Showing 504001 words to 507000 words out of 512766 words
Chapter 169 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1595
mamaki taja ta tsaya a gabansu ido waje ta furta "Wow! what a surprised!!" hannu Fanan ta miƙo mata ta nufesu tana washe baki, a saman jikinta ta ɗaurata gaba ɗaya ta ruɗe sai faman tambayar su Dad ake ma Birthday take, saida Adam ya nuna mata rubutun jikin cake ɗin sannan ta fahimci mi ake, a tare gaba ɗaya suka kama ma Haisam ɗin hannu suka yanka cake Jidderh nata masu Video, bayan an yanka kowa ya ɗauka ya bashi a baki kafin shima ya basu har shafa mashi icing ɗin jiki sukai a fuska suna ta dariyar farinciki daga baya Fanan ta kama hannunshi da turanci tayi mashi kalami masu tsuma zuciya kan muhimmancin shi a wajenta da kuma yadda take son shi ƙarshe tayi mashi godiya da Addu'oi, bayan ta gama Fatuu ma tayi suma su Esha saida sukai mashi abun dai gwanin burgewa daga baya aka shiga yin hotuna, harda music Fanan ta kunna aikuwa Esha ba ƙaramin cashewa tayi ba sosae taba mutane dariya, sosae Haisam ya yaba da abunda sukai mashi shima saidai yay masu kalamai kan yadda suke a wurinshi saida aka kira sallar Magrib suka gama.
A cikin satin akaita zuwa ganin sabon gidan da yi masu Allah yasa Alkhairi har Laila ma tazo daga Kano ita da mijinta da yaranta biyu don ta ƙara haihuwa, ranar Friday su Gwaggo suka zo da Kawu Amadu da Tk da kuma matansu sai yaransu don dukkansu sun ƙara haihuwa ita matar Tk mace ta ƙara haihuwa itama Haulat mace ce mai sunan Gwaggo wato Khadija, zuwan nasu yasa Fatuu ta ƙara zuwa Abujar kowa saida ya jinjina haɗuwar gidan akai masu Allah yasa Alkhairi da Addu'oi, a yadda suka shirya zasu bi Gwaggo ne apartment ɗin da take zama in tazo amman Fatuu ta hana tace anan zasu kwana harda gwaggon tunda ai don su suka zo, ƙarshe dai anan suka kwana don Haisam da Fanan duk sun saka baki kan su kwana anan, Washe gari Asabar bayan sunyi lafiyayyan breakfast suka shirya fita harda su Fanan da Fatuu sukai Mota ukku data Fatuu dasu Gwaggo suka zo da ita sai kuma ta Fanan sai wadda Haisam zai hau, Villa suka fara zuwa duk an nuna farincikin zuwansu karma Hajiya sosae tayi murnar ganin su akai masu tarba mai kyau, daga Villa gidan Mino suka wuce zo kaga murna har tana ce ma Gwaggo amman dai bazata koma ba har ta haihu ko Gwaggon na dariya tace a'a abunda da saura amman zata kwana biyu in ta haihun ta dawo, da ƙyar ta barsu suka tafi harda roƙonsu kan su dawo su kwana anan suka ce to ƙilan su dawo, daga nan gidan Aysha aka wuce itama taji daɗin ganinsu har ta kasa rufe baki gashi tayi masu lafiyayyan abinci don tasan da zuwan nasu, bayan gidan Aysha gidan Kamalu aka nufa nan ma dai sun nuna farincikin zuwan nasu hannu bibbiyu Farha ta kar6e su Babynsu har ta girma tubarkallah, gaba ɗaya ko ina roƙonsu ake kan su kwana ƙarshe saidai rabawa sukai Haulat da Husnah suka koma gidan Mino Tk da Amadu kuma gidan Kamalu zasu kwana Gwaggo kuma gidan Aysha sai dare su Fatuu suka koma gida,
