Showing 294001 words to 297000 words out of 512766 words

Chapter 99 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1579

yayan nashi an amince mashi, ba abunda zamu yi ma Allah sai godiya akan komai na rayuwar mu, Allah ya Albarkace mu da yara shiryayyu duk da yadda zamani ya canza ya cika da ababen rud'u amman hakan bai sa sun kauce hanya ba sam ni'imar da Allah yay masu bata sasu shagala ba a koda yaushe k'ok'arin su suyi abunda zai k'ara mana mutunci da k'ima suke suna mana biyayya bakin gwargwado ni ina ganin duk da mu muka haife su muna da cikakken iko dasu yakamata mu rink'a nuna godiyar mu a gare su ta hanyar faranta masu kamar yadda suke faranta mana sa6anin iyaye da dama ya'yan su sune silar bakin cikin su, wasu suna fama da cututtuka duk silar yaran su kullum Addu'ar su Allah ya shirya masu zuriar su don jarabawar yara babban jarabawa ce Saboda duk yadda hannun ka zai ru6e baka yanke shi ka yadda koda kuwa ka yanken to kuwa ba hutawa kai ba, don haka ni ina ganin mu k'ara gode ma Allah da ni'imar da yayi mana sannan duk abunda ya kawo mana matuk'ar abun nan baida illa to mu kar6e shi hannu biyu muyi mashi godiya don shi yasan sirrin dake tattare da komai sau da yawa abunda muke k'i sai kiga Alkhairi ne a gare mu" yar ajiyar zuciya ta sauke yanayin fuskar ta ya canza dama ita bawai Minon ce bata mata ba kawai tana son k'ara had'a dankon zumunci ne amman koda Nameer d'in ya nuna bai so bazata matsa mashi ba don ita mace ce mai matuk'ar son iyalinta bata da burin daya wuce ta faranta ma ya'yan nata da mijinta, d'an murmushi tay idonta akan shi tace Shikenan Allah ya tabbatar da Alkhairi, faffad'an murmushi Senator yay ya furta "Ameen My Queen" wani kallon love ta sakar mashi ya wani lumshe ido ta saki dariya, shima dariyar yay can yace "ai tunda ma yaran ba k'arewa sukai ba in sha Allah za'a had'a Auren zumuncin, yanzu kinga ga Affan nan ya tasa nan da yan shekaru zaki ga shima ya isa Aure ga Mubeen nan shima, ko bama mazan ba ai kinga ga mata nan Yasmeen da Mubeena tunda shima Yaya Othman d'in yana da Maza sai kiga an had'a, koma ba'ai dasu ba akwae wad'anda za'a k'ara haifa ai" ya k'arasa Maganar yana sakin murmushi idon shi a kanta, wani kallo tay mashi tace waye zai k'ara haifo yara ya d'age gira yace ita mana tunda tasan Aunty ba haihuwa take ba,

"ni kam dai na gama, yara takwas fa ai nayi k'ok'ari kai ma ai nasan wasa kake" Mom da ta d'an ta6e baki tace, tsuke fuska yay ya k'ank'ance ido yace wai taga wasa a idon shi har saida tay yar dariya, ce mata yay yara takwas sun mashi kad'an in son samu ne ishirin yake so to amman tunda ita kad'ai ce zai hak'ura da guda 12 yanzu sauran ta hud'u in kuma Allah yasa an k'ara samun twins Shikenan zai iya hak'ura da goma, da yanayin mamaki tace "pls are you serious?" Kai ya jinjina mata yana mata wani kallo yace yana son yaga yara yan dugui dugui a gidan, yamutsa fuska tay tace in dai wannan ne ai ga Daughter nan zata Haifa in Nameer ma yayi auren shima zasu Haifa, wani kallo yay mata mai kaman harara yace to wannan nasu ne kuma a gidan zasu cigaba da zauna ne abunda kowa kama gaban shi zai yi shi nasu yake so wanda koda yaushe zai rink'a ganin su, sosae ta kwa6e fuska tace hakan bazai yuwu ba taya yara na haihuwa itama zata wani haihu katseta yay yace ai yanzu hakan fashion ne shi ake yayi kana haihuwa yayan ka nayi ai duk Aure gare su ko, yamutsa fuska ta shiga yi a shagwabe take fad'in ita gaskiya wannan abun kunya ne wllh sai dariya yake mata can ya d'aga mata hannu yace Ok Shikenan tunda bata so ai duk ba abun daga hankali bane zai samo wata yar chick ya auro sai tazo taci gaba da haihuwar ita ta huta kawai, ai tun kafin ya rufe baki ta d'auki pillow d'in kujera ta jefa mashi ya ca6e shi yana dariya ita kuwa sai k'una k'uni take tana Allah ya gama k'aro wata a cikin gidan ta dai yi hak'uri ya auro Aunty to Shikenan an gama, d'age mata gira yay yace "to zaki k'ara haihuwa ko kuwa in nemo....." Kafin ya k'arasa ta taso da sauri ta zauna saman jikin shi ta toshe mashi baki sai 6a66aka dariya yake ni kam dai na yak'e baki abun ya ban nishad'i ashe ashe dai ko an manyanta ana buga love, ni wllh ma Senator kazo ina da k'anne don Allah ka za6i d'aya in ma basu yi maka ba akwai yar bahillot itama a kasuwa take abun ai duk namu ne🤓

