Showing 405001 words to 408000 words out of 512766 words

Chapter 136 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1650

murnar samun Sameer a matsayin miji suke ana ta fad'in ta dace ba kamar k'awayenta kowa jinjina irin rabon da take da shi suke, daga baya aka kwashe kowa aka maida su gida su Hajiya Zainab wani gidan nasu daban suka sauka wanda aka sauke su Fauzy kuma aka bar masu sai masu kula dasu.

Washegari bayan sun yi lafiyayyen breakfast wurin k'arfe tara na safe aka sanar wanda za'a maida Funtua su shirya, misalin k'arfe sha d'aya na safe masu tafiyar sun gama shiryawa ciki harda su gwaggo dasu Zainab k'awayen Fauzy iya wad'anda zasu je Nasarawa mutum goma ne aka ware daga dangin Fauzyn harda Aunty Mareeya itace cikon ta goman ko k'annen su maza da mata da suka zo duk komawa za'ai dasu Fatuu dai tana cikin ayarin iyalan Senator dole taje Nasarawa, bayan anyi sallama dasu suka tafi su kuma su Aunty Mareeya suka hau shirin tafiya nasarawa, sai bayan da akayi sallar Azahar sannan aka kwashe su Amarya Fauzy ansha kwalliya tana sanye da babbar atamfa an mata half gown tasa tsadaddun takalma da jaka da kuma gyale da suka hau da kayan nata, su Aunty ma duk sun sha gayu haka ta bangaren Fatuu ma kowa dai yayi kyau. Da yake ba wani nisa ke da akwae ba tsakanin Abuja da Nasarawa basu fi awa d'aya da rabi ba suka isa garin Lafia aka nufi Government House dasu, Alhamdulillah sun isa gidan gwamnati lafiya an yi masu kyakkyawar tarba don anan suka iske su Her Excellency sun riga su isowa, komai dai na gidan mai burgewa ne a part guda aka sauke su yana da babban parlor sai kuma bedroom da zasu kai ukku ko ina an k'awata shi da lafiyayyun furniture, d'aki guda Aunty Mareeya da Fatuu da Amarya Fauzy sai Fareeda suka sauka Aunty sai washe baki take tana fad'in Allah mai iko ko yanzu ta kafa tarihi taje gidajen gwamnati har biyu na Kaduna sai kuma nan Fatuu dai sai dariya take, da yake sai da suka ci suka k'oshi a Abuja kafin su taho d'an abun sha da taunawa aka fara tarbarsu dasu daga baya duk suka kwanta suna huta gajiya, sai bayan da suka yi sallar Magrib ne aka kawo masu lafiyayyun Abinci masu saka kunnuwa su motsa harda farfesun nama da lafiyayyun gasassun kaji da abubuwan sha kai kace wata Walima zasu yi, Aunty Mareeya ce ta zuzzuba ma sauran Mutanen da suka zo tare wanda su gwaggo ne kishiyar Maman su sai Yayye da kuma k'annen mamansu da Baban su sai babbar k'awar maman tasu, bayan ta gama da kowa suma ta zuba masu duk suka zauna anan falo suna ci, suna cikin ci Hajiya Zainab tazo k'ara yi masu sannu da zuwa tana ta fara'a haka suma ta tambaye su ba wata matsala duk suka ce a'a babu komai Alhamdulillah suna godiya Allah ya k'ara d'aukaka ta amsa kafin ta kalli Fauzy data sunkuyar da kai tana murmushi tace " Daughter an sha gajiya ko?" d'an d'agowa Fauzy tayi tana murmushi ta gaishe da ita ta amsa daga baya ta tafi bayan tace ma Aunty Mareeya inda wani abu they should feel free ta kirata tayi magana, bayan tafiyarta ne suka hau yabon ta harda su Mom yadda basu d'auki duniya da zafi ba. Misalin k'arfe goma duk sunyi shirin kwanciya harma sun kwanta saidae