Showing 150001 words to 153000 words out of 512766 words

Chapter 51 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1590

d'aya d'an murmushi sukai banda Fatuu da ta sadda kai Hajiya ta kalli Saude tace suje, ganin gwaggo na niyyar bin su yasa tace in bata gama da ita ba ta tsaya zasu jirata a parlor cike da jin nauyi tace to, don dama bata samu yi ma Fatuu Nasiha ba, bayan fitar su Fatuu ta kalli gwaggon ta kamo hannunta cikin muryar kuka tace ta zauna sai ta girgiza mata kai alamar a'a, magiya Fatun ta hau yi mata kan ta zauna tace bazata zauna a gadon suruki ba tay Maganar da yar dariya dole Fatuu ta k'yale ta sai kuma ta nuna mata bedside drawer tace to ta zauna saman ta, bata musa ba ta nufi inda take ta zauna Fatun taja jiki ta matsa kusa da ita ta k'ara kama hannunta tana yar ajiyar zuciya irin ta wanda yay kuka, bin juna sukai da ido Fuskar gwaggo da d'an murmushi ita kuma Fatun ta d'an kwa6e fuska idanunta sunyi raurau kaman zata cigaba da kukan, nannauyar ajiyar zuciya gwaggo ta sauke ta fara Magana a nutse,

"Ina matuk'ar godiya ga Allah daya nuna man wannan ranar gaki a cikin d'akin ki na aure hakan ba k'aramin abun farinciki bane, dad'in dad'awa kuma wanda ya kasance a matsayin mijin naki mutum ne da kowacce uwa zatay Alfahari in d'iyar ta ta samu irin shi a matsayin miji, bani haufi akan yadda zaki gudanar da rayuwar gidan auren ki don nasan wacece ke fiye da kowa, duk yadda ake son Mace ta kasance a gidan aurenta na tabbatar zaki kasance, saidai ina so in k'ara jan hankalin ki, a yanzu kin baro shek'ar da kika taso cikinta kika saba rayuwa kin dawo wata sabuwa da baki saba ba, dole zaki ga yanayin rayuwar ya bambanta sosae, kada kiga ai kinsan abokin rayuwar naki kun saba dole wasu abubuwan zasu canza, ki k'ara wasu ki kuma rage wasu don yadda kuke dashi a da da kuma a yanzu ba d'aya bane, yanzu shi Mijin ki ne wanda Aljannar ki na a tafin k'afar shi dole ki k'ara girmama shi kiyi mashi biyayya fiye da yadda kike mashi, ki bishi sau da k'afa sannan ki zama mai wadatuwa da duk abunda yay maki kada kiga yanzu kina da hakki akan shi kice zaki rink'a rainuwa kan abunda yay maki, duk abunda yayi maki ki zama mai godiya had'i da Addu'ar k'arin budi a gare shi, sannan kada kice zaki rink'a yawan kai mashi buk'atu kiga ai yana da halin yi maki in dai abu ba ya zama dole ba to ki hak'ura don yawan tambayar abu na sa ka gundiri mutum koda bai fito ya nuna ba, na tabbatar zai tsare maki dukkan hakk'in ki don haka sai ki zama mai kauda kai, sannan 6angaren tsafta nasan baki da kyuwa ko ganda, ki k'ara dagewa wurin gyara jikin ki da Mahallin ku ki hana idon shi ganin abunda zai munana mashi haka ki hana hancin shi shak'ar abunda zai 6ata mashi...." D'an dakatawa tay idanun Fatuu akan ta sun yi rau rau, bayan ta d'an nisa taci gaba "a zaman farkon nan da zakuyi anan zaki k'ok'ari ki fahimci miye yake so da kuma miye bai so ma'ana miye in kinyi zai ji dad'i ya faranta mashi rai miye kuma in kinyi ba zai ji dad'i ba ko zai bakanta mashi, in kin fahimci hakan sai ki kiyaye sai kiga kun zauna lafiya har in kin ji wasu na korafin tsakanin su da mazajen su kita mamaki, a k'arshe inason in ja hankalin ki game da abokiyar zaman ki, ki sani ku biyu keda shi Saboda haka kada ki zamo mai son kai, duk abunda baza ki so ya faru dake ba to itama kada ki so mata haka duk abunda kika so ma kan ki itama ki so mata, ki zauna da ita tsakani da Allah, nasan in Maganar auren ku ta bayyana rai zai iya 6aci kiyi hakuri da duk abunda zai biyo baya ba kamar daga gareta don tabbas an mata ba daidai ba, in Allah ya daidaita tsakanin ku ki ci gaba da daukarta tamkar Yayarki uwa d'aya uba d'aya kar kiyi mata kallon kishiya balle har zuciyar ki ta samu damar sak'a maki wani abu ba daidai ba game da ita, in abun farinciki ya faru da ita ki taya ta murna in na jajantawa ne ki taya ta jajantawa kada ki sake ki bari shaidan yay galaba a kanki game da ita in ma zaki kishi da ita to akan kyautata ma mijin ku ne, haka dangin shi ma ki d'auke su tamkar naki ki zauna da kowa lafiya sannan ki dage da yin ibada don neman dacewa, a K'arshe ina Addu'ar Allah ubangiji ya sanya Alkhairi a zaman ku gaba d'aya Amin,(Wannan Nasiha ce ba ga Fatuu kadai ba ga duk wata Amarya da ke karanta Novel d'in nan, duk abun da kika ji mai muhimmanci ki aiki da shi zai maki amfani in sha Allah).

