Showing 351001 words to 354000 words out of 512766 words
Chapter 118 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1588
take yi duk da ba sosae take yin shi ba amman data ji k'amshi ko taci abunda bai mata ba sai tayi aman ga kuma kwadayin ciki tafi son abu mai tsami ko yaji a lokacin har an tabbatar da ba d'a d'aya bane a cikin nata sosae kuma ya k'ara girma.
Ranar Alhamis lokacin suna cikin Class wayar Fauzy ta fara vibration alamar ana kiranta, fiddo ta tayi daga cikin Aljihun rigarta lokacin data ga mai kiran nata d'an waro ido tayi gashi akwae malami ba damar ta d'auka, bayan kiran ya yanke sai ga wani ya sake shigowa hakan ya tabbatar mata da magana yake son su yi don in dai ya kirata sau d'aya bata kusa to bai sake kira har sai in ita ta gani ta kira sannan ya k'ara kira, d'agowa tay ta juya ta kalli Fatuu suka had'a ido ganin yanayin fuskar ta yasa k'asa k'asa tace mata ya akai ne sai da ta fakaici idon Malamin nasu sannan tace mata Sameer ne keta kira, d'an bud'a ido Fatuu tay sai kuma tace mata ta d'auki excuse sai taje suyi wayar ta d'aga mata kai, bayan ta maida wayar cikin aljihun ta mik'e ta nufi gaban ajin, tambayar malamin nasu tayi don Allah zata je ta yi fitsari da turanci ya d'aga mata kai ta juya da sauri ta fita, can k'arshen barandar ajin taje ta kai hannu ta fiddo wayar ta fara k'ok'arin kiran shi, har ta yanke bai d'aga ba tay tsaye tana jira ya sake kira aikuwa sai gashi bada dad'ewa ba ya sake kira, d'auka tayi a nutse tayi mashi sallama ya amsa tace ya kira tana cikin class ne kuma akwae malami yanzu ma excuse ta d'auka ta fito ya furta Ok, tambayar ta yayi k'arfe nawa suke tashi tace mashi k'arfe biyu saura kwata nan ma Ok ya furta daga haka taji yace ta koma Class, tsaye tayi turus a wurin a ranta ta shiga tunanin to miyasa ya tambaya, wata zuciyar ce ta raya k'ilan nufin shi ya sake kira can kuma wata zuciyar ta raya mata ko kuma zuwa zai yi, har saida gabanta yay wani dammm ta d'an zaro ido, kokonton anya zuwa zai yi ba tare daya sanar mata ko yazo garin ba ta shiga yi wani sashe na zuciyar tane ya shiga raya mata yana iya zuwan fa abunda tasan halin shi, tunanin kiran Aunty Mareeya tayi ta sanar mata,
"To iya haka yace maki?" Aunty ta tambaya bayan ta kirata tace mata eh, "humm, yanzu in zuwan yay ya zamuyi kenan, ace zuwa ba sanarwa in banda abun suriki na mak'erin rocket, shiru Fauzy tay tama rasa abun cewa, "kuma fa wllh da alama zuwan yayi tunda kince sau biyu yana kiran ki gashi kuma ya tambayi k'arfe nawa kuke tashi k'ilan zuwa zai yi Makarantar kuma dai in dai yazo wurin ki nasan ai da wuya bai zo nan ba" still shiru Fauzy tayi Aunty tace wai ta wani yi shiru bazata bada shawarar abun yi ba, d'an yamutsa fuska Fauzy tay ta yarfa hannu d'aya tace to ai ita tama rasa tunanin da zata yi ne, nannauyar ajiyar zuciya ta saki tace mata to ko ta kira shi ta tambayi zuwa zai yi shiru Fauzy ta d'an yi kafin ta d'an yi guntun tsoki tace gaskiya ba sai ta kira shi ba tunda da ya so ai da ya sanar mata ko kuma ma yana iya ganin kaman wani abu ne yasa aka tambaya, cewa Aunty tayi Shikenan bari tana ganin abunda za'ai kawai ayi shirin kota kwana yanzu dai lokaci ma ya k'ure in ace a shirya lafiyayyen Abinci in zuwan yayi tana ganin bari taje tayi ma maman taufiq magana akwae wata k'awarta chef ce
