Showing 330001 words to 333000 words out of 512766 words
Chapter 111 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1614
tana yi masu sannu da zuwa Fauzy ta nuna mata Motar tace ga Motar Zarah ta waro ido tana fad'in Don Allah wai wannan bugaggar Motar mai numfashi ce aka siya ma Zarah duk akai dariya, matsawa tay ta fara bin Motar tana dubawa sai faman fad'in ma sha Allah take tana zuba santi, bayan ta gama gani ta juyo tana fad'in wllh ta taya Zarah murna Allah yasa Alkhairi ya tsare gwaggo ta amsa tace masu suyi hak'uri tabar su a tsaye don Allah su shiga, a parlor duk suka zazzauna aka shiga k'ara gaisawa kafin ta mik'e tace ma Fauzy tazo suka nufi Kitchen, dawowa Fauzyn tay tana ruk'e da babban tray da aka jero kayan abinci Aunty Mareeyar ma ta biyo bayanta ruk'e da Warmers masu kyau babba da kuma madaidaiciya, tambayarta Fauzy tay ta kai dining table ne tace mata a'a akai cikin parlon yadda zasu fi jin dad'in bajewa su ci duk akai murmushi, farko cewa sukai duk basu jin yunwa don saida suka ci Abinci sannan suka fito Aunty tace ai tasan sun ci Abinci amman dole itama a ci nata ba kamar su Amadu da Tk da basu ta6a zuwa ba ta kalli Fatuu tace Maman biyu kedai ai nasan zaki ci ko ta d'aga mata kai tana dariya, Aunty tace "haba ai ina ganin wannan kumatukan da kika aje Tubarkallah nasan bakya wasa da Abinci" duk akai yar dariya ta sake cewa "ai angode ma Allah ma gara laulayin cin Abincin da ai ta amaye amaye" gwaggo tace aikuwa hakan yafi, saida kowa yaci Abincin bayan sun gama Amadu da Tk suka tafi Masallaci yin sallar la'asar da aka kira su gwaggo ma suka mik'e Aunty ta kai ta d'akin ta ita kuma Fatuu ta nufi d'akin Fauzy, bayan duk sun yi sallar har su Amadu ma sun dawo a parlon suka zauna aka shiga hira Aunty Mareeya na ta sasu dariya, sai wuraren k'arfe biyar suka fito Aunty tace ma Fauzy ita ta dawo gida ko da sauri Fatuu tace a'a sai gobe zata dawo Aunty tace "an gama ranki ya dad'e uwar biyu farincikin ki shi muke buk'ata yanzu" duk akai dariya tace gaskiya itama ya kamata ta d'ana Motar Tk yace to ta shiga sai ya zagayo da ita tace Yauwa to, seat d'in baya ta shiga ta wani hakimce har saida ta basu dariya, tsayawa sukai yaje ya zagayo da ita bayan sun dawo ta fito tana k'ara yabawa da Addu'oi, sallama sukai da mata tayi masu godiya tana fad'in taji dad'i sosae wllh Allah ya bar zumunci duk suka amsa tace ma gwaggo sai tazo yi mata yini tana murmushi tace to tana jiran ta daga haka duk suka shiga cikin Motar suna d'aga ma juna hannu suka tafi, k'ara zagaya gari sukai sai gab da Magrib suka koma gida harda tsaraba suka yo, gwaggo da Amadu aka fara ajewa tay ma Tk godiya da Allah ya huta gajiya suka wuce, har bakin part d'in Hajiya ya kai su bayan sun fito suka shiga ciki don kai mata tsaraba. A part d'in sukai sallar Magrib