basu yi bacci ba suna ta hira har Aunty Mareeya na tambayar Fatuu su twins tace taga tun d'azu basu wurinta tace eh suna a wurin su Aunty Laila, Aunty Mareeyar tace ba ruwan su dai basu da rigima tace mata eh gaskiya in dai suna wurin su basu wata rigima saidai ko in suna jin yunwa kuma da an basu Abinci Shikenan har kwana ma suna yi a wurin su, kallon Fauzy dake kwance jikinta sanye da kayan bacci riga da wando tayi shiru Aunty Mareeya tayi tace "Amarya ya da yin shiru ko kinata tunanin Angon naki ne" d'an murmushi tayi bata ce komai ba Fatuu ta kalleta tana murmushi Yaya Fareeda dai har tayi bacci, Aunty bata dad'e da yin Maganar ba wayar Fauzy ta fara ringing ta kai hannu ta d'aukko ta, bin screen d'in tayi da kallo ganin mai kiran Aunty Mareeya ta tambayi waye ko angon ne a hankali ta d'aga mata kai alamar eh tace to ta d'auka mana ko sai ta yanke, picking tayi ta kara a kunne a sanyaye tayi mashi sallama tana jiyo Muryar shi k'asa k'asa ya amsa suka d'an yi shiru kafin yace mata ya gajiya tayi d'an murmushi tace babu gasu nan suna hutawa yace Ok sai kuma taji yace yana son ganinta gashi nan ya turo za'ai guiding nata inda yake, shiru tayi ta kasa ce mashi komai saida yace bata ji bane sannan ta d'an had'iyi abu tace to daga haka ya katse Wayar, ganin yadda tayi tsuru bayan ta gama wayar yasa Aunty Mareeya tambayar ta ya akai ne ta d'an yi shiru tana kikkafta idanu kafin ta fad'i mata wai cewa yayi yana son ganinta zai bata sak'o, jinjina kai Aunty tayi tana murmushi tace to kuma shine tayi kwance ta tashi taje mana ta tambayi tasan inda yake ne Fauzyn na k'ok'arin tashi ta d'an girgiza mata kai alamar a'a kafin tace yace za'a zo a rakata inda yake ta d'aga mata kai still murmushi take yi haka ma Fatuu, wurin kayanta ta nufa don gaba d'aya akwatunan da aka kai mata sun taho dasu tana niyyar bude wani akwati Aunty tace mi zata dauka tace mata Hijab, ce mata tayi ta manta ba Hijabai a cikin kayan ne tace Oh ta manta wllh ta d'ago duk ta wani sha jinin jikinta, kallon Aunty Mareeya tayi tace don Allah ta ara mata Hijab d'in ta da taga tayi salla d'azun tana murmushi tace to in ta bata kuma da Asuba tana son yin salla fa ta yafa gyale mana da sauri Fauzyn tace ai zuwa zata yi ta dawo yanzu kawai abu zai fad'i mata Aunty tace Uhmm ta nuna mata jakar kayanta tace ta duba tana ciki, bayan ta d'aukko ta saka ta koma bakin gado ta zauna tana jiran mai zuwa ya tafi da ita Aunty tace mata to bazata shafa ko d'an turare ba ta tura mata baki kaman zata yi kuka tace itafa ta fad'i mata sak'o kawai zai bata Aunty tace eh duk da hakan ai yakamata a matsayin ta na Amarya aji tana zuba uban k'amshi tunda shima ta tabbatar sai taji yana sakin kamshi sosae a matsayin shi na ango, jimm tayi tana masu wani kallo ganin su duka suna mata murmushi ta yamutsa fuska tace wai miye suke ta mata murmushi da sauri Aunty tace to kuka take son taga sun yi kawai suna murmushin jin dad'i ne ganin Allah ya nufa ta zama matar aure gashi har mijin nata na kiranta, shiru tayi bata ce komai ba Aunty ta k'ara ce mata ta d'an shafa turaren tace ai ta fesa lokacin da ta saka kayan baccin duk da haka ta