Showing 114001 words to 117000 words out of 512766 words
Chapter 39 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1626
ma ba mai yawa bane ke zuba yanzu a hankali zai d'auke, in kuma kun fi so ayi mata D&C d'in to wani lokacin yana taimakawa wurin k'ara conceiving da wuri amman dama ciki k'asa da 10 weeks ba dole sai an yi ba indai ba wata matsala haka" Wani kallo Abbas yay ma Haisam cike da shak'iyanci yace "H,Zakee ina ganin ayi matan ko Saboda ai saurin k'ara samun wanin" banza yay ma shi cikin cool voice d'in shi yace ma Dr shikenan ba sai anyi ba ya gode yana fad'in hakan ya mik'e Abbas ma ya tashi yana mashi dariyar iskanci shima Dr Habeeb d'in mik'ewa yay yana yin dariyar don daga baya Abbas yay mashi bayani game da auran da yadda aka samu cikin, saida ya rako su bakin Office d'in yace tayi duk abunda zata yi bada jimawa ba zai zo ya sa mata jinin Haisam ya amsa da Ok kafin suka tafi, Bayan su Fatuu sun koma kan kujera Feenah tasa ta zauna don taci Abinci cikin wanda ta kawo mata ta zubo mata tace ma Fauzy itama ta zuba tana murmushi tace to, tasa Fatuu gaba tay wai sai ta ci shi sosae Abdul ma na gefen ta yana fad'in taci ta k'oshi ta warke su tafi gida tare tay yar dariya suna haka Hajiya ta shigo harda Saude ruk'e da k'aton Basket din kayan Abinci da kuma Tk, Feenah ta mik'e taba Hajiyar wuri don ta zauna, bayan ta zauna idon ta akan Fatuu ta kai hannu ta dafa kafad'ar ta tace "Sannu Fateema kin ji an ja maki jinyar dole" d'an murmushi kawai Fatuu tay ta gaisheta bayan ta amsa taci gaba "an gode ma Allah daya tashi kafad'un ki, jiyan nan ai hankali na ya tashi sosae wllh yarinya tamkar ba rai ga uban jini da kika zubda, to ya jikin naki yanzu?" tana d'an murmushi tace da Sauk'i sosae Hajiya tace "to Alhamdulillah Allah ya k'aro sauk'in, su Dije sun auna Arziki don da wani abu ya same ki duk sai nayi k'arar su an bi maki hakk'in ki wllh duk da haka ba k'yale su zan ba" kowa yay murmushi su Sauden sukai mata ya jiki ta amsa masu ana haka gwaggo ta shigo cikin d'akin d'auke da plastic chairs guda biyu ta aje tace ma Saude su zauna, bayan sun zauna duk suka gaishe da ita Sukae mata ya mai jiki ta amsa masu dama ta gaisa da Hajiya tun a waje tana ta tura baki ta amsa mata, lokacin Abbas da Haisam suka shigo Hajiya ta bisu da wani wani kallo fuska a tsuke Abbas ne kawae ya gaishe da ita ta amsa mashi ba yabo ba fallasa ya kalli gwaggo yay mata bayanin da Dr yayi game da scanning d'in yace ba sai anyi Mata wankin cikin ba taci gaba da shan magani gwaggon tace to in sha Allah Hajiya tace "ai gwara dae kada ayi matan a kyaleta da wahalan da aka d'ora mata ba sai an k'ara mata wata Azabar ba" kowa dae murmushi kawae yake banda Haisam dake tsaye can ya juya zai fita Abbas yabi bayan shi,