Washe gari gaba ɗaya suka koma gidansu Fatuu a yadda suka shirya tare da ita zasu tafi Zaria su kwana washe gari Monday da safe sai su wuce Gwaggo dai anan zata tsaya sai ta kwana biyu,
Kwance tashi cikin Mino ya shiga wata na tara lokacin watan su Fatuu ɗaya da komawa sabon gida kuma Fatun na gida don sun samu hutu, tun ranar litinin ta fara yin naƙuda tsaitsaye zuwa washegari talata ciwo ya kankama amman koda aka kaita asibiti sai aka ce da saura su dawo gida taita yin exercise, kan kace mi duk ta fita hayyacinta dama abu ga sabon shiga tuni ido ya raina fata sai murƙususun azaba take har zuwa Fatuu tay ta dubata itama taga da saura ɗin haka tay ta ƙarfafa mata gwuiwa har tana ce mata kodai dama bata yin exercise da cikin ya tsufa cikin ciwo tace wllh tana yi, sai dare Fatuu ta koma gida Nameer ya dasa yin jinyar, wuraren ƙarfe sha biyu ba arziƙi ya kwasheta suka koma asibitin, wannan karon an kwantar da ita a vip wato ɗaki na musamman ita kaɗai ce aciki duk da haka an faɗi ma Nameer cewa da sauran lokaci, koda Fatuu ta kira taji ya jikinta Nameer ne ya sanar mata sun dawo asibiti an kwantar da ita amman ance still da saura tana jin haka tace gata nan zuwa, bayan zuwanta Asibitin Auntynsu Nameer ma tazo, shiru shiru ba haihuwa gashi ga dukkan alamu tana cikin azaba wasa wasa sai gashi har asuba bata haihu ba lokacin ta gama jigata ƙarfinta ya ƙare, gari na wayewa Aunty ta bada umarnin ayi mata Cs, sosae hankalin Nameer ya tashi jin zancen aikin amman ba yadda ya iya haka ya saka hannu, Wuraren ƙarfe tara na safe aka shiga da ita ɗakin tiyatar lokacin duk yan uwa sun zo harda Mom, Aysha ma tazo sai kuka take ana ce mata tayi mata Addu'a, ita kanta Fatuu hankalinta a tashe yake ƙarfin hali kawai take tana ta yi mata Addu'oi, bayan kamar minti ashirin da shiga da ita sai ga likitan ya fito yana ta murmushi ya sanar dasu tama haihu da kanta ba'a riga anyi aikin ba, zo kaga murna Aysha har da tsalle sai ga mai kuka ta koma yin dariya Fatuu da Nameer harda sujjadar godiya ga Allah sukai, lokacin da aka fito da Babyn wanda namiji ne baka jin komai daga bakunansu sai tubarkallah ma sha Allah Babyn kyakkyawan gaske gashi ƙato, daga baya itama Mino aka fito da ita saman gado baiwar Allah har an saka mata rigar aiki, bayan an canza mata ɗaki duk aka shiga ana mata ya jiki da barka, su Mino an ɗanɗana tun a asibitin ta rinƙa faɗin ta gama haihuwa aikuwa mi Fatuu zatayi in ba dariya ba tace wasa take ai yanzu ma ta fara sai gata harda kukanta sha6e sha6e tana ta rantsuwar ita Allah ta gama, da yamma aka sallameta ganin lafiyarta lau suka koma gidanta aka cigaba da zaman jego har ranar suna tazo yaro yaci sunan mahaifinsu Fatuu wato Muhammad aikuwa ba ƙaramin farinciki su Fatuu sukai ba, bayan suna da kwana ukku ta koma Yola acan zatayi wanka kamar yadda ta buƙata a wurin Nameer.
