake ta buge shi sai ya 6ata mata rai, wani irin kuka mai sautin gaske ta fashe dashi ta shiga faɗin ita kowa yayi hating nata shiyasa sai ai ta mata sharri, kukanta ne yasa Fanan fitowa tana sanye da wando skin tight da yar top kayan sun bi shape dinta kanta a buɗe brown sumarta ta saketa ta zubo gefe da gefen wuyanta, tana nan yadda take bata canza ba saidai hutu ya ƙara zauna ma jikinta ta ƙara wani irin fayau da ita sannan ta ɗan ƙara jiki kaɗan, da sauri ta nufo cikin parlon tana faɗin "What's Happening Sweetheart....." Esha na jin muryarta ta miƙe daga durƙuson data yi ta nufeta da gudu suna haɗuwa ta faɗa jikinta, ɗago kanta Fanan ɗin tayi ta sake tambayarta mike faruwa waya sakata kuka ne,

"Momy, they made Dad angry with me" Esha ɗin ta faɗa fuskarta jage jage da hawaye ita damuwarta fushin da Haisam yayi da ita, ɗan buɗa ido Fanan tayi tace mata su waye suka sa Dad ɗin yayi fushi da ita cikin kuka tace Teachers ɗin su kuma harda su Twins, kama hannunta tayi suka nufi inda su Haisam suke, a kusa da Haisam ɗin Fanan ta zauna da yake akan kujera mai mazaunin mutum biyu yake ta zaunar da Esha ɗin akan cinyoyinta sai kallon Haisam ɗin take tana sheshsheka shi kuma yaƙi kallon su, hannu Fanan ta kai ta kamo hannunshi tana murmushi ta furta "Babe, What happened?" shiru kaman bazai magana ba sai kuma ba tare daya kalleta ba ya shiga faɗi mata abunda aka kirashi daga School ɗin su aka fadi mashi, zaro ido Fana tayi tana kallon Esha dake yan kifce kifcen idanun rashin gaskiya,

"Sweetheart, Why? Miyasa zaki hakan duk nasihar da nike maki kan ki daina faɗa kina bugun mutane ki natsu ashe baki ji" Fanan ta faɗa da turanci ta ɗan daure fuska cikin kuka Esha tace "Momy ba itane ta karya man colour ba" Fanan ɗin tace mata amman ai tasan ba tana sani tayi mata hakan ba ko, da sauri Adam yace eh zata wuce ne ita kuma Esha tazo sakawa a cikin locker ɗin seat dinta shine color ɗin ya faɗo ƙasa ya gangara ita kuma tazo wucewa shine ta taka mata Esha ɗin ta juya ta wurga mashi harara tare da kumburo baki, nasiha Fanan ta shiga yi mata tana nuna mata ba komai ake fushi ba ta rinƙa haƙuri pls ta hakane zata zama Good Girl,

