Showing 288001 words to 291000 words out of 512766 words

Chapter 97 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1598

tana da rabon haihuwa a duniya ganin tana ta shan Magani kuma ana samun cigaba amman har yanzu ko 6ari bata yi ba tasan ma ko zata iya conceiving, a hankali take kai hannu tana share kwallan dake gangaro mata tana haka taji anyi knocking saida ta goge Fuskarta tass sannan ta bada izinin a shigo, tana ganin shi da sauri ta saukko daga gadon tana sanye da rigar bacci iya gwuiwa kanta ta saka hula gashin ta ya zubo ta gefe da gefe, nufo shi tay da sauri tun kafin ta k'araso ya bud'e mata hannuwan shi tana zuwa ta fad'a jikin shi ya maida hannuwan ya rungumeta sosae ta shiga fad'in she's happy for them bada jimawa ba zasu zama iyaye, murmushin jin dad'i ya shiga saki ya d'aura ha6ar shi a saman kanta tare da lumshe ido, daga lokacin data amince mashi ya cigaba da zama da Zarah ya gane irin son da yake mata, a yadda yake ji he can't live without her, jin tana k'ok'arin d'ago da fuskar ta yasa shi janye ha6ar tashi, d'agowa tay ta kalle shi suka shiga sakar ma juna k'ayataccen murmushi daka kalli fuskokin su zaka fahimci suna cikin farin ciki don cike suke da annuri, suna haka calmly taji ya furta mata "Thank you Sweetheart" d'an bud'a mashi ido tay tace akan me ya lumshe ido yace "For Everything" fad'awa tay jikin shi ta kwantar da kanta a chest d'in shi, yaci gaba da fad'in "har bansan ta yadda zan rink'a gode maki ba, nagode maki da kasance man mafi jin dad'in duniyar nan" wurin kunnanta ya kai bakin shi ya rad'a mata "al'mar'atussaliha" yana jin yadda ta k'ara shige mashi yana ta murmushi,

d'ago kai tay ta kalle shi tace "komai daga wurin ka na koya babe, sadaukarwa halin ka ne, baka da buri sai na kaga kasa mutum farinciki hakan ne yasa kai ma kake kasancewa acikin farinciki koda yaushe, Babe duk yadda na kasance maka kai kaja hakan you're a selfless and just person, da maza zasu yi koyi da halin ka da sun zauna lafiya da matan su koda sunfi d'aya don hakan zai rink'a rage masu radadin kishi, amman da yawa su suke jefa matan su a mawuyacin hali k'arshe suzo suna kauce hanya wanda hakan bashi ne way out ba sai ma mutum ya halaka, Idan ba kayi cuta ba bazaka ga cuta ba all one needs to do shine hak'uri tunda Allah da kan shi yace yana tare da mai shi in mutum yayi sai yaci riba,ina rok'on Allah yasa in ci ribar hak'uri though nama fara cin ribar ga baby nan zamu samu" ta k'arasa tana murmushi, still yay yana kallonta wani irin tausayin ta ne ke ratsa shi, maida kanta yayi jikin shi yace in sha Allah zata samu lafiya itama ta Haifa mashi yara masu irin halinta, tana murmushi tace Allah ya amince amman in ya kaddaro mata bazata haihun ba ba komai tasan daga cikin hikimar sa ne ya kawo Zarah ta Haifa masu, murmushi kawai yake wani lokacin sai yay ta ganin kaman ba ita ba don da kuruciyarta bata da hak'uri ga kukan banza, sigh yay ya d'agota yace bari yaje, tambayar shi tay inda zashi ya fad'i mata da sauri tace to bari ta shirya sai su tafi tare, ba tare da ya sake ta ba gently yace mata yana son yaje da wuri ne Saboda grandma d'inta ta dawo gida jiya ta kwana ba shiri ko blanket babu yasan bata yi bacci cikin dad'i ba ta bari ta shirya a nutse sai suzo da Laila in ma ita bazata zo ba in ta shirya tay mashi magana zaisa a kawo mata makullin Mota sai ya bata address na Hospital d'in, kai ta jinjina mashi ya d'an sunkuyo yay pecking goshinta had'i da furta "I love u" farfar tay da ido ta furta mashi tana son shi da kowane bugu na zuciyar ta, yar dariya yay ya saketa tace in yaje yay kissing baby d'in su dariya Maganar ta bashi yace mata har ya zama baby kenan tace eh ai zai zama ne in sha Allah, bayan ya fito dining area ya nufa ya d'auki basket d'in da yar jakar kayan sannan ya tafi.

