Showing 435001 words to 438000 words out of 512766 words
Chapter 146 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1561
manta da irin raɗaɗin data ji a wanccan lokacin, Fauzy tace hakane haƙuri kaɗan ke haifar da jin daɗi na har abada sannan rashin haƙuri kaɗan na haifar da dana sani na har abada, nima dai mai rubutun nace wannan haka yake Allah ya ƙara mana haƙuri Amin, Hira suka cigaba da yi cike da nishaɗi har Fatuu na mata Addu'ar Allah yasa ta haifi yan biyu tana dariya tace haka ma Aunty Mareeya tace amman ita tafi son ɗayan ma. Ana gama sallar Magrib aka fara shirin kai Mino Fatuu tasa ta canza kaya bayan tayi wanka zuwa lace baiwar Allah duk tayi zuru zuru Gwaggo tazo ta tafi da ita baya wurin danginsu don ayi mata Nasiha,, bayan an kawo motoci bakin entry hall aka sanar a fito Fatuu ce ta kamo ta suka nufo cikin babban parlon gidan lokacin su gwaggo ma duk sun fito suna biye dasu, bayan sun shigo Gwaggo ta kama Minon suka nufi part ɗin Mom harda su Yaya, a falonta duk suka zazzauna bayan an gaggaisa Gwaggo tace sun kawo amarya ne suyi sallama sannan su damƙa amanarta duk da sun san ko basu bada ba za'a ruƙe masu amanarta kamar yadda aka ruƙe ta yar uwarta sannan sai anyi haƙuri don zata iya yin wani abu ba daidai ba saboda ƙarancin shekarunta in tayi kuskure a nuna mata duk da akwae yar'uwarta saidai itama ba wata babba bace kuma ba lalle su kasance tare ba gaba ɗayansu dai duk sukai ba daidai ba a kwatanta masu don su gyara Mom na murmushi tace insha Allahu kada suji komai za'a ruƙe amana yadda yakamata sannan yadda suke nuna ma yaransu in sun yi ba daidai ba suma hakan za'a yi masu tunda suma tamkar Ya'yansu ne, sosae suka ji daɗin Maganarta sukai ta godiya tare da yi masu Addu'o'i daga baya suka fito don tafiya Mom ɗin tayo masu rakiya, cikin masu zuwa harda Hajiya Zainab da Hajiya dasu Aunty Mareeya da Feenah kusan duk mutanen da suka rage zasu je Motocin da aka kawo sun kai goma, bayan duk an shishshiga harda akwatunan kayan da Minon tayi amfani dasu waɗanda su Yaya suka taho dasu kuma da sauran kayan an kai su can gidanta, a tare Motocin suka fara tafiya suka tunkari gate, ba wata tafiya mai nisa sukai ba suka iso gidan dake a Asokoro dama gidan Senator ɗin a Maitama yake basu da nisa sosae, tun a bakin gate zaka fara shaida haɗuwar shi bayan mai gadi ya buɗe masu motocin suka kutsa kai ciki, wuri daban daban akai parking don asamu duk Motocin su shiga wasu a cikin parking space ɗin gidan mai ɗaukar motoci huɗu aka shigar dasu wasu daga can gefe gefe Motar da Minon take ciki har cikin entry hall aka shigar da ita, bayan an samu duk Motocin sun shigo aka bubbuɗe kofofin motocin aka fara fitowa nan fa aka shiga bin gidan da kallo waɗanda basu san shi ba, ba laifi gidan yana da girma tunda har harabar shi ta ɗauke duka motocin hasken Fitilu ko ta ina ga shukokin fulawoyi wurare daban daban a tsare sun sha gyara, daga bakin gate akwae ɗakin mai gadi sai ɗayan bangaren nan parking space din yake sannan gaba ɗaya harabar gidan malale take da interlock daga tsakankanin su anyi adon ratsin grass carpet, bangaren ginin gidan kuwa tun daga cikin entry hall aka malala tiles ga wata babbar