da isha suka ci Abincin dare bayan sun d'an yi mata hira sannan suka komo part d'in su Fatuu. Washe gari Lahadi bayan sun ci Abincin rana sun shirya suka tafi gidan gwaggo har saida tay ma Fatuu Maganar zuwan tace ba jiya ta zo ba tace ai jiya ba nan suka zo ba don zasu fita ne yau ne zuwan nata Fauzy nata masu dariya, bayan sallar La'asar lokacin Mino ta tafi Makaranta Fatuu tace ma Fauzy suje su gaida innar su Haulat suka tafi, lokacin da suka isa gidan sosae tay murnar ganin su tace ma Fatuu maimakon ta bari ita tazo ta dubata ai bata san ta dawo bane da tazo tana murmushi tace mata ba komai, sai gab da Magrib suka baro gidan suka koma gidan gwaggo, ana gama sallar Magrib tace ma Fatuu ta koma gida suka tafi tare da Fauzy da Mino, bayan sun yi sallar isha Fauzy ta fara yin shirin tafiya gida don gobe Monday, rigar material d'inta ta maida Fatuu na fad'in ta bar ta jikinta amman ta k'iya, duk da haka saida ta bata kyautar kayan shafa da turare guda biyu harda panties da vest mai had'e da wando sai sark'a da yan kunne masu kyau, farko k'in amsa Fauzyn tay tace ai abun yayi yawa ina laifin duk abubuwan Alkhairin da aka yi masu acan Abujar, magiya Fatun ta hau yi mata kan ta amsa tana fadin ai don tana da su ne ta bata ko k'arshe saida ta nuna mata 6acin rai sannan ta amsa tayi mata godiya da Addu'ar Allah ya sauketa lafiya, Tk ta kira ta tambayi yana gida yace eh yanzu dai yake niyyar fita ta rok'e shi kan ya aje Fauzy gida yace Ok ta fito, tare suka fito harda Mino suka nufi part d'in Hajiya don tayi mata sallama, tana zaune a parlor suka shigo bayan duk sun zauna suka gaishe da ita ta amsa Fatuu tace mata dama Fauzy ce zata tafi shine tazo yi mata sallama Hajiyar ta tambayi taci Abinci ne Fauzyn tace eh sun ci a gidan gwaggo, ce mata Hajiyar tayi bari a kawo mata ta k'ara sai ta tafi tana murmushi tace ta k'oshi ai basu dad'e da suka ci ba, Tk ne ya kira Fatuu yace gashi yazo parking space bai ganta ba ko bata fito bane tace mashi gasu nan zuwa, kallon Fauzy tay tace suje ga Tk d'in can yazo duk suka mik'e Hajiya tace ta bari a bata kud'in Napep Fatuu tace ai Tk ne zai kaita gashi can ma ya fito tace to hakan yayi tay ma Fauzy godiya da Addu'ar Allah ya bar zumunci ta amsa tana murmushi suka tafi, lokacin da suka fito har Tk ya fiddo Motar Fatun cikin harabar, bayan sun k'arasa a gefen Motar suka tsaya suna k'ara yin sallama Fatuu tace mata sai sun had'u gobe a School Fauzy tace "ai nayi zaton zaki k'ara hutawa tunda ana maki komai online" ce mata tay a'a zata cigaba da zuwa tunda ta dawo dama ba wani jin dad'in karatun take ta online ba tunda ba haka ta saba ba kawai don ya zama dole ne tace Shikenan to sai sun had'u goben tay ma Mino sallama ta shiga gaban Motar dama Tk na driver seat yaja suka tafi su kuma suka koma part d'in Hajiya.....