Bakin gado ta koma cike da zumud'i ta d'auki wayarta ta fara k'ok'arin kiran Mom d'inta, saida kiran ya kusa katsewa sannan tayi picking, gaishe da ita Fanan tayi muryarta ciki ciki ta amsa, cike da Farinciki tace mata dama ta kira tayi mata Albishir Hajiya Maryam d'in tace mata miya faru ne, cikin washe baki ta hau bata labarin cikin da Zarah ta samu tana jiyo sautin d'an tsoki data buga kafin a hasale tace to shine zata tashe ta a bacci kaman dole kuma tasan a lokacin bacci take, hak'uri ta bata tace farinciki ne yayi mata yawa shiyasa ta kira don ta taya su murna, bata ce mata komai ba tay shiru can ta tambayi ina Noor ta bata amsa da tana a wurin su twins ta furta Ok, jin zata katse kiran yasa da sauri tace bata taya ta murna ba a dak'ile tace Allah yasa Alkhairi daga haka ta katse kiran sam Fanan bata ji komai ba, kiran Farha ta shiga yi bayan tayi ringing tay picking, gaishe da Fanan d'in tayi ta amsa ta tambayi ko bacci take ta bata amsa da No tana yin Assignment ne, ce mata tay ta tayata murna bride d'in su is pregnant Farhar tay d'an jimm sai kuma tace ta taya ta murna Fanan d'in tay mata godiya, tambayar ta tay yaushe zata dawo tace msta cikin week d'in da za'a shiga tay mata sai ta dawo daga haka sukai sallama.

Gwaggo na zaune akan kujera tun bayan data gama salla ta koma saman ta tana tasbih jin k'asan sanyi yayi yawa Saboda Ac dake ta aiki tiles d'in duk ya d'auka, Fatuu na kwance saman gado ta koma bacci bayan tayi salla da hijab d'in gwaggo, bata dad'e zaunen ba akai knocking k'opar ta tashi zaune sosae tace a shigo, turo kopar akai Haisam ya shigo da sallama Nameer na biye da shi, da fara'a ta amsa sallamar suka shigo ciki, daga gefen gadon Nameer ya aje basket d'in da jakar kayan ya koma wurin gwaggo da ke cikin gaisawa da Haisam, da murmushi ya gaishe da ita ta amsa mashi tay mashi ya gajiyan hidima yace tabi jiki ai, shiru ta d'an biyo baya kafin cikin girmamawa Haisam yace mata ga Nameer nan zasu tafi tare, tana murmushi tace ai da basu wahalar da kansu sun fito da sassafen nan ba yace mata ba wani abu, k'ok'arin mik'ewa ta fara yi tana fad'i mashi game da farkawar Fatuu jiya da daddare yanata d'an murmushi, sallama suka yi Nameer ya juya ta bi bayan shi suka tafi, wurin gadon ya nufa ya tsaya yana kallon Fatuu dake ta bacci rabin jikinta lullube da farin bargo wani irin Fresh yaga tayi mashi, ya d'an d'auki lokaci a haka yanata kallonta da murmushi akan fuskar ta shi, matsawa yay ya zauna a bakin gadon ya kai hannu ya d'an janye bargon, hannunta guda ya kama yana ta kallonta can ya kai d'ayan hannun ya d'aura a saman cikinta wani irin farinciki yake ji, k'amshin turaren shi ne ya kai mata cikin baccin a hankali ta fara motsi da sauri ya janye hannun shi dake akan cikinta gudun kada ya tasheta kawai sai gani yay ta fara bud'e idanunta, tana gama bud'e su suka sauka cikin nashi yanata sakar mata k'ayataccen murmushi, k'ura mashi ido tay tamkar bata gane shi ba calmly ya