Bayan sati biyu da haihuwar Mino ranar Alhamis lokacin hutun su Fatuu na gab da ƙarewa tana kwance saman gado da safe wurin ƙarfe sha biyu na rana jikinta sanye da turkish dress riga da wando kalar Yellow gyalen kayan na daga can gefe hakan ya bayyanar da kanta da akai ma kitson sunan Mino sati ɗaya daya wuce, tana cikin yin baccin Esha ta shigo ɗakin da gudu koda ta hangota kwance sai ta nufi gadon, hayewa tay ta fara bubbuga jikin Fatuu tana faɗin "Aunty, wake up!, wake up pls!! ki tashi" yanayin yadda take Maganar kamar zata saka kuka, buɗe ido Fatun tayi ganin Esha ce ke tashinta yasa ta tamke fuska da alamun 6acin rai ta furta "Esha! Why do you always disturb my sleep for God's sake! Banda dama in kwanta sai kin tashe ni kuma bada wani dalili ba kawai baki so ki ganni a kwance!" yamutsa fuska Esha ɗin ta shiga yi idanunta suka ciko da ƙwalla, a fusace Fatun ta ƙara cewa "yanzu da kika zo kina buguna haka miye zan maki??" cikin karyayyar murya Esha ɗin tace "Ba Momy ne bata lafiya ba kuma tayi amai da kuka" waro ido Fatun tay ta maimaita "amai da kuka!" da sauri ta jinjina mata kai aikuwa ba shiri ta wuntsilo daga saman gadon ko ta kan gyalen kayan bata bi ba ta nufi hanyar ƙopa Esha data saukko itama tabi bayanta da sauri, lokacin data shiga Bedroom ɗin Fanan kwance ta sameta a saman gado rabin jikinta lullu6e da duvet sai nishi take su twins sun sakata tsakiya fuskokinsu duk ƙwalla, a ruɗe Fatuu ta nufi bakin gadon ta zauna tare da kai hannu ta ta6a fuskarta tana tambayarta mike damunta haka, cikin nishi tace mata tunda ta tashi bata jin daɗin jikinta haka ta rinƙa daurewa har sukai breakfast to bayan sun gama ta dawo ɗaki taji zuciyanta ta fara tashi daga baya kuma sai amai yazo mata bayan tayi ne zazza6i da ciwon kai suka rufeta tana haka su twins suka zo yanzu ma bata daɗe data ƙara yin aman ba gashi harda juwa take ji shiyasa tasa a kira mata ita ganin ciwon na gaba, cike da damuwa Fatuu tace ai da tun da taji bata lafiya tasa aka kirata, wayar Fanan ɗin ta ɗauka ta kira Haisam bayan ya ɗauka cikin tashin hankali ta sanar mashi da halin da Fanan take ciki Shima hankalinshi ya tashi ba kamar daya ga lafiya lou suka yi breakfast, ce mata yay ko ta kaita Asibitin Villa tunda yafi Kusa zai iskesu yayi wasu baƙi ne daga Lagos amman bada jimawa ba zai sallamesu yazo duk yadda ake ciki pls ta sanar mashi da sauri tace to, suna gama wayar Mom ɗin shi ya kira ya sanar mata tace bari ta kirasu, bayan ta kira wayar Fanan ɗin Fatuu ta ɗauka ta tambayi yanayin jikin Fanan ɗin da damuwa Fatun tace to gata nan da gani dai tana jin jiki tana tunanin fever ce ke damunta Mom ɗin tace Ok su taho nan sai a dubata, dama Fanan ɗin a shirye take don duk sunyi wankan safe gyale Fatuu ta ɗaukko mata itama ta ɗauki wani cikin nata ta yafa, a tare harda su twins suka kamo Fanan ɗin yaran duk sun shiga damuwa gwanin tausayi, a Motar Fanan suka tafi, bayan sun isa Mom ta tarbesu aka wuce da ita Asibitin, suna zuwa kwantar da ita akai a ɗaya daga cikin lafiyayyun dakunan da ake kwantar da marasa lafiya da suka danganci gidan gwamnatin tarayyar, tambayoyi likitan daya kar6eta ya shiga yi mata tana bashi amsa ciki harda rabonta da period ta bashi amsa da tayi last Month sai wannan watan ne bata kaiga yi ba amman dama wani lokacin tana fita daga wata sannan har tsallaken wata