Showing 366001 words to 369000 words out of 512766 words
Chapter 123 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1562
nufi can da ita, gaba d'aya harda Haisam suka shiga cikin d'akin aka kwantar da Fatun saman gado bayan Aunty ta cire nata Hijab d'inta itama ta cire after dress dinta, daga gefen kanta Haisam ya zauna ya kama hannunta guda yana cigaba da yi mata sannu Fuskar shi a hautsine, ciwon kaman yasan an zo Asibiti nan ya shiga k'aruwa amman yana yi yana lafa mata in ya lafan har d'an gyangyad'i take, gaba daya Aunty da Nurses d'in biyu na a kanta suma suna ta yi mata sannu sai faman d'aga kai take tana yarfa hannu, in ciwon ya taso sosae hankalin Haisam ke tashi har sai ya lafa sannan hankalin shi ke d'an kwanciya, a haka saida aka shafe Kusan awa bata Haihun ba Haisam sai tambayar Aunty yake ya tak'i haihuwan tace mashi lokacin bai yi bane, sai bayan kamar awa d'aya da rabi sannan ciwon ya taso gaba d'aya daka kalli Fatuu kasan tana cikin Azabar ciwo don a lokacin ko anyi mata sannu bata iya amsawa gaba d'aya ta rurruke Haisam sai murkususu take tana kukan da ba hawaye cikin fitar hayyaci take fad'in "Ya Haisam bazan iya ba....kilan ma Mutuwa zan yi" sosae wannan Maganar tata ta k'ara rud'a shi tsantsar tashin hankali ne bayyane akan fuskar shi tayi wani irin ja fuskar yana ta ce ma Fadin "Pls Baby stop saying that....im here for you ba abunda zai faru in sha Allah zaki haihu lafiya" ganin abun yayi yawa a wurin shi yasa shi mik'ewa tsaye daga bakin gadon still yana ruk'e da hannunta guda, kallon Aunty dake tsaye a gefenta tana k'arfafa mata gwuiwa yayi yace "Aunty this is too much gaskiya, pls kiyi wani abu tana shan wahala da yawa" fuska a yamutse yayi Maganar, idon Aunty na akan Fatun tana mata kallon tausayi tace "bai yi yawa ba Son haka ake yi dama kuma duk abunda yakamata ayi mata an yi so sai mu jira Allah ya sauketa lafiya" wani kalan waro ido yay yace yanzu duk wannan Azabar ciwon da take sha ne da Sauk'i, kai Aunty ta jinjina mashi tace wasu suna spending whole day haka wasu ma 2 days ita kuwa bai fi awa d'aya da rabi da suka zo ba kuma in sha Allahu tana gab da haihuwan, girgiza kai yay idon shi akan Fatuu dake cigaba da murkususun azaba yace gaskiya to in haka ne ayi mata Cs kawai taya Mutum zai jure wannan wahalar, d'an guntun murmushi Aunty tay tare da d'an girgiza kai ta fahimci a wurin shi gani yake hakan sauki ne duk da tabbas in anyi nasarar yin shi lafiya lou yafi sauk'in, kara maimaita mata Maganar ayi mata Cs yayi ta kalle shi cike da jan hankali ta furta "ba sai an mata shi ba zata iya haihuwa da kanta, pls Son You should encourage her instead, wannan Maganganun da kake kana sata tana sarewa and kana anan ne don ka k'arfafa mata gwuiwa so is better if you do dat" d'an yamutsa baki yay jiki a mace yaja k'afa ya koma bakin gadon Aunty tace yayi mata Addu'a ya d'aga mata kai gaba daya rud'ewa tasa ya manta da yayi hakan, lokacin Aunty ta buk'aci amfani da wayarta ta tuna ta baro ta a gida tambayar Haisam tayi wayar shi ya girgiza mata kai alamar bai tare da ita,
