Showing 357001 words to 360000 words out of 512766 words

Chapter 120 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1672

kirji ta nufi gaban dressing mirror, shaf shaf ta d'an yi yar light makeup bayan ta gama ta nufi wurin kayanta dake a cikin Wardrobe d'in bango, bata tsaya ruwan ido ba ta yanke ta saka jallabiyar da Fatuu ta bata dama sau d'aya ta ta6a saka ta da zasu je shopping dasu Hanif, bayan ta saka gaban mirror ta koma cikin sauri ta gyara fakin din gashinta sannan ta shiga nad'a gyalen rigar, sosae tayi mata kyau dama itama tasan tana mata kyaun shiyasa ta saka ta, takalma half cover da yar karamar side bag duk bak'ak'e ta saka saida ta gama shiryawa ta tuna bata fad'i ma Aunty zancen fitar ba, wayarta ta fiddo don ta kirata sanin Abban Hanif na nan, a cikin parlor suka had'e da ita bayan ta sanar mata ta waya tana ganinta ta hau yin murmushi tana fad'in kaga Matar d'an Governor, tambayar ta tayi amman dai yaci Abincin ko tace eh kowanne saida tasa ya ci duk da bada yawa ya ci ba Auntyn tace "yayi kyau hakan ma lafiya lou tunda dai ya ci kwalliya ta biya kudin sabulu, yanzu sai government House kenan your excellency?" Yar dariya Fauzy tay tace mata eh haka yace tace Ok sai sun dawo, saida ta rakota har bakin kopar parlon tana k'ara koya mata yadda zata rink'a mashi tace ta gaida mata da iyalan Governor, yana a d'an kishingid'e idanunshi a lumshe ta shigo cikin Motar bayan driver ya bud'e mata, slowly ya bud'e idon nashi ya sauke su akanta da murmushi tayi mashi sannu tace Allah yasa dai bata bar shi yana ta jira ba shiru kaman bazai tanka mata ba can ya d'an gyara zama yace kaman haka, saida driver d'in ya tambayi umarni kafin yaja Motar, suna cikin tafiyar idon Fauzy a gefe ba zato taji ya kawo hannu ya kamo nata hannun wani irin d'umi taji ya ratsa nata hannun taushin hannun shi kuwa ba sai an fad'a ba, kallon shi tay idanun shi na akanta da kai yay mata alama ta matso, shiru tay kaman bazata matsa ba sai kuma ta d'an matsa da kanshi ya k'ara matso da ita ya rungumeta ta gefe wani iri Fauzy ta ji don tasan hakan bai dace ba tunda ba d'aura masu aure akai ba bai kamata suna had'a jiki ba, shiru tay kanta na a saman kafad'ar shi haka hannunta guda daya fara ruk'owa har lokacin yana a ruk'e dashi tay lamo ta kasa yin wani yunk'uri na raba jikinta da nashi, bayan sun isa Government House d'in baza ido Fauzy tay tana k'are ma ko ina kallo ta yadda baza'a ga k'auyancin ta ba, lokacin data ganta gata ga first lady wadda k'awar Mom d'in Sameer ce mamaki da dad'i ne suka cikata don abu ne da bata taba zaton zai faru ba a rayuwar ta, cikin faram faram ta tarbeta bayan sun gama gaisawa fuska a sake ta d'an yi mata tambayoyi da suka shafeta Fauzyn na amsa mata Sameer na zaune akan d'aya daga cikin lafiyayyun kujerun da suke zaune daga baya ya mik'e ya nufi ciki Fauzyn na kallon shi har ya 6ace ma ganinta tayin Abinci First Lady tayi mata tace gashi can a table tana murmushi tace mata wllh a koshe take ta gyad'a kai, d'akin yaranta ta kai Fauzyn wai tafi sakewa yan mata biyu ne ta gani a d'akin d'aya zata yi sa'ar ta d'ayar kuma zata d'an girme ta, gaba d'ayan su daka kallesu zaka gane hutu ya zauna masu a jikinsu ga fatar su har wani shek'i take duk da ba farare bane can amman kuma baza'a kira su da bak'ak'e ba gaba d'aya k'ananun kaya ne a jikin su, sosae suka sake ma Fauzy babbar na d'an tambayar ta game da ita da yadda suka had'u da Sameer muryarta gwanin dad'i a gayance take magana, tun dai Fauzy bata saki jiki ba har ta saki suka shiga yin hira sosae anan ita babbar take ce mata gaskiya tayi dacen miji don Sameer k'arshe ne a komai amman ita bazata iya auren shi ba har saida Fauzy ta d'an ji mamaki ta kasa hak'uri ta tambayi dalili cikin yamutsa fuska Ammah tace mata ego d'in shi yayi mata yawa dole matar shi ba k'aramar dawainiya zatayi da shi ba ita kuma hakan ke bata iyawa, shiru Fauzy tayi tana d'an murmushi tasan ba k'arya tayi ba a ranta ta raya to dama Mulki ya had'u da Mulki taya d'aya zai dawainiya da d'aya.

