Showing 384001 words to 387000 words out of 512766 words
Chapter 129 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1671
da zuwa harda Gwaggo ma taje ta gaidata tayi mata sannu da zuwa fuska a sake ta amsa harda yi mata barka, wurin Fatuu gwaggo tazo tace mata taje tayi mata sannu da zuwa a sanyaye tace to ta nufe su tunda ta taho Suke kallon juna ita da Farha har ta tsaya a gaban su cike da fargaba ta gaishe da Hajiya Maryam d'in itama ta sakar mata fuska ta amsa tare da yi mata barka, kallon Farha tayi da d'an murmushi tace mata sannu da zuwa ga mamakinta sai gani tayi ta maido mata da murmushin itama ta amsa mata tare da yi mata barka hakan ba K'aramin dad'i yayi ma Fatuun ba dama ita a rayuwarta bata son taga wani ya ruk'e ta yana fushi da ita, lokacin Fanan suka dawo ganinsu tare da Fatun ba karamin dad'i taji ba nan tace suzo ayi masu hotuna kafin su shiga ciki, sai gashi harda Farha anyi masu, ana gama sallar La'asar Aunty Laila ta kunna Sound system d'in cikin parlon ta k'ure volume kai kace Dj ne aka kira nan fa suka shiga tik'ar rawa harda Fanan dasu Jidderh da alama dai Aunty Laila yar casu ce don sosae ta zage tana rawa su Fauzy dai suna a cikin yan kallo Aunty Mareeya da Feenah dai sun shiga, suna cikin rawar yan uwansu yan Ethiopia suka ba Laila wak'ar yaren su ta kunna masu nan fa aka basu fili kallo ya dawo kansu dama shigar su ta al'ada suka yi gashin su ya bud'e Laila da Jidderh ma da yake sun iya rawar da suke suma sukai joining nasu abun dai sai wanda ya gani gwanin k'ayatarwa cikin yan kallo harda Mom da Hajiya Zainab yadda suke ji an tada masu tsumi kamar su shiga saidai ba dama su Laila nata ce masu wai su zo ayi dasu sai dariya suke.
Alhamdulillah taro ya tashi lafiya an ci an sha anyi nishad'i ba kad'an ba an kuma raba souvenirs abubuwa iri daban daban masu d'auke da sunan jarirai amman ba hoto don Hajiya ta hana Saboda gudun bakin mutane dama shima Haisam bai so, abun dai sai san barka da fatan Allah ya raya Adam da Aliyu. Gaba d'aya Fatuu ta gaji likis haka jariran ma a daddafe tayi wanka bayan Magrib suma aka yi masu tana gama shiryawa tayi shirin kwanciya su Aunty Laila ma abun ba'a magana gaba d'aya sun gaji amman duk da haka suka shiga shirya kayan sunan da aka samu wanda suka zube a k'asa gefen gado kili guda kai kace Fatun k'aton shago zata bud'e don kaya ne aka tara ba yan kad'an ba kama daga manyan atamfofi laces materials kayan jarirai abun ba'a magana don ko Hajiya Maryam trolley guda ta kawo na kayan jarirai tsadaddun gaske da kuma manyan atamfofi guda biyu na Fatuu haka su Hajiya Zainab ma ta kawo had'add'un kaya na jarirai dana Fatun mutane da dama dai duk sun kakkawo kaya sosae harda su Baby gift set suma an tara su da yawa wasu had'addun baskets ne an nad'e su da yan flowers irin dai yadda ake ma kyauta, k'arshe dai wasu saidai nan aka barsu da safe an kimtsa su.
