Showing 318001 words to 321000 words out of 512766 words
Chapter 107 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1633
sun gama gida suka koma lokacin da suka dawo an fara kiran sallar isha kowa ya nufi part d'in shi cike da annashuwa, basu zauna cin Abincin dare ba don duk a k'oshe suke saidai wad'anda suka fara jin yunwa ne suka d'an ci harda Fatuu acici ta k'ara.
Washe gari Monday da safe duk gidan ya rairaiye masu zuwa Makaranta sun tafi masu zuwa aiki ma sun tafi, Bayan Fatuu ta gama yin Breakfast na biyu don bayan da tayi sallar Asuba saida taci Abinci sannan ta koma bacci sai wuraren k'arfe goma saura ta tashi shine ta k'ara wani breakfast din, toilet ta wuce don tayi wanka, bayan ta fito ta shirya cikin k'ananun kaya skirt d'in jeans da t-shirt kanta ta saka hula sosae tayi kyau, zama tay bakin gado bayan ta gama tay shiru gaba d'aya ta k'agara su koma Katsina don tafiyar Haisam ta k'ara sawa taji duk zaman gidan ya gundureta, hannu ta kai ta d'auki wayarta dake a gefe ta fara lallatsawa can tay tunanin kiran Fauzy don tasan lokacin anyi break, tana fara ringing Fauzyn ta d'auka suka gaisa ta tambayi jikinta, Fatun da yanayin damuwa tace mata ita fa lafiyar ta lau wllh bata jin komai hakanan take ta zama gashi anata wuce ta a Makarantar don ma tana turo mata abubuwan da akai, tambayarta Fauzy tay an yi Maganar ranar da zasu dawo ne tace mata a'a ita ba wanda yay mata magana kan hakan da Ya Haisam kawae suka ta6a yin Maganar tun lokacin da suka tafi yace ta bari zasu dawo in aka d'an k'ara lokaci gashi yanzu har Sati biyu shiru ba'a ce zasu dawo ba, shawara Fauzyn ta bata tace ko tayi ma Hajiya Maganar taji tace mata to, yar hira suka k'ara yi kafin sukai sallama, aje wayar tay a saman gadon ta mik'e ta nufi Parlor, bayan ta fito cikin parlon ta shigo Hajiya na zaune tayi wanka tana sanye da d'aya daga cikin dogayen rigunan da aka siyo mata jiya, zama tay daga gefen ta idanun su a cikin na juna da d'an murmushi Fatuu tay mata sannu Hajiyar ta amsa tace harta shirya tace mata eh, jinjina kai tay ta maida idon ta akan Tv, shiru Fatuu tay tana tunanin ta yadda zatai mata Maganar, Hajiya na lura da yadda tay sukuku can ta tsaida idanunta a kanta tace mata ya akai ne, kallon ta tay ta fara d'an kikkafta idanu a hankali ta fara magana tace dama Maganar Makarantar ta ne wurin sati biyu kenan da komawa Fauzy ta fad'i mata anata masu karatu, d'an murmushi Hajiya tay tace "to Fateema ai lafiya tafi komai ko yanzu taya zaki wannan tafiya bacin likita ya sa dokar kar ki rink'a yin zirga zirga sosae, kiyi hakuri zaki koma ne ni kaina dole tasa nike zaune Saboda ke bawai don ina son zaman anan bane" kai Fatun ta d'aga ba tare data ce komai ba saidae yanayin Fuskar ta ya d'an canza, cigaba da kallo Hajiya tay ita kuma tay shiru ta kasa tsaida idon ta wuri guda can bayan d'an wani lokaci ta mik'e ta nufi hanyar Bedroom Hajiya ta maido idonta kan ta kafin ta maida su kan tv, tana shiga Bedroom d'in gado ta nufa tana zuwa ta fad'a kan shi nan da nan idanunta suka ciko da k'walla, kuka ta shiga yi k'asa k'asa ta rink'a kai hannu tana goge kwallan a haka bacci ya d'auketa.