Bayan gama sallar la'asar Sameer ya kirata yace ta same shi a parlor, tare da Ammah suka fito har yayi wanka ya canza kaya zuwa k'ananu sai baza k'amshi yake, Ammah na murmushi tace ma Sameer d'in "sannu bro" kai ya d'aga mata fuskar shi a d'an sake ta k'ara cewa ba dai tafiya zasu yi ba sai lokacin ya bud'a baki yace eh amman zata gaisa da Dad ne hakan yasa tace to suje ta raka su, parlon shi suka nufa lokacin da suka shiga yana zaune tare da First Lady da murmushi ya nuna ma Fauzy wuri yace "have a sit my Daughter" jikin Fauzy har wani tsuma yake yau itace gata ga Governor wanda saidai taga motocin su suna wucewa a hanya da jiniya sai kuma a Tv, cike da girmamawa ta gaishe da shi ya amsa ya tambayi tana lafiya da yan gidan su duk ta amsa mashi, shima dai yan tambayoyi yayi mata yadda bata 6oye ma su First Lady komai ba haka shima ta rink'a bashi amsa yana d'an jinjina kai daga baya ya saka mata Albarka da kuma fatan Allah ya nuna masu bikin, tare suka fito harda First Lady Sameer yace zai je ya dawo tace Ok su d'an jirata a parlon ta, kiran Ammah tayi tabi bayanta bada jimawa ba sosae ta dawo hannunta ruk'e da jakar kwali sai walwali take ta mik'a ma Fauzy tace gashi in ji Mom tana murmushi ta amsa tare da yin godiya sosae tace tayi mata godiya pls, har zasu tafi tace ta bata digit d'in ta zasu rink'a gaisawa Fauzyn tace to, bayan ta amsa sukai sallama ta juya ta nufi part d'in su, sosae Fauzy ta jinjina kirkin su sam basu da ji da kai har gara ma k'anwar tata itama ta fahimci bata da yawan magana ne ba wai ji da kai ba, Motar da suka zo ita suka hau saidai yanzu Sameer d'in ne zai tuk'a ta ba driver ba, bayan sun hau hanya ne taji yace tay leading nashi gidan Haisam tace to, ita ke nuna mashi hanya tana cikin haka ta tambayi bai ta6a zuwa bane farko shiru ya d'an yi idon shi akan hanya ta juya ta kalle shi suka had'a ido ta cikin mirror kafin ya kauda lokacin ya bata amsa da sau biyu ya ta6a zuwa Katsina Saboda baida business a cikinta d'an murmushi tay kawai sai kuma ta k'ara cewa amman ai ga grandmother d'in Ya Haisam a garin ya d'an d'age gira ba tare da ya kalleta ba ya bata amsa da ai shine dalilin da yasa yazo sau biyun ko. Lokacin da suka isa gidan Hajiya Fatuu na a part d'in sosae tayi farinciki ganin su tare ji take tamkar ta zuba ruwa a k'asa tasha ganin burin su dai ya tabbata, sosae Hajiya taji dad'in zuwan nashi bayan sun gaisa ta tambayi yan gidan su ya amsa mata daga baya tace wato da ya manta da ita tunda yaushe rabon da ya zo gidan tun suna karatun degree d'in su na farko da suka zo da Haisam sai yanzu dalilin zai mata kishiya ta samu ya sake ziyartar ta, murmushi yay jin abunda tace ba tare daya ce komai ba, koda tayi mashi Maganar Abinci cewa yayi ya k'oshi Hajiyar tace dama tunda Amarya ta cika shi da kayan dad'i ya zai iya cin Abincin tsohuwar mata duk suka d'an yi murmushi harda shi, kiran sallar