Showing 234001 words to 237000 words out of 512766 words

Chapter 79 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1599

ba, kuma duk abunda take so ma kanta ni ma ta so man....." Kuka ne ya taho mata da sauri tasa hannu ta rufe idanunta a rud'e gwaggo ta hau lallashinta kafin ta juya kan Fatuu ta fara mata Nasiha can ta maida Maganar da harshen fulatanci ta ce mata kar ta sake ta canza mata ta rink'a kyautata mata sosae samun abokiyar zama irinta a yanzu zai matuk'ar wahala idan ma tayi mata wani abu da bata ji dad'i ba ita ta fad'i mata zata bata shawara, haka tay mata fad'a sosae Fatun nata k'walla tana d'aga mata kai, daga baya ta had'a su gaba d'aya tayi masu Nasiha, sosae tayi ma Fanan godiya da Addu'oi tana ta amsawa a hankali, ce masu tayi bari ta zuba masu dambun su kai ma Hajiya, lokacin data zubo ta fito har sun fito tsakar gida Mino ma ta fito daga cikin d'akin Fatuu na da yanzu ita ce a ciki, har waje bakin shagon Amadu suka rako su Fatuu ta amshi kular dambun Amadu ma ya fito sukai sallama cike da nuna jin dad'i, jikin gwaggo ba K'aramin sanyi yay ba sai dai kuma yanzu hankalin ta ya fara kwanciya sosae.

Bayan sun koma gidan part d'in Hajiya suka wuce, lokacin da suka shiga ba kowa a cikin parlon dama Hajiya sai tayi sallar isha take fitowa, d'akin da Fanan d'in ta sauka suka wuce bayan Fatuu ta je Kitchen ta aje dambun, yar hira suka shiga yi suna haka aka kira sallar isha. Bayan sun gama sallar Parlor suka fito suka zauna suna yin kallo, basu dad'e da zama ba Hajiya ta fito ta nufo cikin parlon, bayan ta zauna gaba d'aya suka gaishe da ita ta amsa tace masu an dawo ya Dijen, amsa mata sukai da tana lafiya tana gaishe da ita Fanan ta sanar da ita an bada dambu ma a kawo mata tace dambu Dijen tayi kenan aikuwa zata ci don ta kwana biyu bata ci shi ba, Fanan tace ita aka mawa, jinjina kai Hajiya tayi tana murmushi tace lallai Dije na ji da ita, Fatuu ma murmushi take ta mik'e don ta d'aukko mata, A plate ta zubo mata ta sako mata spoon ta dawo cikin parlon, tana niyyar d'aurawa saman sofa table ta kinkimo mata shi Hajiyar tace mata ta barshi ta bata, tambayarta tayi lemun da zata d'aukko tace ta bata ruwa kawae, juyawa tay ta koma hanyar Dining don ta d'aukko, sosae taji dad'in dambun tana ta yabawa Fanan na yar dariya tana fad'in kodai santi take, suna haka Haisam ya shigo cikin parlon hannuwan shi ruk'e da manyan ledoji, kusan a tare Fanan da Fatuu suka mik'e suka nufe shi kowa ya amshi leda guda tare da yi mashi sannu da zuwa yana murmushi ya amsa, Hajiya na yar dariya tace sun hutar da ita ita Uwargida duk sukai yar dariya, bud'e wadda Fanan ta amsa tayi taga su ice cream ne da snacks ta hannun Fatuu kuma Fruit ne, ce ma Fatuu tay taje ta zubo a plate sai ta taho da wasu a zuba snacks d'in ta amsa da to tana niyyar juyawa suka had'a ido da Haisam ya lumshe mata idanu tay d'an murmushi kawae ta wuce, bayan ta dawo kowa aka zuba mashi su shawarma suka d'auki ice cream Hajiya tace bazata sha shi ba Fanan d'in tace mata to akwae Fura a bata tace eh, k'arshe dai basu ci Abincin dare ba don duk sun k'oshi da abubuwan daga baya wurin k'arfe goma Haisam da Fatuu sukai masu sallama Fanan harda yi masu rakiya bakin k'opa bayan sun tafi ta dawo.


