Showing 264001 words to 267000 words out of 512766 words
Chapter 89 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1564
Sameer dake kallon su ya d'an ta6e baki da yanayin d'an murmushi akan fuskar shi, suna fitowa wayar Laila ta fara yin ringing tace masu tana zuwa pls ta d'an yi gaba tana amsa wayar, maido Fatun yay jikinshi ya rungumeta ta yadda suna kallon fuskar juna sai yamutsa mashi fuska take tana fad'in ita kunya take ji don Allah, yana murmushi idanun shi a d'an lumshe yace to mi yay mata da zai zama abun kunya da ido tay mashi nuni da rungume tan da yayi, ce mata yay wannan ba wani abu bane yake ma yan'uwan shi ma balle ita matar shi, sai faman tura mashi baki da ya sha jambaki take gaba d'aya hakan da take ya fara turning d'in shi on, kallon ta kawae yake tana mashi shagwabar kar wani ya gan su don Allah, slowly ya duk'ar da kan shi saitin nata ya kai bakin shi kunnanta ya rad'a mata magana, d'agowa yay ya d'age mata gira tace "Yaushe?" a hankali ya furta "after isha" shiru ta d'an yi kaman mai nazarin wani abu taji yace ko bata so da sauri ta girgiza mashi kai, Laila ce ta dawo wurin su tana murmushi da sauri Fatuu ta juyar da fuskar ta, ce ma Haisam d'in tayi ko ta barta a nan ne ba tare daya ce komai ba ya saki Fatun Laila ta kamo hannunta suka nufi sauka daga benen tana yi tana d'an waiwayen shi yana tsaye bai koma ba fuskar shi da d'an murmushi har suka sauka sannan ya koma ciki.
Lokacin da akai Sallar juma'a hidima ta kan kama bak'i yan Walima tuni sun fara zuwa, bayan an yi salla mai makeup tazo lokacin Fatuu na d'akin Laila ta shirya cikin dandatsetsen lace Swarovski d'an dubu d'aruruwa anyi mata d'inkin riga da skirt tasa su sark'ar diamond abun ba'a magana jikin Fatuu ya zama kud'i ko ince kud'ad'e, ba 6ata lokaci aka fara mata bridal Makeup d'in, tun ana cikin yi ake aikowa kiranta daga d'akin Mom don tazo a ganta, Laila ce ta kira Mom d'in nasu ta sanar mata ana mata kwalliya ne in aka gama zata kawo ta, Jama'a kuzo kuga Fatuu ya fillo don Allah ni Saboda kallon ta ma har saida Alk'alami na ya fad'i, abun sai dai ace Tubarakallah Ma sha Allah an k'ara jik'a kyau da ruwan Naira abun ba'a magana, Nan aka shiga yi mata hotuna harda su Video mai makeup d'in ma tana ta mata don ta d'aura a handles d'inta na social media gashi da yake Fatun a wayancenta take abun sai ya tsaru sosae, ana cikin yi Jidderh ta shigo tasha ankonta an mata yar Arzik'in Fitted gown (bana ce matsiyaciya ba😂) sosae d'inkin ya had'u an tsara shi da mix and match d'in ta fito a yar matan Abuja, ce ma Aunty Laila tayi Mom tace a kawo ta hakanan Friends d'inta ne zasu ganta, wani had'add'an gele mai shara shara ana ganin komai na jikin mutum baida girma sosae ta d'aukko ta yafa mata tasa takalma nasu tsini sosae hannun ta ruk'e da yar purse d'in su Laila ta kama hannunta suka tafi,
