Showing 6001 words to 9000 words out of 512766 words
Chapter 3 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1531
nema don kaina ya k'ulle gaba d'aya gashi dama ba cikakkar lafiya ce da ni ba" tana k'arasa Maganar tasa k'asan rigarta tana goge kwallan idonta, tsananin tausayin ta ne ya kama Abbas d'in ya shiga bata baki yana ta kwantar da Hankalinta in sha Allahu Allah zai kawo mafita duk yadda za'ai baza'a yi auren nan ba, sosae gwaggo tay mashi godiya da Addu'oi daga baya yay mata sallama yace sai yazo goben suka fito gaba d'aya, daga bakin kopar fita gwaggo ta komo ciki ita kuma Fatuu ta bishi har waje, jikin Motar ya jingina yana kallonta kanta a k'asa gaba d'aya duk tausayin su yake ji yasan dole zuciyoyin kowannansu na cikin wani hali, kiran sunanta yay ta d'ago suka had'a ido yace ta daina damuwa in sha Allahu zai yi iya bakin k'ok'arin shi wurin ganin ba'ayi mata Auren da mutumin ba tay d'an murmushi had'i da jinjina mashi kai yace gobe in Sha Allah zasu je can ai masu Addu'a tace to daga haka yace ta shiga ciki ta saida tay mashi Allah ya kiyaye hanya sannan ta juya ya bita da ido har ta shige cikin gida kafin ya koma cikin Motar yaja ya tafi, tana shiga d'akinta cike da farinciki ta nufi gado ta fad'a tana sakin murmushi Haulat dake kallonta ta tambaye ta ya akai ta fad'i mata game da tafiyar da Gwaggo zatayi da Ya Abbas itama d'an murmushin tay tayi fatan Allah ya kaisu lafiya yasa ayi nasara suna cikin haka wayar Fatuu tayi ringing ta kai hannu ta d'aukko tana d'aura idonta akan screen d'in wayar mood d'in ta ya canza tay rejecting kawae ta kife wayar Haulat dake bin ta da ido ta tambayi waye kaman bazata fad'i mata ba sai kuma tace "wanccan d'an iskan ne" nan take haulat ta fahimci wanda za'a aura mata ne, k'ara kira yay Fatun ta buga uban tsoki ta kai hannu a fusace ta d'auki wayar ta saka ta a silent kawae ta sake aje ta ganin yadda ranta ya 6aci yasa haulat yin d'an murmushi tace "ina ma ace Ya Haisam yaji kawae yazo yasa a d'aura auran da shi" wani kallo Fatuu ta bita da shi baki bud'e Haulat d'in ta d'age mata gira tace "in shine ai nasan zaki yarda ko?" D'an ta6e baki Fatuu tay tace Uhmm kawae Haulat dake dariya tace "ko yanzu kin daina son nashi ne?" Shiru ta d'an yi sai kuma ta sauke ajiyar zuciya yanayin fuskar ta ya k'ara canzawa a sanyaye tace "kema Haulat ai kin san in nace na daina son shi nayi k'arya tunda son gaskiya nike mashi kawai dae nasan ba ta6a samun shi zanyi ba zan ta wahala ne shiyasa na rarrashi zuciya ta kawai" d'an girgiza kai Haulat tay itama dama ta fad'a ne kawae tasan har Abada ba lalle ta daina son Ya Haisam ba saidae ta hakuran kawae,
"Amman in ace yace zai aure kin zaki yarda" wani kallo Fatuu tay mata tace "Fad'a ma 6ata baki ne Haulat" gaba d'aya su kai yar dariya Haulat tace "in Allah ya kaddaro mijin ki ne duk aje a dawo wllh sai kin aure shi kina zaune zai kawo kan shi ma" d'an ta6e baki Fatuu tay tana murmushi ta gyad'a mata kai kawae, a ranar da daddare gwaggo tace suzo su je gidan su Haulat tace ma Fatuu ta d'aukko kayan da zatai amfani dasu don a can zata zauna kafin ta dawo Fatun tace to, bayan sun je Innar su Haulat ta matuk'ar girgiza da jin abunda ke faruwa da gwaggo ta mata bayani, itama sam bata goyi bayan ai auran ba daga baya tay ma gwaggon fatan sa'a, tare dasu Fatuu ta dawo zasu kwana nan da safe sai su koma gidan su Haulat d'in. Washe gari ana gama sallar Asuba Abbas yazo ba 6ata lokaci gwaggo dasu Fatuu suka fito bayan an rufe gidan suka shiga cikin Motar Abbas ya gaishe da gwaggo tay mashi ya kwanan iyali su Fatuu ma suka gaida shi, a daidai bakin lungun su Haulat aka aje su suna d'aga masu hannu suna Allah ya tsare saida suka ga tafiyar au sannan suka nufi gidan.