"In kuma ba zuwan yayi ba fa" Fauzy ta tambaya ta bata amsa da "ke zaki cinye shi kuwa" dariya Fauzy ta saka tace to ita miye laifinta tana yar dariya tace ita kuwa keda laifi tunda laifin shi nata ne don mi in baya ga yana 6aud'add'e zai zo bai sanar dasu ba, a kan hakan sukai sallama ta koma aji, sai bayan da malamin ya fita sannan suka yi magana da Fatuu itama dai zargin k'ilan zuwan zai yi tayi, gaba d'aya hankalin Fauzy ya kasu biyu tana tunanin ko zuwa Sameer zai yi tana kuma sauraren abunda ake masu a haka har aka tashi, tare suka fito da Fatuu ta rakata inda take Parking Motar ta kamar kullum, sallama suka yi tace mata k'ilan dai ba zuwan yayi ba tunda bai sake kira ba watak'il dama kiranta ne zai yi su yi magana Fauzy tace eh itama yanzu haka take tunani tayi mata Allah ya tsare sai sun had'u gobe,
Bayan tafiyar Fatuu juyowa tayi ta nufo hanyar hostel bata kaiga barin Class area d'in ba wayarta ta fara ringing, hannu ta kai cikin aljihun rigarta ta curota ganin shine yasa gabanta fad'uwa saida tayi d'an jimm kafin tay picking tana karata a kunne taji yace ta same shi a parking lot na Admin nasu, waro ido Fauzy tay baki bud'e ta curo wayar tana kallon screen d'in nan take gabanta ya hau fad'uwa tamkar ana mata luguden ta6are duk da tayi zargin k'ilan zuwan zai yi sosae taji Al'ajabin zuwan nashi don ko a chat bai sanar mata ba kuma ko jiya sun gaisa, har zata tafi sai kuma ta tuna da Aunty, Da sauri ta shiga kiranta tana d'agawa ta tambayi yaya ake ciki a d'an rud'e Fauzy tace wllh zuwa yayi gashi nan ya kirata wai yana a admin, jinjina kai tayi tare da murmushi mai sauti ta furta wani aikin sai surukin ta makerin rocket, ce ma Fauzy tay kada ta damu duk abunda ya kamata za'ai mashi tace mata to, cikin mutuwar jiki ta ci gaba da tafiya dama Admin d'in wurin hostel d'in su yake, tunda ta tunkaro wurin take ta faman wurga ido tana son gano wacece Motar shi a cikin jerin motocin Malaman su dake a wurin, tana gab da isa taga an bud'e wata galleliyar bak'ar Camry sai faman shek'i take kai da gani kasan sabuwa ce, wani d'an magidancin mutum ne ya fito daga driver seat d'in Motar jikinshi sanye da k'ananun kaya wando da riga mai ma6allai, suna had'a ido yay murmushi tare da yi mata alamar tazo da kai, a d'arare ta tunkare shi tana zuwa gaban shi ya d'an rankwafa ya gaishe da ita da murmushi akan Fuskar tashi, amsa mashi tay a hankali da hannu ya nuna mata back door d'in da take tsaye a gefenta yace mata bismilla yana ciki tare da kai hannu ya bud'e mata k'opar nan take wani irin fitinannan k'amshi ya huro wajen, d'an rankwafawa tay ta kallo cikin Motar idanunta suka sauka akan Sameer dake a hakimce a bayan idanun shi a lumshe, sanye yake da shadda wheat wadda Kusan ta saje da kalar fatar jikin shi kafafun shi na sanye da bugaggun takalma half cover coffee brown haka hannun shi ma agogon hannun shi fatar ta coffee brown ce, irin d'inkin da Haisam yafi so