Showing 483001 words to 486000 words out of 512766 words

Chapter 162 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1527

da sa Albarka suke yan jarida nata yi ma mutanen tambayoyi ciki harda su Fatuu aka tambayesu irin farincikin da suke ciki, bayan an gama duba ko ina saida akayi addu'o'i sannan aka fita daga nan kuma Villa aka nufa don yin lunch event, komai dai ya ƙayatar an ci an sha anyi hani'an sai fatan Allah ubangiji yasa ma kamfanin albarka ake, a ranar kusan kowacce tashar Tv saida aka nuna bikin buɗewar haka Social media Maganar sabon kamfanin kawai ake da gidajen radio ana tallata irin ayyukan da kamfanin zai rinƙa yi har da tashoshin wasu ƙasashen an nuna dasu bbc, a ranar da daddare Khalid na zaune a falon gidanshi yana kallon bikin buɗewar a NTA, lokacin da aka nuno Fatuu na magana da turanci tana murmushi shima ɗan murmushin yayi saidai nashi yafi kama dana takaici don kuwa shi yasan yayi babban rashi kuma har abada bazata fita a ranshi ba, matarshi Hafsat ce ta dawo cikin falon daga kwantar da ɗiyarsu Zarah bayan ta zauna ya nuna mata Fatuu cikin Tv ɗin yace mata wannan itace Fateema, kallon Tv ɗin tayi kafin ta juyo ta kalleshi da alamun rashin fahimta tace mashi wace Fateema yay shiru kawai tana ta kallonshi can yace mata ta garinsu yana faɗin hakan ta gane don tasan labarin da ita zai aura aka fasa saidai bata san dalilin fasawar ba, maida idonta tayi kan Tv ɗin lokaci guda taji Fatun ta burgeta ta juya da ɗan murmushi tace mashi tana da kyau sosae yay ɗan guntun murmushi kawai bai ce komai ba can sai ya miƙe ma ya nufi hanyar Bedroom ta bishi da kallo.

Bayan buɗe kamfanin ranar Monday aka fara aiki a cikin shi, a yadda Haisam ya shirya zasu ɗan daɗe anan daga baya sai su koma America suyo parking ɗin dawowa Nigeria gaba ɗaya dama ya aje aikin kamfanin da yake acan saidai ba kwata kwata ya daina aiki dasu ba akwae wanda zai cigaba da yi masu sannan shima akwae aikin da daga can za'a rinƙa yi mashi a Companyn shi, bayan wata biyu akayi bikin Jidderh da Saurayinta Sadeeq ɗan Minister wanda bayan hawan Senator Ali kujerar shugabanci ya sake ba Mahaifin nashi muƙamin Minister, ba ƙaramin shagali aka sha ba auran ɗiyar shugaban ƙasa da kuma ɗan Minister wanda anan Abuja aka ɗaura ya kuma samu halarta manyan mutane daga ko ina ciki da wajen ƙasar nan sai fatan Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba. Tuni aiki ya kankama a kamfanin Haisam anata neman aiki bayan wata ukku da buɗeshi lokacin wata guda da yin bikin Jidderh suka koma America, sati biyu sukai suka dawo acan aka baro Nameer da Mino sai sun gama karatunsu nan da shekara ɗaya da wasu watanni suma zasu baro can, Bayan dawowarsu Haisam Nigeria a yadda ya tsara zasu zauna a gidanshi ne, dama duk mazan gidansu kowa yana da gida da Dad ɗinsu ya mallaka masu saboda ba zaune suke ba dundundun yasa basu zauna acan ba suke zama a gidansu in sunzo Abuja, shi Nameer wanda yake zaune inda aka kai Mino shine nashi shima Haisam nada nashi shima a Asokoro saidai bayan dawowar tasu Dad ɗinsu yace mashi su fara zama anan gidanshi inda suka baro suka koma Villa don kar a bar gidan hakanan in aka ƙara wasu shekaru sai su koma nasu, hakan aka yi anan gidan suka zauna duk da yayi masu girma sosae, bayan dawowar su bada daɗewa ba Fanan ta samu aiki a National Hospital Fatuu kuma Haisam yay mata magana kan tafiyarta ƙasar india yin karatun Medicine amman sai tace mashi tunda anayi anan kawai ya bari sai tayi nan ba sai ta tafi wata ƙasa ba, ta yanke hakan ne don bata son yin nisa dashi yace mata amman karatun nan zai iya mata wahala tace lafiya lou in dai za'a koya mata to zata iya ya amince da hakan dama shima kawai don ya cika mata burinta ne zai barta taje India amman ba don yana son yin nisa da ita ba, cikin sa'a ta rubuta Jamb kuma points ɗinta ya kai yadda ake so don karatun likitancin, ba tare da wata wahala ba ta samu Admission a ABU Zaria Haisam ya kama mata gida mai kyau a zariar harda Security aka aje mata sannan tasa Iya ta samo mata mai aiki yar'uwarsu wadda dattijuwa ce daga can Daura suka zauna tare, lokacin data fara karatun tayi ma Haisam magana kan yasa akawo mata motarta daga Katsina amman sai yace tunda Amadu ke amfani da ita ta bari za'a kawo mata wata daga Kaduna hakan kuwa akai,