Alhamdulillah kafin la'asar wurin k'arfe ukku na rana suka isa da yake Motar gida ce ba tsaye tsaye tun suna akan hanya Abbas ya tsara ma gwaggon abunda yake ganin yakamata suyi har ya nuna ace Fatun tana da wanda suke son juna hakan zai sa asamu sauk'in matsala tsakanin Mahaifinta da kuma shi Ard'on in Allah yasa aka janye batun Auren sosae gwaggo ta fahimce shi, a kopar gidan Motar Abbas ta parker duk idanun mutanen dake wurin ya dawo kanta gwaggo ce ta fara fitowa akan idon Kamalu da Amadu dake zaune a bakin teburin saida raken shi aikuwa da sauri suka tashi suka nufo ta baki washe itama dariyar take masu, a gabanta suka tsaya suna mata sannu da zuwa tana amsa masu lokacin Abbas ya fito shima yana sanye da manyan kaya shadda ash da hula da takalma yayi too match Amadu na ganin shi ya nufe shi da Murmushi shima murmushin yake mashi yana zuwa ya mik'a mashi hannu suka gaisa Kamalu ma ya zagaya suka gaisa, tuni su Mino sun je sun fad'o ma Yadikko zuwan gwaggon, kallon su Abbas gwaggo tay tace mashi su shigo suka nufi hanyar shiga gidan ta lura da kallon da Mutanen gidan dake zaune a wajen ke mata basu da niyyar yi mata ko sannu da zuwa hakan yasa itama ta share su sai Abbas ne ke d'aga masu hannu yana gaida su suma suna d'aga mashi, suna shiga Yadikko ta tarbe su da fara'a tana masu sannu da zuwa tace su shiga ciki mutan gidan kaman ko yaushe sai lek'owa suke suna ba ido hakkin shi yan kad'an ne suke ma gwaggon sannu da zuwa itama ta gulma, a falo suka zauna yadikko ta zauna a k'asa tana gaishe su fuska a sake Abbas ya amsa mata su Amadu ma suka zazzauna shiru ta d'an biyo baya can gwaggo tace "sai muka ga Amarya ta dawo" d'an rausayar da kai yadikko tay bata ce komai ba gwaggon ta tambayi ina Baffan Fatuu tace yana d'aki bai jin dad'i ne bari tay mashi Magana, saida ta fara kawo masu Abinci da fura sannan taje ta fad'o ma Baffan game da zuwan nasu suka dawo tare yana biye da ita, bayan sun shigo a k'asa ya durkusa yana gaida gwaggon da fulatanci ta amsa Abbas ma ya gaishe dashi suka k'ara yin shiru Yadikko ce ta katse shirun da ce masu su ci Abincin gwaggo tace ba damuwa zasu ci basu jin yunwa ne don sun ci Abinci a hanya, maida idon ta tay kan Baffa da ya sadda kai k'asa ta tambaye shi yayi ma Ard'o Maganar halin da ake ciki ya d'ago yace eh,
"To ya kukai da shi ne?" Gwaggo ta tambaya shiru ya d'an yi yana motsa baki kafin cikin rawar murya yace "ran shi ne ya 6aci yace wai ai ba wani abu bane ita tamkar Matar shi ce tunda ya biya sadaki, yanzu haka yau zuwa gobe ya bani in je in dawo da ita in ba haka ba ko bata nan za'a d'aura Auran wai sai mijin nata yaje ya d'aukko ta k'arshe ma cewa yay mu muka k'ulla komae muka sa ta gudu duk yabi mutan gidan ya fad'a masu mun sata ta gudu" wani murmushin takaici gwaggo tay ta maida idonta kan Abbas da shi ma 6acin rai ke kwance akan fuskar ta shi tace "d'ana Abbas kaji wani son zuciya ko" jinjina mata kai yay kawae gwaggon tace "to sam bazan yarda a lalata ma yarinya rayuwa ba wllh tunda shi kan shi kawae ya sani..." Maida idonta kan Baffan tay ta tambaye shi ance yaron a Jimeta yake ko yace mata eh yaron chairman ne ta kalli Abbas tace ya ci Abinci in sun huta sai suje Jimetan farko cewa yay ya k'oshi Baffan Fatuu yace don Allah ya ci sun kwaso hanya kuma yace bazai ci Abinci ba sai a lokacin gwaggo ta gabatar masu da Abbas a matsayin abokin Haisam duk sukai mashi godiya suka ce Allah ya bar zumunci, ba laifi ya ci Abincin ba kamar da yake yadikko akwae tsafta d'akin tass yake suma tsab da su bayan ya gama ne Baffan yace su je d'akin shi sai ya huta yace to suna fitowa daga falon idon Abbas ya sauka akan Mino dake zaune da k'annanta a gefe don yadikko ta hana su shiga murmushi yay ganin sak fuskar Mom Zarah ya kirata ta mik'e taje gaban shi itama tana mashi murmushi ganin yana yi mata, dafa Shoulder d'in ta yay yace ya sunanta tace mashi Ameenatu amman Mino ake ce mata ya tambayeta tana zuwa makaranta tace mashi Eh aji ukku ma take, sake tambayar ta yay yaushe itama zata zo Katsina still murmushin take tace ai tana son zuwa su Baffane suka hana wai tunda Adda Fatuu na can jinjina kai kawae yay daga haka ya wuce Baffa dake tsaye gefe yana masu d'an murmushi yay gaba suka nufi d'akin nashi, bayan tafiyar Abbas gwaggo ma cikin k'uryar d'akin ta shiga ta shiga band'aki ta watso ruwa tazo ta kwanta don ta rage gajiya saidae tunane tunane sun hanata ta hutan don in dae ba fasa auren nan akai ba to fa bazata samu kwanciyar hankali ba gashi bata san ya zasu kwashe da iyayen yaron ba. Sai da akai la'asar wurin k'arfe biyar suka shirya tafiya Jimeta lokacin da ta fito ne ta shiga gaida Yaya duk aka bita da ido yayar ta nuna mata abun zama ta zauna suka gaisa da ita da sauran Mutanan da ta taras a d'akin Yaya ta kya6e baki tace ma gwaggon ashe sai suka sa Amarya ta gudu, yar guntun murmushi kawai gwaggon tayi Yayar tace "to dae ko bata nan sai an d'aura Auren ta gama guje gujenta ta dawo" still gwaggo bata ce mata komae ba don bata son Maganar tay tsawo k'arshe ma sai ta mik'e tay masu sallama ta nufi hanyar fita sauran Mutanan duk suka ta6e baki suka bita da d'an iskan kallo bayan ta fita aka dasa tsegumi har suna cewa a Wurin gwaggon idanun Fatuu suka k'arasa k'ek'ashewa, tana fitowa waje tay ba tare da ta tsaya gaisawa da Ard'o ba don tasan shima surutan zai mata cikin sa'a kuma bai fito waje ba ta nufi Mota da tuni Abbas ya shige dasu Amadu da Kamalu da zai nuna masu hanya Baffan Fatuu dake tsaye yay masu Allah ya kiyaye yasa a dace tace Amin ta shige. Cikin 30 minutes suka isa gidan bayan Abbas yay horn maigadi ya fito suka gaisa ya tambayi daga ina suka ce su baki ne daga rugar Baffa Ard'o yana jin haka yace ko dangin Amaryar Khalid ne banza gwaggo tay sai Kamalu ne yace mashi eh kawae yana washe baki ya juya ya bud'e masu gate d'in suka shiga, har Main falo ya shigar dasu ya fara kwala ma mai aikin