Sai da akayi la'asar Abbas ya kira Feenah ta fito su tafi lokacin an k'ara sama Fatuu jinin Abdul yasa rigimar bazai tafi ba shi anan zai tsaya dama da yaga za'a saka mata jinin harda kukan shi da kyar gwaggo ta lalla6a shi tace Asibitin ba'a barin yara su zauna da an ganshi za'a zo a tafi dashi ya bari in suka koma gida sai yazo ya zauna har ta warke gaba d'aya yace to yaushe zasu koma gidan tace bada dad'ewa ba da an sallame su zata kira daddy d'in shi ta gaya mashi sannan ya yarda suka tafi Fauzy tay masu rakiya har bakin Mota, tana niyyar dawowa ciki sai ga Aunty Mareeya mai Keke Napep ya tsaya da ita Fauzy ta nufe su tana murmushi tay mata sannu da zuwa ta amsa tace ta d'aukko basket a ciki tace to, bayan ta d'aukko ta sallami mai Napep d'in suka nufi cikin Asibitin, lokacin da suka shiga d'akin Aunty Mareeya ta gaida su Hajiya da Gwaggo tay masu ya mai jiki suka amsa sannan ta nufi gadon Fatuu na kwance jinin nata shiga ta kalli Aunty Mareeyar da d'an murmushi ta gaishe da ita saida ta zauna a bakin gadon da alamun damuwa tay mata sannu da jiki Fatun ta amsa bayan Fauzy ta aje basket d'in tazo daga d'ayan gefen itama ta zauna Aunty Mareeya ta kalleta k'asa k'asa da murya tace "d'azun kina gaya man abun Al'ajabi ashe duk abunan mutumin nan mijin Zarah ne" gyad'a kai Fauzy tay kawae ta sake cewa "amman dai ni kun yi man rashin hankali wllh haba kaman baku san halin shi ba ai bai kamata kuyi saurin zubar da shi ba" cike da damuwa Fauzy tace "wllh nima Aunty ban so akayi saurin zubar dashi ba..." Nan ta fad'i mata yadda sukai da Fatuu kan zubar da cikin gaba d'aya k'asa k'asa suke Maganar yadda baza'a ji su ba, bayan ta gama fad'i mata ta kalli Fatuu tace "na fahimci dalilin ki Zarah haka Allah ya k'addara amman dae da kin bashi dama kin ji abunda zai ce wllh tunda mutumin nan kin fi kowa sanin halin shi bai kamata ki k'i saurarar shi ba koda ace babu auran yayi maki haka na tabbatar zai yi abunda ya dace ya samar maku mafita bazai ta6a bari ki wulakanta ba nasan k'arshe ma cewa zai ya aure ki kuma ai mu abunda muke so kenan" shiru kawae Fatuu tay ita kanta yanzu dana sani kawae take ta rasa ya akai ta kasa yi ma Ya Haisam uzuri amman tasan Saboda son da take mashi ne shi kuma sai taga kaman ya fara sha'awarta ne can taji muryar Aunty Mareeya tana fad'in "ni wllh dana san da Maganar bazan bari a zubar ba, ni in nice ma wllh bazan yi tunanin zubar dashi ba yaushe ma ai ko shi yace a zubar bazan yarda ba adai nemi mafita kawae" hannu Fauzy tasa ta gumtse Dariya ta kai hannu ta bugi shoulder d'in ta tace "to uwar gulma ai don kar a akaita laifi biyu na fad'i hakan" cire hannun Fauzy tay tana ta dariya Fatuu ma saida ta d'an yi, Sai bayan Magrib duk suka tafi har da Fauzy tace nan zata kwana gwaggo tace a'a taje gida ta huta tunda ta wuni, a daren Abinci saidae gwaggo ta ba wasu don yayi yawa sosae,
Misalin karfe tara na daren Fatuu na kwance jikinta sanye da english wears riga da skirt bayan tayi wanka ta saka su gwaggo kuma na kishingid'e kan kujera ta kunna Radio d'in wayarta tana saurara aka kwankwasa kopar d'akin gwaggo tace a shigo kopan a bud'e take, da sallama ya shigo bayan ya turo kopar tana ganin shi ta yunk'ura ta tashi zaune tana murmushi ta hau yi mashi sannu da zuwa, shima yayi wanka ya canza kaya zuwa jeans da t-shirt hannuwan shi ruk'e da manyan ledoji ya nufi daga