Bayan sallar isha Aunty Mareeya na gama salla jikinta sanye da Hijab ta nufi part d'in Mom don amsa neman da Her Excellency ke mata, lokacin da ta shiga cikin Bedroom d'in da sallama ba kowa a ciki sai su biyu duk suna zaune a saman gado jikinsu sanye da dogayen riguna kowannen su ba kallabi a kan shi suna ruk'e da glass cups mai d'auke da ruwan lemu mai sanyi da gani hira suke suna sha, da murmushi gaba d'ayan su akan fuskokin su suka amsa mata Sallamarta ta nufi gadon, daga gaban gadon ta tsaya tana kallon su don kuwa sun rud'a ta bazata iya gane wacece Her Excellency d'in ba a ciki, Mom ce tace mata sannu da zuwa ta amsa ba tare data gane wacece ba tana d'an murmushi tace masu dama tazo wurin Her Excellency ne daga yanayin yadda tayi Maganar suka fahimci bata gane su ba Hajiya Zainab d'in ce tace mata "Ok, ki ganta" jin haka yasa Aunty tayi tunanin Mom ce tayi Maganar don haka sai ta juya kan Mom da tayi tunanin itace Hajiya Zainab tace "ranki ya dad'e gani na dawo kamar yadda kika ce" kasa daurewa Mom tayi ta saki dariya haka Hajiya Zainab d'in ma yar dariyar tayi ganin haka yasa Aunty Mareeya d'an waro ido tana masu kallon rashin fahimta Mom ta nuna mata Her Excellency tace mata gata nan itace tayi mata Magana, d'an bud'a baki Aunty tay sai kuma ta saki dariya don ta gane wasa da hankalinta tayi, saukkowa daga saman gadon Hajiya Zainab tayi still tana yar dariya hannunta ruk'e da cup d'in lemun tayi ma Aunty Mareeya alamar su je da hannu ta nufi doguwar kujerar cikin d'akin tana bata hakurin abunda tayi mata tace it's just for fun Auntyn ma dariya take tace ai ba komai, zama tayi kan kujerar ganin tayi tsaye tace mata ga wuri nan ta zauna, daga d'an can gefenta Aunty ta zauna ta kai cup d'in hannunta baki tay sipping lemun Aunty nata kallonta a cikin ranta tana raya sai kace ba ita ta haifi Sameer ba don sam jikinta bai nuna hakan ba, d'aura cup d'in tayi saman d'an table dake a gefen kujerar kafin ta juyo suka had'a ido da Aunty a nutse cikin girma ta fara magana "amm, dama ba wani abu bane inason muyi magana ne akan shiryen shiryen biki nasan kun fara ko?" Da sauri Aunty tace mata eh tuni anata yi, jinjina kai tayi taci gaba "Yayi kyau, game da kaya da za'ayi nike son sanar dake ba'a buk'atar komai don shi wanda zata auran ba zaune yake anan ba koda yaushe, zai tafi da ita can ne kuma yana da gida da komai haka anan ma so ko anyi su ba wani amfani da zasu yi don haka sai a barshi ba sai anyi komai ba wani abu na al'ada da komai dai duk a barshi ayi Addu'ar Allah ya tabbatar da Alkhairi" wani irin dad'i ne ya cika Aunty sai dai bata nuna ba sosae kawae dai faffad'an murmushi tayi tace "Ma sha Allah, Mun gode, mun gode kwarae your Excellency Allah ubangiji ya saka da Alkhairi ya k'ara girma da daukaka, hak'ik'a wannan ya tabbatar da ku