Magrib da aka fara yasa shi mik'ewa don yaje Masallaci suma duk suka tashi don suje su yi, visitor room wanda yanzu ya koma kamar d'akin Fatun anan take komai taja Fauzy, bayan sun gama sallar cikin washe baki Fatuu ta shiga nuna ma Fauzy irin farincikin da ta ji nan ta shiga bata labarin yadda yasa ta kwaso kayanta daga hostel Fatun nata dariya tana fad'in yayi daidai, harda yadda suka samu Abincin da suka tarbe shi ta fad'i mata tace amman dai Aunty tayi dubara sosae daga baya Fauzy ta koma magana akan cikinta tana fad'in wllh tausayi take bata Fatun na yar dariya tace ai yana gab da zuwa kanta lokacin ita ta sauke sai itama ta rink'a tausaya mata ta d'an ta6e baki can kuma tace "waya ga su Fauzy da ciki alankoso kenan, ai na tabbatar sai kin fini juriya Zarah" Fatuu na dariya tace itama dole zata koyi juriyar in lokacin yayi, anan Mino ta iske Fauzy suka gaisa harda tambayar ta Angonta Nameer tana murmushi tace mata yana Makaranta, anan sukai sallar isha bayan Sameer ya dawo daga Masallaci ya kira Fauzy yace ko zai barta anan ne tace mashi a'a yace Ok ta fito yana parlor, tare suka fito su ukku Fatuu tace bari tay ma Hajiya Magana, bada jimawa ba suka shigo cikin parlon bayan sun zauna Hajiya tace wato dai tafiya zai yi bazai ci Abincin ta ba yana d'an murmushi yace wani lokacin zai ci ta gyad'a kai tace to Allah yasa tana da rabon ganin lokacin don bata sa ran nan kusa ba shi dai d'an murmushi kawai yake, su Fatuu ne suka yo mata rakiya suna zuwa bakin entrance tace mata ta koma ta girgiza mata kai tana murmushi tace suje ta raka ta ai duk cikin exercise ne, bayan sun fito cikin harabar Sameer na daga gaban su a nutse yake tafiya duk idanun su na akan shi k'asa da murya Fatuu tace wllh ganin Sameer yasa taji maraicin mijinta duk suka d'an yi dariya, bud'e Motar yayi ya shiga bayan ya k'arasa inda take suma suka karaso Fauzy tayi masu sallama tace ma Fatuu sai sun had'u School gobe, tana shiga cikin Motar ya bata rafar kud'i guda ukku yace ta ba Fatuu ta kai ma Hajiya ya k'ara bata wasu guda biyu yace ta ba Fatuu, fitowa tay har sun nufi komawa ciki ta tsaida su taje ta bata kudin, saida suka dawo tayi mashi godiya sannan suka tafi Fauzy ta shiga yaja suka tafi. Bayan sun baro gidan gari suka shiga yana driving da hannu d'aya yana latsa wayar shi da d'ayan hannun can taji ya furta Katsina K'aramin gari ne ba wurare masu kyau da mutum zai je yay having fun, ita dai shiru tayi mashi a ranta ta raya tunda dama ya saba zuwa had'add'un wurare harda su club ai dole ya fad'i haka, sai daga baya ta fahimci wayar da take latsawa yana searching wurare ne, bayan wani lokaci suka k'araso wani babban wuri kamar dai Eatery ne Kusan shine wurin cin Abinci daya fi kowanne girma da kawatuwa a garin Fauzy tasan wurin sai dae bata ta6a zuwa ba Saboda ba'a dad'e da bud'e shi ba yan Makarantar su dai na zuwa da samarin su, bayan ya parker jingina