Showing 426001 words to 429000 words out of 512766 words

Chapter 143 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1550

gari aka fara program na Laila a Abuja don su zasu yi abubuwa bayan Dinner da walima da za'ayi in aka kawo Mino su zasu yi Ethiopian Night da Arabian, a ranar yan Adamawa suka iso babbar mota guda nan fa gidan gwaggo ya cika kamar yadda Yaya sukai da innar su Altine duk sun kwaso yan matan gidan a nufin su na suma su samu mazaje a dangin su Haisam, zuwa dare gidan har ya fara fita hayyacinshi don ma Yadikko na ɗan tsawatar ma yaran, har bayan isha Fatuu na gidan anata hira su twins tun bayan da aka cika gidan suka fara koke koke sun ƙi yarda a ɗauke su hakan yasa ta kai su wurin Hajiya don yanzu suna yarda da ita kuma Haisam na nan, suna hirar ne ake tambayar Fatuu inda gidan su yake ta faɗi masu ba nisa da an fita ne nan wasu suka ce wai zasu bita suga gidan sai su kwana kan ta basu amsa Gwaggo tace ai Mijinta na nan hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba don ƙarshe tasan mi zai biyo baya in suka bitan, sai wurin ƙarfe goma saura ta baro gidan ta dawo gidan su lokacin data je part ɗin Hajiya ba kowa a cikin parlon hakan yasa ta wuce Bedroom ɗinta, da sallama ta shiga Hajiyar har ta kwanta amman bata yi bacci ba jin sallamarta yasa ta ɗago Fatun ta shiga, nuna mata bakin gado tayi alamar ta zauna, bayan ta zauna ta gaidata ta amsa kafin tace ai tayi tunanin ta dawo tuni gajiya tasa bata shigo ba Fatun tace a'a yan Adamawa suka zo ta tsaya yin hira dasu ne, tambayar yaushe suka iso tayi ta bata amsa da tun ɗazun zuwan nasu ne ma yasa ta aiko dasu twins don suna ta kuka sunga mutane tace "Allah sarki, sun zo lafiya ko?" amsa mata tayi da eh lafiya lou tace to Ma sha Allah, shiru suka ɗan yi kafin Hajiyar tace mata su twins ɗin na wurin babansu ya tafi dasu can part ɗin nasu ta amsa da to, miƙewa tay tayi mata sallama har zata juya Hajiya ta dakatar da ita da faɗin to maimakon ta taho da wasu nan su kwana tunda ga ɗakuna nan ko wanda suka zo ɗin basu da yawa ne ta bata amsa da suna da yawa tace to ai data rago wasu don su samu walwala gidan, shiru tayi bata ce komai ba a ranta tace ita yaushe zata rakito su suzo suyi ba daidai ba kawai sai gani tayi Hajiyar ta kai hannu gefen pillow ta ɗaukko wayarta, kiran layin gwaggo tayi bayan ta ɗaga ta amsa gaisuwar da take mata kafin tace hidima ta fara kankama Gwaggon na murmushi tace eh wllh Hajiyar tayi fatan Allah yasa taron ya tashi lafiya da sauri gwaggo ta amsa da Amin, ce mata tayi Fateema tace waɗanda suka zo da ɗan yawa to ta turo wasu sai su kwana anan ta amsa mata da to don ba damar ta musa mata, bayan sun gama wayar tace ma Fatuu da tayi tsaye sototo shikenan taje ta ƙara yi mata sallama ta juya ta tafi, sam Gwaggo bata so hakan ba duk da za'a samu sauƙin cukowar da aka yi amman tana fargabar tura wasu su kwana can, ƙarshe Yadikko ta kira gefe ta sanar mata ta bada shawarar a tura su Yaya da Mero sai innar su Altine sai kuma in za'a ƙara wasu amman su tana