fitilar sama mai matukar kyau a saman daga nan zaka shiga cikin gidan ta dakakkar ƙopar da ke a wurin, kana shiga ɗan passageway ne wurin shima akwae fitila a sama da kuma flower vases sun saka ƙopar shiga falon tsakiya ana buɗeta za'a shiga cikin parlon wanda babba ne yasha manyan labulai maroon da akai ma wani irin design mai ɗaukar hankali, gaba ɗaya parlon tiles ne ruwan madara kalar fentin falon daga tsakiya aka saka kujerun Mino wanda haɗaɗɗun royal ne brown da ɗan ratsin maroon an jere throw pillows, daga tsakiyarsu lallausan carpet ne brown tsakiyarsu an aje Ottomon kalar yadin kujerun daga angles ɗin parlon an aje flower vases da suka hau da kayan ciki sai bangaren wurin kayan kallo an manna babbar plasma ɗin da aka siya mata a jikin babban Tv stand mai drawers ta kwance da kuma ta tsaye shima cikin saitin kayan yake daga baki bakin shi anyi mashi irin design na adon da aka ma kujerun daga gefe da gefen Tv stand ɗin sound systems ne, iya wurin kayan kallon abun kallo ne, daga can bayan kujerun matattakalar hawa bene take anyi mata wani irin design ta lanƙwaya ƙarafan jiki silver ne sai ɗaukar ido suke itama matattakalar anyi mata fenti ruwan madara kalar na cikin parlon sannan an shimfiɗa carpet brown yabi jikin stairs ɗin har sama, daga gefen hagun benen Dining Area ce an aje dining table da kujerun shi guda haɗu suma mahaɗin kujerun parlon ne, daga can gefen shi nan aka aje standing freezer daga gaban shi anan ƙopar shiga Kitchen take daga jikin ɗayan bangon wurin wani haɗaɗɗan console ne golden manne daga gefe da gefen shi an aje flower vases sosae wurin yay kyau daga ƙasan Dining table ɗin nan ma lallausan carpet ne maroon da ratsin brown, daga tsakiyar parlon bayan kujerun corridor ne inda bedrooms suke guda biyu suna kallon juna da toilet a tsakiya ba laifi Bedrooms ɗin suna da girma a ɗaya Royal Bed ne Milk da wardrobe ɗin shi mai guda shidda a jikinta anyi adon madubi kana ganin kanka haka a jikin bedside din ma gaba ɗaya set ɗin kayan sun haɗu ba ƙarya wani irin design akai masu mai jan hankali a ƙasa an sa carpet milk, a ɗayan ɗakin kuma Simple Modern Bed ne Coffee brown da wardrobe ɗin shi mai gida hudu sai nightstands da dressing mirror daga gaban gadon an sa carpet coffee labulayan ɗakin ma coffee ne, kowanne ɗaki akwae toilet irin na zamani irin wanda ya amsa sunan toilet ɗin masu kuɗi komai na cikin shi fari da silver ne, a 6angaren Kitchen kuwa drawers ɗin ciki L-shape ne dark ash haka cupboards ɗin sama suma L-shape ne an tsara Kitchen ɗin shima yayi kyau sosai, Bayan yan kawo Amaryar sun shigo ciki nan fa aka hau jinjina haɗuwar gidan Gwaggo sai murmushin daɗi take haka Fatuu ma su Yaya da Kakar su Minon mamaki ne shimfiɗe akan fuskokinsu ganin wai wannan Aljanar duniyar Mino zata zauna gaba ɗaya sun kasa rufe bakunansu, yadda aka shirya komai yayi ma su Gwaggo kyau sai yabawa suke, a ɗaya daga cikin ɗakunan aka kai Mino inda keda Royal Bed su Aunty Mareeya suka fito suna ƙara dudduba gidan danginsu Nameer suma suna ta yabawa suna faɗin gaskiya anyi ƙoƙari da yake sunji Hajiya na magana kan kayan da akayin tana faɗin sun kashe kuɗi sosae hakan yasa suka gane danginta sukai mata