Showing 156001 words to 159000 words out of 512766 words

Chapter 53 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1631

ta zauna,

"Any problem?" Ya tambaya, cikin yar inda inda tace "D...dama cewa nay kaje ka kwanta ciki ni zan kwanta anan" da k'yar ta k'arasa Maganar Saboda kallon da yake jefa mata mai wuyar fassaruwa ba Arzik'i ta sunnar da kan ta bayan tayi Maganar, maida bayan shi yay jikin kujeran still idon shi na akanta kaman bazai ce komae, jin shirun yayi yawa yasata d'an d'agowa suka had'a ido, sigh yay "ba wani abu kije ki kwanta" yanayin fuskar ta ne ya sauya hakanan taji kaman idanunta na son tara k'walla da sauri ta maida fuskarta gefe tana kikkafta idanu don kar su tarun,

"Fatuuh" ya kira sunanta ta d'an yamutsa fuska had'i da d'an cije lower lip d'inta ba tare da ta juya ba, hakanan bata son Fatuu da yake kiranta duk da sunan ta ne kuma yafi kowa iya fad'ar shi don a gayance yake furta shi amman duk da haka bata so sai take ganin kaman bai huce bane yasa yake kiran ta haka ko kuma matsayin da take dashi a wurin shi da yanzu ya ragu, k'ara kiran ta yay sai lokacin ta juya suka had'a ido fuskar shi a d'an sake yace "Don't worry am comfortable here kije ki kwanta it's already late" ba tare da ta ce mashi komai ba ta mik'e ta nufi hanyar corridor walking very slowly don duk jikinta ya mutu, idon shi na kanta still yana zaune bai kwanta ba har ta shige cikin Corridor d'in yana ji ta bud'e kopar Bedroom d'in ta shige, maida kanshi yay jikin kujera ya d'age shi yana facing sama had'i da lumshe ido ba zaka iya karantar yanayin shi ba a lokacin, ya d'an d'auki lokaci a haka kafin ya maido kan k'asa ya koma ya kwanta.

Tana shiga d'akin ta nufi bakin gado ta zauna ta zuba ma wuri guda ido, ta d'an d'auki lokaci a hakan can ta idasa hayewa saman gadon ta kwanta ba tare da ta cire gyalen ba, kwata kwata bacci ya k'aurace ma idanuwan ta sai juye juye take ba kuma wai don tana son wani abu ya kasance tsakanin su ba kawae dai ta rasa mike mata dad'i ne, sam ta kasa gane mashi har ta fara kokonton anya yana son Auren ba Hajiya ce ta matsa ba kuwa, haka tay ta tunane tunane zuciyar ta na sak'a mata abubuwa har dare ya tsala da k'yar bacci ya d'auketa shima kuma ba mai nauyi ba,

Akan kunnanta aka fara kiraye kirayen farko na sallar Asuba ta bud'e ido saidae bata tashi ba tay zuru, ba'a dad'e da gama kiran sallar ba taji an turo kopar ta kai idanun ta wurin tana ganin shi ya shigo da sauri ta rufe ido, saida ya kalleta sannan ya wuce wurin closet ya bud'e, jallabiya ya fiddo yana ruk'e da ita ya nufi laudary room jin k'arar bud'e kopar yasa ta bud'e idon nata, bayan few minutes ya fito ta sake rufe idon nata, saida taji k'arar bud'e kopar Bedroom d'in sannan ta d'an bud'e idon taga ya saka jallabiyar ya fita da alamun Alwala yayi, bayan fitar shi bada jimawa ba itama ta tashi ta saukko ta nufi laundry room d'in, Alwala tayo bayan ta fito ta wuce wurin jakunkunan ta ta ciro wata doguwar riga tare da hijab d'in da sukai salla da Haisam ta dawo bakin gado don ta saka, bayan ta gama ta shimfid'a prayer mat ta kabbara raka'atanil fajr, tana zaune tana ta tasbih har lokacin sallar Asuba yayi ta mik'e don tayi, bayan ta gama tayi Addu'oi ta shafa, zaune tay a wurin kaman an dasa ta ta kasa tashi can sai ma ta kwanta a wurin cikin sa'a bacci ya d'auke ta. Bayan an gama salla saida gari ya d'an fara washewa ya dawo daga Masallaci, a bakin kopar parlon ya cire takalman shi ya nufi kujera ya zauna, had'e hannuwan shi yay ya d'aura ha6ar shi yana kallon wuri guda ya d'an d'auki lokaci a hakan can ya mik'e ya nufi hanyar corridor, Slowly ya tura kopar Bedroom d'in ya shiga idanuwan shi suka sauka akan ta kwance kan Carpet ta takure cikin Hijab d'in kaman mai jin sanyi, tsaye yay a bakin kopar yana ta kallon ta can ya idasa shiga ciki wurin Ac ya nufa ya rage mata ita sannan ya dawo inda take, kiran sunanta yay shiru bata motsa ba ya k'ara nan ma bata farka ba, d'an jimm yay sai kuma ya rankwafa ya kai hannu ya d'an bubbuga shoulder d'in ta nan ta fara motsi ya d'ago, a hankali ta bud'e idanun ta ta d'an d'ago suka had'a ido da sauri ta k'arasa d'agowa ta tashi zaune tana gyara hijab, kallon shi ta d'an yi k'asa k'asa tace mashi ina kwana ya d'aga mata kai,

