Showing 237001 words to 240000 words out of 512766 words

Chapter 80 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1596

ta ba tunda ya nuna yana son cigaba da zama da itan kuma Hajiya ma na so ita ta hak'uri sannan ita yarinyar sam bata da wata matsala zasu zauna lafiya,

rai a tsananin 6ace Hajiya Maryam ta nuna kanta tace "Fanan! Ni kike fad'a ma haka! ni kike k'ok'arin nuna ma kin za6i faranta ma mijin ki fiye da ni duk da komai nike ina yi ne don ki dawwama cikin Farinciki, don in ga rayuwar ki baki shiga cikin matsala ba!" Girgiza kai Fanan ta fara yi k'wallan da suka taru suka fara zubo mata cikin karyayyar murya tace "No Mom ba haka bane wllh, is just dat in life Sometimes we must sacrifice our own happiness for the sake of those we love, yanzu in na za6i farinciki na kad'ai zan bak'an ta ma mutane da yawa, Hajiya bata so, shima baya so sannan ita kanta Zarah bazata so ta zama bazawara ba, sannan yan'uwanta ma bazasu so ace an sake ta ba that's why na hak'ura kuma nasan in sha Allah zan ci riba tunda Allah yace yana tare da mai hak'uri" wani kalan murmushin takaici Hajiya Maryam tay tana jinjina kai da alama ta kashe bakinta ta kasa ma magana, ganin yanayinta yasa Fanan sauka daga saman kujerar ta duk'a saman knees d'inta ta shiga bata hak'uri tana fad'in don Allah ta fahimce ta, can ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tace "Ok, kiyi yadda duk kika ga yayi maki Fanan rayuwar ki ce ba tawa ba, dama katsalandan ne irin nawa yasa na zaqe, amman ki sani ba baki nayi maki ba indai Namiji ne gaki ga shi zaki nadama ne, ina zaune wataran zaki kira ni kina kuka tunda har kika za6i farincikin shi fiye da naki farincikin ma na k'arfafa mashi ya zauna da wadda yake so, uhmmm harna tausaya maki Fanan, duk da a lokacin bazan ji tausayin ba ko misk'ala zarratin!!!" A kausashe tayi Maganar tana huci ta na gamawa ta nufi hanyar Bedroom a fusace Fanan ta fashe da kuka tana bata hak'uri tana fad'in ta Fahimce ta don Allah hakan kaddarar ta ne.......