ganin lafiya lou bazasu yi ba daidai ba tunda sunje Abuja sun san wasu abubuwan na yan gayu gwaggo ta ɗauki sha'awararta, bayan anyi masu magana gwaggo taja Mero gefe don tana da natsuwa ta roƙe ta kan kada ta bari ayi ma Hajiyar ba daidai ba tace to suka tafi tare da Gwaggon ta raka su. Ranar Alhamis Mino tayi Friend's Eve anan part ɗin su Fatuu akayi decoration mai kyau a cikin harabar part d'in harda kujeru, cikin kuɗin da Nameer ya turo mata ta ba Aunty mareeya aka yo abubuwan ci da sha harda wanda zata raba, ba laifi kuma ƙawayenta yan makarantar bokon su da islamiyya da na nan cikin unguwa duk sun zo an ci an sha anyi rawa anyi nishaɗi sosae, a ranar bayan Magrib iyayen su maza harda Baffan su suka iso a gidan Hajiya ɗakin Tk aka sauke su shi kuma ya koma ɗakin Kawu Amadu, yan'uwan su Hajiya mata na nan Katsina da Daura duk sun wuce Abuja mazan kuma sun tsaya ɗaurin aure yan Daura ma sai gobe da safe zasu taho nan Katsina har angwayen da dangin su duk sai gobe in Allah ya kaimu zasu taho, da daddare Hajiya ta kira gwaggo take sanar da ita game da ɗaukar Amarya ance mutum biyar ake so su bada don a jirgi za'a tafi da ita tunda tafiyar bata kusa bace sosae hakan yayi ma gwaggo daɗi Hajiya tace da fatan ba'ai masu ba daidai ba da sauri gwaggo tace a'a wllh hakan yayi ai hidiman da yawa hakan ma ba ƙaramin ƙokari akai ba, Maganar sauran kayan ɗakin Minon da akwatunan lefenta gwaggo tayi ma Hajiyar,

"Wane kayan ɗaki kuma suka rage banda uwayen kayan da kuka takura kai kuka yi mata, ai dana san haka zaku yi mata kaya da bazan bari ba to bansan irin kayan da akai mata ba sai da akai kai su ake man magana abu duk ba an zama ɗaya ba sai a kama a matsa ma kai haka" da faɗa faɗa take Maganar Gwaggo na ɗan murmushi ta bata haƙuri tace ba takura ma kai akai ba an samu gudunmawa ne sosae Hajiyar tace "haka dai kika ce tunda ba sanin yadda akai akayi mata kayan nayi ba, yanzu su kayan da suka ragen su minene?" da sauri Gwaggon tace "dama kayan adon ɗaki ne da zasu iya fashewa sai akwatunan sai kuma kayan gara",

fuska a tur6une Hajiyar tace "dawa yace ayi mata wata gara?" shiru gwaggon tayi Hajiyar tace to ba wata garar da za'a ɗauka zata yi Magana yanzu da Senator kan sauran kayan amman kada a sake a kai wasu kayan abinci da sunan gara in kuma ba'a ji Maganarta ba to rai kuwa zai 6aci, Gwaggo na murmushi tace in sha Allahu baza'a kai ba ta bata haƙuri Hajiyar tace ta saurareta yanzu zata yi Magana game da kayan zata kirata cike da girmamawa tace to, bada jimawa ba sai gashi ta sake kiranta ta sanar mata goben in Allah ya kaimu kafin a ɗaura auren za'a turo Mota da zata kwashe sauran kayan in ma akwae wanda zasu bi Motar lafiya lau su wanda zasu tafi ta jirgin sai su fidda su zuwa da safe zata ƙara kira su yi magana, Sosae Gwaggo tayi mata godiya da Addu'oi kafin suyi sallama saida ta jaddada mata kan kada a sake a saka kayan garar nan suyi amfani da abun su Gwaggo na murmushi tace in sha Allah baza'a saka dasu ba suka yi sallama, bayan sun gama wayar dama