Bayan komawar su Gwaggo su Kawu Amadu suka fara shiryen shiryen zana jarabawar su ta k'arshe shi kuma Tk ya fara shirin yin bautar k'asa, tun bayan da Fauzy ta dawo Katsina bata yi waya da Sameer ba tun tana saka ran zai kira har ta fidda ita kuma bata yi tunanin kiran shi ba don bata san mi zata ce mashi ba tunda shi bai kira ba gashi ta fahimci mutane irin shi ba'a cika yi masu gwaninta ba kuma basa son shishshigi, akai akai Aunty Mareeya ke kira bayan dawowar su ta tambaye ta ko ya kira, haka in taje weekend ma taita tambayar wai da gaske bai kira ba har ce mata ta ta6a yi ta kira shi ita Fauzyn tace gaskiya bazata kira ba to tace mashi mi Aunty Mareeyar tace ta gaishe dashi, ce mata tay a'a gaskiya wannan ai zak'ewa ne, daga baya ita ma Aunty Mareeyar ta rage yawan tambayar ta game dashi, saidai sosae Fauzy ke tunanin shi duk ta zauna tay shiru sai tay ta tuno fuskar shi wani lokacin tay murmushi wani lokacin ta girgiza kai ko ta bud'o hoton shi na wurin Dinner tai ta kallo.
A ranar Monday d'in bayan an tashi su Fauzy ta koma Hostel salla ta fara yi bayan ta gama ta nemi Abincin da zata ci tana gamawa ta nufi toilet tayo wanka, shiryawa tay cikin jan short skirt da bak'ar shirt mai gajeran hannu gashinta a fake, gado ta haye nan da nan bacci ya d'auketa, sai da akai sallar la'asar sannan ta tashi, bayan tayi salla jakarta ta d'aukko ta haye saman gado don tayi Assignment, bata d'auki lokaci ba ta gama ta d'aukko wani littafin ta fara yin karatu can ta aje ta kai hannu ta d'auko wayarta dake ajiye gefe, bud'eta tay ta kunna Data ta shiga WhatsApp, chat ta shiga yi da mutane daban daban harda Fatuu tana fad'i mata yadda sukai da Hajiya ta shiga kwantar mata da hankali tana nuna tasan in sha Allah bazata samu wata matsala ba a Makarantar k'ilan ma Ya Haisam d'in yayi Magana, bayan ta fita daga chat d'in Fatuu tana niyyar bud'e wani sak'o da wata k'awarta ta Funtua ta turo mata kawae taga sak'o ya shigo mata da wata bak'uwar lamba, bud'e sak'on tayi taga an rubuta,
-"How are you doing?"_
iya abunda aka rubuta kenan, maimaita karanta sak'on tayi da alamun mamaki a cikin ranta ta raya to waye wannan, har zata tambaya waye sai kuma ta lura da a Dp d'in akwae hoto, hannu ta kai ta ta6a profile d'in ya bud'e ta ta6a kan hoton, har saida gabanta ya d'an fad'i ganin Mutanen dake a Dp d'in wanda mutum ukku ne kuma duk turawa ne suna tsaye a gaban wani k'aton jirgi gaba d'ayan su k'ananun kaya ne a jikinsu kansu sanye da irin hular kwanon da injiniyoyi ke sawa duk sun yi murmushi sosae hoton yayi kyau, kan Fauzy ne ya d'aure ta shiga tunanin to su waye wad'annan ita miye had'in ta da turawa kuma, zooming hoton tay yadda zata k'ara ganin fuskokin su da kyau lokacin data sauke idonta akan na tsakiyar wanda duk yafi su tsawo sannan bai kai sauran haske ba waro ido tay a fili ta furta "Sameer!" k'ura mashi ido tay ta tabbatar ma kanta da shi d'in ne kuwa, tunani ta shiga yi inane nan da sukai hoton kamar dae ba'a Nigeria bane tana haka taga kiran video ya shigo mata da lambar, d'an jimm tay ta d'age ido kafin ta daidaita natsuwar ta gabanta na d'an