Showing 327001 words to 330000 words out of 512766 words
Chapter 110 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1654
shi ai kinga baida irin cutar su ta miskilanci bawan Allah bakin shi a sake yake adai kamanta don in akai mashi irin nasu ba wuya zai zare" wata uwar dariya Fatuu ta kyalkyace da ita har Fauzy na fad'in ta dai bi a hankali kar tasa Babyn su ya fito, bayan sun gama wayar tay mata godiya suna yin sallama da sauri Fauzy tace bari tayi mata magana, bayan ta bata wayar a d'okance tay ma Aunty Mareeyar Albishir d'in Motar da aka Siya ma Fatuu, wata uwar gud'a ta rangad'a tace taba Fatuu wayar,
"Da kyau yar gidana, Wllh na taya ki murna Allah yasa Alkhairi ya tsare ya kuma raba lafiya, Wannan in dai za'a rink'a bamu kyautar Mota haka ai duk shekara sai mun haifa masa Baby" dariya kawai Fatuu ke yi tace mata sai tazo d'ani Fatun tace ai suna nan zuwa gobe da Motar a nuna mata tace to Allah ya kaimu tana jiran su, bayan sun gama wayar Mino ta kira Yadikko ta sanar mata zancen Motar sosae tay farinciki tasa aka ba Fatuu wayar ta taya ta murna da Addu'oi daga jin muryarta ba K'aramin farinciki take ba, tambayarta Fatun tay baffan su tace bai kaiga dawowa ba amman da ya shigo zata sana'ar mashi suka cigaba da yin wayar ta tambayi ya suka dawo da lafiyar Fatun duk ta amsa mata daga baya sukai sallama tana ta masu Addu'oi, bayan ta aje wayar mik'ewa tay har lokacin rigar da ta dawo da ita ce tace ma su Fauzy bari ta shiga tay wanka suka ce to kowannan su na latsa wayar shi, daga baya Mino ma ta mik'e tace bari taje gida ta canzo kaya Fauzy tace to bari ta rakata suka tafi tare,
After some minutes ta fito d'aure da towel a k'irjinta ganin ba su Fauzy a cikin d'akin yasata yin tunanin ko sun tafi parlor suyi kallo, shiryawa ta shiga yi cikin silky kayan bacci riga da wando blue bayan ta gama saka kayan ta feshe jikinta da turare, tana cikin gyara gashinta wayarta dake a saman side drawer ta fara ringing ta juya ta nufeta, saida ta zauna a bakin gado sannan ta kai hannu ta d'auko, ganin mai kiran nata yasa ta saki k'ayataccen murmushi dama da suna Airport a Abuja sun yi waya da shi, idasa hayewa tay saman gadon sannan tayi picking, tana d'auka taji yace suyi Vedio call tace to, yana zaune a cikin Office d'in shi jikinshi sanye da blue suit shirt d'in ciki fara ce sai bak'in bow tie sosae kayan sukai fitting d'in shi sumar shi a gyare luff, murmushi suka shiga sakar ma juna kafin ta gaishe da shi ya amsa yay mata sun dawo lafiya tace lafiya lou, tambayar ta Hajiya yay tace tana part d'inta su sun dawo nasu part d'in da Fauzy da kuma Mino ya jinjina mata kai still da murmushi a fuskokin su,
"What are u doing?" Ya tambaya idanunshi a d'an lumshe ta bashi amsa da wanka tayi yanzu ta gama shiryawa ya kira, shiru yay yana ta kallonta can ta tura mashi baki ya d'age gira "What?" A shagwabe tace "shine don kasan Mota d'in nan tana da kud'i sosae kak'i fad'a man ko" shiru yay yanata murmushi tace yayi Magana mana, tambayarta yay waya fad'i mata mai kud'i ce tace ita ta gane data ganta,