matsa mata kan ta k'ara fesawa, tana cikin fesawar suka ji an yi sallama a bakin kopar shigowa d'akin jin muryar mace ce yasa Aunty ta bada izinin a shigo, wata mata ce ta shigo da gani yare ce tana sanye da short skirt baki sai farar riga kanta ba kallabi sai hular gashi daga yanayin shigar ta zaka fahimci kamar uniform ne, wurin gadon ta nufo ta tsaya daga gaban shi tana murmushi ta gaishe dasu Aunty Mareeya da turanci duk suka amsa mata cikin girmamawa tace dama itace aka turo zata tafi da bride Aunty tace to ta nuna mata Fauzy tace mata gata nan, a sanyaye ta nufo matar tana zuwa gabanta ta d'an rankwafa ta gaishe da Fauzyn bayan ta amsa mata ta tambayi zasu iya tafiya ta d'aga mata kai Matar ta shige gaba Fauzy tabi bayan ta tana fara tafiya Aunty tace mata Allah ya basu Alkhairi ta juyo ta tura mata baki duk suka sa Dariya, yar tafiya sukai ta wata hanya suka iso wani Corridor Matar ta dakata ta juyo tana murmushi ta nuna ma Fauzy wata dakakkar k'opa dake kallon su tace mata nan ne part d'in shi ta shiga yana nan ciki ta d'aga mata kai Matar ta juya ta tafi, gabanta na d'an fad'uwa ta tura kopar bayan ta bud'e a d'arare sai kace mara gaskiya ta shiga, tsaye tayi daga bakin kopar tana k'are ma wurin kallo wanda madaidaicin Parlor ne mara hayaniya komai na cikin shi Fari ne da ratsin golden tsit kake ji sai Ac dake ta aiki gaba d'aya ta sanyaya cikinshi ga wani k'amshi mai dad'i dake had'e da sanyin, a ranta ta shiga raya to ko yana ina ganin parlon k'walam ba kowa, tana haka wayarta ta fara ringing har saida ta d'an tsorata da sauri ta d'agota ta kalli screen d'in, shine yake kiranta ta kai hannu tay picking tana karata a kunne kafin tace wani abu taji yace tsayuwar mi take har saida mamaki ya d'an kamata don ta fahimci yana ganinta cikin yar rawar murya tace ai bata gan shi ba, ce mata yay akwae k'opa by her left ta bud'e ta shigo ta amsa mashi da to, tana tunkarar kopar gabanta na faduwa bayan ta isa gabanta d'an jimm tay kamar bazata tura ba sai kuma ta tuna da yana kallonta hakan yasa ta tura bayan ta bud'e ta shiga, Ya Subhanallahi shine abunda na furta lokacin da nayi arba da Bedroom din, shima baida wata hayaniya amman fa ya tsaru kuma shima komai na cikin shi fari ne da golden da alama dai yana son irin had'in kalolin don ko a part d'in shi na gidan daya kaita can ma kayan haka kalar su take duk da ba design d'in su daya ba saidai na ko ina sun had'u, nan gadon round bed ne yana da table a gaban shi sai kuma nightstands da akai masu shape wanda ya hau da gadon daga can gefen gadon babbar press c ta glass ana hangen kayan dake ciki sai opposite da ita nan wani elegant dressing mirror ne suma labulayen cikin d'akin sun tsaru suna da kyau da kuma k'auri, a d'an gaban gadon golden brown d'in carpet ne an mashi ratsin fari kai da gani ba sai an fad'a ba dole zai yi laushi don wani irin gashi gashi ne dashi, daga d'an can gaban inda furniture d'in suke reading nook ne wato wurin karatu akwae yar madaidaiciyar kanta wadda itama fara ce tana d'auke da littattafai daga gabanta farin Table ne d'auke da fitilar karatu da kuma wani d'an babban jirgi kamar na