A tare suka fito parlon Hajiya da Saude na zaune suna kallo, tana ganin su ta fara k'ok'arin mik'ewa Saude ma haka, Hajiya tay ma Fatuu saida safe tace taje ta jira Mijinta yazo daga haka ta nufi k'opa, kallon juna sukai ita da gwaggo ganin idanunta sun ciko yasata girgiza mata kai alamar kada tay kukan had'i da yi mata d'an murmushi da k'yar itama ta d'an yi mata gwaggon ta nufi kopa har zata fita ta juya ta kalli Fatuu da tay tsaye tay mata alamar ta koma ciki a sanyaye ta d'aga hannu ta d'an yi mata bye bye ta jinjina mata kai daga haka ta fuce, bin parlon ta shiga yi da kallo har ta kai idanunta sama kan chandelier taga an canza wata da ta fi ta da k'awatuwa, d'an murmushi tay ta sauke idanunta ta juya har zata shiga corridor sai kuma ta juya ta nufi Dining Area tana tafiya kaman mai yin sand'a, tsaye tay tana bin wurin da kallo ya burgeta sosae can ta nufi wurin table d'in ta kai hannu ta fiddo Warmer guda ta bud'e farfesun yan ciki ne sai zuba uban k'amshi yake, fiddo d'ayar tayi wadda tafi girma itama ta bud'e taga Fried Spaghetti ce da tay brown tasha vegetables daga gefe manyan soyayyun tsokokin nama ne a jere, maida murfin tay ta rufe ta jera su kan table d'in kafin ta d'auki basket d'in ta wuce, Kitchen ta shiga don ta aje nan ma ba k'aramin burgeta yay ba fuskarta d'auke da d'an murmushi take k'are mashi kallo, daga baya ta juyo ta fito ta koma Bedroom.