*ASM 077*


~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~



*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


.........Sosae Fanan ke kuka maganganun Hajiya Maryam sun ta6a mata zuciya sosae hakan ya k'ara tado mata rad'ad'in da take ji dangane da Auran Haisam d'in, dama ko a can Katsina ba K'aramin k'ok'ari take ba ta na dannewa, gaba d'aya abun yayi mata yawa a zuciya sosae take ta Kuka cikin kukan ta fara fad'in ita ya zata yi ne, tasan ko ta nuna bata so in dai hakan kaddarar ta ce dole sai yaci gaba da zama da Zarah k'arshe zata tada hankalin ta ne a banza, duk wannan abun Farha na zaune a inda take idon ta akan Fanan d'in dake a durk'ushe tana kuka bazaka gane yanayin da ke akan fuskar ta ba, mik'ewa Farhar tayi tana sanye da doguwar riga roba da ta kamata, wurin Fanan d'in tazo ta kai hannu tana k'ok'arin d'ago da ita Fanan d'in ta kalleta idanunta har sun yi ja fuskar jage jage da hawaye, ce mata tay ta tashi Fanan d'in ta mik'e ta koma kan kujera ta zauna itama Farhar ta zauna daga gefen ta idanunta akan ta, itama Fanan d'in kallonta take tana cigaba da zubar da hawaye can Farhar tace mata tayi shiru karta yi ciwo fuskarta a d'an yamutse tayi Maganar, hannu Fanan ta kai ta kamo hannunta guda cikin Muryar kuka ta fara Magana "Farha kema na baki haushi ko?" shiru tayi fuskarta kamar a d'aure dama ita yanayin fuskar ta a koda yaushe haka yake can tace a'a ita bata ji haushinta ba tunda taji zata iya kawae dai tayi mamakin yadda ta amince ta zauna da wannan yar talakawan a matsayin kishiyanta dama wadda suke the same level ne da sauki, hannu d'aya Fanan ta kai tana share hawayen fuskarta bayan ta gama a nutse ta fara ma Farha magana da sautin kuka tace "I want u to understand wacece Zarah ba yadda kike tunanin ta ba take, she's a very nice person bata da matsala wllh, kuma don ita talaka ce hakan ba yana nufin tana da illa ba Saboda da mai kud'i da talaka we're all the same a wurin Allah kuma in yaso zai iya canza rayuwar su suma su zama masu kud'in da baki ta6a zato ba, muma da kike ganin muna dasu bafa fin su muka yi ba ya bamu, kawai hikiman sa ne yasa ya raba don kowa yay benefiting da kowa, in ya bamu kud'i so yake muyi amfani da su wurin taimaka ma wanda bai ba bawai mu ci mu kad'ai ba kuma mu kyamace su, kinga kenan kamata yay mu rink'a girmama wanda bashi dashi tunda ta silar shi Allah zai k'ara bud'a mana because whenyou give you always get back more in return, sannan ta silar yi masu Alkhairi zai kai ka har Aljanna, Farha i advise u, stop hating the poor pls ki rink'a kyautata masu I assure u zaki ji dad'in rayuwar ki don kema Allah zai rink'a kyautata rayuwar ki zai rink'a baki way out a dukkan matsalolin ki....." Dakatawa tay tana numfasawa ita dai Farhar bin ta da ido kawae take still da yanayin da fuskar ta take tun farko,

Cigaba Fanan tayi "bari in baki Misalin abunda nike fad'a maki, Ya Haisam yana tare da Zarah for almost good five years ba abunda ke tsakanin su face kyautatawa kuma duk abunda yake masu yana yi ne Saboda Allah ba don wani abu ba, tun lokacin daya fara saninta we were engaged bai ta6a sama ran shi son yarinyar ba balle yay tunanin ya aureta har mukai Aure, yanzu bayan mun yi aure an tabbatar inada problem da yasa ban yi conceiving ba already kuma ya auri yarinyar without my knowledge da niyyar ya taimaka mata daga baya sai ya sake ta saidai kuma bai yi hakan ba har Allah yasa abu ya shiga tsakanin su sai gashi ita tayi conceiving, don't you think Allah dama yasan ni k'ilan bazan haihu bane yasa tun farko ya had'a shi da yarinyar? Yanzu idan nace in takura ya rabu da ita kuma dama already an k'addaro matar shi ce ita zata Haifa mashi yara kina ganin na isa in sa ya sake ta ne? Wannan nazarin nayi yasa na d'auki komai da Sauk'i Farha, Allah yasan abunda mu bamu sani ba sai mu k'i abu kuma Alkhairi ne a gare mu, ina fatan zaki fahimce ni my lovely sis, kiyi man fatan Alkhairi sannan ina rok'on ki ki cire komai a ranki tsakanin ki da Zarah naji labarin abunda ya faru tsakanin ku, ina son kiyi hak'uri ki manta da komai, nasan duk abunda kuke yi Saboda ni ne kar in shiga matsala I really appreciate it, amman ina son ku fahimce ni ku bani goyon baya akan hakan in sha Allahu zai zama Alkhairi a gare ni" k'arasa Maganar tay tana k'ara share hawayen dake zubo mata, jin Farhar bata ce komai ba kallon ta kawai take yasa ta d'an matsa hannunta tace tayi mata magana pls, d'an yamutsa fuska tay tace tunda hakan yayi mata Shikenan tana mata fatan Alkhairi, har saida Fanan d'in tay d'an murmushi don taji d'an sanyi a ranta, rok'on ta tayi suje ta tayata ba Momy hak'uri Farhar tace anya zata saurare su don tayi fushi sosae Fanan d'in tace su jaraba,