"Nurse Haleema pls where is your phone?" Aunty ta tambayi d'aya daga cikin nurse d'in cikin girmamawa tace mata tana a station tasa caji tace mata in ba damuwa ta d'an aro mata da sauri tace to, har ta nufi kopar fita Aunty ta dakatar da ita ta tambayi akwae karatun Qur'ani a ciki da sauri tace eh sosae tace to ta kawo mata, bada jimawa ba ta dawo lokacin Haisam nata yi ma Fatun Addu'o'i ya rurruk'e ta, bayan ta kawo wayar Aunty tasa ta kunna karatu tace to, a saman drawer din gadon Fatun aka d'aura wayar karatun ya fara tashi daga Fatiha bayan ta k'are ya shiga baqara Aunty ta tambayi Fatun ta iya surar da ake yi tun kafin ta bada amsa Haisam yace mata eh ta jinjina kai,matsowa tayi ta kai hannu ta dafa goshin Fatun tace mata ta daure su rink'a bi tare ta jinjina mata kai tana ta nishin ciwo idanunta sunyi ja luhu luhu kanta a bud'e manyan kitson da Iya tayi mata guda goma sun bayyana, sosae tayi k'arfin halin bin karatun tana yi tana tsayawa sai kuma taci gaba Aunty ma na bi haka Nurse Haleema, zuciyar Haisam ce ta raya mashi ya tashi yayi sallar Nafila tunda lokacin kar6ar Addu'a ne, yin tunanin yasa shi mik'ewa da sauri Fatuu na ganin tafiya zai yi ta k'ank'ame hannun shi ya juyo ya kalleta cikin muryar wanda ke cikin rad'ad'in ciwo ta fara fad'in "Don Allah Ya Haisam kada ka tafi ka barni....ka tsaya in ma Mutuwa zan yi in mutu a gaban ka don Allah" sosae Maganar tata ta k'aryar mashi da zuciya amman sai yay k'arfin halin komawa ya zauna yasa hannun shi guda yana shafa kanta ta sigar lallashi yace ta daina fad'in hakan ta kwantar da hankalinta in sha Allahu ba abunda zai same ta zata haihu lafiya yanzu so yake yaje yayi salla sai yayi mata Addu'a sosae he's sure in sha Allah Allah zai amsa, shiru tay tana cigaba da nishi yace bari yace ta daure taci gaba da bin karatun ta d'aga mashi kai, mik'ewa yay slowly ya zame hannun shi daga cikin nata ya juya zai tafi Aunty tace mashi yaje Office d'inta sai yayi sallar acan ya d'aga mata kai, har ya kai k'opa idanun Fatuu na akan shi yana kama handle zai bud'e ya dakata ya juyo ya kalleta idanun su suka shiga cikin na juna gaba d'aya abu iri d'aya zuciyoyin su ke ayyana masu, tunda Fatuu ta fara ciwon bata yi k'walla ba sai yanzu suka zubo mata sharr ta fara yamutsa fuska tana kuka still kallonta Haisam ke yi shima kawai sai jin k'walla yay sun zobo mashi a tashi Fuskar da sauri ya juya ya bud'e kopar ya fice,
Bayan yaje Office d'in Aunty da yake babbar likita ce a Asibitin toilet ya wuce yayo Alwala, lokacin daya fito a saman kujera yaga prayer mat ya d'aukko ya shimfid'a kafin da k'yar ya samu ya daidaita natsuwar shi ya kabbara sallar, raka'a biyu ya fara yi bayan ya gama ya d'aga hannu yana ma Fatuu Addu'a k'walla na zubo mashi, k'ara tashi yay ya k'ara yin wasu raka'a biyu nan ma yayi mata Addu'a sosae a cikin sujjada bayan ya sallame zaune yayi zugudum yana tunanin ko a wane hali take ciki yanzu gaba d'aya ba cikakkar natsuwa a tare dashi don koda yana sallar halin da ya baro ta kawai yake gani a haka dai yake yi, ji yayi yana son ya koma d'akin don yaga halin da take ciki har ya mik'e wata zuciyar ta bashi ya k'ara yin raka'a biyu Shikenan sai ya koma gaba d'aya, bayan ya kai ta farko ya mik'e yana ta