"taya zaki ji dad'in bacci anan, ki koma kan bed mana" taji cool voice d'in shi ya fad'a, bata ce komae ba ta mik'e ta d'auke abun sallar ta maida sannan ta nufi gadon idon shi akanta, ganin zata hau ba tare da ta cire k'atuwar hijab d'in ba yasa shi k'ara yi mata magana kan taya zata kwanta da ita zai iya shak'e ta nan ma ba tace komai ba tasa hannu ta cire, saida ta linke ta ta mayar wurin kayan ta sannan ta dawo still yana a inda yake ta hau saman gadon sannan ya juya ya fita, da k'yar ta koma baccin shima parlon ya koma ya kwanta, ba laifi ta d'an yi baccin don sai k'arfe tara saura ta farka ta tashi zaune tana yin yar mik'a da hamma, sosae ta ji dad'in baccin da tayi jin jikinta ba k'arfi yasa ta saukko daga kan gadon ta wuce laundry don ta shiga toilet tay wanka, d'aure da towel a k'irji kanta sanye da hular wanka ta yafo wani short a kafad'arta ta fito, gaban dressing mirror ta tsaya tana k'ara goge ruwan jikinta bayan ta gama ta aje short towel d'in ta fara shafa mai cike da fargabar kar ya shigo ya iske ta haka, bayan ta gama ta shafa su humra nan da nan k'amshin su ya karad'e Bedroom d'in, wurin jakunkunan kayan ta ta nufa bayan ta gama ta duk'a ta janyo babbar mai d'auke da kayan sawa ta bud'e nan ta fara tunanin kayan da zata saka tsakanin lace shadda da kuma atamfa ga kuma jallabiyu, ta d'an d'auki lokaci tana ruwan ido can dae ta fiddo wata hadaddar atamfa mai red flowers riga ce da straight skirt tana ganin kayan ta gane kb ne ya d'inka su don yasan kalan d'inkin da tafi so kuma dama ba'a amshi ko measurement d'in ta ba tunda yana dashi, maida jakar tay ta bud'e mai d'auke da undies ta fiddo wanda zata saka, bayan ta fiddo komae da take buk'ata ta maida jakunkunan ta dawo bakin gado, d'aura kayan tay ta fara k'ok'arin sakawa gabanta na d'an fad'uwa don kar a maimaita na Asibiti, har ta gama bai shigo ba ta koma gaban mirror tana kallon kanta abun saidae ace Tubarkallah, sosae kayan suka amshe ta shape d'inta ya fita kamar an zana ta gashi straight skirt d'in irin mai tsaga ta gaba ne rigar ma tayi mata k'yam k'yam daga wurin hips d'in ta ya bud'e sosae kaman zai fashe yadda ya kamata, d'an jujjuyawa tay tana k'are ma kanta kallo har saida ta d'an yi murmushi don ita kanta taga yadda kayan suka mata kyau, yar light make up tayi tasa red janbaki wow just Ma sha Allah, gashinta ta warware ta sharce shi har zata kulle wata zuciyar ta bata ta bar shi haka a sake tay d'an jimm tana tunanin yin hakan don bata yi mashi haka, can ta yanke barin nashi taga in zata yi kyau ta d'aukko k'aton kallabin atamfar ta lankwasa shi ta gaba ta kashe d'auri gaban sai yay kaman daurin Zarah buhari duk da bata sa komae ba ciki amman ya yi sosae da yake atamfar sabuwa ce, Jama'a ku zo kuga Fatuu ta fito sak Amarya ita kanta sai d'an sakin murmushi take wani irin kyau da bata ta6a ganin tayi ba taga yau tayi ga bak'in gashinta mai santsi yay mata rumfa a k'afadun ta abun dai sai wanda ya gani, turarurruka ta feffesa bayan ta gama ta nufi gefen gado ta kwashe towels d'in da tay amfani da hulan wanka ta wuce laundry don ta kai su, baza su tayi yadda zasu sha iska ta nufi hanyar fita, daidai tana fitowa Haisam ya turo kopar Bedroom d'in ya shigo idanun shi suka sauka cikin nata tay tsaye cak kaman an dasa ta da alamun yar razana take kallon shi shima yanayin kallon da yake Mata irin na baka tsammaci ganin mutum ba balle kuma a yadda take, sakin fuska yay yanayin d'an murmushi ya bayyana itama d'an murmushin tay da hannu yay mata alamar ta wuce ta tafi a nutse, saida ta wuce sannan shima ya wuto ya shiga laundry room d'in, a gefen gado ta zauna a ranta tana raya kar fa yace Saboda wata manufar tay kwalliyar wata zuciyar ta sake raya mata amman dama can ai yasan dai tana yin gayun ta ko, yin wannan tunanin yasa ta kauda wanccan tunanin sai kuma ta k'ara yin tunanin k'ilan wanka zai yi yakamata ta fita ta bashi wuri in ya fito ya shirya koma ta je ta had'a masu Breakfast, mik'ewa tay har zata nufi kopa sai kuma ta wuce wurin kayanta ta bud'e inda takalma suke ta curo wasu flat shoe da suka hau da kayan jikinta ta saka su sannan ta tunkari kopar fita don zuwa Kitchen.