wasa, gefe opposite da kantar farar leather chair ce luntsumemiya mai mazaunin mutum biyu daga gabanta kuma Ottoman ne kalar kujerar. Sauke idonta tayi akan Sameer dake kwance saman gadon yana facing sama yayin da k'afafun shi dake a bayyane suke zube k'asa suna sanye cikin flip flops jikinshi yana sanye da jar robe da gani yayi shirin kwanciya ne, fargaba ce ta kama Fauzy ba kamar data ganshi haka don ita bata yi zaton a bedroom zata same shi ba, ganin bai d'ago ba kuma tasan yasan da ta shigo yasa tayi k'arfin halin shiga ciki tana tafiya kamar wadda k'wai ya fashe mawa a ciki, daga gaban shi ta tsaya d'an nesa dashi tana kallon shi gabanta na cigaba da d'an fad'uwa, ganin bai da niyyar tashi yasa a hankali tace mashi gata yay shiru kaman bai jita ba tanata kallon fuskar shi ya lumshe ido, sai da ya d'an d'auki lokaci sannan slowly ya fara bud'e idon tana ganin haka da sauri ta maida nata idanun k'asa, bayan ya bud'e su ya yunk'ura ya tashi zaune jin motsin tashin nashi yasa ta d'an saci kallon shi karaf suka had'a ido ta shiga yan kame kame da k'yar ta k'ak'alo Kalmar ina wuni tace mashi, bai amsa ba yana dai ta kallonta da idanun shi da suke adan lumshe kaman mai jin bacci ko kuma wanda ya farka baccin bai ishe shi ba, da hannu yay mata nuni da dab da shi yace mata ta zauna, saida ta had'iyi abu sannan ta matsa don ta zauna amman ba inda ya nuna mata ba sai da ta d'an matsa sannan ta zauna, kasa kallon shi tay ta zuba ma carpet ido sosae yanzu gabanta ke fad'uwa duk da ba wannan bane karo na farko da suka samu kusanci haka tunda da akai masu hotuna ma kusancin yafi wannan sai dai a yanzu harda yanayin shigar shi ta k'ara mata fargaba don gaba d'aya chest d'in shi a bud'e yake kwantacciyar sumar da take gani wani lokacin in suna yin Vedio call da daddare yau gata tana gani a zahiri, shiru kake ji kai kace ba mutane a cikin d'akin yana ta kallonta saidai ita batasan halin da yake ciki ba amman tayi tunanin kallon nata yake, suna haka taji ya kira Sunanta da wata irin murya gabanta yay wani irin bugu da k'yar ta amsa taji ya k'ara cewa bata son kallonshi ne da turanci da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a, gaba d'aya tsoron shi ne ya fara kamata ba kamar yanayin data ji yana mata magana, shiru bai k'ara cewa komai ba can kwatsam sai ji tayi ya kawo hannu ya jawota gabanshi ta yadda jikinsu ya had'u dana juna aikuwa nan take jikin ta ya fara rawa, k'ok'arin cire mata hijab d'in jikinta ya shiga yi aikuwa ta k'ank'ameta tak'i bashi dama hakan yasa shi dakatawa yana kallonta jikinta ya shiga yin 6ari sosae da k'yar ta d'aga idanunta da suka fito waje ta kalleshi taga ya d'aure fuskar tashi har saida ta had'iyi miyau Kutt da sauri ta janye idanunta daga barin kallon shi tana haka taji yaci gaba da kokarin cire Hijab d'in da sauri ta k'ara kankameta tana numfashi da d'an karfi, dakatawa ya k'ara yi cikin yar kakkausar murya yace mata miye hakan da take yi shiru bata ce komai ba ya k'ara ce mata ko yanzu ma ba kyau ne ya ta6a ta nan take ta gane Magana ya gaya mata don ta ta6a ce mashi haka lokacin daya fara zuwa wurinta a Katsina, kasa ce mashi komai