Washe gari tun da Fatuu ta tashi take jin ta wani iri sanin yau Haisam d'in zasu tafi Lagos duk tayi wani sukuku da ita, Lokacin da zai kaita Makaranta bayan sun aje Mino sun wuce ganin yanayin ta yasa ya kai hannu ya kamo hannunta ya tambayi mike damunta ta d'an girgiza mashi kai kawai alamar ba komai, shiru yay kawai don ya fahimci dalilin canzawar tata yaci gaba da driving squeezing her hand lovingly. Bayan sun tashi ya d'aukko su saida aka aje Mino gida sannan suka wuce, Abinci suka fara ci kafin suka shiga faranta ran junansu, tare sukai wanka bayan sun fito ya fara taimaka mata ta shirya cikin doguwar riga kafin shima ya fara shiryawa tana zaune a bakin gado tana kallon shi, bayan ya gama shafe shafen jikin shi sanye da bathrobe ya nufo inda take zaune, zama yay daga gefenta cike da nuna damuwa ya kai hannu ya ruk'o hannunta yana ce mata karta damu kanta haka sosae is just 2 days ai zai dawo shima ba son tafiya yake ya barta ba shiyasa ma tun farkon yace a jira sai bata da test to kuma tace kusan kullum zasu yi gashi ya riga yace ma Fanan d'in zasu je tare, kuka ta saka mashi dama dannewa take ta yi, hannu ya kai ya jawo ta jikin shi, sosae ya shiga rarrashinta yana nuna mata ai zasu rink'a yin Vedio call kafin ya dawo, sai kace yana zugata sai k'ara sautin kukan take gaba d'aya ta fara rikita shi a da ma bai son kukan ta balle kuma yanzu, haka yay ta aikin rarrashi cikin salon k'auna, har aka kira la'asar suna abu d'aya k'arshe dai sai a d'aki yayi Sallah tare da ita bayan ya samu tayi shiru sai sakin ajiyar zuciya take, bayan sun gama ya fara shiryawa cikin shadda light blue itama d'aukko mata riga da skirt na atampa yay don doguwar rigar jikinta duk ta yamutse, kusan a tare suka sa kayan ya taimaka mata, bayan an gama saka kayan gaban dressing mirror suka nufa da kanshi ya shafa mata powder yanata mata murmushi itama tana d'an maida mashi, jambaki ya d'aukko zai shafa mata ta tare hannun ta d'an girgiza mashi kai yace bata so a hankali tace mashi bashi ba, yace Ok wanne ta nuna mashi lip glow ya d'aukko ya shafa mata, kai fuskar shi wurin tata yay ta d'aga ido ta kalle kawai sai gani tai ya kai bakin shi ya manna ma lips d'in ta kiss, yana d'agowa taga ya gogi lip glow d'in hakan yasa ta saki faffad'an murmushi, yar dariya yay dama so yake yaga ta saki fuskar yasa yayi mata hakan tunawa da yadda sukai na jambaki, bayan ya gama yi mata komai kama hannunta yay suka nufi bakin gado shi ya fara zama ya d'aurata akan laps d'in shi idon su cikin na juna, da d'an murmushi yace "za'a rakani Airport?" shiru tay ta kafeshi da ido sai da taga ya d'age mata gira alamar amsa yake jira sannan murya a disashe tace "kana so?" Lumshe mata ido yay ta d'aga ma shi kai alamar to, hannuwan shi ya kai ya rungumota jikin shi ya duk'a da kanshi saitin nata whispering in to her ear ya furta "promise me bazaki k'ara kukan ba har in dawo?" jimm tay ta kasa cewa tayi alk'awarin don ita kanta kawae ji taje kukan na zuwa, k'ara ce mata yay tayi mashi alk'awarin cikin karyayyar murya tace "ai shine ke zuwa da kan shi" k'ara matseta yay yace Ok amman ta daure ta daina yi hankalin shi ba zai kwanta ba in ya tafi ya barta tana kukan ta d'aga mashi kai alamar to, shiru suka d'an yi ha6arshi a saman kanta can taji yace mi take so ya siyo mata, d'an girgiza mashi kai tayi alamar ba komai yace bai yarda ba kullum sai tace ba abunda take so yanzu dai ta fad'a komi take so zai kawo mata,