ma tana yi nan tayi mashi bayanin lalurar data yi a baya amman tace mashi ta samu sauƙi, lokacin da ake mata tambayoyin Mom ta kira Hajiya Maryam ta sanar mata ga Fanan an kawo ba lafiya nan take hankalinta ya tashi ta shiga tambayar abunda ya sameta Mom ɗin tace ba'asan taƙamaimai ba amman gashi nan likita na bincikawa tace to gata nan zuwa, jininta aka ɗiba aka tafi yi mata gwaje gwaje, ba'a jima ba Hajiya Maryam ta ƙaraso tana ganin yanayin jikin Fanan ɗin a ruɗe ta hau tambayarta abunda ke damunta Fatuu dake zaune a wurin kanta tayi mata bayanin yadda ciwon ya fara sam ba wanda ya kawo komai a ranshi Mom tace su jira likita yazo ya faɗi sakamakon gwaje gwajen, bayan wani ɗan lokaci Hajiya Maryam ɗin ta miƙe tace bari dai tabi bayan likitan don ta ƙagara taji mike damunta haka, tana niyyar fita likitan ya sako kai da sallama taja gefe, yana shigowa ta hau tambayar shi mike damunta ne fuskarshi ɗauke da murmushi yace ta kwantar da hankalinta abun farinciki ne, su Mom na jin haka duk suka miƙe suka nufo shi, tambayarshi Hajiya Maryam ta sake yi miye abun farincikin yace sakamakon gwajin ciki da akai mata ya bayyana tana ɗauke da ciki na tsawon sati ukku, yadda kasan wutar jikinsu ta ɗauke gaba ɗaya bin shi sukai da ido ba mai ko ƙwakkwaran motsi shi kuma likitan sai murmushi yake,
"Wait Dr, wai abunda kake son faɗi mana shine kana nufin ita Fanan ɗin ke ɗauke da ciki?" da tsananin mamaki Hajiya Maryam ta tambaya cikin girmamawa yace mata eh haka sakamakon ya nuna tana dashi na sati ukku yay maganar tare da miƙo mata wata farar takarda da aka naɗe, har saura kaɗan ta saki wayarta dake a hannunta wurin rawar hannun ta amsa, bayan ta buɗe Mom da Fatuu suma suka shiga dubawa nan idonsu ya tabbatar masu, da tsananin farinciki suka shiga washe baki Fatuu harda sa hannu guda ta rufe bakinta alamar mamaki, nan fa aka shiga yin murna su Esha harda tsalle suna faɗin Momy is pregnant zata haifa masu baby Allah ya amshi addu'ar su, nan fa aka fara kiraye kirayen waya ana ma yan'uwa albishir, ko ban faɗa ba ansan dole ai tsananin farincikin samun cikin, Mom ce ta kira Haisam lokacin ma yana kan hanyar zuwa tayi mashi albishir to shima dai ba ƙaramin mamaki da murna yay ba , kan kace mi ɗakin ya cika har Hajiya tazo da Farha anata farinciki, kyautar miliyan guda Hajiya Maryam tayi ma likitan daya faɗi masu zancen cikin Haisam ma ya ƙara mashi wata miliyan guda ɗin kakar likita ta yanke saƙa har ya rasa irin godiyar da zai yi, Mom na dariya tace to ai itama yakamata a bata kyautar tunda ita ta kirata ta sanar mata zancen ciwon duk akai dariya Hajiya Maryam ɗin tana dariya tace to ta bata kyautar Mota duk akai shewar murna, Mom nata dariya tace ita ta yafe Doughter yakamata a ba kyautar tunda ita ta kawota asibitin Hajiya Maryam ɗin tace to ta ba Fatun Motar, da sauri Fatuu tace a'a ta barta ai duk abun farincikin nasu ne Hajiya Maryam ɗin tace ta riga ta bata in bata so sai ta bayar, Esha na jin haka ta ruƙe ƙugu tace to ai suma tare dasu aka kawo Momyn a basu kyautar, hannu Hajiya maryam ta kai ta ɗan ja kumatunta tace ta faɗi abunda duk take so da sauri tace stroller take so da zata rinƙa tura baby aikuwa mi za'ai in ba dariya ba Hajiya Maryam ɗin tace an gama in ma guda goma take so zata siya mata ta juya kam Adam tace shi mi yake so yace kayan wasa da zai rinƙa yima