Cikin yamutsa fuska Esha ɗin tace "Momy, am i not a Good Girl?" da sauri Fanan ɗin ta kai hannu tana shafa kumatunta tace "Oh no, Sweetheart you are a Good Girl, kawai dai in kina haƙuri da abubuwa shine zaki ƙara zama yarinyan kirki ki rinƙa jan Friends ɗin ki a jiki da yan'uwanki kuyi wasa ba tare da kunyi faɗa ba amman yanzu kowa bai jin daɗin yin wasa dake saboda yawan faɗan ki, We are not happy yadda kowa ke maganan baki ji pls ki bari yadda za'a rinƙa cewa Esha Good Girl ce tana da haƙuri da kirki" kai Esha ɗin ta ɗaga mata tace to zata rinƙa yin haƙurin, Fanan ta tambayi ta yi promise ta bari da sauri ta ɗaga mata kai alamar eh tace yauwa haka take so amman in ta ƙara ji ta bugi wani har tayi mashi rauni itama zata 6ata da ita, da sauri Esha ɗin ta girgiza mata kai tace Allah bazata ƙara ba, kallon Haisam Fanan tayi da duk abun nan bai kallesu ba tayi ɗan murmushi kafin ta maido idonta kan Esha ta kai hannu ta matso da kanta ta raɗa mata ta sauka ta duƙa gabanshi ta bashi haƙuri da sauri ta ɗaga mata kai don sosae ta damu da fushin da yayi da ita, saukkowa tayi a ɗarare ta matsa saitin shi tayi kneel down cikin karyayyar murya ta furta "i'm Sorry Daddy, i won't do it again i promise you" shiru bai ce komai ba bai kuma kalleta ba har lokacin fuskar shi a ɗaure take, cikin mutuwar jiki Esha ɗin ta juya ta kalli Fanan tana ta6e baki da kai tayi mata alamun ta ƙara matsawa kusa dashi ta bashi haƙurin, sanin tunda suke dashi bai ta6a bugunsu ba yasa bata ji tsoron matsawa dab dashi ba ta ƙara maimaita haƙurin data bashi sai lokacin ya maido idanun shi kanta ganin haka yasa ta marairaice mashi fuska tana dan motsa baki, ganin baice komai ba yasa ta kalli Fanan ta ƙara yi mata alamun ta kama hannun shi ta bashi haƙurin, hannunta har ɗan rawa yake ta kai ta ɗan kama hannun Haisam guda ganin bai janye ba yasa ta kai ɗayan ta kama duka hannuwan shi tace "pls My Daddy, am Sorry..." tana faɗin haka su Twins suka haɗa baki suka ce please Dad Sorry, hannu Fanan ta kai ta dafa kafaɗarshi tace "Sorry Babe, please forgive her, tayi alƙawarin bazata ƙara ba" Sigh yay cikin muryarshi mai cike da natsuwa idanun shi akan Esha ɗin yace mata kada ta ƙara aikata abu irin haka in ba haka ba zai ɗauki mataki akan ta kuma ba ruwanshi da ita, da sauri ta jinjina mashi kai ya saki fuska tare da ɗago da ita aikuwa da sauri ta faɗa jikin shi tana murmushin farinciki haka su Twins ma murmushin suke harda yi masu gwalo Fanan ma dariyar take ta furta "Esha, Daddy's pet", harda Fanan aka zauna yin Assignment ɗin abun gwanin burgewa, Washe gari Haisam ɗinne ya kai su Makarantar yayi shigar zuwa aiki yana sanye cikin suit, har class ɗinsu yaje yasa aka kira mashi yarinyar data buga ya bata haƙuri itama Esha yasa ta bata haƙurin yace ma Esha daga yanzu su abokai ne su rinƙa yin wasa tare kada ya ƙara jin tayi faɗa da wani tace mashi to, harda kyautar kuɗi masu yawa yaba class Aunty ɗinsu kafin ya tafi, ba laifi a lokacin ta rage rashin jin saidai ance wai mai hali baya barin halin shi koda ya barin wani lokacin bata cikin sauƙi ba.

Cikin sa'a Mino ta kammala karatunta na nursing saida Fatuu taji ba daɗi zata koma Abuja ta barta sauƙinta ma Aysha na nan lokacin itama Aysha ajinta shidda suna gabda yin jarabawar gama Makaranta, bayan result ɗin Mino ya fito wanda yayi kyau sosae ta fara shirin fara yin bautar ƙasa, a wani Weekend da Haisam zaije Zaria ne ya tafi tare da abokinshi Na'eem yayi mashi rakiya daga nan shima zai gaido danginshi don ɗan Zaria ɗinne amman iyayenshi a Abuja suke zaune, bayan sallar Juma'a suka iso Zaria lokacin da suka isa gidan Fatuu bata dawo daga makaranta ba sai Aysha kawai da mai aikinsu, tana sanye cikin riga da skirt na atampa ta zama budurwa sak irin jikin Mino gareta itama doguwa ce kuma bata da jiki gashi tana da kyawun Fuska saidai bata kama dasu Fatuu sosae kamar yadda Mino ke kama da ita, ita ta tarbesu cikin fara'a tana masu sannu da zuwa gaba ɗayansu fuskokinsu a sake suna mata murmushi suka amsa mata, a parlor suka zauna ta kawo masu ruwa da lemu tace bari ta shirya masu table Haisam yace ta bari ba yanzu zasu ci abincin ba sun ci a Kaduna sai ko zuwa ɗan anjima tace to, har zata tafi taji ya tambayi ya karatunta ta tsaya tana murmushi ta amsa mashi da Alhamdulillah suna ta shirin yin jarabawa yay mata fatan sa'a haka ma Na'eem daketa kallonta yana murmushi shima yay mata fatan sa'a ta kalleshi tay mashi godiya kafin ta juya ta tafi, bayan tafiyarta ne Na'eem ya maida idonshi kan Haisam yace mashi amma daga ganin wannan sister ɗin Madam ce ko ya ɗaga mashi kai, tambayar shi yay zuwa tayi Haisam din ya bashi amsa da anan take wurinta tana tayata zama itama tana karatu, jinjina kai Na'eem ya ɗan yi yay shiru can kuma sai yace mashi zasu bashi ita don ya ganta kuma tayi mashi,