yay da kujerar ita dai Fauzy nata kallon wurin, bada jimawa ba wasu ma'aikatan wurin guda biyu suka fito hannuwan su ruk'e da ledoji suka nufo wurin parking d'in, horn Sameer d'in ya latsa hakan yasa suka nufo Motar tasu suka tsaya daga bakin kopar driver d'in slowly glass d'in ya d'an sauka ma'aikatan suka gaishe shi tare da yi mashi barka da zuwa yadda ya amsa ba lalle ma in sun ji ba yace masu su saka a seat d'in baya, bayan sun saka d'aya ya dawo gaban yace mashi ansa ya jinjina mashi kai har zai juya ya dakatar da shi, kud'i ya mik'a mashi masu yawa nan take ya hau washe baki yana godiya don ya gane kyauta ce yayi masu Saboda ya biya kud'in abubuwan da ya siya ta online d'ayan ma ya matso yayi godiyar, bayan barowar su wurin direct gida ya nufa da ita yace ta rink'a nuna mashi hanya da zata maida su tace to, a k'opar gidan ya parker bayan sun k'araso ta juya tana kallon shi, shiru sukai na d'an wani lokaci can taji yace mata gobe zai wuce in akwae wani abu ta fad'i mashi, shiru ta d'an yi kafin tace da wuri haka kaman bazai bata amsa ba yace to wani abu zai tsaya yi tay shiru kawai,

"You can go, zamu yi magana" ya fad'a tare da yi mata nuni da baya yace ta d'auki abubuwan da aka je, d'an jimm tay akwae Maganar da take son yi mashi amman tana jin shakkar yinta saidai tana ganin yakamata tayi mashi ita, kaman ya lura da tana son yin magana yace mata inda wani abu yana jin ta, saida ta tattaro karfin hali sannan murya na d'an rawa ta fara magana,

"D...dama akwae abunda nike son tambayar ka ne.....Ina so ka fahimce ni don Allah...." shiru tay tana jiran taji mi zai ce idonta akan shi taji yace yana sauraron ta, ci gaba tayi "dama akan aurena da zaka yi ne, nasan ba wani abu a tsakanin mu sai kawai naji Maganar aure kuma bacin bamu ta6a haka da kai ba...to shine nike son in tambaye ka miyasa zaka Aure ni tunda baka ta6a nuna kana...so na ba" da k'yar ta k'arasa Maganar da in ina tare da d'an nishi duk a lokaci guda, maida idon shi yay ya koma kallon gaban shi ta kafe shi da ido tana son gane yanayin fuskar shi da yake akwae haske sosae a layin ya d'an haska cikin Motar, sun d'an d'auki lokaci kafin taji ya furta "why did you ask me that?" Yay tambayar tare da Kallon ta, abu ta had'iya a Sanyaye tace "kawai hakanan ne inason in sani Saboda nayi mamakin hakan" tana rufe baki yace bata yarda dashi ba kenan da sauri tace "a'a wllh...kawai dai kai ne ka ta6a ce man kar in rink'a bada yarda gaba d'aya to shiyasa nike son in ji dalilin da yasa kake son aure na" kauda idon shi yay daga barin kallon ta sannan ya furta shima bai sani ba hakanan zai aure ta, tsit kake ji wani iri Fauzy take ji a cikin ranta hakan da ya fad'a, kallon ta yay daidai lokacin itama ta d'ago ido ta kalle shi calmly ya ce in tana ganin hakan bai mata ba lokaci bai k'ure ba za'a iya fasawa ai, tun kafin ya rufe baki k'irjinta ya hau bugun uku uku hannunta