fad'uwa ta latsa d'auka video call d'in ya bud'e, lokacin da idanunta suka sauka akan shi wani irin bugu gabanta yay, babbar waya ta had'u da gingimemiyar waya hakan yasa tarr take ganin shi sai kace a fili, yana kishingid'e saman wani abu data kasa gane gado ne ko kujera jikin shi sanye da vest fara K'al data bayyana surar k'arfin shi don ta kama shi zanen jikin shi ya fito rad'am kai da gani kasan yana bodybuilding ga cikin shi a d'ame yake tamkar bai cin Abinci, murd'add'un damtsen hannuwan shi dake a bud'e sun bayyanar da chocolate fatar shi da take a mulke har wani sheki take alamar hutu ya zauna yadda ya kamata, wani abun mamaki kamar yadda ake gane iyayen su da Haisam ta bambancin ido to suma launin k'wayar idon su ta bambanta tsakanin shi da Haisam sai ka natsu zaka fahimta shi Sameer d'in kwayar idon shi brown ce sa6anin Haisam da take bak'a sosae saidai gaba d'aya idanun nasu farare ne tass haka ta bangaren lips d'in su na Haisam sun yi kaman peach ne shi kuma Sameer pinkish lips gare shi, kasa magana Fauzy tay sai faman motsa baki take da d'an murmushi shi kuma ya kafeta da ido hannun shi d'aya na aje gefe d'ayan kuma sai lokacin ta lura da akan pillow ne ya d'aura shi yadda yay zaman ya d'an zame da kuma yanayin yadda hannuwan shi suke zaka gane ta laptop ne yake Vedio call d'in, baida niyyar yin Magana da k'yar Fauzy ta bud'e baki tace mashi ina wuni, shiru yay mata bai amsa ba still kallon ta yake hakan yasa ta shiga yan kame kame sai lokacin ta ankare da a yadda take ko kallabi babu a kanta gashi rigar jikinta ta kama jikin ta don roba ce boobs d'inta sunyi fam gashi ko bra bata saka ba dama kuma tana dasu Tubarkallah ta wannan bangaren har tafi Fatuu don ita kuma su ta gada a wurin Mahaifiyar su da take barumaya harda ma Hasken Fauzyn duk da shima Mahaifin su barumayen ne kuma ba bak'i bane sai dai Mahaifiyar tasu tafi haske sosae don fara ce tass gasu duk ba gajeru bane hakan yasa Fauzy ke da tsawo har Aunty Mareeya ma irin giant d'in matan nan ne tana da tsawo da jiki ita ma kuma akwae k'irji Tubarkallah,
"Can't you call people and greet them?" Sai da ya mula sannan ya furta mata hakan tare da d'an d'age mata gira, murmushin yak'e ta shiga yi cikin kama kai tace a'a tana ta son ta kira shi, shiru yay sai kuma taji yace miyasa bata kira ba ta shiga kikkafta idanuwa ta rasa mi zata ce, ganin ya kafeta da ido yasa tace mashi bata san ko bai son hakan bane, bai ce mata komai ba saima ya maida idon gefen da gani wani abu yake yi don hannun shi dake a kan gadon yana d'an motsawa, bin shi da ido tay tana ta k'are Mashi kallo ita sai ma yanzu take k'ara ganin kyaun shi sosae, tana cikin kallon nashi ya juyo suka had'a ido da sauri ta sunnar da kanta k'asa tana haka taji ya tambayi tana ina ne,
"Ina a School" ta bashi amsa a hankali bayan ta d'ago sun sake had'a ido nashi idanun a d'an lumshe kamar dai yadda Haisam ke yi, ce mata yay yanzu nan a Class take da sauri ta girgiza mashi kai "a'a ina a Hostel ne an tashi daga Class" shiru ya d'an yi kafin ya tambayi mi take a Hostel ta bashi amsa da ai ita boarder ce, maida idon shi yay gefe yaci gaba da yin abunda yake yi wanda bata san ko minene ba, bayan d'an wani lokaci ba tare daya juyo ba yace mata ba ayin Day ne School en nasu,