***** *****

Bayan Abbas ya aje su inna Zaliha direct G.r.a ya wuce, Haisam zaune acikin Bedroom d'in shi saman 3 seater ya d'an kishingid'a ya cire rigar shaddar jikin shi daga shi sai farar singlet da wandon shaddar, Video call yake da Fanan ta cikin computer d'in dake ajiye saman c-table sai faman zabga mashi shagwa6a take kan ya koma tana missing d'in shi sosae shi kuma yana rarrashin ta kan ta kwantar da hankalin ta ya kusa komowa, daga ita sai wasu yan fingilallun half vest da wandon ta wanda da kad'an ya d'ara ma pant sai faman yin abubuwan jan hankali take yanata d'an murmushi don ya gane mata sam bata da Sauk'i ta wannan 6angaren don in dai yana a kusa da ita hana mashi sakat take, suna cikin haka Abbas ya turo kopar Bedroom d'in ya d'an juya ya kalli wurin kafin ya juyo kan screen Fanan d'in ta tambaye shi waye can k'asan makoshi ya furta Abbas aikuwa da sauri ta tashi ta sauka daga saman gadon da take kwance tayi ruf da ciki ta nufi closet, Zama Abbas yay gefen shi yana sakin murmushi ya tambayi da wa yake Video call ne slowly ya furta mashi Fanan,

fad'ad'a murmushi Abbas yay yace "kace da uwar gida kake ganawa, to in ka gama ga Amaryar ka can mun kai maka tana jiran ka" wani kallo Haisam d'in yay mashi mai kaman harara, ba don Fanan d'in ta mik'e ba da tabbas sai taji abunda Abbas d'in yace, dariya sosae Abbas ke yi yana fad'in ya gama boye boyen shi dole asiri ya tonu, Haisam d'in bai tanka mashi ba saima ya maida idon shi kan Screen, lokacin Fanan d'in ta dawo ta zura doguwar riga kanta tasa hula sa6anin da babu hulan sai brown sumar ta da ta zuba gefe da gefen fuskarta duk da haka yanzun ma ta fito daga gefen wuyanta, tambayar ina Abbas d'in yake tay Haisam ya juya laptop d'in ta kalli Abbas dake dariya yace "gani nan uwar gida",

itama yar dariya take tace "uwar gida and also Amarya" wata yar iskar dariya Abbas yasa har saida haisam yay mashi wani kallo suka had'a ido hakan ya k'ara bashi dariyar da k'yar ya tsagaita Fanan d'in tace mashi ko ta fad'i ba daidai bane da sauri yace "No, no daidai kika fad'a kawae yanayin yadda kikai Maganar ne naga kaman akwae son kai a ciki, da sai ki tsaya a uwargidan ita kuma Amaryar sai tazo" wani kallo ta watsa mashi ta had'e giran sama da ta k'asa tace ashe bai k'aunar ta har haka bata sani ba, da sauri ya d'aga hannu yana fad'in tuba yake, cikin d'an d'aure fuska tace to ya daina mata irin wannan mummunan fatan ita kad'ai ce ba k'ari wannan Alk'awari ne Until death do them part itama d'in tare zata d'auke su, jinjina kai Abbas ya hau yi yana k'ok'arin danne dariyar dake ciyo shi yace to ya bari Allah ya bada ikon ruk'e Alkawari tace Amin ai yasan waye mijinta tunda ya d'auka zai ruk'e da sauri Abbas yace gaskiya ne,