Bayan da ta shiga cikin Kitchen d'in duk iya dubawar da tayi bata ga wasu kayan abinci ba da zata yi amfani da su sai iya su cincin da dublan kawae, tsaye tay ta jingina da drawer tana k'are ma Kitchen d'in kallo a ranta tana k'ara yaba kyan shi ganin abun take har yanzu kaman al'mara wai nan Kitchen d'in ta ne, idanunta ne suka sauka akan drawer d'in da Aunty Mareeya ta nuna mata da ta zuba mata magungunan ta, a yadda ta fad'a mata yakamata da safen nan ta sha amman sai taji kaman bazata sha d'in ba tunda tasan dalilin shan magungunan, tana ta tsaye k'arshe ma sai tay d'an tsalle ta haye saman drawer d'in ta zauna sai yan kalle kalle da yan tunane tunane take, ta d'auki kusan minti talatin a haka ta jiyo k'amshin Haisam cikin hancin ta da sauri ta kalli kopar shigowa daidai lokacin ya sawo kai cikin wurin wato tun ma kafin ya shiga wuri Kamshin shi ke sanar da isowar shi, ya yi wanka ya shirya cikin k'ananun kaya bak'in jeans da farar t-shirt daga gabanta an d'anyi style d'in bak'in rubutu, sosae kayan suka amshi jikin shi yay wani Fresh sumar nan sai kyalli take tasha gyara haka sajen shi ya kwanta luf, daga can bakin kopar ya tsaya tana ganin shi ta diro k'asa tana kallon shi, tambayar ta yay mi take yi a nan ba ga parlor ba,

"Dama na shigo inyi breakfast ne amman na duba banga kayan Abinci ba" a sanyaye tay Maganar sai faman bin bakin ta da ya sha jan jambaki yake da kallo har ta gama, ganin yadda yake ta kallon ta kaman ba zai ce komae ba yasa ta d'an sunkuyar da kan ta, "Ba sai kin yi ba za'a kawo" taji ya fad'a, d'agowa tay ta d'aga mashi kai alamar to suka ci gaba da kallon juna tana yi tana d'an maida idanunta k'asa da d'an motsa baki,

"ko kina buk'atar wani abu ne?" da sauri ta girgiza mashi kai ta nufi inda yake don ta fita ta gefen shi ta wuce, bin bayanta yay shima ya fito ganin zata shiga bedroom yasa shi ce mata taje ta zauna a parlor mana, juyowa tay ta kalle shi tace zata gyara d'akin ne ya d'aga mata kai ya wuce cikin parlon ta bi bayan shi da kallo yana tafiyar shi mai cike da k'asaita, d'an murmushi tay ta tura Kopar ta shige..............



_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2063*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