can wurin drawer ya aje ya juyo yana gaishe da gwaggo ta amsa tare da mik'ewa tace ya zauna ita kuma ta koma gefen gadon ta zauna shiru ta biyo baya Fatuu dae tayi zuru can ya d'ago a nutse yace ma gwaggo yanzu Abbas zai zo zasu koma gida da sauri ta tari numfashin shi tace "a'a baza'a yi Haka ba yau dae ni zan kwana ka koma gida kai baccin ka zurga zurgar da ake ma ta isa tasa a gaji ai" d'an shiru yay yana kallon gabanshi shi bai iya gardama ba can ya d'ago yace mata ba wani abu ai zai kwana da sauri ta sake cewa "yau dae da wani abu gaskiya d'ana Haisam" har saida yay d'an guntun murmushi tace ya kira Abbas d'in yace basai ya zo ba kar yay wahalar zuwa ya furta Ok sai kuma ta mik'e ta nufi hanyar fita, bayan ta bud'e kopar ta fita suka rage su biyu d'akin yay tsit Fatuu dae na kwance lamo can ta d'an d'aga ido ta saci kallon shi yana zaune idon shi na kallon gaban shi tana ta kallon shi can taga yana niyyar juyowa da sauri ta maido idonta, gaban ta ne ya fara fad'uwa Jim k'amshin shi ya fara cika mata hanci alamar kamar yana tunkaro ta har dai taji k'amshin ya gama cika ta gaba d'aya hakan yasa ta d'aga ido da sauri ta ganshi tsaye a bakin gadon hannuwan shi zube a cikin Aljihunan jeans d'in shi gabanta ne ya hau fad'uwa suka k'ura ma juna ido ta fara d'an motsa baki ganin irin kallon da yake mata a dabarbarce tace mashi ina wuni shiru bai amsa ba hakan yasa ta sauke idanun ta k'asa cikin mutuwar jiki, saida ya mula yasha iska sannan taji yace ya jikinta ba tare data d'ago ba ta amsa mashi da Sauk'i taji ya k'ara cewa ko akwae abunda take buk'ata da turanci ta girgiza mashi kai alamar a'a still bata d'ago ta kalle shi ba,
"So this is d result of being stubborn" taji ya fad'a ba shiri ta d'ago suka had'a ido ya d'aure fuska kai kace bashi yay Maganar ba, idanun ta ne suka ciko da k'walla kan kace mi suka fara zubowa shar cikin raunanniyar murya ta furta "kayi hakuri" shiru bai ce komae ba idon shi akan ta itama kallon shi take k'wallan na cigaba da zubowa can kawai sai ya juya ya nufi hanyar fita ta bi bayan shi da kallo yana ficewa ta kife fuskar ta a jikin pillow ta saki kuka mai cin rai, sai bayan wani lokaci taji shigowar gwaggo hakan yasa tay saurin shanye kukan ta gyara kwanciyar ta ta yadda taba gwaggon baya, ledojin da ya kawo ta shiga bud'awa su Fruit ne da uban nama harda su shawarma da ice cream har saida gwaggo ta d'an girgiza kai ta d'auki shawarma guda da ice cream ta nufi gadon, a gefe ta zauna ta kira sunan Fatun shiru bata amsa ba har saida ta k'ara sannan ta amsa k'asa k'asa tace ta tashi ga shawarma da ice cream tasan zata ji dad'in su ba tare data juyo ba tace mata ta k'oshi gwaggon tace "to ai in aka bar su lalacewa zasu yi" daga yadda take tace mata ai akwae fridge ko sai a saka bazasu yi komae ba, shiru gwaggon tay tana kallon ta kaman mai nazarin wani abu can ta kira sunanta ta amsa tace ta tashi zaune har saida gabanta ya fad'i bata da yadda zatayi dole ta yunk'ura ta tashi kan ta a k'asa,