90
~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~
..........Washe gari Fatuu na gama sallar Asuba ta tashi Mino suka fara shirin tafiya Makaranta, Mino ce ta shiga Kitchen don ta had'a masu breakfast ita kuma Fatuu ta shiga wanka, bayan ta fito ta fara shiryawa itama Mino ta shiga tayo wankan, anan ta shirya dama tun jiya da daddare taje gida ta d'aukko Uniform d'inta, saida suka gama shiryawa sannan suka yi Breakfast suna gamawa Fatuu ta kira Tk ta sanar dashi sun shirya yace to su fito, a cikin Motar ta suka tafi saida aka fara ajiye Mino kaman ko yaushe sannan aka wuce da Fatun, lokacin data je sosae yan class d'in su suka nuna murnar ganinta aka shiga zuwa yi mata sannu da dawowa da tambayar jikinta, bata dad'e da zuwa ba Fauzy ma ta zo. Bayan an tashi Tk yazo ya d'auketa suka biya suka d'auki Mino, a gida Mino tace a ajiye ta sukai sallama da Fatuu tace sai ta dawo islamiyya zata zo suka wuce, part d'in Hajiya ta nufa bayan sun isa gidan don wata irin yunwa take ji a haka ma wai taci Abinci sosae da break sannan gab da za'a tashi ma saida tasha youghort da cake da ta aje Saboda in taji yunwa, saida ta cika cikinta sannan ta koma part d'in su tana zuwa ko Uniform bata cire ba ta haye gado ta hau yin bacci, saida akai sallar la'asar sannan ta farka ta nufi toilet, wanka tayo ta dauro Alwala ta fara shiryawa cikin doguwar rigar Atamfa ta kabbara salla, bayan ta gama gaban mirror taje ta shafa yar powder da lip glow tana yi tana murmushi itama tana ganin canzawar da tayi sosae, gyale ta d'aukko ta yafa ta d'aukko jakar Makarantarta ta nufi part d'in Hajiya, lokacin data isa Hajiyar na zaune a parlon ta nufo ciki da sallama ta juyo tana amsa mata, kujera ta nufa ta zauna idon Hajiya a kanta ta gaishe da ita ta amsa kafin tace "an dawo" kai Fatuu ta d'aga "Eh tun d'azu nan ma na fara zuwa lokacin kina bacci naci Abinci sannan na tafi" kai ta jinjina mata, tana k'ok'arin fiddo littafi taji tace "Yanzun wannan rigar da kika saka baki ji kin takura ba, illar matsattsun kayan kenan dole wani lokacin kana ji kana gani baka iya saka su yanzun d'an nan gaba kad'an ya za'ai ki saka wannan rigar ai bata sanyuwa a wurin ki kinga da wadatattu ne ko yaushe zaki saka abun ki amman irin wad'annan kayan ko bayan kin haihu da k'yar in zasu yi maki don wani lokacin k'ibar ciki bin mutum take" shiru Fatuu tay idon ta akan littafin data fito tana d'an murmushi,
"Sauran kayan da ba'a d'inka ba ki bada ayo maki wadatattun dinkuna da ko cikin naki ya tsufa zaki iya sakawa" d'agowa tay ta kalleta ta d'aga mata kai, karatu ta fara yi ita kuma Hajiyar na kallo can tace mata ko akawo mata fruit zata shi ta d'aga mata kai, Saude ta fara k'wala ma kira jin shiru bata amsa ba tace k'ilan tana baya jin haka yasa Fatun mik'ewa tace bari taje ta d'aukko har zata fita daga wurin kujerun ta dakata ta tambayi Hajiyar itama ta kawo mata tace eh, a cikin bowls ta yayyanko ta dawo saida ta fara aje ma Hajiya nata akan c-table sannan ta koma ta zauna, kallon Fruit d'in Hajiya tay ganin harda abarba ta d'ago ta kalli Fatun tace badai itama harda abarbar ta yanko ba tace mata a'a ai tun Abuja bata shan ta ta jinjina kai, cigaba da karatun tayi ta haye saman kujerar gaba d'aya tana yi tana shan fruit d'in, suna haka suka ji an yi