bayan sunje a parlor suka tsaya Mutanen ciki suka hau yabon gayun Amarya daga baya ta wuce da ita cikin Bedroom, duk k'awayen Mom ne a ciki wasu anko ne a jikin su na full embroidery har Hajiya Zainab ma da Mom ankon ne a jikin su anyi masu dogayen riguna sunyi kyau abun har ba'a magana, harda Hajiya Kubra ta Comment section a cikin su ashe itama mutuniyar First Lady ce tasha anko full embroidery, ciki Laila ta shiga da ita Jidderh ma na biye da su, bin su d'aya bayan d'aya ta shiga yi da Fatun suna ganinta tana gaishe dasu sai yabon kyaun ta suke nan aka shiga bata kyautar kud'i Laila na amsar mata harda wadda ta bata kyautar yan kunnan zinari ita dai Fatuu sai murmushi kawai take bakin ta ya mutu abun ya girmi tunanin ta, abun mata sai ya zama kamar gasa ma, ita Hajiya Zainab Account details d'in Fatun tace abata aka sa sowa ana mata kirari sai murmushi take daga baya aka kaita wurin Mom ta zaunar da ita kusa da ita a hankali Fatuu ta gaisheta tana murmushi tace "Ma sha Allah Daughter kin yi kyau" tace mata ta gode, bayan sun gama da nan Laila ta fito da ita suka nufi part d'in Hajiya daga nan kuma bayan sun fito baya suka nufa gaba d'aya rud'ewa su kai da ganin yadda Fatuu ta had'u, anan Laila ta barta ta tafi itama ta shirya don duk kusan kowa ya saka ankon shi kowa ka gani atamfar tayi mashi kyau daga bak'ak'en har fararen, sosae Fauzy da Mino suka yi kyau ita Fauzy fitted gown ce Mino kuma riga da skirt, su Aunty Mareeya da Feenah duk dogayen riguna aka masu styles masu kyau kalar na yan Abuja Fanan itama fitted gown aka mata sosae tayi kyau gashi a jikin atamfar akwae kalar gashinta, da Laila zata tafi ta bita don ayi mata makeup itama.
Da lokacin cin Abinci yayi a parlor aka shiga jerawa saman Dining tables an k'ara wasu guda ukku suma masu cin mutum sha biyu sai aka matsar da set guda na kujeru aka had'e su, Abinci ne kala daban daban sai wanda Mutun ke so sai kuma mutum ya ci ya ture nama kuwa ba don kar inyi k'arya ba sai ince duk tsoka tayi dunkulan hannun mutum in ma bata yi ba to ta kusa🤧 ga kaji Malam, drinks da ruwa su wannan kaman company d'in su ka zo ma, bayan an gama tsara wurin aka je aka sanar ma Mom da Aunty suka fito da Mutanensu aka zazzauna yan baya ma su Aunty Mareeya aka masu magana suka fito, yadikko bata son suje ai kauyanci hakan yasa taje tayi ma gwaggo magana kan in zai yiwu akawo masu nasu can gwaggon ta fahimceta tace to,
Table guda duk k'awayen Mom ne harda Hajiya Zainab Wani kuma Aunty ce da K'awayen ta wanda wasu k'awayen su ne gaba d'aya ita da Mom, a d'ayan table na ukku su Aunty Laila ne harda Amarya Fatuu da K'awayen su sai table na k'arshe nan su Aunty Mareeya suke harda Fanan da wasu yan uwan su yan Daura Ma'aikata nata Serving nasu abun gwanin burgewa kowa harkan gaban shi yake bai damu da yadda wani ke cin Abincin shi ba, a can cikin parlon ma a saman kujeru akwae mutane zazzaune suna cin Abincin, Haisam na part d'in shi da Abokan shi harda Najeeb da ya iso da daddare ya sauka a guest house d'in baban shi suma suna cin Abincin haka Nameer ma yana a part d'in shi da su Kawu Amadu da Tk da wasu Abokan shi, Senator ma na a part d'in shi da wasu Abokan shi da kuma yan uwan shi harda Baffan Fatuu dasu Ardo, sai da Baffan yayi masu hud'uba cikin hikima da zasu zo ya nuna masu abunda yakamata suyi don nan ba komai a ke masu ba sudai gyad'a kai ne nasu don yanzu mulkin ya koma kan Baffan Fatuu, duk wanda yazo sai Senator ya nuna masu dangin Amaryar sun gaisa, abun dai sai dae ace Ma sha Allah don