ya fara d'an rawa, kafeta yay da ido alamar amsarta yake jira ta fara motsa baki da k'yar cikin rashin dad'in rai ta furta "Shikenan, in hakan yayi maka nima yayi man" tana k'arasa Maganar da sauri ta sunkuyar da kanta jin k'walla sun fara tarun mata a cikin idanunta sam ba haka ta so taji daga gare shi ba a ranta ta raya Mujaheed yayi tarayya da ita don tana burgeshi shi k'ilan ma tasan koma burge shi d'in bata yi, kallon shi tay bayan tayi kokarin maida kwallar ta d'an k'ak'alo murmushi tace "Nagode Allah ya saka da Alkhairi Allah kuma ya maida ka lafiya" jinjina mata kai yayi tace mashi saida safe bin ta da ido kawai yay ya d'an yi jimm can ta juya ta kai hannu zata bud'e kopar..,

"I will marry u because....i love you Fauziyyah" kaman saukan aradu haka taji Maganar ta sauka akanta, da sauri ta juyo tana kallon shi idon shi na akanta amman sai ka rantse ba shi yay Maganar ba don Kalmar k'arshe daya furta kalma ce mai matuk'ar tsada a wurin shi in ba Mom d'in shi ba ba wadda ya ta6a fad'i ma hakan duk da uban matan dake rok'on shi kan ya furta masu hakan, d'an murmushi tay ta fara motsa baki cikin yar in ina tace "are you telling the truth?" wani irin lumshe ido yay duk da acikin duhu ne ta gani ta d'an hasken cikin Motar, dad'i ne ya kama Fauzy har bata san lokacin data ce mashi don Allah ba don taji dad'i ya fad'i hakan ba, d'an ta6e baki yay yace dama mutum na auren wanda baya so ne, murmushi kawai Fauzy ke saki tace mashi ta gode in sha Allahu zata zame mashi mata ta gari wadda zata bashi Farin ciki na har abada tana ganin d'an murmushin gefen da yayi, sai faman k'ayataccen murmushi take gaba d'aya dad'i ya cikata don abunda take fata ne ya kasance yana son ta, ce mata yayi taje sai sunyi magana tace to, har zata juya taji yace haka yakamata su rabu dakatawa tayi ta maido idonta kan shi ko da bai fito ya fad'i ba ta gane yadda yake nufin yakamata su yi bankwana, shiru tayi a cikin ranta tana raya gaskiya bai kamata tana biye mashi ba tunda hakan ba kyau kuma in dai tana son ta hana shi hakan dole ta fara ta kan su, cikin yar rawar murya tace "k...kayi hak'uri naga bamu kai ga yin aure bane ina tsoron mu samu zunubi....kuma hakan na iya shafar rayuwar Auren mu don naji anata wa'azi akan hakan" shiru yay still idanun shi na akan ta sai kame kame take can taji yace ta tafi wani iri taji sai taga kaman yayi fushi ne zata so ace tayi mashi abunda zai faranta mashi ba kamar da shima yanzu yay mata abunda ya saka ta farinciki amman tasan hakan shi yafi masu Alkhairi, a sanyaye ta furta mashi "Gud nyt" kai ya d'an jinjina mata kafin yace karta manta da abun baya daga yadda ya furta Maganar bazata iya gane yanayin da yake ciki ba. Lokacin data shiga cikin gidan a parlor ta iske Aunty Mareeya da su Hanif tana yi masu Assignment, da sallama ta shiga suka taso da gudu suna

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login