wato Senator style ne aka yi ma shaddar hannun yasa wasu had'add'un links masu d'an adon coffee brown daga tsakiya, sumar kanshi a kwance ta kawo har tsakiyar wuyan shi haka sajen shi ma a kwance yake luff, duk da shadda ce a jikinshi hakan bai 6oye komai ba na daga suffar shi kana ganin shi zaka gane k'arfafa ne na gaske, slowly ya fara bud'e idanun suka sauka a kanta ya bita da kallo still bai bud'e idon baki d'aya ba, d'an murmushi tayi mashi gabanta na bugawa a hankali tace mashi "ina wuni, an zo lafiya" shiru bai amsa mata ba sai kallon ta yake hakan yasa ta shiga yan kame kame tana cigaba da d'an murmushi, tana haka taji yace in bazata shigo ba ta rufe mashi k'opa yana fad'in haka ya janye idanun daga kanta ya maida su ya lumshe, d'agowa tayi ta d'an waiga bayanta sannan ta shiga cikin Motar ta d'an jawo kopar ba tare data rufeta baki d'aya ba, bin shi tay da kallo gaba d'aya yau tafi ganin kwarjinin shi fiye da sauran lokuttan da ta ganshi a baya,
"Ina wuni" ta sake gaishe da shi ya jinjina mata kai kawai ba tare daya kalleta ba, "an zo lafiya?" Shiru bai bata amsa ba atunaninta ko bai ji ba ne hakan yasa ta k'ara ce mashi hakan, jin shiru bai amsa ba yasa ta gane yana jinta ra'ayin amsawar ne bai da shi, tana cikin kallon shi ya juyo idanun shi suka shiga cikin nata ya shiga jefa mata wani mayen kallo nan take tasha jinin jikinta ta shiga yan kame kame tana d'an motsa baki kaman mai son fad'in abu ta kasa,
"Is that how you should welcome me?" cikin husky voice d'in shi ya furta hakan tare da d'age mata gira, wani k'afaffen miyau ta had'iya ta kasa bashi amsa sai faman zare ido take don ita a ganinta ai hakan da tayi ne daidai tunda shi kanshi ba sake mata yayi ba balle ta nuna tayi murnar ganin shi, tana haka taji yace ko bata yi farincikin ganin shi bane da sauri ta hau girgiza kai murya na d'an rawa ta furta "n...nayi sosae kawae dai naji mamaki ne tunda baka fad'i man zaka zo" d'an yamutsa baki yay ya d'age mata gira yace dole ne yayi hakan ta k'ara girgiza mashi kai tace a'a, kasa jure ma kallon shi tay ta maida idonta k'asa tana kallon yatsun hannunta ba zato sai gani tay ya kawo tattausan hannun shi mai d'an fad'i da kuma dogayen yatsu masu d'auke da dogayen gyararrun k'umbuna ya kamo hannunta bata gama Al'ajabin hakan ba sai ji tay ya jawota gaban shi ya had'e ta da jikinshi ya rungumeta ta gefe, wani irin shock Fauzy taji ya ratsa dukkan jikinta gabanta ya hau wani irin mugun bugu tsoro da Al'ajabi lokaci guda suka kamata jikinta ya fara d'an rawa, kai fuskar shi yay saitin kunnanta cikin wata irin magana mai kamar rad'a ya furta mata haka yakamata tayi welcoming nashi da sauri ta runtse idanunta jin yadda Maganar ta sauka a cikin kunnanta nan take wasu abubuwa suka fara mata yawo a jiki, sam ta kasa cewa komai wani iri take jinta don a rayuwarta in ba Mujaheed ba bata ta6a had'a jiki da wani Namiji ba haka ko yan uwanta saidai ko lokacin da bata mallaki hankalinta ba shima Mujaheed sai da k'yar ta fara yarda yake ta6a ta da yayi mata dad'in bakin Auren ta zai yi, suna haka taji ya tambayi karatunta da k'yar ta iya bud'e baki