Walima kam tayi Walima an ci an sha anyi hani'an kowa ka gani fuskar shi cike take da annuri bayan an gama aka hau yin hotuna gwaggo taje ta kira su Yadikko suka zo suma akayi hotunan da su, Fanan da kanta taje part d'in Haisam ta kira shi don ayi hotuna suka dawo dashi yana sanye da Farar shadda haka takalman shi da agogon shi duk farare ne yau dae Allah yayi an rufe kan da hula babbar rigar shi na ruk'e a hannun shi tare da Abbas suka fito shima yana sanye da riga da wando na farar shadda, idon Fatuu akan shi har suka k'araso wani irin dad'i take ji kaman ta kama yin rawa a yau ta k'ara jinjina girman Ubangiji ta k'ara gasgata Kalmar nan ta mahakurci mawadaci ne, bayan sun shigo Photographer yaci gaba da aiki, Mom da kanta ta kirawo Senator da Nameer don su zo ai hotuna dasu harda su Kawu Amadu su ka zo daga baya Senator d'in ya koma Saboda mutane d'aya baro, ana cikin hotunan Jidderh tazo wurin Fatuu tace mata ga bak'uwa Daddy yace akawo ta wurin ta, da farko Fatuu bata gane bak'uwar ba dake ta kallonta tana dariya hannunta ruk'e da yarinya da bazata wuce watanni ba, sai can da tay magana tace ma Fatun hala bata ganeta ba sannan Fatun ta d'an waro ido tace "Kaman Aunty Sadeeya?" tana dariya tace itace, mamaki ne ya kama Fatuu ganin k'anwar Khalid a wurin, hoton akayi masu tare bayan an gama ta nufi cikin parlon da ita suka zauna a saman 2 seater,
"Amman Aunty Sadeeya ya akai kika san da walimar nan har kika zo?" Fatuu ta tambaya da alamun mamaki akan fuskar ta, tana murmushi tace "tare da Dad muka zo shi ya kira ni ya sanar dani yace zamu zo dashi, ni da yake ina nan ina Aure ban fi shekara guda da watanni ba, gyad'a kai Fatuu tay tace Allah sarki,
"kin yi kyau sosae wllh kaman bake ba duk da dama kina da kyau an ma kin canza sosae kin k'ara girma kuma, na taya ki murna sosae Allah yasa Alkhairi ya baku zaman lafiya da zuriya d'ayyiba" Fatuu nata Murmushi ta amsa mata da Amin, shiru suka d'an yi dukkan su murmushi ne akan fuskar su can Fatuu ta tambaye ta Mom d'in su tace tana nan tama san zasu zo don sunyi waya take sanar mata tace ma ta kirata tayi mata Allah yasa Alkhairi, kai Fatun ta jinjina suka d'an k'ara yin shiru can Sadeeyar tace "baki tambayi Ya Khalid ba" har saida gaban Fatuu ya fad'i jin sunan Khalid, d'an murmushi tay a sanyaye tace ma Sadiyar yana ina,
"Yana nan yanzu a koma Yola acan yake aiki tare ma akayi bikin mu don bayan an fasa naku yayi nadama sosae, don har gwuiwa k'asa ya rok'i Dad kan ya bashi dama ta k'arshe kada a fasa Auren anan yake sanar mashi ai an ma d'aura maki Aure don haka ya hak'ura dake ba matar shi bace, aikuwa anan ya sume mashi abun ya kai shi ga kwanciya har gadon Asibiti, sosae yayi nadama wllh don akwae lokacin da muka zauna dashi yana k'walla yake fad'i man Allah ya jarabe shi da son ki sosae dama tunda ya gan ki matsayin wadda zai Aura yaji kin mashi gajan hak'uri yaja mashi amman yasan Allah ne ya kama shi, lokacin da aka zo neman Aure na shine Dad yayi mashi Maganar ya fito da wadda yake so tunda yasan bai rasa yan mata sai a had'a shine yace ma Dad d'in ya bar mashi komai ya nemo mashi kowacece zai Aura, farko Dad cewa yay ya fidda hannun shi akan shi saida