Hajiya kira bayan ta fito yace taje ta sanar ma Hajiya ga bak'i anyi dangin Amaryar Khalid ne tace to bayan ta gaishe dasu ta juya, bada jimawa ba sai ga Hajiyar ta Fito tana sanye da doguwar riga jallabiya ta yafa mayafinta ta nufo su fuskarta d'auke da murmushi ta zauna, gaisawa suka shiga yi a mutunce tay masu an zo lafiya gwaggo tace lafiya lau daga baya suka d'an yi shiru can tana murmushi tace "an ce man daga ruga ko?" Gwaggo tace "eh amman ba yan rugar bane daga Katsina muke" Momy tace "Allah sarki yan biki ne kenan, ya hanya an zo lafiya" gwaggo ce ta k'ara amsa mata da lafiya lou lokacin mai aikin ta kawo masu lemu da ruwa ta aje masu ganin basu da niyyar sha Momy na murmushi tace don Allah su sha ruwa lokacin gwaggo tace "dama mun zo wurin mai gidanne in yana nan sai ai mana iso" d'an jimm Momy tay kafin tace "eh yana nan bai dad'e ma da shigowa ba kuwa" gwaggo tace to don Allah a sanar mashi tace to ta mik'e lokacin su Kamalu suka bud'e bottle water d'in da aka kawo suka tsiyaya a cup suna sha ita gwaggo ma bata jin zata iya ko shan ruwan in ba anyita ta k'are ba can sai gata ta dawo bata k'araso cikin parlon ba tace masu bismilla su shigo gwaggo ce ta fara mik'ewa tace ma Amadu yaje ya shigo da Abbas ya amsa da to, parlon chairman ta kai su yana zaune shima jallabiyar ce a jikinshi da murmushi yake kallon su suna shigowa ya nuna masu Sofas alamar su zauna, bayan sun zauna su Abbas suka shigo da sallama ya amsa masu suma ya nuna masu wurin zama duk suka zazzauna, gaisawa suka fara yi cikin girmama juna daga baya shiru ta biyo baya Chairman d'in ne yace yaji ance dangin Amaryar Khalid ne daga Katsina ko gwaggo tace "Eh hakane nice kakarta dake ruk'onta" yana fara'a yace Allah sarki to sun zo lafiya tace lafiya lau Momy ma dake zauna ta k'ara fad'ad'a murmushin ta tace mata sun zo lafiya ta amsa da Alhamdulillah suka k'ara dan yin shiru, again Chairman d'inne yace yaji ance suna son ganin shi Allah yasa lafiya sauke ajiyar zuciya gwaggon tay ta juya ta kalli Amadu tace su jira su a Parlor suka amsa da to had'i da mik'ewa, saida suka fita sannan ta maida kallon ta kan chairman ta fara Magana "Alhaji nasan ba lalle in kun san abun da ke faruwa ba..." da sauri suka had'a ido da Momy kafin ya d'an gyara zama ya tambayeta Mike faruwa ne gwaggo taci gaba "game da auran yaron ku da ita yarinyar waje na, to dae zancen da nike maka ta komo gida tun shekaran jiya tace bata son auren har tayi ikirarin mutuwa zatai in ka d'aura mata aure da shi" waro ido sukae gaba d'aya a rud'e Chairman yace to mi yay zafi haka gwaggo taci ba "koma miya faru Alhaji laifin yaron ku ne shine ya k'ara cusa mata k'iyayyar auren har hakan ta faru sakamakon wasu abubuwa da basu dace ba da ya rink'a yi mata...." Nan gwaggo ta kwashe komae ta fad'a masu a razane su duka suke kallon gwaggo har ta gama kora masu bayani chairman yasa hannu ya kama ha6arshi ya kasa cewa komae ma Saboda Al'ajabi sai faman