cire hannun tayi har lokacin sai yamutsa fuska take shi kuma sai dariya yake, ce mashi tay don Allah yaran su sun isa haka tun kan ta rufe baki ya hau girgiza mata kai yana mata wani kallo yace "indai irin yaran da kike Haifa man ne basu ishe ni ba ina buk'atar K'ari" Murmushin jin dad'i tay ba tace komai ba ya d'age gira yace za'a k'ara Haifa mashi ko, d'an rolling eyes d'in ta tay tace Shikenan amman saidai tun daga rainon cikin har zuwa haife shi ba'a K'asar nan zata yi ba da sauri yace in hakan yayi mata ai ba matsala bane duk inda take so sai akaita kuma zai bi ta, dariya tay ta girgiza kai, tambayar shi tay ta k'ara mashi shayin ya d'aga mata kai, tashi tay daga saman jikin shi ta k'ara mashi, bayan ya shanye ta k'ara tambayar a k'ara yace a'a ya isa, mik'ewa tay zata dauke flask din yana kallon ta yace ta bari sai da Safe mana ta fitar da shi, mik'ewa tay tana d'auke da tray d'in tace mashi tana son taje ta tambayi Daughter ko akwae abunda take so kafin tay bacci ya jinjina kai ta juya, bin ta yay da kallo tana tunkarar hanyar fitan a kullum gani yake ta na k'ara mashi yarinta a maimakon manyanta, in yace ga wani nakasu nata daya sa shi k'ara Aure to yayi k'arya kawai dai yasan duk abunda Allah ya k'addaro ma bawan shi to tabbas sai ya faru da shi amman yana matuk'ar k'aunar matar shi a yanzu kam sam baida ma ra'ayin k'ara aure, su yar Munah da bahillot sai a fidda rai🤧

Misalin k'arfe goma sha d'aya da wasu mintuna su Fauzy na zaune a parlor suna kallo ita da Mino da Zainab Haulat dai tunda ta tafi kwantar da babynta bata dawo ba da alama tayi bacci, harda su Aunty Mareeya da su Yadikko ake ta kallon Film d'in, Fauzy na zaune jikinta sanye da doguwar rigar atamfa ta soke d'aurin kallabi ta yadda gashinta ya fito ta k'asa, wayarta ce dake a gefenta ta fara ringing ta kai idon ta, d'aukko wayarta tay ta zuba ma kwankwatsattsen glass d'in ido tana kallon bak'uwar lambar da ake kiran nata da ita, kaman bazata d'aga ba sai kuma tay picking, karata tay a kunne ba tare data ce komai ba tana jiran taji mi za'a je, jin shirun yayi yawa yasa tay sallama,