Mom tay ta rok'on shi tana nuna mashi da gaske ya canza ba zai bashi kunya ba anan har take mashi Maganar wata k'anwar ki wai da akayi magana da suka je Dad d'in yace ai kuma shi ba K'aramin mutum bane ya riga yace a kyaleta tayi karatun ta yanzu bazai Koma ba yace a bashi ko ba don haka ba ma don abunda Ya Khalid d'in yay maki bazai nema mashi k'anwar ki ba, k'arshe dai wata d'iyar Abokin shi ya samo mashi Hafsat itama Secondary ta gama ba laifi tana da kyau itama bafullatana ce a cikin Yola suke shine akayi bikin mu tare, Yanzu suna acan Yola d'in yasa taci gaba da karatu tana nan ma da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe, gaba d'aya Ya Khalid ya canza ta sanadiyyar abunda ya faru, sosae yay sanyi duk wani hali mara kyau da kika sani ya bari wllh don ni bai 6oye man komai tun lokacin da yana cikin ciwon son ki ya maida ni kamar k'awar shi yay ta fad'i man damuwar shi in ta lallashin shi ina k'arfafa mashi gwuiwa yanzu haka shima yasan da zamu zo nan" idanun ta cike da k'walla ta k'arasa Maganar itama Fatuu sosae jikinta yayi sanyi zuciyar ta sai tunano mata abubuwan da suka faru tsakanin su take, Allah mai juya Al'amari a yadda yaso a kuma lokacin daya so da rabon ta silar hakan zata auri Haisam yanzu data k'i yarda kota yanke ta gudu da tayi ma kan ta, k'arshe rayuwarta ta wulakance ta kuma jefa iyayen ta a matsala, shiyasa ake son bawa ya rink'a yarda da k'addara mai kyau da mara kyau, duk abunda Allah yayi ma bawan shi mai kyau ne don yafi mu son kan mu, sau da yawa abubuwa marasa dad'i da suke faruwa damu wasu kan haifar da abubuwa masu dad'i agare mu matuk'ar zamu dogara da Allah muyi rik'o da yin Hak'uri, suna zaunen Laila ta zo tace mata Dad d'in su na nemanta tace to ta nuna mata Sadeeya tace bak'uwarta ce yar uwarsu ce a Adamawa tana aure anan, a mutunce suka gaisa harda tambayar ta Unguwar da take anan Abuja ta d'auki Baby d'inta, daga baya ta kira Jidderh ta had'a su tace a kaita d'akinta a bata Abinci kafin su dawo, part d'in Dad d'in suka wuce gaba d'aya parlon shi cike yake da Manyan Mutane masu tumbin Naira kama daga shahararrun masu kud'i zuwa masu Mulki, Laila ta shiga bin su da ita suna gaishe su suma dae har da kyautar kud'in suka mata daga baya Dad yace akawo ta wurin Alhaji Lawal dake a kusa dashi, a k'asa ta tsugunna ya kai hannu ya dafa Shoulder dinta da fara'a yace "Ma sha Allah Daughter, nayi matuk'ar farincikin yadda abu ya kasance, wannan aikin Albarkar da muke sa maki ne, matuk'ar zaka yi biyayya ga iyayen ka to kuwa rayuwar ka zata yi Albarka, Allah yasa Alkhairi ya baku zaman lafiya da zuria dayyiba yasa gidan zaman ki ne na har abada" Mutanen dake a kusa dashi sai amsawa da Amin suke harda wani abokin shi d'an Majalisa da suka zo tare, kasa jurewa Fatuu tay ta shiga yin hawaye komai daya faru a baya yana dawo mata, Envelope ya fiddo daga cikin Aljihun shi ya mik'a mata kawae sai ta fashe da kuka ya hau rarrashinta yana fad'in ai ba abun kuka bane, Senator dake ta murmushi yace "Kukan dad'i ne kasan shima yana sa ayi kuka" ya kalli Fatuu yace "Hakane ko Daughter?" A hankali ta d'aga mashi kai duk aka yi dariya daga baya Dad d'in yace ma Laila taje da ita.