jinjina kai yake can ya kai hannu gefenshi ya d'auki wayarshi, Khalid ya kira yace komi yake ya bari yazo yanzun nan gida yana son ganin shi daga haka yay cutting kiran, ganin yadda duk fuskokin su suka nuna tsantsar damuwa yasa gwaggo tace masu sai hakuri yara ne ka haife su amman baka haifi halin su ba jinjina kai kawae sukae bada jimawa ba sai ga Khalid d'in don dama yana kan hanya ya kira shi yayi shigar complete black riga mai dogon hannu da ma6allai harda necktie sai bakin wando mahad'in rigar da gani daga wurin aiki yake, da yar sallama ya shigo parlon ya bi bak'in fuskar da ya gani da kallo kafin ya nufi gefen Momy ya zauna suma su Abbas kallon suka bi shi da shi gwaggo a ranta tana raya gashi dai in ka ganshi a ido baka cewa yana da aibu in ma da abunda za'ai mashi sharrin shi to rashin jiki ne, gaida Dad d'in shi yay kaman bazai amsa ba sai kuma k'asa k'asa ya amsa ya kalli Mom d'in shi itama ya gaida ta kafin ya k'ara bin su gwaggo da kallo Chairman ya d'an yi gyaran murya Khalid d'in ya kalle shi yace bai ga Mutane bane sai lokacin ya gaida gwaggo ta amsa mashi tun kafin ya tanka ma Abbas ya d'an d'aga mashi hannu alamar gaisuwa shiru ta sake biyo baya,
"Khalid yaushe rabon ka da wadda zaka aura?" Yaji Dad d'in shi ya jefo mashi tambaya idon shi akan shi yace tun shekaran jiya da ya maidata daga wurin gyaran jiki dad d'in yace shikenan basu k'ara had'uwa ba Khalid yace a'a jiya ya kirata yana son yaje saidae bata yi picking ba sai kuma wani uzurin ya taso mashi bai je ba amman d'azun wurin 12:00 yaje sai brother d'in ta yace bata nan sun fita, shiru dad yay yana d'an jinjina kai idanun shi akan carpet Khalid nata bin shi da ido don ya lura da canzawar da yanayin fuskar shi tay, d'agowa chairman yay a kausashe yace "miya kai ka gidan gona da ita???" Rasss gaban Khalid ya fad'i don tambaya ce da bai tsammaci jin ta ba shiru yay ya rasa amsar da zai bashi don yasan tunda yay mashi tambayar to tabbas yasan yaje da ita gidan gonar, har saida ya sake maimaita mashi sannan cikin trembling voice yace "b...ba komae just na biya ne da ita" Dad yace "ka biya da ita ka ci zarafin ta ko!" da sauri ya girgiza mashi kai yace "No Dad na kaita ta ga gidan ne" d'an murmushin takaici Dad d'in yay gwaggo ma ta kya6e baki Abbas kuwa d'an juyar da kan shi yay gefe wani irin haushi yake bashi, Dad yaci gaba "shi maganin bacci da ka saka mata a drink fa ko shima duk cikin ganin gidan ne?" Wani abu Khalid ya had'iya ya shiga motsa baki saidae ya kasa cewa komae ganin haka yasa Dad buga hannun Sofa ya daka mashi tsawa yace "Am asking my Friend!!!" runtse ido kawae Khalid yay bai taba zaton maganar zata je kunnan wani ba bare yay tunanin iyayen shi zasu sani can ya kalli Dad d'in cike da k'arfin hali yace "Dad ban bata wannan ba" duk kowa kallon shi yake Dad d'in ya yamutsa baki yace Ok bari ya d'aukko mashi Al'qur'ani sai ya rantse mashi, ganin yana kokarin tashi yasa da sauri Khalid