"Meet me in the parking lot" shine taji an fad'a da yar kakkausar murya daga haka kuma akai cutting kiran, cire wayar tay daga kunnanta ta bita da ido, tunanin waye wannan da yace ta iske shi a wurin ajiye motoci ta shiga yi, tunanin muryar waye ta fara yi can zuciyarta ta raya mata ta Sameer ce har saida gabanta yay wani bugu, kokonto ta shiga na anya kuwa shida sun tafi kuma in ma shine ta ina ya samu lambarta, zuciyar ta ce ta raya mata taje ba sai ta ga koma waye ba, mik'ewa tay ba wanda hankalin shi ya kawo kanta duk idanunsu na akan Tv, d'aki ta nufa ta d'aukko gyale ta yafa sannan ta fito tana ruk'e da wayar, tana a kan hanyar zuwa aka k'ara kira da lambar, tana d'agawa taji ance "Don't waste my time!" tana jin hakan ta tabbatar da Sameer, sauri ta shiga yi gabanta na d'an fad'uwa sai fargabar dalilin kiran nata take, lokacin data k'araso tsaye tay tana kallon cikin parking space d'in wanda yake dankam da motoci rasa a ina yake tay sai faman waige waige take, horn d'in da taji anyi ne yaja hankalinta da sauri ta kai idon kan Motar da taga ta saki danja wadda ke a d'an gabanta daga wajen parking space d'in, nufar Motar tayi a d'arare ta zagaya d'ayan 6angaren, tsaye tay a bakin kopar ta sake ji anyi horn hakan yasa ta kai hannu har rawa yake ta bud'e k'opar, wani irin k'amshi ne ya bugi hancinta ta d'an lek'a kanta yana zaune a driver seat jikinshi sanye da k'ananun kaya, murya na rawa ta gaishe dashi yay shiru tamkar bai ji ta ba kuma bai kalle ta ba, saida ya mula sannan taji yace ta shigo, a tsorace ta shiga ta zauna a kujerar gaban ba tare data rufe kopar ba hannun ta guda na ruk'e da ita, juyowa yay ya kalli kopar kafin ya kalleta ya d'aure fuska tamau nan take ta gane mi hakan ke nufi ta rufo k'opar, k'ara gaida shi tay yay d'an Jim sai kuma taga ya jinjina mata kai, shiru sukai sai Ac dake ta aiki tana bugun fuskarta, a k'alla sun d'auki wasu mintuna a haka ba tare da yace mata komai ba sai latsa waya yake tana ta d'an satar kallon shi saidai sam bata ji ta gaji da zaman ba, tana satar kallon nashi ta lura da wayar hannun shi kamar ba wadda ta fashe ba don wannan ta hango glass d'in ta lafiya lau, sai can sannan yay mata nuni da wani abu dake a gefen shi da Hannun shi taji yace ta d'auka cikin d'aurewar kai ta kai hannu ta d'aukko abun wadda yar jakar kwali ce k'arama tana da yan igiyoyin kamawa daga jikinta akwae hoto saidai bata duba ba balle ta gane ko ta miye, rik'e jakar tay a jikinta ta maida idon ta akan shi lokacin taji yace gashi nan ya biya ta damage d'in da yay ma wayarta saura ita, yamutsa fuska ta fara yi a marairaice ta fara bashi hak'uri tana fad'in Allah tasan bazata iya biyan shi ba, banza yay mata kuma har lokacin bai kalleta ba can tace mashi to ga wannan d'in ya bar shi ba sai ya biya ta ba Shikenan, kawai sai gani tay yay wani guntun murmushi wanda yafi kama da a kira shi na mamaki, sai lokacin ya juyo suka had'a ido gabanta yay wani irin bugu ganin yadda ya d'aure fuskar, "kina da waya ne?" Ya tambaya had'i da d'age mata gira wani miyau ta had'iya don ta fahimci tambayar yana nufin wayarta waya ce, a hankali ta girgiza mashi kai alamar a'a cigaba da kallon ta yay da yake wurin fayau yake da hasken fitilu kuma glass d'in Motar baida duhu sosae hasken ya d'an haska cikin Motar ba kamar da yake a inda suke akwae fitilar data haska saitin Motar, sai yan kame kame take ganin yadda ya kafeta da ido, janye idon yay taji yace ta tafi godiya tay mashi har ta juya zata bud'e Motar kamar daga sama taji yace "zaki aure yaushe?" Da sauri ta juyo ta kalle shi, sai ka rantse ba shi yay Maganar ba idon shi na akan Wayar shi, kokonto ta shiga yi na kodai kunnuwan ta ne suka ji mata ba daidai ba nan take ta gasgata hakan tana niyyar juyawa taji yace ba tambayar ta yay ba, maida idonta tay kan shi da tsananin mamaki take kallon shi har saida ta had'iyi abu kafin tace mashi ita ko rana ba'a saka mata ba ai,
"Why?" taji ya fad'a ba tare daya kalleta ba, ce mashi tay bata da wanda ta tsaida zata aura, shiru ya d'anyi kafin taji yace ko dai bata da masu sonta ne, har saida tay d'an murmushi tare da girgiza mashi kai tace mashi ana cewa ana sonta sosae itace dai bata bada dama Why, ya k'ara ce mata tay d'an jimm kafin tace akwae wanda ta tsaida zata aura amman sai ya guje ta ita kuma sai bata k'ara jin tana son wani ba, dakatawa yay da latsa wayar ya juyo ya kalleta suka had'a ido har lokacin Fuskar shi kaman a d'aure take har ta fara tunanin kodai haka yanayin fuskar tashi take, tambayar ta yay mi tay mashi ya gujeta idon shi a cikin nata, kikkafta idanu ta shiga yi ta fara bashi labarin tun farkon had'uwar ta da Mujaheed har zuwa lokacin da ta samu labarin auren shi sai dai a tak'aice take gaya mashi, lokacin data gama idanunta ne suka ciko da k'walla da sauri ta sunkuyar da kanta tasa gefen gyalenta tana goge kwallan, tana haka taji yace ai wannan ba wani abu bane he found someone da yake tunanin is better than her so he left her, da sauri ta d'ago ta kalle shi cikin muryar kuka tace "amman fa tsawon lokaci muna tare da shi in yasan bazai aure ni ba miyasa tun farko zai sa ni in yarda da shi har yayi man Alk'awarin Aure, Saboda shi bana saurarar kowa kuma yasan hakan amman ya yaudare ni, dama ashe yasan ba aure na zaiyi ba wai haka yace ma abokin shi daya fad'a man zancen yayi aure wai burge shi nike shiyasa yake tare da ni" har ta gama Maganar idon shi na akan ta, janye idon yay yana wani d'an murmushin bata san miye duniya ba shiyasa ta d'auki hakan wani babban abu, tanata goge k'walla ya juyo suka had'a ido cikin Maganar shi mai cike da isa yace mata in a relationship she shouldn't trust completely don abunda yafi hakan ma za'a iya mata koma miya faru da ita shi a wurin shi itace tay kuskure amman yasan hada don bata da wayau ne tana rayuwa a k'auye, shiru tay tana sauraran shi saidai sam bata ji komai ba a Maganganun da yayi don ita bata ma yi zaton zai iya yin magana da ita ba haka,