Bayan sallar la'asar Nameer ya d'auki Mino suka fita Tk ma ya d'auki su Kawu Amadu da Kamalu suka shiga gari, Lokacin Laila tasa Fatuu ta canza shiga zuwa rantsatstsiyar shadda gray data sha ubansun aiki harda alkyabba aka d'aura mata lokacin Malamar da aka d'aukko zata yi Wa'azi wadda sananna ce ta zo, tuni an gyara main parlor d'in tsaf anan aka zazzauna Malamar itama a kan kujera ta zauna ta fara Wa'azin hannunta ruk'e da lasifika da ta karad'e ko ina, Wa'azi mai tsuma zuciya kan rayuwar Aure tayi, sai gab da sallar Magrib aka gama nan aka shiga rabon souvenirs abubuwa kala kala masu d'auke da sunan Haisam Ali Adamu Zakee da Fatima Muhammad Ardo, ba masu hotunansu cikin abubuwan da aka raba don Haisam d'in ya nuna bai so. Alhamdulillah Walima ta tashi lafiya abun dai sai san barka wllh, mun ci mun sha munyi hani'an yan Comment section an sha da ku da baku yi anko ba kun zo, kar ku manta gobe in Allah ya kai mu akwae Dinner itama kuma in ba anko ba shiga zaku yi ba ato😹.
Da daddare bayan isha gaba d'aya Su Fauzy bajewa sukai a parlor harda su Aunty Mareeya gaba d'ayan su dai yan part d'in ana hirar Walima cike da nishad'i, Wayar Fatuu dake hannun Fauzy had'e da tata ce ta fara ringing ta kai idonta kan screen d'in, ganin Haisam ne yasa ta mik'e don taje ta kai mata, har lokacin ankonta ne a jikinta rigar ta kamata kanta tayi d'aurin kallabi mai steps da akayi mata gashinta dake fake ya fito ta tsakiya ya bud'e sosae, sauri sauri gudu gudu ta nufi cikin gidan ganin kiran ya yanke ya kuma sake kira, hanyar d'akin Mom d'in su Haisam ta nufa don tun bayan da aka gama Wa'azi Fatun na can Mom tasa ta zauna Saboda masu son ganinta ba sai an ta nemota ba, tana zuwa daidai bakin corridor tana niyyar shiga da d'an gudu gudu kwatsam taci karo da Mutum wanda har saida tai taga taga tayo baya, ba arziki ta kai hannu ta dafe goshinta idanunta a rufe ta shiga fad'in "wayyo..wai...wai.wai...." A yadda taji sai kace ta bugi dutse, a hankali ta d'ago still hannun na a goshin slowly ta fara bud'e idanunta, koda tay arba da wanda tay karon ai ba shiri ta idasa bud'e idanun ta waro su, tsaye yake k'ik'am sai kace an dasa shi don koda sukai karon bai ko yi gezau ba, Sameer ne yana sanye da farin jeans da farar riga ta ciki sai aka d'aura Yellow a sama ma6allan ta a bud'e hakan ya bayyana ta cikin agogon hannunshi fara ce itama daga wurin glass d'in kan yana reflecting yellow sai k'afafun shi ma sanye suke da fararen takalma, daga wurin Mom d'in shi yake Hajiya Zainab data kira shi bayan ya fito ya d'aga waya yana magana sukai karon, gaba d'aya wayar shin da glass d'in shi daya ruk'o a hannu sun fad'i k'asa, bin shi da kallo Fauzy tay gabanta na wani irin Fad'uwa ganin mugun kallon da yake mata ya tamke fuska sosae, Murya na rawa tace "D...don Allah kayi hakuri bansan ka taho bane ina sauri ne zan kai waya ana kira"