murya a disashe tace mashi da gaske ba abunda take so kawai sai ji tay yace "Ok I will buy you a teddy bear" ba shiri ta d'ago ta kalle shi da alamun mamaki akan fuskar ta, idanun shi a d'an lumshe yana d'an murmushi ganin kallon da take mashi ya d'age gira yace "or a Barbie doll wanne kike so ko duka?" tura mashi baki tay a shagwabe tace "to ni k'aramar yarinya ce da zaka siyo man wannan" still idanunshi a lumshe suke ya furta "Yes u'r my baby",

murmushi tayi tace "to ni ban son su in ma abun wasan zaka siyo man to kan ka zaka siyo man" yana murmushi yace shi ai ta riga da ta mallake shi tuni, itama murmushin take tace to tana jira ya dawo sai tayi wasan da shi shine teddy d'in nata sukai yar dariya, wayarshi ce ta fara ringing ta sauka daga jikin shi tace bari ta d'aukko mashi, wurin mirror taje ta d'aukko ba tare data duba mai kiran ba ta kai mashi, sunan Fanan ya gani alamar ita ke kira bayan yayi picking ba tare da ya bari tayi magana ba yace gashi nan fitowa yanzu, yana gama wayar ya mik'e tana tsaye daga gefe ya kama hannunta suka nufi Wardrobe, bayan ya fiddo mata gyale da kan shi ya yafa mata shi suka tafi bai d'auki komai na kayan shi ba anan abunda ya ke son d'auka d'azun ya d'aukko a G.r.a da ya aje ta school harda jakar computer d'in shi, koda suka zo shiga harabar gidan ba yadda bata yi ba ya sake mata hannu amman ya k'iya haka da suka zo shiga part d'in Hajiya ma k'in sakin hannun yay suka shiga haka duk kunya ta kamata, a cikin parlon suka samu Hajiyar da Fanan ta shirya dama shi kad'ai take jira, zama sukai Fatuu ta gaishe dasu duka shima ya gaisa da Hajiya daga haka suka yi sallama duk suka mik'e don lokaci na neman k'urewa Hajiya na k'ok'arin mik'ewa tayi masu rakiya Haisam d'in yace tayi zaman ta kawae tayi masu Allah ya tsare, a parking space suka iske Tk a gefen Motar da zasu hau, ita da Fanan suka shiga baya shi kuma ya zauna a gaba Tk ya zauna a driver seat bayan ya rufe ya tashi Motar suka fito daga cikin wurin kafin yaja suka tunkari gate.

Ba K'aramin k'ok'ari Fatuu tayi ba wurin hana idanunta zubar da k'walla har suka raka su suka dawo, gaba d'aya jinta take wani iri duk tayi sukuku da ita, suna zuwa kusa da gidan su tace mashi ya ajeta a gidan, lokacin data shiga Mino bata nan tana islamiyya sai gwaggo kawai ta iske a cikin d'akin ta tana zaune a saman gado tana linkin kaya, a saman kujera ta zauna bayan sun gaisa ta tambaye ta daga ina da d'an murmushi ta fad'i mata ta raka su Aunty Fanan ne nan gwaggon tayi masu Allah ya tsare, daga baya tsohon dakinta ta koma ta kwanta tayi lamo tana ta tunanin Masoyinta har Mino ta dawo ta isketa anan, tana a gidan har aka yi sallar isha lokacin har Haisam ya kirata ya sanar da ita sun sauka, bayan sun ci Abinci suka tafi tare da Mino zata taya ta kwana.