tace mashi Alhamdulillah, shiru sukai gaba d'aya k'amshin jikin shi ya cika mata hanci nan take wata kasala ta fara rufar mata jikinta taji ya fara yi mata wani iri aikuwa da sauri ta d'ago tana k'ok'arin raba jikinta da nashi taji ya saketa, bin juna sukai da kallo wani irin nauyi taji idanunta sun mata hakan yasa da sauri ta juyar da fuskarta daga barin kallon shi, jin yayi shiru yasa ta d'an juyo karaf suka had'a ido da shi yana kallonta da kaifafan idanun shi, tsarguwa tay da kallon da Yake mata cikin yar in ina tace mashi Makarantar tasu akwai tsauri ne in aka ganta haka zata samu matsala ne kuma nan wurin parking d'in motocin Malamai ne ana iya ganinta, har ta gama Maganar idon shi na akanta yanayin kallon da yake mata ne ya canza zuwa harara ya d'aure fuskar tashi da sauri ta janye idanunta daga kanshi ta koma kallon k'asa,
"Go and gather all your things!" Kaman daga sama taji ya fad'i haka, d'ago kai tayi da sauri ta kalle shi ya jinginar da kanshi jikin seat fuskar shi na kallon gaba ya d'an lumshe ido, da alamun rashin fahimta ta shiga bin shi da kallo ta kasa gane mi yake nufi da taje ta tattaro kayan ta, mi hakan ke nufi? shine abunda take juyawa a ranta ba dai fushi yayi da Maganar data fad'i mashi ba shiyasa yace haka, kenan ta daina karatun yake nufi ko mi, haka take ta sak'e sak'e a cikin ranta gashi yak'i ko kallonta balle ya bata amsa can da alamun rashin fahimta tace mashi bata gane abunda yake nufi ba da bud'ar bakin shi sai cewa yay bata understanding turanci ne tace a'a ta gane abunda yace amman in ta tattara kayan mi zatai da su, shiru kamar bazai bata amsa ba kafin taji yace ta daina boarding School a tak'aice yayi Maganar still idanun shi na a lumshe, kai ta jinjina kafin ta juya ta kai hannu ta bud'e kopar, Mutumin daya tuk'o shi na tsaye ya jingina da k'opar gaban suna had'a ido yay mata murmushi tare da Fad'in barka da fitowa a hankali tace Yauwa, daidai lokacin data fito akan idon su Zainab da Sa'adatu dake tahowa daga class zasu Hostel gaba d'aya idanun su na akanta har ta fito daga cikin parking space d'in ta nufi hanyar zuwa hostel aikuwa cikin d'aga murya Zainab ta k'wala mata kira, tsayawa tayi har suka k'araso ta d'an k'ak'alo murmushi tana yi masu, tambayarta Zainab d'in tayi bak'o tayi ne taga ta fito daga cikin wanccan galleliyar Motar kai ta d'aga mata alamar eh ta d'an waro ido tace "da sa ranar wani akan ki shine kuma kike saurarar wani ba kyau hakan wllh, kinga don Allah kawai ki had'a ni dashi tunda ke dai kin saida" yar dariya Fauzy tay Sa'adatu ta 6aka ma Zainab d'in bugu tana fad'in ita dai ta shiga ukku da son kudi wllh daga ganin Mota mai kyau shine zata ce a had'a su, a d'an harzuk'e tace a'a to wa zai k'i mai kud'i suma duk tasan inda mai Motar zai ce yana son su da gudu zasu yarda wllh, ganin suna 6ata mata lokaci yasa tace masu bari taje ana jiranta ne da sauri Zainab ta bita tana fad'in yanzu don Allah bak'in ciki zata mata ita tunda Allah ya bata mai kud'i ba sai ta taimake ta ba, tasan in ba fad'i mata wanene tayi ba bazata k'yaleta ba don ta cika nacin magana yasa tace mata ai wanda