sallama alamar wani ya shigo, a Kusan tare suka kai idanun su saitin k'opar suna kallon wanda yay sallamar, nufo ciki yay saida ya matso sannan Fatuu ta gane ko waye har saida gabanta ya d'an fad'i ganin shi, Gaye ne yana sanye da riga da wando na yadi kan shi ba hula harda agogo sanye a hannun shi yana ruk'e da leda gari yayi zafi, da murmushi ya k'araso inda suke ganin yana k'ok'arin duk'awa k'asa yasa Hajiya nuna mashi kujera tace ya zauna mana, bayan ya zauna ya gaishe da ita fuskarta a sake ta amsa ya juya suka had'a ido da Fatuu still da murmushi a fuskar shi itama ya gaishe da ita ta amsa a hankali tana d'an murmushi, hakanan taji wani iri ganin shi a parlon duk da suna had'uwa a hanya a haka ma don bata san da Hajiya tasan abunda ya ta6a faruwa tsakanin su ba,
"kwana biyu Malam Ashiru ka daina lek'owa mu gaisa Allah yasa lafiya" Hajiya ta fad'a idon ta a kanshi yanata murmushi yace mata lafiya lou tace ma sha Allah, Fatuu dai sai kallon shi take abubuwa na dawo mata, mik'ewa yay ya matsa gaban Hajiya ya aje ledar daya shigo da ita ya koma ya zauna, kallon leda d'in tay ta ce "To, mi na samu haka" ta d'ago ta kalle shi yana murmushi yace mata yaje Jos ne kafin ya tafi ma yazo bata nan, jinjina kai tay tace sun je Abuja ne yace eh haka aka fad'a mashi,
"kace tsaraba ce aka kawo man kenan" yace eh, godiya tay mashi ta tambayi ya ya baro Mutan Jos d'in yace duk suna lafiya, shiru suka d'an yi can ta tambayi ya aiki da yake ta sa an samu mashi aiki yana teaching a primary, amsa mata yay da Alhamdulillah
"Yanzu sai aure ko tunda kana sana'a ga kuma aiki ai lafiya lou zaka iya rik'e iyali" yana murmushi cikin girmamawa yace mata sai nan gaba dai,
"To Saboda mi, ai aure shine cika kamalar mutum ko baka son yin Auren ne?" da sauri ya girgiza mata kai yana yar dariya yace ba wadda yake tare da ita ne yan mata basu son malamin Makaranta, har saida Fatuu tay yar dariya Hajiya tace "to don me, aikuwa inda wanda yakamata aso to bayan malami ne tunda ai shine tushen kowane aiki ko, kawai dai ba'a basu k'arfin da Yakamata bane wannan kuma saidai aita Addu'a Allah ya kawo Shuwagabannin da zasu duba masu, in dai mutum zai rik'e ka ya tsare maka hakkokin ka ai kuwa ba abun gudu bane kwanciyar hankali shi ne abun buk'ata a gidan aure kuma ba Arzik'i ne ke samar da wannan ba, gaba d'aya Arzik'in ma ai na Allah ne in akai hak'uri sai akai matakin da ba'a ma ta6a zato ba ga misalai nan akan masu Arzik'in, da yawa in kaji ta yadda suka faru sai ka jijjina kai don mamaki rabon mutum ai baya ta6a wuce shi" gaba d'aya sun yi shiru suna saurarenta har ta gama duk suka jinjina kai, jin ta gama Magana yasa shi kallon Fatuu yana murmushi yay mata Allah yasa Alkhairin Auren ta tana murmushi tay mashi godiya,
"In kana son yin Auren akwae yarinyar da zan had'a ka da ita bata da matsala akwai kyaun hali sai kaje in Allah yasa kun daidaita to sai muyi Addu'ar Allah yasa ayi damu" jinjina kai yay ta kai hannu gefenta ta d'aukko wayarta ta fara latsawa, alamun ya taso tayi mashi ya matsa daga gefen ta, mik'a mashi wayarta tayi tace ga Lambar yarinyar nan ya d'auka ranar da ya shirya zuwa su gana ya fara kiranta ya sanar mata yace to, bayan ya d'auka ya bata wayar cikin girmamawa yay mata sallama tace ya gaida Maman shi Allah yasa kuma