biyu lokacin Nurse Chioma ta fad'o cikin d'akin duk da ba saitin kofa yake kallon ba ya fahimci nurse ce ta shigo don ta gefen idonshi ya hango fararen kayanta, wani irin bugu gaban shi ya shiga yi ba kamar da yake da sauri ta shigo cikin d'akin tsoro da kuma fargabar shigowar tata ne suka cika mashi zuciya har baisan ko yana karatun sallar ma daidai ba a haka dai yaci gaba da yin sallar bai yi tunanin ya yanke ta ba, lokacin daya sallame a tsorace ya juyo ya kalleta kawai sai gani yay ta washe baki ta furta "Sir, Your Wife has deliver....." ai tun kafin ta rufe baki da sauri ya mik'e ya nufo hanyar k'opar saida ta tuna mashi da takalman shi sannan ya juyo ya dawo inda suke maimakon ya saka a k'afafun nashi kawai sai ya kwashe su a hannu ya juyo a haka ya fito daga Office d'in Nurse Chioma na biye dashi saida ta k'ara yi mashi magana tace da ya saka takalman don nan Asibiti ne akwai had'ari tafiya ba takalma sannan ya zubo su k'asa ya saka tare da furta mata thanks kafin yaci gaba da tafiya da saurin da shi bai san ma in ya ta6a yin irin shi ba a rayuwar shi, yana bud'e kopar ya shiga sai kuma yaja ya tsaya turus ido a ware yake kallon Fatuu dake faman jujjuya kai tana nishi da k'arfi tare da cize baki maida idon shi akan Aunty dake a gaban k'afafun Fatuu an lullube tun daga kan cikinta zuwa saman k'afafunta dake a d'age da blue d'in yadi, jiki a sake ya k'arasa gaban gadon cikin d'aurewar kai yace ma Aunty aka ce kuma ta haihu, d'an girgiza kai Aunty tayi tare da d'an murmushi don ta fahimci a rud'e yake kan matar tashi shiyasa har bai ji kukan jaririn daya karad'e cikin d'akin ba, da hannu tay mashi nuni da saitin da Nurse Haleema take tana goge jaririn dake ta faman tsanyara kuka sai lokacin ya dawo cikin hayyacin shi ya tuna da yan biyu ne aka ce a cikin nata, tambayar Aunty yay bata haiho d'ayan bane ba tare data kalle shi ba ta d'aga mashi kai tace gashi nan yana hanya tace yaje wurinta da sauri ya nufi wurin kan Fatun ya zauna tana ta kallon shi tana cigaba da nishi idon ta na d'an lumshewa ya kai hannu ya fara shafa kanta dayan kuma ya kamo hannunta guda yana "Sorry Baby kin kusa haihuwan d'ayan ki daina jin ciwon" kai ta jinjina mashi, bai dad'e da zama ba ta k'ara sautin nishin da take da sauri Aunty ta fara fad'in tay pushing sosae saidai da ta fara yunkurin sai kuma ta bari, hannu Aunty ta d'aga ma Haisam tace ya sata taci gaba da pushing ga Babyn nan nason fitowa aikuwa da sauri ya shiga ce mata "Push Baby..." da tayi sai ta bari tana ta jujjuya kai fuskar shi a yamutse yake ce mata don Allah ta daure tayi Ko babyn ya fito ta huta, a wahalce ta shiga fad'in "Ya Haisam k'arfi na ya k'are wllh....bazan iya ba" da k'yar take Maganar muryarta ta shak'e gaba d'aya ya k'ara rud'ewa ya juyo ya kalli Aunty ya fad'i mata abunda tace Auntyn tace mashi dole sai tayi hakan zata samu ta fito da shi don komawa yake, hannu Haisam ya kai ya ruk'e gaba d'aya shoulder d'in Fatuu yana k'ok'arin daidaita natsuwar shi cikin d'an kwantar da murya yace "listen Baby, I know you're strong so you can do it, nasan ke ba raguwa bace, pls ki daure ki pushing sosae" kai ta d'aga mashi tana nishi