d'in masu tausayin talakawa ne kuma duk d'aya kuka d'auke mu da ku, irin ku K'asar mu ke buk'ata ina Addu'ar Allah ubangiji yayi maku President ko mun amfana" wata irin dariya Hajiya Zainab tayi ta amsa da "Ameen ya Rabbi, in Alkhairi ne amman yanzu su Sis ne akan layi sai mu taya su da Addu'a" kai Aunty ta jinjina "Allah ya tabbatar da Alkhairi, ai your Excellency duk d'aya kuke wllh in Allah ya baku K'asar nan tamu nasan zamu more don irin ku take buk'ata bama kamar mu talakawa tabbas zamu ji dad'i, in Allah ya basu suna gamawa sai kuma ku dasa Allah ya amince" fad'ad'a dariyar ta Hajiya Zainab tayi tace mata hakan kuwa bazai zama son kai ba Aunty na dariya tace a'a wllh ai dama Ana cewa da yuyuyu gwamma d'aya kwakkwara jinjina kai Hajiya Zainab tayi tace Allah dai ya tabbatar da Alkhairi ya za6a mana Shuwagabanni nagari Aunty ta amsa da Amin, hannu ta kai ta d'aukko lemunta ta kur6a bayan ta cire Cup d'in cikin girmamawa Aunty Mareeya tace mata ko zata iya kiran Mahaifiyarsu su gaisa ta jinjina mata kai tace eh lafiya lou ai tuni ma yakamata ace sunyi hakan to ita abubuwane ke mata yawa don ko ita Daughter Fauziyya basu ta6a Magana ba sai yau, kiran Maman tasu ta shiga yi bayan ta d'auka suka gaisa ta tambayi ya Abuja da masu jego tace mata duk suna lafiya nan ta sanar mata dama zasu gaisa da Her Excellency ne, cikin alamun rashin fahimta Maman tasu ta tambayi wacece nan ta sanar mata Mahaifiyar wanda Fauziyya zata aura ai tana jin hakan ta yunk'ura dama a kwance take ta tashi zaune ta shiga daidaita zamanta Aunty Mareeya ta k'ara cewa in sun gaisa sai tayi mata godiya don tace ba sai anyi ma Fauziyya komai ba na kayan d'aki, jin hakan yasa Maman tasu kai hannu ta rufe baki alamar Al'ajabi, bayan ta ba Hajiya Zainab wayar cike da girmamawa Maman tasu ta shiga gaishe da ita duk da kuwa ta girmeta nesa ba kusa ba itama Hajiya Zainab a mutunce take gaisawa da ita, sosae Maman tasu tayi mata godiya da kuma Addu'oi fuskarta da murmushi take amsawa, bayan sun gama wayar ne tace ma Aunty Mareeya Shikenan zata iya tafiya in kuma da wani abu sai tayi magana tace mata ba komai wllh ta k'ara mata godiya har zata tashi sai kuma ta dakata cikin yar ina ina tace don Allah in ba damuwa ko zata bata lambar ta don a rink'a gaisawa tace sure bari ta bata ta amshi wayar tata ta rubuta mata daga haka sukai sallama, wurin gadon Aunty ta nufa don tayi ma Mom sallama, da murmushi Mom tace mata har an gama tattaunawar Aunty tace mata eh sai kuma tace "Don Allah Mom a k'ara taya mu godiya wurin Her Excellency tace ba sai anyi ma Fauziyya komai ba naji dad'i wllh Allah ya k'ara maku girma da d'aukaka" tana murmushi ta amsa da Amin tace mata ai ba wani abu bane duk an zama d'aya tayi Addu'ar Allah ya bar zumunci Aunty ta amsa da Amin kafin tayi mata sallama ta tafi.
