Showing 477001 words to 480000 words out of 512766 words

Chapter 160 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1578

don ke kin dace sai kike ganin kowace mace ma hakan take a wurinta to kije ki bincika na tabbatar zaki samu mata da dama wanda kuɗaɗen mazajensu basu sa sun kasance a cikin farinciki ba face damuwa",

ɗan yamutsa fuska tay da yanayin damuwa tace "Yanzu dai fatana Farhar ta bayyana shine kawai, gani kince kina son ganina",

Hajiya na ɗan murmushi tace ta dameta ko shiyasa take son a canza Maganar, da sauri tace mata a'a kawai dai taga ba abunda yakamata su maida kai akai bane tunda wadda ake Maganar don ita ba'a san inda take ba Hajiyar tace hakane Allah ya bayyana masu ita ta amsa da Amin,

"Kinzo na tsare ki da surutu ban baki abinci ba kuma halan ko breakfast baki yi ba" Hajiya ta faɗa idonta a kanta, warware gyalen haɗaɗɗar doguwar rigar dake jikinta data laga tayi ta kwanta a saman gadon tana faɗin tasha ɗan tea Abincin ne kwata kwata bai mata daɗi gashi duk in tazo ci sai tayi ta tunanin ko Farha taci abinci, yadda ta ƙarasa Maganar kamar zata saka kuka Hajiya na murmushi tace in sha Allahu taci mai kyau ma,

"Yanzu tea ɗin za'a ƙara haɗo maki sai a haɗa da wainar ƙwai muna da farfesun kaza ma, in kuma duk baki son su sai ki faɗi abunda kike so a haɗa maki" shiru ta ɗan yi kamar bazata yi magana ba can ƙasa ƙasa tace rana tayi abar tea ɗin a kawo mata farfesun taga in zata iya sha Hajiya tace to ko a soya doya sai ta haɗa da sauri ta girgiza mata kai tace abu mai ruwa ruwa kawai take ɗan iya ci Hajiya tayi murmushi tace to bari tasa a kawo mata anan, wayarta ta ɗaukko ta shiga yin kira bayan an ɗaga umarnin kawo ma Hajiya Maryam farfesu ta bayar tare da lemu da ruwa daga haka ta kashe wayar idanunta akan Hajiya Maryam data rufe ido kamar mai yin bacci, ba'a jima ba aka turo ƙopar ɗakin Farha ta shigo tana sanye da ƙananun kaya kaman ko yaushe kanta ba kallabi sai dark ash ɗin sumarta dake a fake ta lanƙwasa ta, bata yi sallama ba Hajiya tay mata nuni da gaban gadon saitin inda Hajiya Maryam ke kwance tace taje ta aje anan kan carpet, har ta aje Hajiya Maryam bata buɗe ido ba Farhar ta ɗago tana kallonta wata irin kewar Mahaifiyar tata taji ita kanta taga canzawar da tayi bata ta6a tunanin za'a samu ranar da zasu samu sa6ani da Mom ɗin tata ba don sun shaƙu kamar abokai haka suke dalilin shaƙuwarsu ne ma yasa Farhar bata fita ƙasar waje yin karatu ba tayi a nan, da hannu Hajiya tayi mata alamun ta gaishe da ita cikin ɗan rawar murya tace mata ina kwana still bata buɗe idon ba da alama ma bata ji ba, saida Hajiya tace mata ana gaisheta sannan ta ɗan ɗaga hannu alamar ta amsa, tsaye Farhar tayi tana ta kallonta a hankali ƙamshin turarenta ya fara kurɗaɗawa cikin hancin Hajiya Maryam lokacin data shaƙe shi sosae da mamaki ta ayyana ƙamshin kamar na Farha, zuciyarta na raya mata hakan da sauri ta buɗe idanun nata suka shiga cikin na Farha dake tsaye ai a sukwane ta tashi zaune tana kallonta idanu waje, muryarta har tana sarƙewa wurin faɗin "Wannan kamar Farha a gabana Hajjaju kodai gizon data saba yi man ne dama sai inta ganinta koda yaushe" Hajiya na murmushi tace itama kamar ita take gani, maido idonta tayi kan Farha dake ta kallonta sai kuma ta maida kan Hajiya, murmushin da taga tana yi ne yasa ta gane Farhar ce aikuwa da sauri ta miƙe tsaye cikin rawar murya ta furta "F...Farha, it's You...???" shiru ta ɗan yi kafin a hankali ta furta "Yes, Mom" zaro ido Hajiya Maryam tayi gaba ɗaya ta juya kan Hajiya cike da al'ajabi tace "Amman Hajjaju ya akai kika samota ko nan tazo?" ɗan ta6e baki Hajiya tayi tare da ɗan girgiza kai tace dama tana nan, cikin ɗaurewar kai ta maimaita abunda Hajiya ta faɗa ta ɗaga mata kai alamar tabbatar wa,