"Kuka kike yi ne?" Gwaggo ta tambaya da sauri ta girgiza mata kai tana k'ara d'ukar da kanta, d'an jimm gwaggon tay kafin tace "miya faru ne ko kina jin wani ciwo ne?" Nan ma kai ta girgiza,
"in baki fad'a man damuwar ki ba wa zaki fad'a mawa ko kin fi son ki 6oye abu har wani ciwon ya kama ki?" jin yadda tay Maganar a tausashe yasa ta d'ago ta kalleta idanunta cike da k'walla cikin karyayyar Murya tace "Ya Haisam ne ke fushi kan abunda ya faru" d'an guntun murmushi gwaggon tay tace "to ba dole yay fushi ba ko ke baki ga laifin da kika aikata mashi ba, ba d'azun nan naji kina fad'a ma Fauziyya saida yay ta kiran ki harda sak'o ya tura maki amman kika k'i saurarar shi sai ke yanzu kike son ya saurare ki kome?" Shiru bata ce komae ba k'walla na zubo mata gwaggo taci gaba "ni kaina da naji hakan in fad'a maki gaskiya ban ji dad'i ba wllh nayi zaton zaki amfani da hankali kafin ki yanke hukunci" cikin muryar kuka tace "Gwaggo ni ban sani bane nayi zaton hakanan hakan ya faru shiyasa naji tsoron abunda zai biyo baya gashi Makaranta har an fara gulman ciwon da nike ina tsoron abun ya fito in samu matsala ga kuma ke da kuma zumuncin dake tsakanin ku da Hajiya da kuma surutan mutane in aka sani shiyasa na k'i saurarar shi don nasan yana iya cewa in bar shi" 6ata rai gwaggo tay sosae tace "wato kin fi tsoron wad'annan abubuwan akan Mahalliccin ki? Ko baki san girman laifin zubar da ciki ba?" d'an yarfa hannu tay "na sani gwaggo naga cikin k'arami ne sosae kuma bada son raina na same shi ba sannan in na barshi zan fuskanci matsaloli da yawa shiyasa naga gara in zubar" d'an ta6e baki gwaggo tay "baki tunanin matsalolin shi kuma zubar da cikin ba? Baki tunanin har ranki zaki iya rasawa ba?" shiru tay ta sadda kai gwaggo taci gaba "nayi mamakin duk irin yardar dake tsakanina dake har kika iya 6oye man wannan babban Al'amarin ashe zaki iya cutar dani har haka Fatuu??" A rud'e ta fara girgiza mata kai k'walla na zuba ta kai hannu ta kamo hannunta guda tace "a'a gwaggota don Allah kar kice haka wllh tallahi kin ji na rantse bada son raina nayi hakan ba saboda gudun matsalolin da zasu biyo baya ne kuma wllh ke na fi ji ma Saboda ni bansan ya aure ni ba nayi tunanin in kika ji zaki shiga mawuyacin hali ne Saboda kina yawan gargadi na da bani misali da yar wajen aikin ki gashi naga kuma shi an yarda dashi an amince mashi hakan yasa naji tsoro don nayi tunanin zuciyar ki ma zata iya bugawa wllh wannan ne dalili amman Allah ne shaida ta ban ta6a yunkurin aikata abu makamancin wannan ba, wllh gwaggo ko saurayi bani dashi duk da ana yawan nuna ana so na amman ban saurarar su balle ta kai ni ga aikata wani abu ba daidai ba shi kan shi koda muka je can G.r.a d'in raina bai so in shiga ba kawae don na yarda dashi nasan bazai cutar dani ba yasa na bi shi" yar ajiyar zuciya gwaggon ta sauke tace "amman miyasa tunda abun ya faru baki sanar da ni ba in har akwae yarda a tsakanin mu, washe garin ranar har d'akin ki nazo da safe kika nuna man kan ki na ciwo miyasa baki fad'i man ba sai kika za6i ki 6oye man k'arshe ma kika gudu Makaranta wannan abun ya ta6a ni Sosae bazan 6oye maki ba yasa na