"nayi laifi kenan?" ya k'ara d'age gira, a shagwabe tace "a'a, kawai dai naga akwai wasu hidindimun bai kamata ka siyan man mai tsada ba sosae" yana murmushi yace "anything for you Baby ko banda halin abu indae kina so zan yi bakin k'ok'arina ki mallake shi wannan kuma ina da halin shi ne in ma fin shi kike so zan siya maki" wani kalan murmushin dad'i tayi ta lumshe ido irin yadda yake yi bayan ta bud'e a tare suka sa dariya,
"Where is our Baby, ya fara kicking?" waro ido tay ta d'an bud'e baki sai kuma ta saki dariya tace ai bai isa wannan ba ko abunda ko antenatal bata fara zuwa ba, tambayar ta yay sai yaushe zata fara zuwa tace kaman in yayi 4 Month amman ko yanzu tunda ta ya wuce 3 months zata iya fara zuwa ya jinjina mata kai, shiru suka d'an yi sai kuma tace bari babyn yaga Daddy d'inshi ta kai hannu ta d'aga rigarta farar fatar cikin da ya turo ta bayyana ta kai wayar saitin cikin, Kusan kullum ne in sukai waya sai yaga cikin wani lokacin shi ke cewa ta nuna mashi wani lokacin kuma ita ke nuna mashi kamar yanzu, maido wayar tay saitin fuskarta tana dariya shima ita yake yi yace mata yaga ya k'ara girma tace eh ai bata dad'e da gama cin Abinci ba taci ta k'oshi stiil yar dariya yake yace ai an fad'i mashi Abinci take ci sosae, jin haka yasa ta fara bashi labarin yadda a kai ta mamaki wai tayi uban kumatu harda Maganar da Hajiya tayi d'azun tace Saboda cin Abincin da take ko yan hud'u akace zata Haifa ba za'ai gardama ba dariya yay itama ita take yi, bin juna da kallo su kai mai cike da tsantsar k'auna bayan sun lafa da dariyar sun koma yin murmushi,
"Yar fillo zata Haifa yaron Ya Handsome" suna cikin kallon junan taji ya furta hakan, dariya ta k'ara sakawa ta kai hannu ta rufe idanunta alamar kunya can ta cire idanunshi akanta yana murmushi tace mashi mamaki yake a hankali ya girgiza mata kai alamar a'a, tambayar shi tay yaushe zai zo d'in yay d'an jimm kafin yace mata yay postponing lokacin sai nan da 3 weeks, k'amewa tay tana mashi wani kallo ta tsuke fuska yay d'an murmushi, yamutsa fuska ta shiga yi kaman zatai kuka tace ita dae bata yarda ba kenan ma bai yi missing d'inta ba an kusa fa wata biyu da tafiyar shi kuma shine yanzu zai ce ya d'aga lokacin da zai dawo, sigh yay yace itama tasan ko bai fad'i mata ba yana missing nata in every second yana jin kewarta a tare da shi,
"To miyasa ka d'aga dawowar" ta tambaya a shagwabe, hannu ya kai ya shafi gaban kanshi calmly yace mata an kusa bikin Saleem ne shine ya bari sai lokacin yazo so that he can stay a bit long, k'una k'unin shagwa6a ta shiga yi tana jujjuya kai ya hau bata hak'uri yana d'an murmushi, ganin tak'i barin abunda take yi yasa shi ce mata "Ok, in kina so in zo this coming week zan zo but bazan dad'e ba zan dawo tunda ina son zuwa bikin Saleem d'in amman hakan zai sa a ga na fara wasa da aiki tunda ban dad'e dana dawo ba kuma kinga na d'au lokaci anan" dakata tay da abunda take yi na shagwabar tace "Shikenan to na yarda ka bari sai lokacin ka zo amman fa sai ka maimaita man lokacin da kayi anan in kazo wata biyu da rabi zakai sannan ka koma" ta k'arasa ta d'an kumburo baki, yar dariya yay yace tayi mashi hak'uri kar tasa a kore shi a wurin aiki, kafin ta bashi amsa taji an turo k'opar bedroom d'in ta d'aga ido, Fauzy ce ta lek'o suka had'a ido tay mata murmushi, juyawa tay ta koma dama sun dawo ne shine ta lek'o taga mi Fatun ke yi,