su ji Alkhairi a kunyance ya amsa ya juya kan Fatuu dake cigaba da shan fruit idon ta akan shi itama yay mata sallama ya tafi ta bishi da ido gaba d'aya mamakin shi take sai ka rantse da Allah ba Gaye bane don sosae ya canza yay fresh hatta Maganar shi ma ta canza a nutse yake yin ta gashi kuma sam ba mummuna bane kuma yana da haske ashe dama can harda shaye shaye suka k'ara mashi bak'i. Bayan sallar Magrib Mino tazo har lokacin Fatuu na a part d'in Hajiya a d'akin Saude ta isketa lokacin bata dad'e da gama yin salla ba, suna anan d'akin aka yi sallar isha bayan Fatuu ta gama tace mata suje Parlor yunwa take ji, saida taje Kitchen ta zubo Abincin harda Mino sannan suka nufi cikin parlor don yanzu bata jin dad'in cin Abinci akan dining table, akan carpet suka zauna basu dad'e da fara ci ba Hajiya ta fito, bayan ta zauna Fatuu tace mata ta zubo mata Abincin ne tace a'a taci gaba da cin Abincinta in Saude ta zo ta zubo mata, bada jimawa ba Sauden ta shigo part d'in ta baya ta nufo cikin parlon, daga gefen Hajiya ta duk'a suka gaisa harda Mino kafin ta tambayi Hajiya a shirya table tace mata a'a waye mai ci a table d'in itama ta kawo mata nan tace to, bayan sun gama Mino ce ta kwashe kayan da sukai amfani dashi ta kai Kitchen ita kuma Hajiya tana cikin cin nata, suna Zaune suna yin kallo Tk ya shigo ta baya zai d'auki Abincin shi hango su da yay a zaune yasa shi nufo cikin parlon, daga bakin kujerun ya tsaya ya d'an rankwafa yana gaishe da Hajiya data juya tana kallon shi ta amsa Mino ma ta gaishe da shi,
"Tk yaushe zaka fara koya man Motan?" har zai juya Maganar Fatuu ta dakatar da shi kafin ya bata amsa Hajiya ta tambayi waye za'a koya ma Mota ne Fatuu tace mata ita, wani kallo ta bita dashi kafin tace "kaman dole, kina a cikin wannan halin za'a koya maki wata Mota, in kinyi hakuri Allah ya sauke ki lafiya ba sai a koya maki ba" yamutsa fuska Fatuu ta fara yi tace in aka koya mata yanzu lokacin tasan ta k'ware,
"kaji fitina don Allah, to bada ni za'ai wannan aikin rashin hankalin ba gaskiya ba wata Mota da za'a koya maki sai Allah ya sauke ki lafiya" ta k'arasa Maganar ta d'aure fuska, magiya Fatun ta fara yi mata Hajiya ta ruk'e ha6a tana fad'in wato ciki yasa ta koyi kafiya ko to ta ga ta inda za'a koya mata wata Mota, tana rufe baki kawae sai ji tay Fatun ta saka Kuka, waro ido Hajiya tay ta kai hannu ta rufe baki,
"Ku ji jan sharri don Allah, daga nace kiyi hak'uri in kika haihu a koya maki shine zaki k'ware baki ki saka man kuka" cikin kukan tace to ai in ta Haihu Ya Haisam yace Us zasu tafi Shikenan kuma bazata yi amfani da Motar ba,
"To a can Us d'in ba'a saida Motoci ne?" tace to Shikenan ita wannan d'in hakannan aka siya baza tayi amfani da ita ba,
"Dole sai in ke kika tuk'a zai zama anyi amfanin da ita, baga Tukur nan sai yaci gaba da yi maki amfani da ita ba kuma in ita kike so sai akai maki ita US d'in bayan kin haihun" wani kallo take bin Hajiyar da shi fuska a yamutsa bayan ta gama Maganar ta shiga yi mata magiyar ta bari a koya mata Allah ba abunda zai faru in sha Allah,
"Uhmm Fateema da alama wasa kika d'auki koyon Mota to iya fargaba ma ai tana iya haddasa maki matsala ni kaina har na manta yaushe rabon da in tuk'a Mota tun ma ban tsufa ba haka na hak'ura Saboda fargaba duk da na iya,