"To amman wai ya akai kika k'yale shi yay zaune anan ne naga ma kaman bai da niyyar dawowa nan" d'an 6ata fuska tay "nima na k'osa ya dawo bana jin dad'in rashin shi a kusa dani duk na takura, amman yace man wani aiki ne ya ruk'e shi ya kusa dawowa" d'an ta6e baki Abbas yay ya jinjina kai yace "Tabbas hakane na manta, ko yau ma ya k'ara samun wani babban aikin mai cike da Alkhairi don haka sai kin d'an k'ara hakuri kin d'aga mashi k'afa" d'an rausayar da kai tay tace shikenan ya zata yi tana yi mashi fatan nasara, da sauri Abbas yace "Yauwa, haka ake son matar kwarae duk in mijinta yazo mata da wani Al'amari ta fahimce shi ta yiwu Alkhairi ne" murmushi tay kawai tace bari ta k'yale su suyi hira yace ok, juyo da Laptop d'in Haisam yay sukai sallama cike da nuna kauna kafin ya katse, maida idon shi yay kan Abbas dake dariya ya hau jinjina kai yace "Wato har na fara tausaya maka wllh, waya fad'a maka ana ma mata irin wannan Alk'awarin? Ai koda baka da ra'ayin k'ara Aure bai kamata kai mata Alk'awari ba don bamu ke da iko da kan mu ba komai na iya canza wa just like it happens now, yanzu in tazo ta san da zancen wane kallo kake tunanin zata maka in ma ta saurare ka kenan" bin shi da ido kawae Haisam d'in yay kaman ba zai ce komae ba, can yay sigh slowly ya furta "she was already my wife then" Abbas yace "amman ai ita bata sani ba ko" d'an d'age gira yay yace zai fahimtar da ita in buk'atan hakan ya ta so, d'age kafad'a Abbas yay yana murmushi yace Allah ya taimaka bai amsa mashi ba saima ya juyar da idon shi,

"Yanzu ka tashi muje in kai ka an bar yar mutane ita kad'ai kuma kasan ba sabawa tay ba" ba tare daya kalle shi ba yace yaje kawai, still dariya Abbas ke yi can ya mik'e ya nufi hanyar fita sai lokacin ya juyo ya kalle shi, bayan wani lokaci Abbas d'in ya dawo abunka da wanda yasan gidan hannun shi ruk'e da mug d'an tiriri na fitowa alamar abunda ke ciki mai zafi ne, wurin kujerun ya nufa ya koma inda ya tashi ya zauna ya kai hannu ya kama igiyan tea bag d'in data lek'o waje yana dan tsoma ta ciki yadda zai yi Sosae, bayan wani lokaci ya mik'a ma Haisam dake kallon shi yana murmushi yace ga shi ya sha, wani kallo ya bi shi da shi kafin ya maida kallon kan cup d'in baida niyyar amsa, k'ara kallon Abbas yay ganin irin murmushin da yake yi yasa ya fahimci ko na minene tunda ko da bikin su da Fanan ya bashi irin su, d'an girgiza mashi kai yay slowly ya furta "No need" Abbas d'in yace "kai dai ka amsa don kuwa kana buk'atar shi ko an gaya maka ita ma hakanan za'a kawo maka ita ba tare da an gyara taba ba kamar yadda kai mata aika aika" kallon shi kawai Haisam d'in ke yi baida niyyar amsa, duk yadda Abbas yay dashi kan ya amsa ya sha ya k'i k'arshe dole ya k'yale shi yace yayi ma kansa shi bari yasha Allah yaso zai mashi amfani, bayan ya shanye ya mik'e yace bari ya maida mug d'in daga can zai wuce, mik'ewa Haisam yay ya taka mashi suna zuwa bakin k'opa Abbas yace yaje ya shirya ya tafi gun yar mutane tana can ita kadae, tsaye yay yana kallon shi ya fita yana murmushi har zai rufe kopar sai kuma ya dakata yace "saura ka k'ara bari ka zama uncontrollable kazo kana fad'a man k'auli da ba'adin u feel like ur life depends on it" sai lokacin Haisam ya saki murmushin da har hak'oran shi suka d'an bayyana Abbas d'in ma dariya yake yi yace makullin Motan na nan a wurin da ya zauna ya d'aga mashi kai daga haka sukai sallama ya tafi,

Wurin kujerun ya koma ya zauna kan ta farko ya d'aura kafa d'aya akan d'aya ya zuba ma gaban shi ido da alama tunani yake yi, ya d'an d'auki lokaci a haka can ya mik'e ya fita daga wurin ya nufi hanyar corridor, saida ya d'auki kusan 30 minutes sannan ya fito da alama wanka ma yayi don ya canza kaya zuwa farar shadda Sol sai salk'i take da alama sabuwa ce bata ga ruwa ba, hannun shi d'aure da agogon diamond k'afafun shi na sanye da fararan half cover, kan shi ba hula sai nad'add'ar bak'ar sumar shi da gani an gyara ta don sai shining take yana janye da d'an madaidaicin trolley, saida yaje ya kauda laptop d'in dake saman c-table sannan ya dawo bakin dressing mirror ya d'auki Car Key ya kai hannu ya kama trolley d'in da ya aje, bayan ya latsa switch hasken d'akin ya d'auke ya bud'e kopar ya fita,