"To ba Shikenan ba in sun kore kan sai ka baro masu K'asar su ka dawo nan kawai" ta bashi amsa,
d'age gira yay "to in na dawo ya zamu rink'a samun kud'i?" da sauri tace "to mi zamuyi da kud'in tunda muna da komai" yana yar dariya yace ta ta6a ganin rayuwa ta yuwu ba kud'i dole ai su buk'aci abubuwa kaman Abinci, kaya, da kuma kud'in yin wasu hidindimun gashi ma zata haihu dole su buk'aci kud'i,
nok'e kai tay tace "to ba sai Hajiya dasu Daddy ba su rink'a mana wannan" fad'ad'a dariyar shi yay itama dariyar take yace mata ta dai bari gara su nemi nasu yadda bazasu takura ma kowa ba har a gaji da su,
"to ai zaka iya samun wani aikin ma anan ko da baka fara ba kafin ka tafi" d'an rolling eyes d'in shi yay yace mata ai anfi samun kud'in sosae anan, tambayarshi tay wai dama Saleem bai yi aure ba yace eh an dai dad'e da akai engaging nasu to wadda zai auran tana karatu a London da za'ai auren sai tayi completing karatun a gidan shi daga baya kuma sai aka bari ta gama don shima Saleem d'in yaje ya k'aro karatu sai yanzu za'ai Auren, jinjina kai Fatun tay suka cigaba da hirar su ta k'auna, ganin ta fara hamma yace bari ya barta tayi bacci kar a takura ma Baby tay yar dariya, tambayarta yay ko akwae abunda take buk'ata da sauri ta d'aga mashi kai alamar eh yace miye take so, ce mashi tay irin tuwan Madara da gullisuwa da Popcorn d'in da yake siyo mata take son ci yace Ok zai ma Nana magana sai a kawo mata tomorrow, jin sunan Nana yasata tambayar wai tana nan yace eh, ta tambayi har yanzu bata yi Aure ba yace eh amman anyi engagement,
"Allah sarki na taya ta murna wllh, kai dai ai ka k'i ta" ta fad'a tana murmushi, shiru ya d'an yi sai kuma yace ai lokaci bai k'ure ba in tana son ya auretan da yayi Magana yasan za'a fasa da wanda aka sa masu rana sai ayi dashi, wani kallo tay mashi a d'an k'ufule tace "to a'a wllh, ba kasan da wasa nike ba" yadda ta yi ne ya bashi dariya yace "tunda tana sona da ki bari in k'ara da ita kinga kema kin yi man Alfarma irin na Fanan" yana rufe baki da sauri ta hau yamutsa tana girgiza kai tare da yarfa hannu tana fad'in "Don Allah Hubby mu bar Maganar nan, tunda an sa mata rana ba Shikenan ba nima dama ai wasa nike ko" dariya kawai yake ganin yadda tay k'utun k'utun da rai sai kace ba ita ta ja Maganar ba, ganin irin kallon da yake mata yasa taci gaba da fad'in "Allah ka gama aure, ba wata da zaka k'ara aura mu biyu mun ishe ka" dariya ya k'ara yi har jerarrun hakoransa suka bayyana sosae ita kuma taci gaba da yamutsa fuska tana k'una k'unin Allah bazai k'ara aure ba,