Gidan Haisam ya zama biyu Abuja da Zaria, duk Weekend yake zuwa Zaria wani lokacin a mota ko kuma ya hau jirgi zuwa Kaduna daga nan ya wuto Zaria idan kuma bai samu zuwa da Weekend ba cikin ranakun aiki yake ware rana yazo ya kwana sai ya koma wani lokacin kuma Fatun ce ke zuwa can Abujar akwae driver musamman dake kai ta, su Twins da Esha dai duk suna a Villa wurin Mom sai Weekend Fanan ke ɗaukkosu nan wurinta, sosae Fatuu ke jinjina ƙokarin da Haisam ke yi na zaryar zuwa wurinta ta san duk don ƙaunarta da yake yi ne, duk in yazo haka zatai ta mashi godiya da Addu'o'i, bayan wasu watanni da fara karatun nata suka ji Yadikko ta haihu abun yazo masu a bazata don basu san da tana da ciki ba aikuwa sunyi murna karma Fatuu da Mino suji don ta daɗe bata haihu ba sun ma ɗauka ta gama ne duk da Yadikkon bata wani manyanta ba haka shima Baffan nasu ba wani manyanta yayi ba haihuwa ta biyar ce tayi gashi namiji ta haifa dama bata da ɗa namiji Fatuu taji daɗi data haihu cikin Weekend, da satin suna ya zagayo ranar Friday tana gama lectures ta wuce Abuja washe gari Asabar suna da safe suka bi jirgi zuwa Yola ita da Esha harda Fanan, daga gidan gwamnatin Yola aka tura Motar da zata ɗaukesu harda ta Security suka wuce garin nasu, lokacin da suka isa tayi mamakin ganin yadda aikin hanyar da ake masu yayi nisa harda rijiyoyin burtsatse aka yi masu Fanan sai yaba garin take tana faɗin ya burgeta, anan ta iske Gwaggo da Haulat su jiya suka zo sosae kowa ya nuna farincikin zuwan nasu sai nan nan ake dasu ba kamar Fanan, Yadikko ma sosae tayi murnar zuwansu nan Fatuu ta bata saƙon su Mom harda Aunty kayane masu kyau da tsada atamfofi da laces sai kayan baby wanda yaci sunan Arɗo wato Ibrahim, Fatuu sai santin Babyn take harda ce ma Yadikko ta bata shi tana dariya tace ta ɗauka Fanan da tunda suka zo tana ruƙe dashi tace a'a ita za'a ba sai dariya ake masu, lokacin da Fatuu ta kira Mino Vedio call harda ƙwalla tayi ganin an haɗu banda ita, washe gari da wuri suka fara shirin tafiya saboda bayan sun koma Abuja a ranar kuma Fatuu zata wuce Zaria, tunda Aysha taga suna shirin tafiya ta shiga roƙon Fatuu ta tafi da ita harda ƙwallanta Gwaggo tace da kuma tace ita zata bi Ayshar tace a'a yanzu Adda Fatuu take son bi, to itama Fatun taji tana son tafiya da ita dama Mino na niyyar ɗaukarta tace mata ta shirya kayanta su tafi, Yadikko najin hakan tace ya za'ai ta kama ta tafi da ita ba tare da izinin mijinta ba ai bai kamata kawai ace ta ɗauketa taje masu da ita ba Gwaggo tace hakane kamata yay ace sai ta ambayi izinin shi duk da tasan bazai ƙi ba amman dai yana da kyau ta tambaye shi izni tace to, lokacin data kira Haisam ta faɗi mashi tana son tahowa da Aysha don ta nuna tana son biyota Murmushi yay yace yanzu don zatayi hakan shine sai ta faɗi mashi kada ta manta shi da ita abu ɗaya ne duk abunda yayi mata to shima yayi mashi tana murmushin jin daɗi tayi mashi godiya, wurin ƙarfe sha ɗaya na safe aka zo ɗaukar su suka yi sallama da kowa sai Godiya da Addu'ar Allah ya bar zumunci ake ma Fanan, harda uban naman suna aka basu dana su Mom dama saboda su aka fara aikin naman tunda wuri, kamar kar a rabu haka aka rakosu tare da Aysha dake ta faman washe baki harda su Gwaggo da Haulat su sai gobe zasu tafi suma ta jirgi suka zo kuma tashi zasu koma. Tare da Aysha Fatuu ta koma Zaria Asabe mai aikin Fatun ke kula da ita in ta tafi Makaranta daga baya itama Ayshar Haisam ya sakata a wata private dake anan layout unguwar da suke aka sata aji ukku na Secondary.