ta baki lokacin Aunty ta k'ara cewa tayi Haisam d'in ya hau jinjina mata kai still yana ruk'e da kafadun nata da k'arfi ya furta "push Baby...." ta daddage da iya karfinta na k'arshe tayi wani uban nishi kanta ya d'ago sama can kuma sai ta koma ta fad'a kan gadon yaraf idanunta suka shiga lumshewa a wahalce take fad'in ta gaji bazata iya ba ita dai, juyawa Haisam yay a hautsine yace "Aunty she's completely exhaust........" Bai k'arasa ba sakamakon jaririn da Aunty ta d'ago sama wani irin fari fat dashi jikinshi sam ba wata kazanta sosae Subul dashi gashi k'aton gaske, janye jaririn tay suka had'a ido da Haisam ta d'an tabe mashi baki tare da d'age gira ido waje yake kallon ta da babyn, nurse Chioma ta kira ta mik'a mata shi ta nufi inda d'ayan yake tana washe baki tare da Fad'in "What an Identical twins!" ta k'arasa inda nurse Haleema take nan suka shiga santin jarirai, ganin Aunty na niyyar maida idonta kasan Fatun yasa da sauri Haisam yace mata amman dai su kenan ko d'an girgiza kai tayi da d'an murmushi tace mashi da sauran wasu biyun ya gane wasa take hakan yasa shi yin shiru ya maida idon shi kan Fatuu da idanun ta ke a lumshe ya kai hannu ya rungumota jikinshi ta gefen shi yana mata sannu tare da fadin Shikenan ta haihu zata huta ta d'aga mashi kai, bin ta da ido yay wani irin mugun tausayinta ne ke ratsa mashi zuciya bama ita kad'ai ba gaba d'aya halittar mace tausayin su ya kama shi don yanzu yasan ainihin micece haihuwa, a hankali ya juya ya kallo inda jaririn suke cikin warming bed ana masu weighting and apgar test Aunty ce ke yi Nurse Haleema na rubuta sakamakon da take fad'i mata a jikin wani d'an white board dake a jikin bango, bayan an gama yi ma na farko komai Aunty ta kawo shi ta kwantar dashi rub da ciki a saman k'irjin Fatuu ta kalli Haisam da yayi zuru tana murmushi tace "Wato hankalin ka gaba d'aya yana akan Baby shi yasa ko tambayar abunda muka samu baka yi ba" murmushi yay cikin cool voice d'in shi ya tambayeta ta d'an harare shi tace bazata fad'a ba ya duba da kanshi, saida zata bar wurin sannan tace mashi duka Baby boys ne ya d'aga kai, gaba d'aya suka zuba ma jaririn da ta aje ido Fatuu ta bud'e idanunta sosae tana kallon jaririn da d'an murmushi wata irin k'aunar shi taji tana ratsa mata zuciya a hankali ta d'ago hannu guda ta d'aura a jikin shi ta rungume shi, zuba ma jaririn ido Haisam yay mamaki ne fal a cikin ranshi ta yadda Babyn shi ta haifo yaro haka ya shiga raya dole ta wahala ace daga jikinta ya fito kuma ta d'an wannan opening d'in ya k'ara raya iya wannan kawai ya isa mutum ya jinjina girman Ubangiji, kai jaririn ya fara d'agowa da alama yana jin k'arfi ne don tubarkallah K'ato ne, kallon Haisam yake yana yi yana rufe idon yana d'an lila kan shi Fatuu dake ta kallon shi tana sakin murmushin farinciki ta d'aga ido ta kalli Haisam cikin disasshiyar murya ta furta "He's looking at his Dad" Murmushi shima Haisam d'in yayi tace ya d'auke shi yay d'an shiru gani yake kaman in ya d'auke shi a haka ba kaya zai iya ji mashi ciwo a hankali yace ta bari a saka mashi kaya ta jinjina kai tana dai ta murmushi ita kanta tsantsar mamaki take a cikin