...........Bayan shigarta tsayawa tayi daga gaban gado tana tunanin abunda zatai ma d'akin don fes yake, can dai ta fara gyaran gadon ta kakka6e abunda zata kakka6e bayan ta gama da gadon laundry ta nufa ta d'aukko floor wiper ta dawo ta fara gyara tsakar d'akin, bata d'au wani dogon lokaci ba ta gama ta maida ta ta dawo da d'an towel mai taushi ta goge furniture d'in, bayan duk ta gama ta kunna burner dake jone jikin socket ta zuba turaren wuta nan da nan daddad'an k'amshi ya fara karad'e d'akin, bayan d'akin ya turaru ta cire burner d'in ta nufi Parlor don shima ta turara shi, yana zaune a inda ya saba zama ya d'an kishingid'a Tv nata aiki wayar shi ruk'e a hannun shi yana lallatsawa, tana fitowa ya d'aga ido ya d'an kalle ta kafin ya maida su kan wayar, anan wurin kayan kallon ta jona ta tsaya tana jira ya gama turaruwa, tana cikin tsayuwar aka k'wank'wasa kopar parlon Haisam ya bada izinin a shigo, Saude ce ta shigo hannun ta ruk'e da d'an babban basket mai d'auke da kayan Breakfast ta tsaya daga bakin kujerun tana gaishe da shi ya amsa tare da d'an kallon ta ta nufi c-table zata d'aura yace ta kai dining area ta amsa da to ta wuce, Fatuu na tsaye tana kallon ta da murmushi tun da ta shigo itama murmushin take mata ta nufo in da take, tana zuwa Fatuu ta amshi basket d'in tana gaishe da ita ta fad'ad'a murmushin ta tana amsawa, godiya Fatun tayi mata k'asa k'asa da murya tace "Yayi kyau Amaryar mu, naji dad'in ganin ki haka sosae" yar kunya ce ta kama Fatun tana ta murmushi ta d'an sadda kan ta, tambayar ta tay mi take so a dafa masu da rana ta d'ago tace mata ko mi ta dafa tana ta murmushi tace in dai akwae abunda take so ta fad'i kar ta ji nauyi Fatun tace mata da gaske duk abunda ta dafa yayi tace to shikenan sukai sallama ta juya, kan Dining table ta kai basket d'in ta d'aura sama, juyowa tay ta nufi Kitchen plates da cups da sauran abun da zata buk'ata ta d'aukko saida ta d'auraye su tare da hannuwan ta da tay aikin sa turaren wuta sannan ta fito ta koma dining d'in, wata babbar Warmer a cikin kayan ta fiddo ta bud'e nan take wani irin k'amshi ya bugi hancin ta, Kaza ce guda d'aya babba ta gasu tasha kayan yaji da spices sun manne a jikinta daga k'asanta kuma a tsage yake tasa spoon ta juyata ta bud'e wurin nan take taga ashe Chicken and Chips ne ta ta6a gani Sauden tayi ba dai dad'i ba soyayyen dankalin turawa da dafaffen kwai ake cusawa a cikin Kazar bayan an tafasa ta sai a d'inketa a shafe ta da butter a bad'a kayan yaji da spices sai a gasa su tare a Oven, gani tay in ta yaga zata 6ata ta hakan yasa ta k'yale ta fiddo ledan sliced bread dake ciki ta aje kan table d'in sannan ta fiddo kayan tea da Flask mai d'auke da ruwan Lipton da ya sha kayan k'amshi sai wani bowl mai murfi ta bud'e shi nan kuma wainar k'wai ce murtuka murtuka, tunanin ta fara mashi magana kafin ta had'a tay hakan yasa ta nufi cikin parlon tana tafiya a hankali kai kace yanga take saidai kamata da kayan sukai ne yasa hakan, tana zuwa bakin kujeru kafin ta k'arasa taga ya mik'e ya tunkaro inda take yana zuwa saitin ta yay mata wani kallo ya wuce abun shi ta juya ta bi bayan shi, bayan ya zauna ta fara had'a mashi tea d'in tana yi tana tambayar yadda zata saka mashi komai har ta gama ta tura gaban shi ta fiddo kazar ta d'aura akan plate itama ta tura mashi ta curo waina d'aya daga cikin bowl d'in tasa a wani plate ta tura mashi sauran dake a cikin bowl d'in duka sannan ta d'aukko ledan biredi ta bud'e ta curo yanka biyar ta d'aura a gefen wainar k'wan da ta d'auka ta tura mashi ledan itama yana dai ta kallon ikon Allah, har ta gama had'a tea d'in ta ta zauna bai ta6a komae ba, hannu ya kai ya ciro slice na bread ya yagi wainar kwai ya had'e sannan ya d'auki cup d'in tea ya fara sha a nutse, kallon shi tay bayan wani lokaci ganin bai ta6a kazar ba yasa a hankali tace "gashi nan ka ci while it's still hot kar ta huce" shiru bai ce Komai ba bai kuma kalleta ba saida ya k'ara sipping tea kaman sau biyu sannan ya d'aga ido suka sauka cikin nata, da hannu tay mashi nuni da kazar ya kai idon shi kan ta kafin ya sake maido su a kanta "miye wannan d'in?" d'an waro ido tay jin wata tambaya kenan ma bai gane shi ta aje mawa ba, cikin yar inda inda tace "C... chicken and Chips ne" hannu ya kai ya d'an ruk'e ha6ar shi taji yace "mi za'ai dashi?"

"Kai na aje mawa ka ci" tay Maganar tana d'an kikkafta idanu,

"Na zama ke kenan?" ya tambaya had'i da d'an d'age mata gira ta d'an zaro ido sai kuma ta d'an tura baki "ai ba ina nufin ka cinye shi ba duka kawae naga in na 6ara ta zan 6ata ne shiyasa na

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login