Gwaggon ware kanta tayi da suna wayar ta shiga tunanin to suwa za'a bada su tafi ta jirgin bata son wani yaga an yi mashi ba daidai ba, tunanin kiran Fatuu suyi shawara tayi dama tana gidan, bayan tazo ne tayi mata bayanin da Hajiya tay game da ɗaukar Minon Fatun tace "ni hakan ma wllh yayi man daɗi dama ji yadda suka kwaso uban mutane kuma nan nufin su duk gaba ɗaya za'a dasu kai Amaryar, kawai mutum biyar ɗin asa Aunty mareeya, Aunty Feenah sai ke sai kuma babbar ƙawar Mino sai cikon ta biyar ɗin asa...." shiru tay tana tunanin wadda za'a sa ta tambayi Gwaggo ko hada Yadikko za'a tace mata a'a ita da take Uwar Amarya tace to wa take ganin za'a sa na biyar ɗin gwaggon tace "sai ke ko, ai baki sa kan ki ba" Fatun tace shikenan hakan yayi da yanayin yar damuwa Gwaggo tace amman hakan baza'ai ma abun wata fahimta ba ace ba dangin Baffan su da kuma Mahaifiyarta Fatuu tace to su kawai sai a saka su a Motar da aka ce suyi gaba Gwaggon tayi ɗan shiru kafin tace ita bata son abunda zai ja rashin fahimta aga tayi ba daidai ba bari dai a kira Yadikko a faɗi mata aji mi zata ce, bayan an kira ta faɗi mata hannu ta kai ta rufe baki kafin ta cire tace mi zai ja a ɗaura yan Adamawa a jirgi ai abun kallo da magana zasu ja gara ayi yadda Fatuu tace ala bashshi su Yaya da Mero da innarta wato Kakar Mino sai Yayarta hansai su sai a ɗaura su a Motar Gwaggo tace tana ganin hakan lafiya lou tace eh in ma wani yayi tsegumi kan hakan sai ace basu da abubuwan da ake buƙata na yin tafiyar dasu a jirgi, hakan da tace yayi ma Gwaggo akan wannan matsayar suka tsaya, sai wurin ƙarfe sha ɗaya da rabi Fatuu ta koma gida direct part ɗinta ta wuce ba kowa a parlon ta wuce Bedroom, lokacin data tura ƙopar ta shiga a saman gado ta hango haisam yayi shigar bacci haka su twins ma ya saka masu kayan baccinsu da alama ma har wanka yayi masu Abie na a saman ƙirjin shi yana bacci Grandpa kuma na a ta gefen shi ya rungumo shi jikinshi da hannun shi guda gaba ɗayan su bacci suke yadda sukai kwanciyar abun gwanin burgewa, ta ɗan ɗauki lokaci tana ta kallonsu tana sakin murmushi kafin ta nufi hanyar laudary, after some minutes ta fito ɗaure da towel da ƙaramin towel tana goge jikinta kanta yasha kitso da Mero tayi mata ɗazun, press ta nufa ta fiddo kayan baccin da zata saka Nursing pajamas, bayan ta gama sawa gaban mirror ta nufa tana kallon kitson da aka mata yar yar sosae taga yayi mata kyau ko don bata saba yi bane, mai da take shafawa da daddare ta shafa harda na tafin hannu da yatsu sannan ta goga roll-on bayan ta gama ta feffeshe jikinta da turarurruka masu sanyin ƙamshi, wurin gadon ta nufa saida ta gyara ma twins nasu gadon kafin ta kai hannu a hankali don kada ta tada Haisam ta ɗauko Abie ta kai shi saman gadon shi, tana ƙoƙarin daukar Grandpa Haisam ɗin ya buɗe ido slowly suka sauka kanta ta sakar mashi murmushi tare da kashe mashi ido shima yay mata murmushin, shima Adam gadon shi ta kai shi ta juyo tana ce ma Haisam sun ci Abinci ne taga har ta kwantar dasu ba wanda ya farka ya lumshe