"Ki kwantar da hankali, tunda na same ki Baby na gama aure am just teasing you" wani irin murmushin jin dad'in Maganar ta shiga saki harda d'age kai sama, sauke kan nata tay idanunta suka shiga cikin nashi a wani slow ta lumshe mashi ido ta furta "Ina son ka har abada abadan abada Hubby" shima lumshe mata idon yay cikin cool voice d'in shi ya furta "You are the best thing that has ever happened to me Baby, you made me feel complete" murmushi kawai take saki looking at him with much luv, sallama sukai yace ta kwanta shima sun samu break ne zai yi lunch tace to ai duk yama cinye lokacin suna hira yana murmushi yace ba wani abu ai ko bai ci komai ba ganinta da yayi ya k'osar dashi tana dariyar jin dad'i tace duk da haka dai yaje ya ci Abincin kuma Baby yace ya tabbatar yaci ya k'oshi, yace a fad'i ma Babyn Dad d'in shi zai bi umarni gaba d'aya sukai dariya daga haka suka gama Vedio call d'in, kwance tay saman gadon tana ta faman sakin murmushi wani irin nishadi na ratsata ita kanta tasan ba K'aramin so take ma Haisam ba a yadda take ji yanzu da suka zama d'aya she can't survive without him, a haka bacci yay awon gaba da ita, bada jimawa ba Fauzy ta shigo don tayi wanka ganin yadda Fatun tay bacci yasa ta yin d'an murmushi, saida ta tashe ta don ta gyara kwanciyar ta sannan ta nufi hanyar laundry, d'aure da towel a kirjinta ta fito ta nufi gaban mirror don ta shafa mai bayan ta gama ta nufi closet ta bud'e, wata doguwar rigar baccin Fatuu ta fiddo don ta saka, tana gama shiryawa Mino ta shigo ita dama tun a can gida da suka je ta shiryo cikin kayan bacci riga da wando, gado ta nufa tana fad'in wllh bacci take ji Fauzy data juya tana kallonta tace ta hak'ura da ganin k'arshen film d'in kenan tace eh ai taga basu da niyyar gamawa daga haka ta haye gadon ta ja duvet ta lullube, bakin gado Fauzy ta nufa ta zauna tay shiru, gaba d'aya ganin Fatuu da ciki ya k'ara mata jin son yin aure, dama dalilin auren Fatun taji ta fara sha'awar itama tayi, "gashi ba mijin..." wata zuciyar ta raya mata har saida tay yar dariya, ita gaba d'aya ma ta kasa gane ko tana son Sameer kawai dai tasan yana burgeta, wayarta dake ruk'e a hannunta ta bud'e ta fara latsa ta, gallery ta shiga ta bud'e inda hotunan bikin Fatuu suke ta bud'o wani hoton Sameer da aka yi mashi a wurin Dinner dama tana yawan kallon hoton, k'ura mashi ido tay yana a hakimce kan kujera fuskar nan ba annuri a cikin Zuciyarta ta shiga raya shin da gaske yana sonta, in hakane to miyasa yak'i bayyana mata, kai anya ma kuwa ita sam bata tunanin hakan gaskiya don tana ganin bata kai ya so ta ba,
"in yanzu yazo yace yana son ki zai aure ki zaki amince?" wata zuciyar ta jefo mata tambayar tay shiru kamar mai nazarin wani abu lokaci guda jikinta yay sanyi tunowa da wasu abubuwa, fita tayi daga wurin hoton a sanyaye ta mik'e ta nufi bedside table ta aje wayar har zata juyo ta dakata ta kai hannu ta kunna lamp sannan ta juyo, wurin Switch ta nufa ta kashe hasken d'akin kafin ta juyo ta dawo wurin gadon ta haye gefe ta yadda sun saka Fatuu a tsakiya, lamo tay tana ta zancen zuci ta d'auki lokaci a haka kafin daga baya bacci ya d'auketa.