Tun bayan da suka sauka Driver d'in gidan su Fanan ne yazo ya d'auke su, lokacin da suka isa gidan kusan ba kowa Hajiya Maryam bata nan ta d'an fita ta dawo haka sauran yara ma basu kaiga dawowa daga Islamic school ba Dad d'in su kuma na Asibiti wurin aiki sai Farha kad'ai tazo tayi masu sannu da zuwa, part d'in da suka saba sauka suka nufa, bayan Fanan ta aje masu kayan su kwanciya sukai don su huta har lokacin Magrib yayi sannan Haisam ya tashi don zuwa Masallaci itama ta tashi tayi sallar, ana gama salla Hajiya Maryam ta dawo, part d'in nasu tazo ganin ba kowa a cikin parlon yasa ta kira Fanan d'in a waya ta sanar mata tana a parlor, fitowa tay da murmushi itama Mom d'in nata d'an murmushin take mata tana zuwa ta rungumeta tana fad'in tayi missing nata itama tace tayi nata, bayan ta d'ago bin ta da ido Mom d'in tayi kaman mai nazarin wani abu can tace mata bata lafiya ne taga idanunta sun fad'a, har saida gaban Fanan ya d'an fad'i, tana murmushin yak'e tace mata tundai halin data shiga ne acan Us na sanin zancen Auren da Haisam d'in yayi a 6oye shiyasata har ta rame, jinjina kai tay cike da gamsuwa ta kama hannunta tace suje part d'in ta, Bedroom d'inta suka wuce suka zauna a bakin gado gaba d'aya ta maida hankalinta akan Fanan d'in ta tambaye ta ya suka k'are da Hajiya to, jimm tay tana tunanin abunda zata ce mata, tasan muddin ta fad'a mata ta amince to tabbas ran kowa sai ya 6aci har Haisam d'in ba k'yale shi zatai ba ita kuma bazata so hakan ba, d'an yamutsa fuska tay tace "Mom ki bari in huta sai mu yi Maganar we didn't arrive long ko Abinci bamu ci ba" wani kallo ta bita dashi tace to miyasa basu ci Abincin ba bacin already table a shirye yake tace mata sun bari su huta ne kuma basu jin yunwa sosae, tambayar ta Haisam tay tace yaje Masallaci daga baya gudun karta matsa mata kan Maganar ta mik'e tana fad'in bari taga in ya dawo sai su ci Abincin ta nufi hanyar fita Mom d'in ta bita da ido, tana komawa part d'in su ta shige Bedroom tay kwanciyarta a ranta tana raya ko zata fad'i mata sai Haisam ya bar gidan,

sai bayan sallar isha ya dawo Fanan tace mashi suje suci Abinci, kusan gaba d'aya suka ci Abincin harda Farha da Hajiya Maryam da ba laifi ta sakar mashi fuska da suka gaisa, sai can wurin k'arfe goma na daren Dad d'in su ya dawo har part d'in nasu yazo suka gaisa Fanan ta rungume shi tana mashi shagwa6ar tayi missing nashi sosae shima yana fad'i mata yayi nata Haisam dai sai murmushi yake daga baya ya tafi, tun daga lokacin Fanan ta fara zille ma Mom d'in nata bata bari su zauna tare su dad'e don karta yi mata zancen, Sosae Haisam yake k'ok'arin faranta mata duk suka kasance tare, haka Fatuu ma yana yawan kiranta a waya tay ta zuba mashi shagwa6a,