kayan ɗakin hatta Hajiya Zainab saida tace gaskiya anyi ƙoƙari, har saman bene suka hau wanda nan part ɗin Nameer ne babban falo ne an zuba luntsuma luntsuman baƙaƙen leather chairs da ƙaton carpet baƙi da ratsin ruwan toka mai duhu da kuma mai haske sai labulaye suma baƙaƙe ne da ratsin ash akwae kuma kayan kallo harda freezer falon baida hayaniya amman yayi kyau sosae, Bedroom guda ɗaya ne mai ɗauke da set ɗin gado ɗan Dubai sai toilet ko ina dai yayi kyau sai yabawa ake, har bayan gidan suka je akwae wurin yin basket ball da kuma ɗan madaidaicin Swimming pool daga gefenshi kuma akwai rumfa ta shaƙatawa mai ɗauke da tebur da folding chairs irin wanda ake linkewa, bayan sun gama zazzagaya gidan Aunty Mareeya da Fatuu suka ɗaukko kwalin kayan adon da aka kawo suka fara jera su a jikin gidajen Tv stand wasu kwalaben turaren wuta ne an masu ado wasu kuma kayan ƙawata wuri ne kowanne aka sashi a inda ya dace sosae falon ya ƙara ƙawatuwa suka jona wata jigunannar burner aka saka turaren wuta nan da nan ƙamshi mai daɗi ya fara karaɗe parlon ya haɗe da sanyin A.c, su Amadu ne suka shigo da katan katan na lemuna da abubuwan ci suka aje a saman carpet Aunty Mareeya tace sannunsu abokan ango sukai murmushi kafin suka shiga bin falon da kallo suna murmushin daɗi don ya burge su Hajiya ce tace masu to su zagaya mana su gani da kyau suka ce to, zama sukai kan kujeru suka fara cin abubuwan da aka kawo ana ɗan yin hira Hajiya tasa Fatuu ta ɗiba ta kaima Mino da ƙawarta dake a cikin Bedroom, suna cikin ci Hajiya ta kalli Gwaggo tace wato Dije kwance kwance ashe kuɗi ne daku ko shiyasa kuka zuba ma Ameenatu kaya haka duk aka yi dariya Hajiya Zainab dake cikin cin Shawarma tana murmushinta na manya tace ba Fulani bane su Hajiya tace sune na asali ma tace ai dama kuɗi garesu da an saida shanaye sai kaga uban kuɗi duk akai dariya Gwaggo dai murmushi kawai take don an kashe bakin, bayan wani lokaci suka miƙe don tafiya wasu suka fita wasu kuma suka je yin sallama da Mino harda Gwaggo da Hajiya dasu Aunty Mareeya, ai tana jin zasu tafi ta ruɗe ta saka kuka duk tabi ta ƙanƙame Gwaggo aka hau bata haƙuri Hajiya tace Ameenatu sai kace an kawo ki gidan yari, sam taƙi jin rarrashi sai fullanci take tana ce ma Gwaggo don Allah kada a barta ita kaɗai su tafi da ita Fuskarta duk tayi jage jage da hawaye har saida tasa idanun Gwaggon suka ciko da ƙwalla ita Fatuu ma har sun fara zubowa Hajiya ta tambayi Gwaggo mi Minon ke cewa ne ta faɗi mata wai su tafi da ita tay ɗan murmushi tace ina su ina tafiya da ita ai nan gidantane tazo kenan tayi haƙuri zata saba, ganin taƙi jin rarrashi yasa Hajiya ta kira Nameer a waya bayan ya ɗaga ta tambayi yana ina yace gasu nan a harabar gidan tace to ya shigo ya samesu a Bedroom yace to, bada jimawa ba sai gashi ya shigo cikin ɗakin da sallama yana sanye da riga da wando na Farar shadda fuskar nan sai annuri take ga uban ƙamshi dake tashi daga jikinshi, gaishe dasu yay bayan sun amsa mashi Hajiya ta nuna mashi Mino tace gata nan yazo ya rarrashi matar shi ta hana su tafiya wai bin su zatai, kai idon shi yay kan Minon da tabi ta ƙanƙame Gwaggo ta kifa Fuskarta a jikinta, tsaye yay kawai yana kallon