"A'a ana yi, ai ko matar Ya Haisam Day take ni kuma Saboda ba garin nike ba yasa nike yin boarding" sai lokacin ya juyo suka had'a ido yace mata amman ba tace tana a wurin Elder sister en ta bane, shiru tay tana kallon shi sam tama manta da tace mashi haka don lokacin da sukai Maganar a rud'e take, tana kikkafta idanu tace mashi eh haka ne amman da Weekend ne take zuwa wurin ta, shiru ya d'an yi sai kuma yace to miyasa bazata zauna a wurin ta ba,
"Ai a boarding d'in an fi yin Karatu ne shiyasa" tana rufe baki taga yayi mata wani kallo mai kaman harara kawai sai ji tay yace sai dae dama in ita bata da k'ok'ari ne, waro ido tay ya d'age mata gira ya furta "Yeah" d'an murmushi tay tare da yamutsa fuska tace mashi wllh ita tana da k'ok'ari kuma sosae, tunda suka fara Maganar sai lokacin yanayin fuskar shi ya canza yay kaman zai murmushi tare da d'an ta6e bakin shi ganin haka yasa ta k'ara cewa "ai nan School d'in ma wllh mara k'ok'ari ma bai iya yin ta, da banda k'ok'ari ai da tuni ma sun kora ni tun kafin in fara karatun" yamutsa fuska yayi tare da d'an murmushi itama murmushin take tana kallon shi suna haka ya d'ago hannun shi ya d'an shafi beard d'in shi can ya furta dama ya ganta online ne shine yayi mata magana just to check on her, bata ji abunda yace ba sosae hakan yasa tace mashi bata ji mi yace ba dama tunda suka fara Vedio call d'in k'asa k'asa take jin voice d'in shi, shiru yay baida alamar zai k'ara fad'in abunda yace d'in, rantsuwa tay mashi tace bata ji ba yace mata Shikenan, marairaice mashi tay tana yamutsa fuska ta furta "Don Allah kayi hakuri wllh kaji na rantse banji mi kace ba" yanayin sautin Maganar tata da yar shagwaba tayi ta wanda ita bata san tayi hakan ba kawai sai gani tay yay d'an murmushi har gefen kumatun shi ya d'an lotsa, lumshe idon shi yay tare da yin yar hamma ya kai hannun shi ya rufe bakin bayan ya gama ya bud'e idon suka shiga cikin nata tay mashi zuru sai lokacin ya maimaita mata abunda yace d'in tay murmushi kafin tace ta gode, shiru bai ce komai ba sai ma d'age kai da yayi idanun shi a lumshe, bin shi da ido Fauzy tay sun d'an d'auki lokaci a haka can ya d'ago slowly ya fara bud'e idanun nashi suka shiga cikin nata, d'age mata gira yay ya furta "any problem?" da sauri ta girgiza mashi kai tace mashi sai anjima ya jinjina mata kai a hankali ya furta "Take care" kai ta d'aga mashi tana murmushi kafin ta kai hannu tay disconnecting kiran, bayan ta kashe kiran Murmushi ta shiga saki ba abunda take gani sai fuskar Sameer hakanan take jin komai nashi na burge ta bata ta6a zaton haka daga gare shi ba a yadda farko take mashi kallon mai girman kai, maida bayanta tay jikin bango ta d'age kai tana cigaba da sakin murmushi tana haka taji wayarta tayi k'ara alamar shigowar sak'o, sauke kanta tayi ta fara k'ok'arin duba sak'on, lokacin data ga sak'on wanda credit alert ne na kud'i dubu d'ari biyar aka turo mata gaba d'aya zaro idanu waje tay ta kai d'ayan hannunta ta