tayi sosae tsoron shi ya shigeta idanunta sukai rau rau kamar zata saka kuka a lokacin ya k'ara kawo hannu zai cire Hijab din yanzu bata hana shi ba saidai yana cireta ta k'ank'ame jikinta tun ma kafin yayi mata wani abu ta fara yin k'walla cikin rawar murya ta fara ce mashi don Allah yayi hak'uri yay shiru yana bin ta da ido sai faman kerma take, d'age mata gira yay yace dame zai yi hak'urin da sauri tace kada yay mata komai don Allah, bai ce mata komai ba still bin ta yay da ido can yay yar ajiyar zuciya yace mata ta tashi taje shiru tayi don ta fahimci kaman da fushi yay Maganar amman Saboda halin tsoron shi da take yasa da sauri ta kai hannu ta d'auki hijab d'in ta maida kafin ta mik'e har zata tafi taji muryar shi yace "Su malaman da kika ce kinji suna preaching kan taba mace da ba muharrama ba baki ji suna yi akan mace data k'aurace ma mijinta ba?" dammm gabanta ya fad'i kaman an latsa mata remote ta tsaya cak zuciyarta ta hau harbawa don kuwa tun ma kafin ta mallaki hankalinta ta san kan abun a islamiyya tana jin malaman su suna fad'in duk macen data k'aurace ma mijinta Allah yana fushi da ita kuma zata kwana mala'iku suna tsine mata da ace zata mutu a wannan daren to kuwa ba makawa yar wuta ce, tuna hakan yasa da sauri ta juyo ta kalleshi idanun shi na akanta yana mata wani kallo mai tattare da 6acin rai, motsa baki ta shiga yi idanunta suka k'ara yin raurau suka cika da k'walla abu biyu suka tarun mata a cikin zuciya na farko fargabar abunda Sameer d'in zai mata sai kuma tsoron hukuncin ta in ta k'i amince mashi, jiki a mace ta koma ta zauna cikin rawar murya tace "D..don Allah kayi hakuri, d..dama ba wani abu yasa ba kawai naga kaman ba'a gama bikin bane tunda ko su Auntyna basu tafi ba yanzu ma muna cikin yin hira ka aika a taho da ni ina tsoron kada su gane wani abu in suka ga ban koma ba tunda ce masu nayi sak'o zaka bani" banza yay mata sai ma ya juyar da fuskar shi don abunda tay mashi sosae ya 6ata mashi rai ita kad'ai ce mace ta farko da take mashi abubuwa irin haka tun farko kawai don yana sonta ne yasa yake bi da ita yadda take so ta hana ya rink'a ta6ata duk da yasan hakan da tayi daidai ne amman bai yi tunanin a yanzu da aure ya shiga tsakanin su ba zata k'ara hana shi ya ta6a ta, mata da dama sun sha bashi damar ya aikata alfasha dasu wasu har rok'on shi suke amman bai ta6a kusantar wata ba koda yake ta6a mata bai ta6a aikata hakan da sunan ya biya ma kan shi buk'ata ba kawai don abun ya zame mashi jiki ne amman shi ba don yaji dad'i yake hakan ba, harda wannan dalilin yasa abunda tayi mashi ya 6ata mashi rai ganin yana da right da zai yi abunda yake so da ita amman ta hana kuma shi bai ma da niyyar aikata mata abunda ya fahimci tayi tunanin shi zai aikata mata, k'walla ne suka shiga zubo mata tana cigaba da bashi hak'uri amman yak'i ya kalleta don bai ma san mi zai ce mata ba a yadda ran shi ya 6aci yasan yana iya 6ata mata nata ran shiyasa yay banza da ita, can ba tare daya kalleta ba taji yace Shikenan taje da sauri ta girgiza mashi kai don sai taga kaman bai huce ba hakan da ya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login