su Hajiya tace yaje ya kamata ko sun tafi in kuma so yake su kwana to still bai matsa ba don kunyar yaje ya kamata yake sai ɗan murmushi yake ganin haka yasa Fatuu ta kai hannu ta ɗago da ita suka haɗa ido tace mata ya isa ta daina kukan ita zata zauna tare da ita jin hakan yasa ta faɗa jikin Fatun Hajiya tace masu su tafi, bayan duk sun fita ya rage saura Fatuu da Safnah sai Nameer da hannu Fatuu tay mashi alamar yazo ya rarrasheta, Moving yay zuwa inda suke ya tsaya a gabansu cikin kwantar da murya ya kira sunanta shiru bata amsa ba bata kuma ɗago daga jikin Fatun ba, hannu ya kai ya fara ƙoƙarin ɗago da ita ta turje su Fatuu nata bata haƙuri ganin taƙi rabuwa da jikin Fatuu yasa shi nuna mata ƙarfi ya ɗagota da ƙarfi tana barin jikin Fatun da sauri ta kamo hannun Safnah suka nufi hanyar fita daga ɗakin Minon nata rizgar kuka tana ƙoƙarin kwacewa ta bisu hakan yasa shi haɗeta da jikin shi ya rungumeta tightly ya kai bakin shi saitin kunnanta a hankali ya shiga rarrashinta yana faɗin ba gashi tare da ita ba, sukuku Fatuu ta dawo duk tausayin Mino ya kamata daga baya ta sake suka shiga yin hira da Fauzy kowa na tuna lokacin da aka kai shi ɗakin miji Safnah dai har ta kwanta don itama jikinta yayi sanyi saboda yanayin da suka baro Aminiyarta, suna cikin yin hirar Sameer ya kira Fauzy ta ɗaga kiran, tambayarta yay tana ina tace gata nan sun dawo gidansu Ya Haisam yace Ok gashi nan zuwa zai dauketa tace to, bayan sun gama wayar Fatuu na murmushi cike da tsokana tace su Fauzy ana waya da miji an wani kwantar da murya dariya tayi tace ai saida hakan, faɗi mata tay zai zo ya ɗauketa ne Fatun tace maimakon tace mashi zata kwana anan su kwana tare Fauzyn ta ɗan buɗa ido tare da jinjina kai tace ai tasan ko tace haka ba lalle ya bari ba Fatuu tace bai iya kwana ba tare da ita ba kenan,
"Kusan hakan, kinsan fa koda muna London bayan mun dawo daga Honeymoon in zaije wani wuri indai kwana zai yi dani yake tafiya, ai Honey ba sauƙi sai da na samu cikin nan ne ganin ina wahala ake ɗan raga man" Fatuu na dariya tace ai hakan ake so a damu da kai sai ta dage taita gyara kanta don ma halin da take ciki ba komai zata iya sha ba Fauzyn tace eh tama daina shan wani magani Aunty ma tace a halin da take ciki ba sai tasha komai ba, bada jimawa ba Sameer ɗin ya kirata ya sanar mata gashi a gaban entry hall, tare da Fatuu suka fito tayo mata rakiya suna ƙarasowa gaban Motar ya buɗe Motar tun kafin ya idasa fitowa ƙamshin turarenshi ya karaɗe wurin, sanye yake cikin ƙananan kaya Fuskarshi tayi wani irin Fresh har yar ƙiba ya ƙara da yake wurin fayau yake da haske, bayan ya fito gaisawa sukai da Fatuu fuskarshi a sake yay mata ya hidima ta amsa da Alhamdulillah yace Allah yasa alkhairi, bayan ta amsa ya ambayi ina yaranshi tace suna wurin Mom yace a gaishe mashi dasu, maida idon shi yay kan Fauzy data jingina da Motar ta langa6ar da kai slowly yace "hope u'r Ok?" lumshe mashi ido tay ta ɗan ɗaga mashi kai yace to suje tare da yi mata alama da kai, tare suka zagaya ɗayan bangaren ya kai hannu ya buɗe mata ƙopar saida ta juyo ta kalli Fatuu dake tsaye tana ta murmushi ta ɗan ɗaga mata hannu itama ta ɗago mata sannan ta shige ya