tare suka mik'e hannun su cikin na juna suka nufi Bedroom d'in Hajiya Maryam, lokacin da suka shiga a saman gado suka hango ta kwance ta d'aura kafa d'aya akan d'aya tana d'an Jujjuya su ta tada kanta da pillow tana kallon sama, sallama suka yi ta d'an kai idon ta kan su kafin ta janye ba tare da ta amsa masu sallamar ba, nufo gadon suka yi gaban Fanan na fad'uwa suka tsaya daga gaban gadon, sakin hannun juna suka yi Fanan d'in ta duk'a idanunta cike da k'walla ta kira sunan Hajiya Maryam d'in, banza tay mata sai ma cize baki da tayi ta rufe ido, kallon Farha Fanan d'in tayi tay mata alamar taci gaba da kai, maida idon tayi kan ta cikin rawar murya ta k'ara cewa "Mom do....." bata samu damar k'arasa abunda take son fad'a ba sakamakon d'agowa da Hajiya Maryam d'in tay a fusace cikin tsawa tace "Don't Mom Me Fanan! Don't....!!" ban son jin komai daga gare ki I heard enough pls, nace kije kiyi duk abunda kika ga ya fi maki don haka ki tashi ki ban wuri ko kuma ni zan bar maki d'akin" jujjuya kai Fanan ta shiga yi k'walla na zubo mata, fuska d'aure Hajiya Maryam ta saukko da k'afafunta Fanan na ganin haka ta gane barin d'akin zata yi da sauri har tana gocewa kaman zata fad'i ta matsa ta kama k'afafun nata cikin kuka ta ke fad'in "pls Mom don girman Allah ki fahimce ni kar ki fushi dani abun zai man yawa, nasan duk abunda kike Saboda farin ciki nane saboda k'aunar da kike man kuma wllh na yaba da hakan....." A fusace ta katse ta "K'arya kike Fanan baki yaba ba shiyasa kika za6i 6ata man rai duk da ni ina hango maki abunda kika kasa hango ma kan ki ne, ta ina kishiya take zamar ma mutum Alkhairi koda tana zama kafin a samu haka sau d'aya nawa ake samu da suke zama sharri, kina ji kina gani za'a raba ki da Mijin da kike tak'amar yana son ki zai maku Adalci kuma ya kasa tsinana maki komai a lokacin kuma ko kinyi k'ok'arin maido shi gare ki wllh bazaki iya ba don lokaci ya riga da ya k'ure maki" ta k'arasa tana huci, d'an shiru Fanan tayi kafin cikin kuka tace "Mom saida nayi nazari sosae sannan na Amince, in ka d'auki abu matsayin Alkhairi sai kiga ya zamar maka hakan koda bai zama ba hakan k'ilan jarabawar kace in kayi hak'uri kuma sai kiga kaci riba, idan baka yi cuta ba Mom ba wanda ya isa ya cutar da kai kuma ko na rantse bazan yi kaffara ba Zarah bazata ta6a cutar da ni ba balle har ta raba ni da miji na, haka shima Ya Haisam na yarda dashi bazai ta6a juya man baya ba don ya k'ara aure kema kin san waye shi Mom kin san halin shi, nayi dogon nazari Mom there is reason for everything dama can Allah ya k'addaro ita matar shi ce shiyasa ya had'a su idan kuma ba'a kaddara zasu rabu ba wllh ni ban isa in raba su ba duk abunda zanyi k'arshe zan wahalar da kai na ne a banza, Mom baki tunanin k'ilan ni Allah bai kaddaro zan haihu ba shiyasa ya had'a su itace zata Haifa mashi yara, nayi tunani in har na hana shi hakan ba soyayya bace tunda Allah ya bashi mafita kuma kema Mom Haisam d'an ki ne bazaki so ace ya rayu bai da ya'ya ba" tunda ta fara Maganar Hajiya Maryam d'in ta ta6e baki tana sauraren ta idon ta akan ta har ta dakata sannan ta d'an girgiza kai da murmushi wanda yafi kama da ace na takaici ta d'age gira tace "Good, sarkin iya yin dogon nazari da tsara zance, wato ni ban iya yin zurfin tunani ba ko sai ke shine harda yanke ma kan ki hukuncin bazaki haihu ba, sai ki fad'i man a ina aka ce bazaki haihu ba ko kuwa kin yi gadon rashin haihuwa ne?"