Washe gari bayan sun yi sallar Asuba komawa Fauzy tay ta kwanta Fatuu kau Kitchen ta nufa don ta samu abunda zata ci ita kuma Mino dama bata tashi ba don ba sallar take ba, sauran Abincin da suka ci jiya data ga bai yi komai ba ta d'umama sai ta had'a da tea, anan cikin kitchen d'in ta zauna taci bayan ta gama ta koma d'akin itama ta koma ta kwanta, wuraren K'arfe takwas saura Mino ta farka lokacin su Fatuu nata shan bacci ta wuce toilet, bata dad'e ba ta fito tayo wanka ta maida kayan baccin jikinta gaban mirror ta nufa ta shafa mai bayan ta gama ta juya ta nufi k'opa, a parlor ta d'auki hijab d'inta data cire da daddare ta saka sannan ta nufi gida don tayi shirin islamiyya.
Wuraren k'arfe sha biyu na rana suka fara shirin tafiya zaga gari kamar yadda akai jiya, bayan duk sun yi wanka suka shiga duba kayan da Fauzy zata saka saidai duk kayan Fatun bazasu yi mata daidai ba Saboda yanayin jikin su ba d'aya ba, k'arshe wata jallabiya suka samu da tayi mata daidai sabuwa ce acikin kayan lefenta da gani ita Fatun in tasa zata d'an yi mata yawa dama ko wadda taba Fauziyyar a Abuja itama tayi mata yawa yawanci dama da ganin dogayen rigunan wasu zasu yi mata yawa amman in ta saka takalma masu tsini ko tudu zasu iya yi mata daidai, itama Fatun shiryawa tay da riga half gown da straight skirt na atampa Fauzy ce tayi mata d'aurin kallabi mai kyau bayan an gama ta fiddo takalma da jaka da suka hau da atampar takalman masu dan tsini ne har Fauzy saida tay mata magana kansu tana murmushi tace ai tsinin nada gwa6i, rolling veil d'in jallabiyar Fauzy tay Fatuu kuma ta d'aukko mayafi daya hau da kayan sosae tayi kyau Fauzy ma ta yaba tace bari tayi mata hoto, atare sukai wasu hotunan bayan sun gama suka tafi gidan gwaggo don suga in su Mino sun shirya dama bayan sun yi Breakfast da suka je gaishe da Hajiya Fatuu ta sanar mata zancen fitar tasu. A can gidan suka ci Abincin rana lokacin Mino ta yi wanka kaya kawai zata saka haka Kawu Amadu ma ya shirya yana d'akin shi gwaggo ma da ita za'aje farko da tace bazata je ba suka matsa mata dole ta shirya, bayan kowa ya gama shiryawa Fatuu ta kira Tk ta sanar dashi yace gashi nan zuwa, bada jimawa ba yazo ya kira Kawu Amadu ya sanar dashi su fito, a tare duk suka fito gwaggo ta kulle gidan tana sanye da riga da zani na atampa tasa Hijab data hau da kayan hannunta ruk'e da purse, kowa fuskar shi da murmushi suka nufo Motar da sai shek'in sabunta take, ganin in suka zauna baya zasu iya matsewa yasa Kawu Amadu yace ma Mino tazo su zauna a gaba sai su kuma su ukku suka shiga baya, zagaya gari suka shiga yi suna hira cikin nishad'i ga Ac na ratsa sassan jikin su sai faman santin Motar suke ita dai Fatuu murmushi kawai take saki don ganin abun take kamar wasa wai wannan Motar ta ce, sosae suka zaga gari saida aka fara kiran sallar la'asar suka wuce gidan Aunty Mareeya, suna zuwa bakin layin gidan Fauzy ta kirata tace tazo ta tarbe su, Fauzy ce ta nuna ma Tk gidan yana Parker Motar gaban gidan sai ga Aunty Mareeyar ta fito tana sanye da doguwar rigar material ta yafa gyale saman kanta da ya bayyanar da gaban kanta daya sha kitso da alama dai tana son dogayen riguna koda yake mutane irin ta dama ita tafi dacewa da su don tana amsar su sosae, cikin washe baki ta nufo Motar duk suka bud'e suka fito, gaisawa suka shiga yi