dafe k'irji baki bud'e take kallon screen d'in wayar, mamaki ne ya cikata don ta gane Sameer ne ya turo su, "to ya akai ya san account number d'in ta??" Itace tambayar da ta shiga jefa ma kanta, zuciyar ta ce ta fara raya mata k'ilan lokacin da ya d'auki wayar a gidan daya kaita wanda dama a lokacin take tunanin ya d'auki number d'in wayarta can kuma ta k'ara yin tunanin ko kuma ranar da ya bata waya da suka taho a hanya ya amshi wayar tabbas a d'aya daga cikin hakan ne ya d'auka, tama rasa murna zatai ko mi don sosae mamaki ya kamata na yadda ya turo mata wannan iyayen kud'in, ta d'an d'auki lokaci tana ta mamakin kafin tay tunanin kiran shi don tay mashi godiya, sau biyu ta kira bai d'aga ba kiran na biyun ma kafin ya katse taji yayi rejecting, Aunty Mareeya ce ta fad'o mata a rai da sauri hannunta har yana rawa ta shiga kiran ta, tana yin ringing biyu ta d'auka, gaisawa sukai tay mata ya School da yake yau Fauzyn ta dawo daga Weekend,
"Aunty Albishirin ki!" tana rufe baki da sauri tace "Goro d'an Governor ya kira ne? don Allah Fauziyya kice man shi ne ya kira" dariya Fauzy ta kyalkyace da ita Aunty ta buga wani tsoki a k'agare ta furta "dalla ni ki fad'i man in shine d'in ya kira" tsagaitawa da yin Dariyar tay tace mata eh ya kira, wata uwar hamdala ta saki ta fara fad'in Alhamdulillah Allah ya amsa Addu'ar da take tayi,
"Ya kukai da shi da ya kira?" Cikin washe baki Aunty ta tambaya,
"Kawai fa na hau online sai gani nayi an yi man magana da bak'uwar lamba na shiga cikin chat naga an tambayi ya nike to dana ga bansan ko waye ba sai na duba hoton dp naga shine ina cikin dubawar ma sai ga Vedio call ya shigo..
......." Nan ta kwashe komai ta fad'i mata, a d'okance Aunty tace "Kai Ma sha Allah abu yayi dad'i wllh, ai kece da shegiyar kafiya wllh ba yadda banyi dake ba akan ki kira ki gaida shi amman kika k'i da yanzu an wuce wurin k'ilan anata Maganar saka rana ma, su mutane irin wannan ai ba'a masu sanya tunda dai an samu dama irin haka ma mantawa suke da mutum wllh shima nasan Allah ne ya amsa Addu'a ta ya karkato hankalin shi gare ki, to yanzu Shikenan iya gaisuwar kukai ko da wani abu?" Fauzy dake ta yar dariya tace "a'a....." bata k'arasa ba Aunty ta katseta "yace zai zo kenan?" Dariya Fauzy ta k'ara sakawa tace "ni fa Aunty bamu yi hakan da shi ba, kud'i ne ya turo man yanzu bayan mun gama wayar 500k bamma san ya akai ya samu account number dina ba amman nafi tunanin k'ilan dai d'auka yay a wayata" jin har ta gama Maganar Auntyn bata ce komai ba yasa ta kira Sunanta tace mata tana jin ta, wata uwar ajiyar zuciya Aunty Mareeya ta sauke a razane ta furta "Yar gidan Hajiya dubu d'ari biyar fa kika ce, rabin miliyan fa kenan!"cike da tabbatarwa Fauzy tace mata eh wllh gama alert d'in nan, shewa Aunty Mareeya ta saka tana fad'in "Wayyo Allah dad'i kashe ni ni Mariyatu, Yar gidan Hajiya na fad'i maki komar ki ta kamo mana gingimemen kifi wllh Manya masu babbar kyauta, wannan irin kyauta haka farko Wayar fin miliyan yanzu kuma kud'i rabin miliyan a hakan ma wai ba soyayya ake ba to inaga in an fara Soyewa kina sakar mashi kalamai ai sai baki