ranta na wai wannan d'anta ne ita ta haife shi kuma tare da Haisam, k'ara kallon Haisam tayi tace "Allah ya amsa Addu'a ta kaga Babyn sak kai ne" kai ya d'aga mata don shima yaga Kamannin shi sosae yaron ya d'aukko, Nurse Chioma ce tazo zata d'aukki Babyn don a saka mashi kaya da murmushi ta kalle su ta taya su murna Haisam ne yayi mata godiya ita kuma Fatuu ta jinjina mata kai gaba d'ayan su da murmushi akan fuskokin su tana tafiya Aunty tazo da d'ayan jaririn shima ta d'aura shi a saman k'irjin Fatun tana fad'in gashi nan shima yaji dumin Mom Fatuu ta d'an fad'ad'a murmushin ta a hankali ta kai hannu ta d'ago da fuskar shi da alamun mamaki take kallon shi sai kuma ta d'aga kai ta kalli Haisam da shima fuskar jaririn yake kallo har Aunty zata wuce yace mata wannan ba shine aka d'auka ba yanzu ta d'an girgiza mashi kai tana yar dariya tace d'ayan ne identical twins ne suma sunyi k'ok'arin samun abunda za'a rink'a bambanta su sun kasa Haisam ya d'aga kai ta tafi, shima wanda aka kawon bin shi sukai da kallo suna ta murmushi gaba dayansu wani irin dad'i ne ke ratsa zukatan su ganin jariran, bada jimawa ba aka kawo Hassan d'in an shirya shi cikin set d'in fararen kayan sanyi masu kyaun gaske, Haisam aka mik'a ma shi saida ya gyara zama sannan ya amshe shi aka d'auki d'ayan shima don a shirya shi, shima kayan sanyin aka saka mashi amman nashi light blue ne anyi hakane don a iya bambanta su Aunty ce ta kawo shi tana ta murmushi tace ma Fatuu gashi itama ta d'aukka a hankali tace to ta fara k'ok'arin tashi Haisam yasa hannu guda ya taimaka mata ta zauna ta jingina da kan gadon dake a jikin bango har lokacin kuma rabin jikinta na lullube da blue yadin da aka rufa mata, sai faman washe baki suke gaba d'ayan su suna kallon yaran tsabar farinciki ma sun kasa magana sai dariya kawai suke yaran na d'an bud'e ido a hankali can na hannun Haisam ya fara kai hannu baki yana d'an tsotsa kallon Fatuu yay yace wannan k'ilan yunwa yake ji wane madara ake basu yaje ya samo bata san lokacin da tasa dariya mai d'an sauti ba tace su ai yanzu breast milk ake basu sai bayan wani lokaci ake fara basu Madara ya d'an jinjina kai a hankali yace yasan shi ake basu kawai yayi tunanin akwae wani Madara da za'a iya basu kafin ta warware sosae ta fara feeding nasu ta d'an girgiza mashi kai, dawowa wurin su Aunty tayi itama ta zauna bakin gadon daga wurin kan Fatuu ta d'ayan bangaren kallon Haisam tayi tana murmushi tace mashi yayi masu huduba ne sai lokacin ma shi ya tuna da hakan yace Ok bari yayi ta tambayi to wane suna za'a saka masu yay d'an jimm sai kuma ya juya ya kalli Fatuu da itama kallon nashi take tana son ta ji sunan da zai saka masu ganin haka yasa Aunty cewa bari ta basu wuri sai suji dad'in za6ar masu sunayen bayan ta mik'e tsaye tace ma Haisam sai yayi sauri don lokacin salla ya kusa yace to, dama tun lokacin da Fatun ta haifo na biyun akai kiran sallar farko,
"Wane suna kike so a sa masu?' calmly ya tambayeta tana murmushi tace mashi ai shine Baba ko shi yakamata ya zabar masu ya d'an girgiza kai yace ita tafi cancanta ta za6a masu sunan da take so tay d'an jimm kafin tace to shi ya zaba ma d'aya