"Ita kuma wife en naka fa?" Haisam ya tambaya yana murmushi shima Na'eem din murmushin yake yace zai ƙara ne kamar yadda shima yake da biyu, murmushi kawai Haisam yay bai ce komai ba ganin haka yasa Na'eem yace shi yake saurare Haisam ya tambayi wai is he serious ya ɗaga mashi kai yace Allah tayi mashi da gaske yaji yana sonta da aure, murmushin gefe Haisam yay yace mashi ai ƙarama ce yanzu zata gama Secondary Na'eem din yace ai abun ba'a nan yake ba tunda dai ta balaga lafiya lou za'a iya yi mata aure tunda ta isa, shiru ya ɗan yi kafin ya gyaɗa kai yace in da gaske yake sai ya nemi soyayyar yarinyar Na'eem ɗin ya gyaɗa kai ya tambayi sunanta ya faɗi mashi, anan falo suka zauna suna kallo har akayi sallar La'asar suka tafi Masallaci, bayan dawowarsu Haisam yace suje ciki ya huta yace a'a yana son zai yi magana da Aysha Haisam yace Ok shi zai shiga ciki Na'eem ɗin yace Ok pls ya turo mashi ita, a saman doguwar kujera ya zauna bada daɗewa ba sai ga Ayshar ta fito ta nufo cikin falon, daga gabanshi ta tsaya tana murmushi shima shi yake mata tace gata Yaya Haisam yace yana kiranta yace mata eh tare da nuna mata gefen shi yace tazo ta zauna, saida tayi ɗan jim kafin ta nufi inda ya nuna matan ta zauna daga can ƙarshe ya gyara zaman shi ya dawo yana kallonta,

"Aysha ya School?" ya tambaya da muryarshi ta yan gayu, tanata murmushi tace mashi lafiya lou ya sake tambayar tana dai maida hankali ko tace mashi eh ya tambayi wane department take tace mashi Science,

"Ko kema kina son zama Doctor ne?" kai ta ɗaga mashi alamar eh yace ashe da future Doctor yake zaune tayi yar dariya,

"To za'a rinƙa duba ni in an zama Doctor en?" kai ta ɗaga mashi kafin cikin yar muryarta tace in yana so yay yar dariya yace in mutum bashi da lafiya har sai yana so likita zai duba shi murmushi tayi bata ce komai ba, ta lura da irin kallon da yake mata hakan yasa ta fara yin wasa da yatsunta tana yi tana ɗan kallonshi tana murmushi,

"Yanzu in kiga gama karatun zaki aure ne sai kici gaba da karatun ko?" da sauri ta kalleshi tare da ɗan waro ido tace "Aure kuma!" kai ya ɗaga mata ta ɗan girgiza mashi nata tace ba aure zata yi ba Karatun zata cigaba,

"Why bazaki aure ba, ai ana karatu koda aure ba kiga sister en ki ba itama tana da aure harda yara ma kuma tana karatunta",

"To ai ni ko Saurayi ban dashi" ta faɗa tana ta murmushi, wani kallo yayi mata yace wasa dai take mashi amman kamar ita ya za'ai tace bata da saurayi, da sauri tace "Allah da gaske nake maka ni ko ance ana sona ban yarda saboda Karatu nike son yi" yadda take mashi magana sosae yake burgeshi gashi daga yanayin Maganarta zaka gane yarintar ta,