Baby wasa harda Mota da zasu rinƙa shiga tare suna zagaye gida tace to shima za'a siya mashi, juyawa tay kan Abie da yayi shiru kai kace babu shi a wurin tana dariya tace "kai kuma miskilin mu mi kake so?" shiru yay yana bin ta da idanunshi da suke a ɗan lumshe duk da idanun nasu manya ne amman wani lokacin sai su lumshesu kamar dai yadda na Haisam ke yi, shiru yay bai tanka mata ba duk idanunsu na akan shi ana son aji mi zai ce don Magana mugun wuya take mashi wannan da alama ma sai yafi Haisam miskilanci dama ance wai kyawun magaji ya zarta, ganin baida niyyar magana yasa tace mashi in fa bai faɗi mi yake so ba to in aka haiho Babyn saidai ya rinƙa kallonshi do n baza'a bashi ba ya ɗauka balle har ya yi mashi wasa, ana jin abunda tace su Mom suka ce mashi ya faɗi mata ko so yake su Esha su rinƙa ɗaukar baby suna mashi wasa banda shi, a hankali ya fara motsa baki kafin da ƙyar cikin sanyayyar muryarshi ya furta Water Bottle yake so da zai rinƙa ba Babyn ruwa aikuwa mi za'ai in ba dariya ba har Haisam saida yayi dariyar Hajiya dake zaune tace ai shine Water Bottle ɗin aka ƙara yin dariyar, Fatuu dake zaune gefen Fanan ta lura da ita kamar bata farincikin samun cikin don ko uffan bata ce ba duk abun nan tana kwance sai ɗan murmushi da take in anyi abun dariya hakan yasa ta dafata tace "Aunty Fanan ya naga kamar baki farincikin samun cikin ko jikinne?" wannan Maganar da tayi ce ta maido hankulan yan ɗakin kan su Hajiya Maryam tace itama ta lura don ta ɗauka jin zancen cikin zai sa ma ta wartsake, ganin duk sun zuba mata ido yasa tayi ɗan faffaɗan murmushi tace tana farinciki mana saidai ita a wurinta already tana da yara so bata jin wannan kamar a cikinta na farko, gaba ɗaya Maganar tayi masu daɗi Hajiya dake murmushi tace gaskiya ne Maganarta, Auntyn su Haisam ce tace ya kamata a barta ta huta sun zo suna ta surutu a kanta Mom tace abun farinciki ne ya samu dole ayi murna, tambayar likita Aunty tay in ba wata matsala zasu tafi da ita ta huta sosae yace eh lafiya lou zai bata magunguna saboda zazza6i da ciwon kan sai kuma na amai da take, bayan sun koma cikin Villa a ɗaki daban ta kwanta aka kawo mata abinci da ƙyar ta ɗan ci bayan ta gama Fatuu ta bata magunguna tasha ta buƙaci yin wanka Fatuu ta taimaka mata, bayan tayi wanka kwanciya tayi nan da nan bacci ya ɗauketa, a ranar iyalan cikin farinciki suka kasance koda aka sanar da Laila itama tayi murna har tana cewa wannan dole tazo ta dubata, Fatuu nata so ta sanar ma Gwaggo saidai ta baro wayarta a gida, anan suka wuni sai bayan Magrib suka shirya komawa gida Hajiya Maryam tace ma Fanan ita mi zai hana ta tsaya ta ɗan kwana biyu tunda ba sanin irin yanayin tayi ba zata fi samun kulawa anan tana murmushi tace ai sister Fatuu ta sani zata kula da ita tunda tana cikin hutu dole tayi shiru amman ba don taso Fanan ɗin ta tafi ba a lokacin, bayan sunyi sallama da kowa Haisam ya ɗaukko su a jigunannar Jeep ɗin shi da bai daɗe da siyanta ba ita kuma Motar Fanan aka barta anan, saida Hajiya Maryam ta rakasu bayan sun isa gidan haka tay ta faman faɗi ma Fanan ɗin abubuwan da zata kiyaye gudun kada cikin ya samu matsala tace ma Haisam aiki ma ta daina zuwa ta ɗauki hutu har zuwa ta ƙara warwarewa yace Ok, ta ƙara cewa abinci ma asata ta rinƙa ci akai akai koda tana amayar dashi wani zai tsaya nan ma yace mata to