Tana fitowa baya ta tsaya ta shiga kiran Fauziyya, bayan ta d'aga tambayar ta tayi tana ina tace tana a inda suka sauka har ta kwanta ma tace to ta fito waje ta sameta tace to, bada jimawa ba Fauziyyar ta fito tana sanye da kayan bacci riga da wando sai hula a saman kanta, nufo Aunty tayi gabanta har d'an fad'uwa yake don tasan da Maganar cewa Hajiya Zainab na son ganin Auntyn tasan kuma bai wuce game da hakan yasa Auntyn kiranta, tana k'arasawa gabanta kawai sai gani tayi ta rungumota cike da Farinciki take fad'in "Fauziyya ki taya mu murna ance ba sai anyi maki komai ba wllh iya ke suke buk'ata, da sauri Fauzy ta d'ago daga jikinta ta waro ido da tsananin mamaki ta maimaita abunda Auntyn ta fad'a cikin washe baki tace mata Wallahi kuwa yanzun nan ta dawo daga wurin Hajiya Zainab din, nan ta shiga fad'i mata yadda suka tattauna harda gaisawar da sukai da Maman su ta shiga yabonta tana fad'in tana da kirki sosae tayi dacen suruka, shiru Fauzy tay ba baki sai murmushi kawai da take gaba d'aya ganin abubuwan take tamkar a mafarki,
"Ya naga kin yi shiru ne, ko baki farinciki bane yanzu fa Shikenan Baba ba sai ya sayar da gonakin shi ba hakan kuwa ai abun murna ne" yar dariya Fauzy tay a sanyaye tace "a'a Aunty naji dad'i sosae wllh, kawai abubuwan ne keta ban mamaki wllh duka yaushe akai Maganar gida yanzu kuma ga wannan",
"Ai kinsan haka abun Allah yake lokaci guda yake juya al'amurra, baki ji ana cewa dare d'aya Allah kan yi Bature ba to misalin hakan ne, ai tsakanin mu da Ubangiji wllh sai godiya Yar gidan Hajiya kin tako mana arzuki Allah yasa a wurin bikin wata ma cikin kannanmu ta samo mana wani irin Sameer d'in koma k'anin shi" dariya sosae Fauzy ta saka tana fad'in kai Aunty,
"Allah kuwa ai abun fata ne ke baki ji ana cewa da arzuki a garin wasu ba gara a naku a nakun ma a cikin gidan ku duk da bansan ma ko yana da K'ani babba ba k'ilan kuma wannan da na gani lokacin da suka zo shine ke bi mashi shima dai ai lafiya lou don ya isa Aure naga kamar Nameer yake, amman wannan ma anya zai iya Auren talaka shima naga alamun kamar Sameer d'in yake, koda yake shima Sameer d'in ba gashi ya fad'a komar yar manomi ba" Dariya kawai Fauzy ke yi Aunty ta shiga yin godiya ga Allah tana fad'in wllh har ta rasa ina zata sa kanta don farinciki Allah dai ya nuna masu bikin da rai da lafiya dole taci uwar sabada har ta hango shigar da zatayi, dariya kawai Fauzy ke yi suka nufi komawa part d'in da suka sauka, bayan Fauzy ta koma d'aki zama tayi a bakin gado tayi shiru ba komai take tunani ba face Sameer don a yanzu sosae take jin son shi duk in bata ji Muryar shi ba ko sukai Vedio call bata jin dad'i duk da har yanzu d'in ba wata soyayya suke ba amman ba laifi sun fi yin magana yanzu, ji tayi bazata iya kwanciya batare da taji muryar shi ba ta d'ago wayarta ta shiga kiran shi bayan ta yanke ta zauna tana dakon ya biyo kiran......
95
~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~
.............Bada jimawa ba sai gashi ya kira, bayan tayi picking a hankali ta gaishe shi da tambayar shi ya aiki, har saida ta d'an lumshe ido Jin muryar shi da ya amsa, shiru tayi tama rasa mi zata ce mashi tana hakan taji yace ya Abuja tana d'an murmushi tace lafiya lou yau anyi suna sai kuma tace mashi har ma sun gaisa da Mom d'in shi taji ya furta Ok, shiru sukai can ya k'ara cewa koda wani abu ne ta d'an tura baki shi haka yake duk ta kira shi tana jin shauk'i sai ya wani kama tambayar ta koda wani abu, Ji tayi ya k'ara cewa inda wani abu ta fad'a mashi ta d'an kara tura baki sai kuma a hankali tace "No, babu komai dama kawai na kira ne in ji mur....." Kasa k'arasawa tayi ta d'an waro ido don bata ta6a ce mashi hakan ba,