zata aura d'in ne yazo yanzu ma zuwa yay daukarta zata bar zama a hostel, gaba d'ayan su saida suka ji ba dad'i Zainab tace maimakon tace mashi ya barta taci gaba da zama tunda dai da sauran lokaci bikin nasu Fauzyn tace mata bai so, tare suka je d'akin nasu gaba d'aya don taya ta kwasar kayan, duk wani provisions dinta su ta raba mawa haka wasu daga cikin kayanta duk abunda wani yace mata yana so sai tace ya d'auka ba kamar Zainab duk tafi kwasar abubuwa har su bokitan ta da su robobi da plates duk su ta raba mawa iya trolley d'in kayanta sai wata yar babbar jaka ta saka sauran abubuwan da take so bata bayar ba, tare suka fito su hud'u Zainab tace to bazata yi ma mutane bankwana ba tace kawai sai gobe in Allah ya kaimu tazo har d'akin ma sai taje ta sanar ta saki, dama tunda Fatuu ta bar zama a hostel ita kad'ai take rayuwa a d'akin saidai masu zuwa taya ta zama ko kwana, a tare suka iso parking space d'in har lokacin mutumin ko ace driver d'in yana a tsaye yana ganin su da sauri ya bud'e kopar gaban ya rankwafa don ya bud'e boot d'in, bayan ya bud'e ya nufo wurin ya bud'e boot d'in suna kokarin saka kayan da sauri yace su barshi zai saka, kallon su Sa'adatu tay tana murmushi tace ta gode sai sun had'u in Allah ya kaimu suma godiyar suka yi mata har zata juya Zainab tace to 6oye masu mijin nata take da bazata had'asu su gaisa ba, d'an jimm Fauzy tay don bata san taya zata aikata hakan ba, ganin sunyi tsaye suna bin ta da ido alamar duk so suke su gaisa da shi d'in yasa tace bari tayi mashi magana, bud'e k'opar bayan tayi yana zaune a inda ta barshi yana latsa waya, rasa mi zata ce mashi tay tana a rankwafe ta bishi da ido, Slowly ya d'ago suka had'a ido tace mashi ga kayan nan ta d'aukko har an saka a boot ya d'aga mata kai kafin yace ta shigo, jimm tay tana d'an kikkafta ido ganin bata shigo ba yasa shi k'ara d'agowa tun kafin yace wani abu cikin yar in ina tace "d...dama wai k'awaye nane zasu gaida ka" shiru kaman bazai tanka mata ba sai kuma ya d'age gira yace mata yace yana son haka ne har saida ta had'iyi abu, d'an girgiza mashi kai tayi tace a'a dama sune suka taimaka mata ta tattaro kayan to sun tambayi miyasa zata bar hostel shine ta fad'a masu shine yazo daukarta, "ni wa?" taji ya jefo mata tambayar ta d'an waro ido don bata tsammaci jin tambayar ba da k'yar ta bashi amsa da wanda zata aura kawai sai gani tay ya d'an ta6e baki ya maida idon shi kan wayar dake hannun shi, tambayar shi tayi tace suzo su gaisan taga ya jinjina mata kai ba tare daya kalleta ba, d'agowa tay tace masu suzo su gaisa duk suka matso bakin Motar Fauzy taja gefe, a tare suka rankwafa suka ce mashi ina wuni a wani slow ya juyo gaba d'ayan su saida gaban su ya fad'i karma Zainab taji wani kallon k'urulla ta shiga bin shi dashi tana k'ok'arin tuna inda ta san shi, jinjina masu kai yayi kamar anyi mashi dole koda yake Kusan hakan ne yace masu ya School a tare suka had'a baki wurin amsa mashi da lafiya lou suka ce anzo lafiya anan dai kai suka samu ya jinjina masu daga haka suka ce sai anjima suka janye kan su, idanu a waje Zainab ke kallon Fauzy dake d'an murmushi