Wani irin tsoro ne ya fara kama Fatuu ganin dare yayi sosae don sha d'aya ta kusa, duk ta takure kanta a saman gadon sai wuwwurga ido take ga wata irin yunwa da take ji, lokaci bayan lokaci take duba time a jikin wayar ta dake a gabanta har ta fara fidda ran zuwan Haisam d'in ta shiga tunanin yadda zata kwana ita kadae a part d'in, can bayan wani lokaci taji ana k'ok'arin bud'e kopar aikuwa a tsorace ta tashi zaune jikinta har ya fara yar rawa kanta ba kallabi ta zaro idanu tana kallon kopar, a hankali ya turo k'opar ya shigo da yar sallamar da ko Fatun bata ma ji ba, yana shigowa idanun shi suka sauka cikin nata da ta zaro ya dakata suka bi juna da kallo, ya lura da a tsorace take hakan yasa shi k'ara yin sallama a hankali sai lokacin taji ta amsa tare da sauke nata idanun saman gadon shiru ta biyo baya, jin bai k'ara cewa komai ba yasa ta d'ago ta kalle shi, still yana tsayen suka k'ara had'a idanu cikin yar rawar murya tace "Sannu da zuwa" kai ya d'aga mata kawai ya juya ya nufi wardrobe yana janye da trolley d'in ta bishi da kallo, aje trolley d'in yay ya kai hannu gefenta ya latsa sai gashi ta fara zugewa da kanta sai lokacin Fatuu ta gane yadda ake bud'e ta, bayan ta gama bud'ewa ya kai hannu ya zuge trolley d'in ya fara k'ok'arin fiddo kayan ciki tana ta kallon shi, bayan ya saka na farko ta kai hannu ta d'auki kallabinta ta yafa saman kai ta sauka daga saman gadon a d'arare ta nufe shi, lokacin data isa ya saka na biyu yana juyowa ya ganta a gefen shi ya bita da ido, saida ta had'iyi abu sannan cikin yar in ina tace "b....bari in saka.." bai ce mata komai ba sai kawai ya juya ya tafi tabi bayan shi da kallo, Laundry room ya nufa ya tura kopar ya shige, a sanyaye ta kai hannu taci gaba da fiddo kayan tana jerawa har da su underwear d'in shi, har ta gama bai fito ba ta zuge trolley d'in ta maida shi gefe wurin jakunkunan ta ta aje, komawa tay wurin gado tana niyyar zama ya bud'e kopar ya fito fuskar shi da alamun ruwa haka k'asan hannun rigar shi mai links, tsaye tay ta kasa zaman tana kallon shi tana yi tana maida idon k'asa, tsayawa yay daga d'ayan bangaren gadon yana kallon ta kaman zai yi magana, sai da ya d'an d'auki lokaci sannan taji yayi Maganar saidae bata ji mi ya ce ba ta bishi da kallon rashin fahimta, ya gane bata ji mi yace ba ya d'an maida idon shi k'asa sai kuma ya d'ago slowly da turanci yace ta samu tsarki, kai ta d'aga mashi alamar eh tare da maida idon ta k'asa taji yace taje tayo Alwala tace to, ba tare da ta kalle shi ba ta nufi hanyar Laundry room d'in sumi sumi, lokacin data fito har ya shimfid'a prayer mat guda biyu a saman lallausan carpet d'in dake a gaban gadon yana zaune a bakin gado, wurin jakunkunan ta nufa ta bud'e ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login