mata ido kafin a hankali yace ya basu kafin suyi bacci yana gama Maganar ta faɗa jikin shi tana faɗin thank you Daddy wai a madadin su twins ɗin ya ƙara faɗaɗa murmushin shi, bin juna sukai da kallo kowa fuskarshi da annuri can yace yadda ta kwantan baza tayi hurting kan ta ba tace ai bata danne cikin sosae ba ya lumshe ido, tambayarta yay ya hidima tace anata yi gaba ɗaya a gajiye take don ma Gwaggo na hanata aiki sosae ya jinjina kai kafin ya kai hannu ya fara shafa kitsonta ya furta yayi kyau ta furta thanks tare da lumshe mashi ido irin yadda yake, yana ɗaya daga cikin abunda take so tattare dashi kenan duk in kayi abunda ke buƙatar yabawa sai ya ya6a sa6anin da yawan wasu mazajen basu iya yaba ma matan su in suka yi kwalliya ko wani ado wasu har sai matan sun tanka sun ce wai baka ga nayi abu kaza ba sannan in an ci sa'a yace yayi kyau wani kuwa saidai yace shi bai ma lura ba irin hakan kaman cin fuska ne ace kana tare da mace a wuri guda amman tayi abu kace wai baka lura ba shiyasa da yawan matan basu yin adon akai akai tunda wanda suke yi domin su basu yabawa sai waɗanda ya zamar ma jiki ne sun saba suke cigaba da yi koda mazan basu yabawa, Maza yakamata su gyara yaba kwalliyar mace nasa taji daɗi ta ƙara ƙaimi wurin yi akai akai sannan yana ƙara soyayya don ita mace abu kaɗan kesa a siye zuciyarta, sauketa yay daga jikin shi yace mata yana zuwa ta ɗaga mashi kai, toilet ya nufa yana shiga wayar Fatuu ta fara ringing har saida gabanta ya ɗan faɗi ta raya wake kiranta a wannan lokacin sha biyu har ta wuce, saukkowa tayi ta nufi gaban dressing mirror inda wayar take har lokacin ringing take ta kai hannu ta ɗaukko tana duba mai kiran ta saki murmushi ganin Fauziyya ce,

"Ƙawata Amarya ko kun iso ne?" ta fada bayan ta ɗaga daga can ɗayan bangaren Fauzy ta bata amsa da eh yanzun nan suka sauka Abuja, cikin nuna farinciki Fatuu tayi mata anzo lafiya ta amsa ta sake tambayar Nasarawa zasu wuce tace mata a'a gidan su na Abuja zasu tsaya don gobe yana son zuwa ɗaurin aure dasu Daddyn Haisam Fatun tace suma goben zasu haɗu kenan in suka kawo amarya harda cewa ta ƙagara taga yadda ta koma Yaya Sameer ya iya kiwo Fauzyn tay yar dariya mai sauti daga baya sukai sallama, aje wayar tayi ta juya zata koma gado lokacin Haisam ya buɗe ƙopar laundry ya fito ta juya ta nufe shi suna haɗuwa ya rungumeta tana kallon fuskar shi da murmushi ta faɗi mashi Fauzy ce ta kirata ta sanar mata sun sauka Abuja yanzu ya jinjina kai kafin yace sun yi waya da Sameer kafin su taho, ɗaukarta yay ya nufi gado da ita tana ta dariya tana faɗin wai sai yaushe zai fara jin nauyin ta yay murmushi kawai, bayan ya kwantar da ita mikewa yay ya kunna lamp ta side ɗin da yake kafin ya nufi wurin Switch ya kashe hasken ɗakin ya dawo gadon ya fara mata tausa cikin salon ƙauna tana ta lumshe ido tare da yaba abunda yake matan sun ɗan ɗauki lokaci yana mata massage ɗin kafin ya fara canza salo tana ganin haka itama ta fara bashi nata salon daga haka suka lula wata duniya da ma'aurata ke zuwa.