furta ta tashi maimakon ta bashi amsa sai tace "Hubby kai ne?" yanayin yadda sautin Maganar ya fita muryar tata ta d'an dishe, lumshe mata ido yay nan take ta tabbatar da shi d'in ne da sauri ta juyar da kanta ta hango babu gwaggo cikin d'akin, maido kan tayi taci gaba da kallon shi a sanyaye ta gaishe shi, bai amsa ba sai ya matsa gaba ya sunkuyar da kanshi ya had'e fuskokin su, slowly ya furta "ni yakamata in gaida ki Baby, a huge thank you to u for the amazing gift" lumshe ido tay ba tare data ce komai ba, d'ago fuskar yay yana kallon ta a hankali ta bud'e idanun nata ta bi shi da kallon rashin fahimta, ganin irin kallon da yake mata ne yasa k'asa k'asa tace mashi wace kyautar ban mamaki ce ta bashi jin haka da yanayinta yasa ya fahimci grandma d'in ta bata sanar mata ba, maida Fuskar shi yay gefen tata ya rad'a mata "mun k'ara samun abunda muka rasa ne" waro ido Fatuu tay with mouth agape ya d'ago yana kallon ta da murmushi ya d'age mata gira aikuwa da sauri tasa duka hannuwanta ta rufe fuskar ta yay yar dariya, hannu ya kai ya janye hannuwan nata suka had'a ido ganin tana k'ok'arin juyar da fuskar yasa shi k'ara had'e fuskokin nasu taji yace "I don't even know how to thank you enough Baby" murmushin dad'i kawai take saki, d'agowa yay ganin tak'i sakin baki tay mashi magana sosae yace ko bata farinciki ne, da sauri ta girgiza mashi kai da hannu tay mashi nuni da bakinta nan take ya gane tana nufin bata wanke bakin ba kawai sai gani tay ya kai fuskar tashi ya had'e mouth d'in nasu wato tama gane bai k'yamar bakin nata, ya d'an d'auki lokaci kissing her deeply kafin ya d'ago da sauri ta juyar da fuskar ta tana dariya, hannu ya kai yana k'ok'arin d'aga ta zaune yace ta tashi taci Abinci, bayan sun Mik'e tace mashi zata je toilet yace Ok bari ya taimaka mata tana ta murmushi tace mashi zata iya nan ya sanar mata tana akan bed rest ne sai an bi a hankali ta jinjina mashi kai, zaunar da ita yay bakin gadon yace yana zuwa, jakar kayanta ya bud'e ya ciro towel da brush da toothpaste sannan ya dawo bayan ya mik'ar da ita yay mata d'aukar jarirai ya nufi hanyar toilet d'in suna ta sakar ma juna murmushi,

bayan sun je toilet d'in taimaka mata yayi tay wanka har brush shi yayi mata tana ta dariya don abu ne wanda da wayon ta ba'a ta6a mata ba, kaman yadda ya d'auketa ya kai ta ciki haka yay mata ya fito da ita a gefen gado ya zaunar da ita, saida yaje ya kullo kopar d'akin ya dawo, shirya ta ya shiga yi harda mai cikin kayan ya shafa mata sannan ya fiddo kayan bayan ta saka undies, doguwar riga ce tasa da hula bayan sun gama ya kama hannunta suka nufi inda doguwar Leather sofa take ya zaunar da ita, d'aukko basket d'in yayi ya dawo wurin daga gefen ta ya zauna, warmer d'in ciki ya bud'e chips ne a ciki, d'aukar plate d'in cikin basket d'in yayi ya mik'e, wurin gado ya nufa ya d'auki bottle water ya nufi window don ya d'auraye shi Fatuu nata kallon shi, idon shi a cikin nata ya dawo suna ma juna murmushi, zuba