Girgiza mata kai tayi "No Mom nima ba ina nufin wai bazan haihu ba ina fatan in samu lafiya kawae misali nike baki tunda hakan yana iya yuwa, kuma ko da ace na haihu ne in Allah ya k'addara zasu zama mata da miji wllh bazan iya hana hakan ba you know dat Mom, Koda ace nayi yadda nayi nayi nasarar raba su in zaman su bai k'are ba dole su k'ara kasancewa tare koda kuwa bayan RAI na ne" wani kallo Hajiya Maryam ke jefa mata taci gaba "it happened more than once Mom, sau da yawa iyaye zasu ce ya'yan su bazasu Auri wani ba sai dai bayan ran su kuma k'arshe su zo su Mutun ayi auran, Mom wllh hakan na iya faruwa dani in dai nace zan ja da ikon Allah, kuma indai na cutar da su don Farinciki na kinsan sai Allah ya saka masu, nasan a kullum fatan Alkhairi kike man a rayuwata don haka duk abunda ya faru dani ki d'auka Alkhairin ne Mom na kuma tabbatar zan ci ribar kar6ar kaddarata da nayi k'ilan silar hakan kiga Allah ya bani lafiya nima in ta haihuwa kuma ya d'aga daraja ta, koda ma ban haihu ba Mom wllh Zarah bazata ta6a man iyaka da yaranta ba tana so na sosae she has good intentions toward me, Mom ki bini da fatan Alkhairi Don girman Allah in kika juya man baya Saboda haka sai yafi ta6a man zuciya abubuwa zasu man yawa, don na Amince su zauna hakan ba yana nufin ban jin komai ba a rai na kawae ina daurewa ne nasan kuma hakan na d'an lokaci ne ba kamar in kika fahimce ni kikai man fatan Alkhairi" ta k'arasa Maganar tana share hawayen fuskarta, shiru Hajiya Maryam tay fuska a kwa6e a bad'ini jikinta yayi sanyi da Misalin da Fanan ta bata na Allah zai iya d'auketa don su zauna tare Saboda tabbas yana faruwa, Fanan d'in ce tace mata don Allah tayi magana, sauke nannauyar ajiyar zuciya tayi tace "Shikenan tashi kije ina maki fatan Alkhairi" ganin fuskarta ba a sake tayi Maganar ba yasa Fanan d'in cewa to ta daina yin fushi da ita, d'an guntun murmushi tayi had'i da d'an ta6e kawae, tunda suka shigo Farha na a tsaye sai lokacin ta matsa kusa da gadon Hajiya Maryam d'in ta d'aga ido ta kalleta Farhar ta d'an yamutsa fuska tace pls ta daina fushin, juyar da fuskar ta tay gefe duk suka bita da ido can ta k'ara sauke ajiyar zuciya ba tare da ta kalle su ba tace ta bari Allah yayi masu Albarka da sauri Fanan ta mik'e ta fad'a jikinta ta fashe da wani irin kuka mai ta6a zuciya Farha ma d'an murmushi tay ta duk'a ta manna mata kiss a kumatun ta, d'ago kai tayi tay mata wani kallo mai kaman harara kawae sai itama ta rungume ta ta baya, sun d'an d'auki lokaci a haka idanun Hajiya Maryam a rufe wani iri take ji Kukan da Fanan d'in ke yi can ta d'ago da ita ta fara share mata hawayen tana fad'in ya isa haka sai wani ciwon ya kamata, godiya Fanan d'in ta shiga yi mata da Addu'oi tana ruk'e da dukkan hannayenta, tana d'an murmushi take amsa mata, jin an fara kiran sallar Magrib yasa tace masu suje suyi salla suka amsa da Ok Fanan d'in ta mik'e ta kamo hannun Farha suka nufi hanyar fita idanun Hajiya Maryam a kan su har suka fita, girgiza kai ta shiga yi takai yatsa baki ta d'an cize, tasan bata da wata mafita da ya wuce ta zubar da makamanta dama abunda yafi damunta shine tunanin halin da Fanan d'in zata shiga sai gashi ta bata mamaki sannan kuma ga furucin da Hajiya tayi mata, dangane da yadda take ji game da Fatuu kuma bazata iya fad'a ba.