fara tunanin zaki iya cuta ta" idanunta ne suka ciko hakan ya k'ara tada hankalin Fatuu ta k'ara k'ank'ame hannunta dake cikin nata a rud'e tace "a'a gwaggota kar ki wannan tunanin a kai na don Allah wllh bansan taya zan fad'i maki abu irin wannan ba ina tsoron wata matsala ta biyo baya ne banson in rasa ki kaman yadda na rasa Mahaifiyata ke nike gani madad'in ta ban son rasa ki gwaggota ganin Al'amarin na da girma, ki yarda dani Don Allah wllh ban taba munafuntar ki ba kinji na rantse" sosae take kuka itama gwaggon har kwallan sun fara zubo mata can ta sa hannu ta fara goge ma Fatun k'wallan ta tace "shikenan ya isa kar kija ma kan ki wani ciwon amman daga yanzu kar ki k'ara 6oye man koma miye da ya shafe ki zan fahimce ki tunda ai ni musulma ce na yarda da k'addara mai kyau da kuma mara kyau komi ya faru da bawa dama can an riga da an rubuta tuni alkalumma sun bushe ko wata matsala gare ki kar Kiji komae ki fad'a man in inada iko sai in maki maganin ta in kuma ban iyawa sai in taya ki rok'on mai kowa da komae tunda shi yace mu rok'e shi zai amsa mana wannan shine amfanin Mahaifiya daga inda ta gane kana 6oye mata abubuwa kana rushe yardar da ke tsakanin ku ne" da sauri Fatuu ta jinjina mata kai tace "in sha Allahu bazan k'ara 6oye maki komai ba mahaifiyata" hannu gwaggon ta bud'e mata tana murmushi ta fad'a jikinta ta rungume ta sosae wata irin natsuwa zukatan su suka samu sun d'an d'auki lokaci a haka kafin gwaggo ta d'agota tana fad'in tasan halinta yanzu ta kama yin bacci Fatun tay murmushi, warware mata shawarmar tay tace "ki saki jikin ki kici tunda dae shi ba sanin baki cin zai yi ba nasan kawae yana maki hakan ne don ki gane kin yi mashi ba daidai ba amman nasan zai fahimce ki sai kuma muga abunda Allah zai yi dangane da Al'amarin auran na ku" shiru Fatun tay ta mik'a mata shawarmar ta amsa ta fara ci a hankali, tana cikin ci tace ma gwaggo itafa in ba wata shawarmar su ci tare tace akwae zata ci, matsa mata tay saida ta d'aukko harda youghort ta k'aro ma Fatun, suna cikin ci Fatun ta tambaye ta yadda akai Ya Haisam d'in ya aureta tana murmushi ta fara bata labari tiryan tiryan har ta gama, sosae Fatuu ta jinjina abun a ranta wato ashe ma taimakon ta yay ita dama abun ya matuk'ar d'aure mata kai data ji wai ya aureta gashi yanzu abunda ya k'ara bata mamaki irin kud'in da ya biya matsayin sadaki nan take taji bata ji dad'i ba data 6ata mashi rai saidae ta wani bangaren kan ta ne ya kulle kan tunanin dalilin da ya sa bai sake tan ba kamar yadda aka tsara har abu yazo ya shiga tsakanin su, kamar gwaggo tasan abunda ke ranta taji tace "nayi zaton bayan auren zai sake ki to amman sai bai yi hakan ba k'arshe har Abbas na tuntu6a don yay mashi Magana Saboda kar kici gaba da karatu ga auren da baki sani ba akan ki amman sai ya nuna a k'yale shi kawae tunda ai yasan da hakan aka tsara k'arshe ma sai ya nuna shi dama yafi son auran ya d'ore to farko dae ni gaskiya ban so ko don Saboda Matar shi ganin amincin dake tsakani to amman kuma daga baya sai nay tunanin in hakan Allah ya k'addaro ba