Ranar Alhamis da yamma ya shirya zai koma saidae a ranar da safe Mom d'in shi ta kira shi ta sanar dashi tana son ganin shi yaje Abuja kafin ya koma don tasan yana Lagos d'in, lokacin daya kira Fatuu ya sanar da ita yayi tunanin zata nuna damuwa amman ga mamakin shi bata nuna ba tana murmushi tace mashi ba komai Allah ya dawo dashi lpy sosae yaji dad'i dama duk itace damuwar shi, a ranar da yamma yayi sallama da Hajiya Maryam Fanan ce ta tafi kai shi Airport, ita ke driving Motar yana gefe hannun shi ruk'e da nata, cike da k'auna sukai sallama da shi ta dawo cike da jin kewar mijinta, bayan ta parker Motar a parking space, tana shigowa cikin parlor ta iske Hajiya Maryam zaune da Farha suna kallo a Tv, nufar su tay tana sanye da jallabiya tayi rolling veil ta tsaya a bakin kujerun tay mata sannu tana kallon ta tace har ya tafi tace eh, shiru suka d'an yi kafin ta juya zata tafi d'aki taji muryar ta tace "Wait I want to talk to you" daramm gaban Fanan ya fad'i, dakatawa tayi ta kai idonta akan Mom d'in su ta nuna mata sofa d'in gefen ta tace ta zauna,

"Yanzu dai ai nasan kin huta sosae so am all ears ya kukai da Hajjaju ta amince an saki yarinyar nan?" Shiru Fanan tayi idonta a kan had'add'an carpet d'in k'asan parlon, maimaita mata tambayar tayi sannan ta d'ago ta kalleta gaba d'aya sun kafeta da ido harda Farha itama tana son taji amsar da zata bada, Sigh tay a sanyaye tace mata Hajiya ta k'i amincewa tace tayi hak'uri su zauna tare da ita, tun kan ta k'arasa Hajiya Maryam ta yamutsa fuska tana kallon ta har ta gama sannan cikin d'aga murya tace "You're telling a lie Fanan, daga yanayin face d'in ki nagane ba gaskiya kike fad'a man ba, kar ki manta ni na tsugunna na haife ki, so zan iya gane in kina 6oye man abu, dama tun da kika zo na fara zargin wani abu k'in tsayawa muyi magana ya k'ara k'arfafa zargin nawa, Now tell me the truth, else, ranki zai yi mummunan 6aci!" A fusace tay Maganar, abu Fanan ta had'iya kafin murya na rawa tace Ok zata fad'i mata gaskiyar, nan ta fara fad'i mata yadda sukai da Haisam ya nuna mata in ya saki Yarinyar za'a cuceta ne tunda shi ya fara saninta ya san hakan ne ma yasa Hajiya tun farko ta hana ya saketa, tun kafin ta gama ta katseta da tambayar "sai kika amince yaci gaba da zaman da ita???"

Cikin yar in ina tace mata yayi mata alk'awarin zai masu Adalci kuma daga ita bazai k'ara Auren wata ba shiyasa ta amince don tasan ko sun zo wurin Hajiyar ba amincewa zata yi ba tunda shima ya nuna zai cigaba da zama da ita.....,

Buga hannun kujera Hajiya Maryam tayi tare da mik'ewa tsaye cikin daka tsawa tace "Enough Fanan! I never knew you were such a fool until Today, ba a iya sakarci ko wawanci kika tsaya ba har hankali baki da shi, yanzu ke ashe dama baki da wayau har haka, wato ya zauna yayi maki dad'in baki shine kika hau kika zauna ke gaki shashasha har ki ka kasa gane cewa son yarinyar yake shiyasa ya fake da hakan, in don abunda ya shiga tsakanin su ne ba sadaki ya biya ba to miye abun cuta ko wani cin zali a ciki......!" Sosae take fad'a ta inda take shiga ba tanan take fita ba a k'arshe tace sam bata yarda da amincewar da tayi ba don haka dole ta canza ra'ayi ta nuna mashi bata amince ba, shiru Fanan d'in tayi kanta a k'asa, ganin yadda ta d'auki zafi yasa ta d'ago kai idanunta cike da k'walla tace ma Mom d'in nasu ita gaskiya ta riga ta amince bazata canza ra'ayin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login