mata Chips d'in yayi mai yawa ya bud'e ledar slice bread ya deb'o, d'aura plate d'in yay a saman kujerar ya shiga had'a mata tea mai k'auri, d'agowa yay tana ta kallon shi ya kai cup d'in bakinta ta fara sha, ganin yana ta bata yasa tace shi fa yace mata yayi safiya sosae ba yanzu zai ci ba ita dai da baby d'in su suci su k'oshi, mak'e mashi kafad'a tay ta tura baki tak'i amsar wanda yake bata a shagwabe tace in dai bai ci ba to itama ta k'oshi, d'an bud'a ido yay yana murmushi, hannu ta kai ta d'auki fork d'in itama ta d'ebo ta kai bakin shi dole ya bud'e ta ba shi, haka suka cigaba da ci a tare cikin salon kauna da k'yar ta yarda in aka bata sau ukku sai ta bashi da cewa tay bata yarda ba ayi sau d'add'aya dai yace mata to ai ita ba ita kadae bace akwae baby tana dariya tace ai bai fara cin Abinci ba ko, nuna mata yay ai sai tana cin Abincin zai girma ko tace to ita a bata sau biyu shi sau d'ayan yace ai yayi kad'an, da k'yar dai ta yarda da ukkun sai kace wata yar yarinya haka yake ta bi da ita, sosae taci ta k'oshi don saida ta cinye duka duk da dashi aka ci amman ba wani sosae ya ci ba, bayan sun gama ya kamata suka nufi toilet aka wanko baki da hannu duk da ba da hannun ma aka ci ba, akan kujera suka zauna suna kallon Tv ta kwantar da kanta a shoulder d'in shi, shima dai kallon ana yi ana shan love ake yin shi daga baya ta fara gyangyad'i har baccin ya d'auketa sosae, d'aukar ta yay ya kaita gado bayan ya kwantar da ita ta d'an bud'e idanunta ta kalle shi suka sakar ma juna murmushi, lullube mata rabin jikinta yayi ya sunkuyar da kan shi yay pecking goshinta ta furta mashi thanks, zama yay a bakin gadon yana ruk'e da hannunta guda yana d'an matsa mata shi tana ta murmushi a haka har ta koma baccin, mik'ewa yay ya koma kan Kujerar yaci gaba da yin kallon, ya d'auki lokaci a haka Yana yi yana kallo Fatuu dake ta shan bacci, wuraren k'arfe goma da wasu mintuna akai knocking d'akin sai lokacin ma ya tuna da kopar a rufe take ya mik'e don yaje ya bud'e lokacin Fatun ta bud'e idanunta sakamakon buga kopar da akai, Fanan ce ta shigo tana sanye da jallabiya coffee brown tay rolling veil d'in Laila na biye da ita itama tana sanye da jallabiya Navy blue ta d'aura gyalen saman kai, matsa masu yay suka shigo duk suna murmushi, Fatuu na ganin su ta fara k'ok'arin tashi zaune Fanan ta nufo ta da sauri, zama tay a bakin gadon tana washe baki ta kamo hannunta guda, gaidata Fatun tayi bayan ta amsa tace "we're really happy about this pregnancy Zarah" murmushi kawai Fatun ke yi mata ita kam sai washe baki take, Laila ce ta k'araso bakin gadon tana kallon Fatun da murmushi, gaishe da ita Fatuu tay ta amsa tay mata ya jiki tace taji sauki, Fanan ce ta tambayeta taci Abinci ta d'aga mata kai, kallo Haisam daya koma kan kujera tay tace mashi ya dai tabbatar taci ta k'oshi ko yana murmushi ya lumshe mata ido tace Yauwa to don kar abar masu baby da yunwa gaba d'aya Laila da Fatuu sukai dariya, komawa wurin Haisam Laila tay ita kuma Fanan ta shiga yi ma Fatuu tambayoyi da suka shafi cikin daga baya kuma ta koma yin hirar Babyn da za'a Haifa masu duk su Haisam na jinta sai dariya take ba su har Laila na cewa da alama tafi kowa murna da cikin tace mata abunda take ta fatan su samu kenan. A nan Haisam ya barsu Ya dawo gida,