Cikin ɗan lokaci HAIFAT TechWorld ya samu kar6uwa a faɗin ƙasar nan, bama nan kaɗai ba harda wasu ƙasashen don kamfani ne da babu kamar sa a yankin Africa ta bangaren technology dama kuma yanzu harkar fasaha ba ƙaramin ci take ba, akwae abubuwa da dama da kamfanin ke samarwa wanda ada sai an dangana da ƙasashen turai yanzu kam nesa tazo kusa a kowacce rana ba ƙaramar riba Kamfanin ke samu ba. A kwana a tashi ba wuya a wurin Ubangiji gashi har kamfanin yayi shekara ɗaya da buɗewa anyi Addu'o'i da bikin murnar cika shekarar inda aka bayyana irin nasarorin da companyn ya samu da kuma irin ayyukan cigaba da ya kawo ma ƙasar nan aka ƙara samun masu son saka hannun jari, an ci an sha an ba ma'aikatan kamfanin masu ƙwazo kyaututtuka shima Haisam ya samu lambobin yabo abun saidai ace Alhamdulillah, bayan cikar kamfanin shekara ɗaya da wasu watanni su Nameer suka dawo Nigeria gaba ɗaya don duk sun gama karatun su, bayan dawowar su Nameer ya fara aiki shima a kamfanin a matsayin Software engineer, ganin Fatuu na karatu a Zaria kuma tana zaune a can Nameer ya yanke nemawa Mino Admission don ta yi degree kan abunda ta karanta a America wato Nursing dama matsayin diploma ce tayi, ba tare da wata wahala ba aka samar mata itama ta fara karatu a can ta zauna a gidan Fatuu, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma Fatun ba dama gidan babban gida ne kowacce da part ɗinta in mazajen su suka zo amman in suka tafi gaba ɗaya harda Aysha a part ɗin Fatuu suke zama rayuwar karatun nasu gwanin daɗi sam basu da wata matsala.

A bangaren Kamalu har ya shiga shekara ta ukku itama Farha tana cikin yin Master's Degree ɗinta a jami'ir Lagos, a bangaren soyayyarsu suna cigaba da gudanar da ita sosae saidai matsalar da Kamalun ke fuskanta a wurinta shine ta cika kishin tsiya ba dama ta kirashi taji yana waya ko bai ɗauka ba sai ta fara zargin ko da wata yake waya ko kuma ya rage sonta haka dai yake ta haƙuri don yasan saboda son da take mashi ne yasa take mashi hakan kuma shima yana son ta sosae.