"ina jin ki" taji ya fad'i hakan, abu ta had'iya kamar ta canza abunda ta fad'an wata zuciyar ta shiga k'arfafa mata gwuiwa ta fad'i mashi hakan, "Dama naji ina son jin voice en ka ne" wani kalan murmushin gefe yay taji yace mi voice en nashi gare shi, d'an Farfar tayi da ido da k'yar ta furta mashi "Yana da dad'in sauraro ne" shiru taji yayi har saida gabanta ya d'an fadi don tasan shi wani lokacin ba'a cika yi mashi gwaninta ba, tambayar ta yay tana ina ne ta bashi amsa da tana a d'akin da suka sauka ya k'ara tambayar ita da waye tace su biyu ne kuma d'ayar bata kaiga shigowa ba taji ya furta Ok suyi Vedio call tace to, lokacin daya maida kiran na gani yana kwance a saman gado yau ma robe ce a jikinshi chest d'in shi a bud'e ya tashi zaune tare da jingina da headboard, bin juna sukai da kallo Fauzy nata mashi d'an murmushi shima yanayin fuskar shi kaman zai murmushin, ganin yanayin idanun shi a lumshe kaman mai jin bacci yasa tace "ko bacci kake ne?" saida ya k'ara lumshe su sannan ya d'an girgiza mata kai,
"Naga kaman har ka kwanta" ta k'ara fad'a idanunta cikin nashi yay d'an shiru can ya bata amsa da ya gaji ne yayi tafiya bai dad'e daya dawo ba ta jinjina mashi kai kafin tace "to bari in bar ka ka huta" wani kallo yay mata ya d'an shigar da lip d'in shi na k'asa kafin taji yace har ta gama sauraron muryan nashi ne, yar dariya tayi ta girgiza mashi kai alamar a'a sai kuma tace "to ai kai baka magana sosae" d'an yamutsa baki yay yace mata bai iya bane ta gyad'a kai ta k'ara cewa "in kana so sai in koya maka" murmushin gefen baki yay tare da girgiza kai yace yafi jin dad'in hakan tunda hakan ya sa6a nan ma kai ta gyad'a mashi suka k'ara yin shiru suna kallon juna,
"A gida kake ne ko hotel?" shiru kaman bazai bata amsa ba taji yace da wani abu ne ta tambaya da sauri ta girgiza mashi kai "hakanan kawai na tambaya" ta bashi amsa, ce mata yay yana a gidan shi ne ta gyad'a kai sai kuma ta k'ara cewa "kuma kai kad'ai kake zaune?",
"Zan zauna da wa?" Ya fad'a, tana murmushi tace "a'a dama ina nufin kai kad'ai ne ba wani wanda ke taya ka zama?" shirun dai yay yana bin ta da ido sai can yace mata yakamata ya samu abokin zama ne tace "kawai naga in kai kad'ai ne kaman kad'aici zai dame ka shiyasa nayi tunanin ko akwai wani da kuke zaune tare" lumshe ido yay tare da d'an girgiza mata kai alamar a'a sai kuma taji yace "akwai wata da zata zo" har saida gaban Fauzy ya fad'i da alamun rashin fahimta tace mashi wata zata zo nan ta zauna ya d'aga mata kai alamar eh, wani irin abu taji ya tokare mata k'irji a zuciyarta ta shiga raya kenan mata suke zuwa suna kwana tare dashi kuma a haka ace bai neman su cab, wani bangaren na zuciyar ta ya raya mata kika san wacece ko yar uwar shi ce, kasa daurewa tayi yana ta kallon ta yanayin fuskarta ya d'an canza tace mashi ita wadda zata zo d'in yar uwar shi ce kawai sai gani tayi ya girgiza mata kai alamar a'a yace kawai zata zo su zauna tare ne ya rage loneliness, abu Fauzy ta had'iya yanayin fuskar ta ya k'ara sauyawa ta koma kallon gefe tana d'an kikkafta idanu, "Any problem?" taji ya fad'i hakan ta juyo suka had'a ido wani irin abu mai zafi take ji a ranta ta bishi da kallo yanayin fuskar ta kaman zata saka kuka, d'age mata gira yay ya k'ara tambayar da matsala ne a sanyaye ta d'aga mashi kai yace miye matsalan to, ce mashi tay kawai taga ya zai kawo wata su zauna bayan ba muharramarshi bace ai yasan hakan ba kyau