maida ƙopar ya rufe bayan ya zagayo driver side yayi ma Fatuu sallama ya buɗe ya shige, saida yaja Motar sannan ta juyo komowa cikin gidan tanata murmushin daɗi ganin yadda Sameer yake kulawa da Fauzy harda su buɗe mata ƙopa abunda bata ta6a zaton zai yi ma mace ba, bayan sun hau titi sosae ya juya ya kalli Fauzy data kwantar da kanta jikin headrest ya kai hannun shi dake gefenta ya kamo nata daga yadda take ta juyo da kan ta kalle shi yace mata ko jikin ne ta girgiza mashi kai alamar a'a ya sake cewa ko tana jin yunwa ne nan ma ta girgiza mashi kai yaci gaba da driving da hannu ɗaya ɗayan kuma yana ruƙe da nata can bayan wani ɗan lokaci ya sake juyowa ya kalleta ya tambayi ko tana son wani abu ta ɗan yi shiru kafin tace tana son ice cream yay ɗan shiru tare da maida idon shi kan hanya taji yace tana shan abu mai sanyi sosae ba ba'a son suna sha ba, ɗan yamutsa fuska tayi ta sigar shagwa6a tace to ai cikin ne yake mata zafi sai tasha abu mai sanyi take jin sauƙi ya jinjina kai, a bakin wani babban cold store ya parker tare da buɗe Motar yace mata yana zuwa ta ɗaga mashi kai, nufar shiga wurin yay tanata kallon shi ta glass wata irin ƙaunar shi na ratsata, After few minutes ya fito ruƙe da leda mai tambarin wurin ya dawo wurin Motar, bayan ya shiga ya miƙa mata ta amsa tare da furta "thank you Honey" jinjina mata kai yay ya ja suka tafi, bude ledar tayi ta fiddo roba ɗaya bayan ta buɗeta fara sha, tana cikin sha ta ɗebo ta kai bakin shi idon shi akan hanya ya buɗe ta zuba mashi bayan ya shanye ya furta mata "Love you Babes" tana murmushi tace "love you too Honey.....the best Husband ever" ɗan juyowa yay yayi mata wani kallo tana murmushi ta kashe mashi ido yay faffaɗan murmushi tare da maida idon shi kan titi bayan ɗan lokaci suka iso gidan su inda ya ta6a kawota.
Bangaren Amarya Laila tuni suka isa Kano aka ɗaukko su daga Airpot a cikin jigunannun motoci masu numfashi, gidan su Angon aka nufa dasu dake a Nasarawa G.r.a, katafaren gida ne daya amsa sunan gidan masu kuɗi sosae gari guda zagaye shi a ƙafa ba ƙaramin aiki bane an narka uwar dukiya tun daga kan ginin, gidan yana da part part da yawa don matan Mahaifin Angon nata ukku surukar Laila ɗin ce ta farko hakan yasa gidan suna da ɗan yawa, a part ɗin Momyn Bashir ɗin wanda ƙarshe ne wurin haɗuwa aka saukesu sun samu kyakkyawar tarba daga danginsu, bayan sun huta aka kawo masu lafiyayyun abinci da abubuwan sha, misalin karfe biyar aka shiga shirin yin buɗar kai da za'ayi anan cikin harabar gidan har an yi haɗaɗɗan decoration gidan ya ƙara cika da Jama'a harda anko aka yi, bayan duk an shirya Amarya Laila ma ta canza shiga haka su Jidderh duk sun canza kaya ba 6ata lokaci aka shiga gabatar da buɗa kan, Sai bayan isha'i aka gama An ci an sha an yi hotuna da Vedios Sosae aka nishaɗantu, ana gama yin buɗar kan aka fara shirin kai Laila gidanta wanda shima ke anan cikin G.r.a ɗin dama duk mazan gidan masu aure anan unguwar gidajen su suke don Mahaifinsu nada gidaje a cikin unguwar sosae wasu hayar su ake, jerin motoci ne aka kawo don ɗaukar yan kai Amaryar bayan duk an shishshiga a tare motocin suka tafi, ba wata tafiya akai sosae ba aka iso gidan tun daga