"You should forget about him and move on, in kin zauna a haka ke da shi waya ci gaba, I guess shine tunda yayi auren shi yana can yana enjoying life en shi, in kina ganin ya cuceki Allah yana nan ai, so you should focus on your self and your own happiness, ki ba masu cewa suna son ki chance you will definitely find the right person" jinjina mashi kai tay bayan yayi shiru, sosae taji ta samu k'warin gwuiwa ta wani bangaren kuma mamakin shi take yadda har ya yi Magana da ita haka, maida idon shi yay kan waya taji yace mata taje, godiya tay mashi ya jinjina mata kai ta juya ta bud'e kopar, bayan ta fita ta maido kopar ta rufe, nufar hanyar komawa baya tay sai murmushi take hakanan take jin wani irin nishad'i, jin k'arar rufe kopar Mota yasa ta juya baya shine taga ya fito daga cikin Motar ya nufo hanyar da take bi kawai sai ta tsaya tana kallon yadda yake tafiya irin ta kakkarfan namiji, tana tsayen har yazo saitin ta kaman bazai tsaya ba har ya d'an gota ta sai kuma taga ya tsaya taji yace mi taje jira, d'an murmushi tay tace taga ya taho hanyar ne shiyasa ta tsaya ya wuce, juyawa yay yaci gaba da tafiya, bai fi taku d'aya zuwa biyu yayi ba taga yayi mata alamun ta taho da hannun shi, a tare suke tafiyar tana daga d'an bayan shi, suna cikin tafiyar taji yace "When are you leaving?" amsa ta bashi da gobe bai ce komai ba yaci gaba da tafiyar shi can taga ya mik'o mata hannu cikin rashin fahimta ta kalle shi sai kawai ta mik'a mashi jakar hannun ta, girgiza hannun yay ya furta "Your phone" da sauri ta mik'a mashi wayar tata har zai bata ta cire password sai yaga a bud'e take don tunda ta fashe ta cire Saboda wuya take sha wurin bud'ewa, yana ta latsa wayar batare data san mi yake ba har suka iso baya, a daidai k'opar da zai bi ya tsaya ya mik'a mata wayar, amsa tay ya juya zai shige yaji tace "Kai yaushe zaka tafi?" Ita kanta sai dae jin Maganar tay ta fito, a wani slow ya juyo har saida gabanta ya fad'i ganin kallon da yay mata, motsa baki ta shiga yi ta waro ido duk ta sha jinin jikinta,
"Na zo don ke ne?" taji ya tambaya da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a, d'age gira yay yace to miyasa zatai mashi tambayar, cikin yar in ina tace "d...da..dama d'azunne naga yan gidan ku sun tafi,t.. to nayi tunanin ma harda kai aka tafi" da k'yar ta k'arasa Maganar, d'an k'ank'ance ido yay yace sa mashi ido take kenan a dabarbarce tace a'a wllh kawai don taga tare suka zo ne, yadda tay Maganar ne a tsorace yasa shi yin d'an guntun murmushi gefen kumatun shi ya d'an lotsa Fauzy ta bi shi da ido don ba K'aramin kyau murmushin ya k'ara mashi ba, juyawa yay ya nufi hanyar har zai shige ta ji da turanci yace gobe da sassafe zai tafi, da d'an d'aga murya tace "Allah ya kiyaye hanya" kaman bazai amsa ba sai kuma taji ya furta "Ameen" daga haka ya shige, washe baki Fauzy tay gaba d'aya yau abubuwan nashi burgeta suke, wucewa tay ta nufi part d'in da suke har ta kusa kaiwa taja ta tsaya, d'ago jakar kwalin tay sama tana duba hoton jiki wanda na inda ake saida wayoyi ne da kuma hotunan wayoyi kala kala da accessories nata, sauke jakar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login