Suna fitowa Fanan ta rungume Farha tana k'ara yi mata godiyar fahimtar ta da tayi, bayan ta saketa Farhar na d'an murmushi tace mata "We're blood sisters" Fanan d'in tace hakane, kowa d'akin shi ya nufa. Bayan Fanan ta gama yin sallar Magrib d'aga hannu tayi tana k'walla ta shiga rok'on Allah akan kada yasa Maganar da Mom d'in ta tayi d'azun ta tabbata, Allah yasa kada Ya Haisam ya juya mata baya ya had'a kan su ita da Zarah, sosae tayi Addu'oi bayan ta shafa zaune tay saman prayer mat d'in ta kwantar da kanta a jikin gado tana tunane tunane, Wayarta ce ta fara yin ringing ta juya ta kallo ta a saman gadon kafin ta mik'a hannu ta d'aukko, ganin Haisam ne mai kiran yasa ta saki murmushi tay picking, gaida shi tayi ya amsa ta tambayi ya isa yace mata eh ya bari yayi salla ne sai suyi magana, an isa lafiya tayi mashi yace mata lafiya lou ta tambayi yadda ya iske kowa, jin yanayin voice d'inta ta d'an disashe yasa ya tambayi ko wani abu na damunta ne, tana d'an murmushi tace mashi eh cike da kulawa ya tambayi abunda ke damuntan tana d'an murmushi tace mashi missing d'in shi, shima murmushin yayi yace mata ai saida yace ta bari ba yanzu ba ta tafi ta k'iya, ita dai murmushi kawai tayi don baisan ba K'aramin k'arfin hali take ba zaman ta a gidan Hajiya tana ganin shi yana kwana da wata, rarrashinta yayi yace ai bada jimawa ba zai dawo, sosae ya kwantar mata da hankali cikin salon nuna kauna kafin daga baya sukai sallama,

*ABUJA NIGERIA*

Bayan sallar isha iyalan Senator suka zauna cin Abincin dare harda Haisam da tuni ya isa, ba laifi Haisam yaci sosae har Senator na mashi tsiyar dama yanzu in bai rink'a cin Abinci ba Sosae sai ya rink'a fad'uwa Saboda figewa zai yi su Aunty da Mom sukai yar dariya don sun fahimci dalilin daya sa ya fad'i hakan, shima Haisam d'in murmushi kawai yayi, bayan sun gama gaba d'aya cikin parlon suka koma duk suka zazzauna kusan kowa na nan banda Mutum biyu Laila da Nameer duk basu K'asar suna Makaranta, Mom d'in su ce ta fara yin magana tace ma Haisam d'in sun ji dadin yadda Fanan ta amince bata tashi hankalin ta ba Senator ma ya karba yace sosae Daughter ta burge shi Allah ya had'a kan su duk suka amsa da Amin Aunty ma ta yaba mata tace tayi namijin k'ok'ari gaskiya, yar Nasiha Senator yayi mashi kan yin Adalci a tsakanin su,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login