Kwance tashi har Kamalun ya gama karatun shi na Degree, cikin sa'a result ɗinshi yayi kyau sosae saura kuma yin Nysc, result ɗin nashi na fitowa Fatuu tayi ma Haisam magana kan in zai yuwu ya ɗauke shi aiki a company ɗinshi tunda abunda ya karanta ya danganci aikin kamfanin yace mata lafiya lou zasu ɗauke shi daya gama Service sosae taji daɗi dama ita abunda bata so shine ace Hajiya Maryam ce ta samar mashi aiki gudun wata rana a goranta mashi, Abuja Haisam yasa aka kawo shi yin bautar ƙasan a kamfanin shi ya zauna a gidan su kullum in Haisam ɗin zai tafi aiki tare suke tafiya hakan kuma ba ƙaramin daɗi yayi ma Fatuu ba, tun ma kafin Kamalun ya zama ma'aikacin kamfanin Haisam ya yaba da ƙwazon shi cikin ɗan lokaci Kamalun ya ƙara murmurewa ya zama kalar samarin Abuja, gab da Kamalu zai kammala bautar ƙasar aka fara shirye shiryen yin za6e yayin da waɗanda ke akan mulki duk suka bayyana muradinsu na yin tazarce ciki harda Dad ɗinsu Haisam wanda shi tun kafin ma ayi za6en mutane har sun za6e shi kawai don ya zama dole sai anyi zaben amman Al'umma basu ƙi kawai yaci gaba ba don a mulkinshi sun shar6i romon demokaraɗiyya ba kaɗan ba, a cikin shekaru huɗun da yayi abubuwa da dama sun inganta kama daga ilimi, lafiya, harkar tsaro, wutar lantarki, ruwan sha hanyoyi da dai sauransu gashi an tallafa ma talakawa ta yadda da yawa sun samu abun yi yanzu tun a makaranta ake koya ma yaro sana'a don ya tashi yana da sana'ar yi haka manoma ma harkar abinci ta inganta sosae ake amfani da abincin nan gida gashi da yawan mutanen mu masu ƙwazo dake aiki a ƙasashen waje yayi yadda yay suka dawo suna ma ƙasa aiki hakan ba ƙaramin inganta bangarorin da suke aiki yayi ba ciki harda Asibitoci yanzu saidai don ra'ayin mutum yaje asibitin ƙuɗi ko ya kai ƴaƴanshi makarantun kuɗi ba wai don rashin ingancin na gwamnati ba don komai ya gyaru haka tsofaffin masana'antu da suka daɗe da daina yin aiki duk an farfaɗo dasu abun dai sai son barka (Allah ka bamu shuwagabani irin haka Alfarmar Annabin rahama (S.A.W), Amin ya Hayyu ya ƙayyum).