Wurin k'arfe sha biyu su Hajiya Zainab sun gama shirin tafiya, zasu biya Asibiti su gaishe da Fatuu daga can zasu wuce, bayan ta fito tare da Mom da su Aunty da wasu mutane Security detail d'inta na biye da ita, Jidderh na a part d'in da su Fauzy suke suna zaune a parlor harda su Aunty Mareeya suna firar Dinner d'in jiya da kuma tashin hankalin da suka shiga lokacin da suka ji Fatuu ta fad'i, Yasmeen ce ta shigo da gudu ta nufe su tana d'an haki idon ta akan Jidderh tace mata ga Momy d'in Nasarawa can zasu tafi, zumbur Jidderh ta Mik'e ta ce ma su Fauzy suzo suje duk suka mik'e harda su Aunty Mareeya tana fad'in bari suma suyi mata bankwana don mace ce mai mutunci wllh, suna akan hanyar zuwa Aunty Mareeya ke ce ma Feenah in ka ga Sameer sai kace ba itace ta haife shi ba ta 6angaren hali Feenah na murmushi tace shima k'ilan in aka zauna dashi aga Mutuncin shi Aunty Mareeya tace amman dai da gani ba sai an fad'a ba yana da girman kai ba kamar Mahaifiyar tashi ba, gaba d'aya an fito waje bakin Entry Hall inda Motocin su suke a fake, tun bayan da Fauzy ta fito take ta wurga ido wai ko zata ga Sameer amman bata gan shi ba sai dai K'annan shi, tunanin ko yana a cikin Mota tay tabi Motocin da kallo saidai bazata iya ganewa ko yana ciki ba, Sallama Her Excellency tay da kowa ta nufi Mota da sauri aka bud'e mata bayan duk sun shishshiga ta d'aga ma mutane hannu kafin aka rufe kopar, a jere Motocin suka tashi ana ta d'aga masu hannu suka tafi jiniya na tashi, juyawa sukai suka koma cikin gidan, hakanan Fauzy take jin ta wani iri sai ganin fuskar Sameer take, a ranta ta raya k'ilan Shikenan bazata k'ara ganin shi ba har saida taji jikinta yayi sanyi yin tunanin, can kuma wata zuciyar ta raya mata k'ilan kuma sai ko bikin Mino da Nameer in Allah ya k'addara zasu auri juna, sukuku da ita ta koma part d'in su, koda ta shiga d'akin su ta nufa ba kowa a ciki ta nufi gado ta kwanta ta shiga tunano abubuwan da suka faru a tsakanin su wani lokacin tay murmushi wani lokacin kuma ta yamutsa fuska can zuciyarta ta raya mata wai ko dai son shi take shiyasa take ta tunanin shi haka da sauri ta hau girgiza kai saima ta yunkura ta mik'e ta nufi Parlor.

Wuraren sallar Azahar aka fara zaryar zuwa Asibiti ganin Fatuu, Yadikko tsabar farin ciki kamar ta zuba ruwa a k'asa ta sha, har su Baffan Fatun da Ard'o sai da suka zo gaba d'aya Asibitin saida aka shaida an kwantar da dangin masu Mota don Motoci ne iri iri ke ta sintiri cikin Asibitin, da la'asar Mom da Hajiya da Aunty da gwaggo suka zo, bayan sun shiga d'akin sun duba Fatun Hajiya tace ma Aunty ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login