FRIDAY

Alhamdulillah Allah ya kawo mu ranar ɗaurin aure, ana tashi aka shiga yin hidima ba kama hannun yaro, tunda safe jirgin yan ɗaurin aure ya sauka daga nan gidan su na G.R.A suka wuce kafin lokacin ɗaura auren yayi, suna isa gidan ango Nameer ya kira amaryar tashi ya sanar mata gasu sun iso yana son yaga fuskar kyakkyawar amaryarshi ta sanar mashi tana gidan Hajiya part ɗin su Adda Fatuu yace Ok gashi nan zuwa, yan Abuja basu daɗe da zuwa ba suma 6angaren angon Laila convoy ɗin su ya iso daga Kano, jerin danƙara danƙaran motoci ne masu numfarfashi tare da na security a gaba da baya da yake wanda zata auran wato bashir ɗan sanannan mai kuɗi ne a Nigeria, a Vip na haɗadɗan hotel Hillside Royal Suites suka sauka kafin lokacin ɗaura auren yayi, tunda wuri Aunty Mareeya ta taho gidan bikin saida ta biya ta ɗaukko Feenah kamar yadda sukai da ita, bayan isowarsu aka shiga yin aiki ba kama hannun yaro don ma Abincin wasu ba anan za'ai ba abunda za'ai a nan gidan kaɗan ne, ganin yadda Fatuu ke ta kujiba kujiba yasa aka fara mata magana kan ta rinƙa hutawa saboda halin da take ciki sai lokacin wasu da yawa suka san da ciki gareta har Haulat da Feenah basu gane ciki gareta ba duk an zata ƙibar da ta ƙara ne yasa ta ɗan yi tumbi, wuraren ƙarfe sha ɗaya Hajiya ta kira Gwaggo tace a fiddo da sauran kayan Minon ga wanda zai ɗauka nan yazo Gwaggo tace to ta sanar da ita akwae wanda zasu bisun sannan akwatunan na nan part ɗin su Fatuu aka maido su bari tayi mata magana sai tazo a fiddo su Hajiyar tace to ayi ma mutanen magana su fito kar a 6ata lokaci don tafiyar bata kusa bace, suna gama wayar tayi ma su Yaya da sauran wanda Yadikko tace aje dasu magana dama tun jiya ta sanar masu zasu tafi da safe, zo kaga rawar jiki wurin Yaya anji zanjen tafiya Abuja ita kuwa innarsu Altine kamar zata saka kuka tsabar takaici ita bama don yaran yan matan da suka kwaso da baza'a tafi dasu ba ita kanta da bazata ba yasa ta shiga matsananciyar damuwa sai faman roƙon a tafi da ita take Gwaggo tace ta bari aga Motar inda wuri sai ta bi su, cikin sa'a sai gashi Motar yar babba ce mai seat ukku a boot da bayan Motar aka saka akwatunan da kwalayen sauran kayan ba'asa kayan gara ko ɗaya ba tunda Hajiya ta hana, a layin tsakiya Mutum huɗu suka zauna harda innar su Altine data kasa rufe baki don murnar za'a da ita a gaba Mero ta zauna wasu harda cewa ai za'a iya ƙara mutum guda a gaban Driver ɗin yace a'a zai takura a bar mutum ɗaya yayi, Altine na tsaye bakin ƙopar Motar harda ƙwallarta tana roƙon aje da ita don Allah kofa da bikin Fatuu ba'a je dasu ba, daga cikin Motar innarsu ta wurgo mata harara tace ina za'a je da ita ra6e ra6e da Y'ay'a ko an gaya mata Abujar ruga ce Gwaggo ce ta rarrasheta tace tayi haƙuri watarana zasu je ko in Minon ta haihu fuska a yamutse tace ai ana iya ƙin zuwa da ita Gwaggon tace in sha Allahu in Allah ya kaisu lokacin ita zata sa aje da ita sannan ta ɗan kwantar da hankalinta, har Driver zai tada Motar Fatuu ta nufo Motar da yar sassarfa tana ruƙe da hannun ƙanwar su Aysha ganin tana ɗaga hannu yasa aka yi mashi magana ya dakata, bayan ta ƙaraso roƙon shi tay kan a bari ta zauna a gaban jikin inna mero da yake yasan wacece Fatun cikin kwantar da murya yace abunda yake gani Abuja ba

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login