Bayan gudanar da za6e tuni President Ali Adamu Zakee ya koma kan kujerar shi aka ci gaba daga inda aka tsaya, bayan yin za6en Kamfanin Haisam ya cika shekara ukku batun nasarorin da ya samu ko yake samu abun ba'a magana, a yadda suke yi duk ƙarshen shekara ake raba ribar da aka samu kuma duk in suka raba sai yaba Fatuu da Fanan wani kaso mai tsoka zuwa shekaru ukkun sai gashi Fatuu ta tara kuɗi masu ɗan yawa a yadda ta tsara in suka kai kuɗin zuwa Hajjin mutum biyu sai ta biya ma Baffanta da Gwaggo. Kamalu na gama bautar ƙasar shi aka fara shirye shiryen auren shi da Farha lokacin itama ta kammala karatunta, ba ƙaramin shagali aka sha ba bikin ɗiyar Minister ɗiyar shugaban ƙasa, gaba ɗaya hidimar bikin a Abuja aka yi ta gashi wata gwaninta da Hajiya Maryam tayi ta ban mamaki itace gaba ɗaya Amaryar da Angon ta haɗa tayi masu lefe dama tunda bikin ya taho ta sanar ma Hajiya a faɗi ma su Gwaggo kada ayi ma Farhar lefe lokacin har wasu sukai tunanin ko don tasan ba lalle Kamalun yayi lefen daya dace bane sai gashi ta bada mamaki ai kuwa gaba ɗaya ƙasa ta ɗaukka sai zancen ake na ta ba talaka ɗiyarta kuma tayi masu lefe gaba ɗaya, tun kafin bikin Haisam ya roƙi Dad dinshi kan yaba Kamalun gidan da zai zauna kafin ya mallaki nashi tunda zasu fara aiki tare, ɗaya daga cikin gidajen shi na Sabuwar Estate ɗin shi dake a Gwarinpa ya ba Kamalun, ganin babban gidane yasa Haisam ɗin yace mashi ya faɗi mashi yadda zai rinƙa biyan haya Dad ɗin nashi yace dama ɗa yana haya a gidan babanshi ne ai Kamalun kamar ɗan shi yake don haka bashi yay ya zauna kafin Allah yasa ya mallaki nashi, sosae Haisam yaji daɗin hakan yay mashi godiya da Addu'oi, lokacin har Hajiya Maryam tayi niyyar basu gidan da zasu zauna aikuwa hakan da Haisam yayi ba ƙaramin daɗi yayi ma Fatuu da Amadu ba dama sune masu gudun ayi ma Kamalun abun da za'a iya goranta mashi, ko ban faɗa ba kunsan ba ƙananun kayan ɗaki akai ma Farhar ba wanda in nace zan bayyana to ni kaina wasu abubuwan bansan ya zan faɗe su ba gida dai yayi kyau! yayi kyau!! abun saidai ace Ma sha Allah Kamalu anyi auren gata abun na Allah ne, ƙarshe dai Farha ta zama matar Kamalu ɗan fillo duk wanda yaga hotonunsu da sukai na pre wedding sai ya sake kallo wasu mutanen ma har ƙaryata cewa Kamalun ɗan talakawa ne suke domin ba kama ba alama, sai fatan Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba Amin, bayan bikin Hajiya Maryam ta basu kyautar motoci masu kyau Kamalun ya fara yin aiki a Kamfanin Haisam ita kuma Farhar Mom ɗinta ta samo mata aiki a Federal Inland Revenue.

A cikin shekarar lokacin da zuwa aikin Hajji yayi Kawu Mani ya biya ma Gwaggo bayan duk Matan shi ya biya masu sunje aikuwa sosae su Fatuu sukai Farinciki itama Gwaggon tayi farincikishi sai hamdala take, bayan gama murnar biya ma Gwaggon Haisam da Nameer sukai ma su wata irin bazata Haisam ya biya ma Baffansu shi kuma Nameer ya biya ma Yadikko wayyo daɗi! farincikin yayi yawa saida aka dangana da yan koke koke, bayan tafiyarsu ne ciwo ya tasar ma Arɗo sosae har saida su Fatuu da Haisam da Nameer suka je dubashi kafin su baro saida su Haisam ɗin suka kai shi Yola asibiti aka kwantar dashi ya miƙa kulawar shi a hannun Khalid, bayan kwana biyar aka sallame shi ba laifi ya ɗan samu sauƙi suka koma gida, gaba ɗaya hankalin Baffansu Fatuu a tashe yake da jin zancen ciwon sosae yake ma mahaifin nashi Addu'a acan Makka kan Allah ya bashi lafiya, Alhamdulillah Mahajjata sun dawo gida lafiya su Gwaggo an zama Hajiya ma sha Allah, kwana ukku da dawowar su Baffa Allah yay ma Arɗo cikawa, akace mahaifi mahaifi ne duk da dama arɗon ya tsufa sosae Baffansu Fatuu yaji mutuwar tashi harda kukan shi don yasan mahaifin nashi ba ƙaramin son shi yake ba ko kafin ya rasu saida ya bar wasiyyar cewa shi zai gaji mulkin shi na arɗo kuma ya roƙe shi kan ya haɗa kan iyalin kada ya bari a samu 6araka, lokacin da Fatuu taji labarin rasuwar sosae ta damu harda kukanta sa6anin lokacin da tana yarinya bata da burin daya wuce arɗon ya rasu duk da harda ƙuruciya, washe gari suka tafi gaisuwa suna can Mom da Aunty suka je dasu Fanan da Jidderh har Aunty Laila ma tazo Lokacin Fauzy basu ƙasar shiyasa bata zo ba amman Hajiya Zainab tazo, sosae suka yi ma su Fatun kara har mai

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login