"Yanzu ace ki samu wanda yake son ki kuma kema kina son shi bazaki yarda kuyi auren ba sai kici gaba da karatun?" da alamun rashin fahimta tace "wa?" yace mata misali ne ya bata tay ɗan shiru alamar tunani yana ta kallonta can tana murmushi tace to in su Adda Fatuu sun amince sai tayi,

"Ai ba su zasu zauna maki ba ko Aysha, in kina so nasan bazasu hana kiyi auren ba" kai ta ɗaga mashi alamar eh yace in ta samu wanda take son kenan zata yi auren ta sake ɗaga mashi kai kafin ta sunnar da kanta alamar kunya,

"Ok, dama wani ne ya ganki kin yi mashi yaji yana son auren ki da Kin gama School, to har nayi ma Yayan ki Haisam Maganar yace ya nemi amincewar ki shiyasa nace to bari in maki magana" ba shiri ta ɗago tana kallon shi da alamun mamaki har ya gama ta waro idanunta tubarkalla tace mashi "ni kuma!" kai ya ɗaga mata ta sake cewa "a ina ya sanni"? Yadda tayi ne ya sashi yin yar dariya kafin yace yaga hoton ta ne tay shiru tana kallon shi,

"Aysha baki ce komai ba game da wanda na faɗa maki yana son ki" dan yamutsa fuska tay ta ɗan yarfa hannu alamar bata san mi zata ce ba, ganin ya kafeta da ido yasa tace to ai ita bata san shi ba,

"In kin ganshi yayi maki zaki amince?" shiru tayi tana ta kikkafta idanu, ɗage mata gira yay yace ita yake sauraro a sanyaye ta ɗaga mashi kai alamar eh, bin ta yay da wani irin kallo ta ƙara maida kanta tana wasa da yatsunta, tana haka taji muryarshi yace "Aysha ni ne na ganki naji ina son ki kuma auren ki nike son yi in kin gama School amman sai in nayi maki nima" da sauri ta ɗago ta kalleshi idanunta a ware fuskarta ta nuna tsananin mamakin Maganar shi yana murmushi ya ɗan lumshe mata ido, ƙirjinta ne ya fara bugu da sauri da sauri ta maida idonta ƙasa,

"Sunana Na'eem, ni abokin Yayinki Haisam ne, inada mata da yara biyu sannan ina aiki da Central Bank, ban san ko na ta6a ganinki ba kafin yanzu tunda muna yawan kasancewa da Haisam duk wata hidima data danganci Family ɗin su ina zuwa saidai a wurina yau na fara ganinki zuwan mu nan, kuma cikin ikon Allah ina ganinki naji na kamu da son ki abunda bature ke cewa, Love at first sight, nayi ma shi yayan naki magana kan haka shine yace to in nemi soyayyar ki idan Allah yasa kinga nayi maki to zan aure ki da kin gama School sannan zan barki kici gaba da Karatun ki in sha Allahu" shiru bata ce komai ba bata kuma ɗago ba abun ya ɗaure mata kai sosae don bata yi tunanin zai mata wannan Maganar ba, ganin taƙi tace komai yasa shi kiran sunanta ta amsa ba tare data ɗago ba yace tayi shiru bata ce komai ba still taƙi cewa komai ɗin,

"Ayshat" amsa mashi tayi ba tare data ɗago ba yace "Look at me" saida tay ɗan jimm kafin a hankali ta ɗago idanunta suka sauka akan kyakkyawar doguwar fuskarshi mai ɗauke da kwantaccen saje, yanayin fatarshi ba za'a ce mashi fari ba kuma ba baƙi bane yafi kama da a kira shi da wankan tarwaɗa, sosae yanayin hutu ya bayyana a jikin fatar ta shi yana da kyawun fuska wadda take a cike ɗauke da dogon hanci da kuma madaidaicin baki mai dauke da jerarrun fararen haƙora harda yar wushirya, a bangaren yanayin jiki sam ba gajere bane don da kaɗan Haisam ya ɗara shi tsawo sannan kuma ba siriri bane yana da cikar jiki, ganin tanata kallonshi yasa shi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login