"Yanzu Hajjaju kina nufin duk abun nan Farha na wurin ki?" Hajiya tace mata eh ita ta tsara mata komai tasa ta taho wurin ta, wani kalan yarfa hannu Hajiya Maryam tayi tare da yamutsa fuska ta koma gado ta zauna yaraf kamar zata yi kuka tace "But Why, Hajjaju, miyasa don Allah zaki tada mana hankali har haka kika sa anata cigiya mutane nata kashe kuɗi suna zuwa jaje amman ashe tana wurinki kuma kina sane da dole hakan zai tada mana hankali ba kaɗan ba" wani irin ɗaure fuska Hajiya tayi da hannu tayi ma Farha alamar ta zauna a kan carpet, bayan ta zauna ta maida idonta kan Hajiya Maryam fuska a ɗaure ta fara magana,

"Nasani hankalin wanda bai san da tana wurina ba zai tashi kamar ke sannan Maganar kashe kuɗi da zuwa jaje duk nasan za'ai hakan saidai ina son ki sani na za6i yin hakan ne don in baki misalin irin tashin hankalin da kike niyyar janyo mana kenan koma wanda yafi wannan, saboda taurin kan ki kina ƙoƙarin ki saka mu a damuwa da danasanin da har mu mutu bazamu daina ba to aka me zamu zura ido muna kallo ki jefa mu a hakan, kina sane da illolin da auren dole ke tattare dashi amman shine kika rufe ido saboda wani kurman ra'ayin ki zaki jefa rayuwar yarinya a halaka, baki tunanin zata iya kassara rayuwarta ba ko kuma ta ƙyaleki ki ɗaura mata auren shi mijin ta illata shi ba, in hakan ya faru wane irin tashin hankali kike tunanin hakan zai haifar mana, so kike mu zama abun misali a idon duniya ki jaza mana tambarin da bazai ta6a goguwa ba har ƙarshen rayuwar mu?"" a fusace take yin Maganar,

jin tayi shiru ne yasa Hajiya Maryam ɗin cewa "amman Hajjaju wannan ai ba auren dole bane tunda akwae soyayya tsakaninsu ta tsawon lokaci kuma su duka suna son junansu kwatsam kuma sai ta dawo tace wai bata son shi....."

Katseta Hajiya tayi taci gaba "tace bata son shin ai ba laifi tayi ba dama yana faruwa yau kaji kana son mutum gobe ka dawo kaji baka son shi dama ana samun haka wanda aka ɗauki lokaci ana soyayya sai kiga bashi Allah ya ƙaddaro za'a aura ba sai daga baya mijin ya 6ullo ta inda ba'ai zato ba yasha faruwa koma yana kan faruwa ma shiyasa wasu suke gudun 6ata lokaci wurin yin soyayya suke bari sai sun shirya ma aure sannan su fara wasu kuma suna yin soyayya da shirin kota kwana, shiyasa ba'a so ana soyayya ai ta ma juna ƙaryayyaki da alƙawura tunda mutum bashi keda kan shi ba ta yuwu wanda kake hasashen aura bashi Allah ya ƙaddaro zai zama abokin rayuwarka ba shiyasa yana da kyau a gina soyayya kan wannan turbar kowa yasa hakan a zuciyarshi sai kiga koda rabuwar tazo baza'a ji ciwo sosai ba, don haka ki rabu da yarinya ta auri wanda take so wataƙil dama wannan shine wanda Allah ya ƙaddaro zai zama abokin rayuwarta" ba alamun wasa Hajiya ke yin Maganar,

"Naji Hajjaju, in bata son Emran ɗin shikenan amman nidai gaskiya ban goyon bayan ta auri yaron don haka ta nemi wani" fuska a yamutse tay maganar aikuwa a fusace Hajiya tace "bata neman wanin wanda take son shi zata aura matuƙar Allah ya ƙaddara hakan, ke waya hana ki auren wanda kike so, wato yanzu kin kawo ƙarfi ke ga uwa shine zaki nemi ɗaga ma mutane hankali ke wa yay maki haka, inace lokacin da kika haɗu da Mahaifinsu kina da samarin da kuke soyayya lokacin in ban mance ba yaron nan soja ɗan wurin abokin Mahaifinku gashi nan da suna.....Nasir yauwa ba wanda bai yi tunanin shi zaki aura ba daga haɗuwa da mahaifunsu duk kika ruɗe ke kinga mai jan kunne rana ɗaya kika zo mana da zancen ke shi zaki aura, a lokacin Allah ya jiƙan rai mahaifin ku shine ma yaso ya ƙi abun don shi mutum ne mai kishin ƙasar shi da al'ummarshi ni na rarrashe shi kan ya ƙyale ki har Allah yasa kukai aure, in ma kin manta ne to gashi nan na tuna maki don haka yadda ba wanda ya hana ki auren wanda kike so haka itama ba wanda zai hanata auren wanda take so" idanun Hajiya Maryam ne suka ciko da ƙwalla suka zubo mata sharr cikin 6acin rai ta shiga faɗin amman ita ko a lokacin data kawo mahaifin su ai ya gina rayuwar shi ko shikenan sai ace an taru anata auren dangin su kowa su Haisam da Nameer sun auresu ga Kakar tasu ma kan su za'a ƙare,

"Zancen gina rayuwa ko ɗazun nayi maki maganar saurin mi kike ki jira shima kiga baki san yadda Allah zai da tashi rayuwar ba sai kiga ya zamo abunda baki ta6a zato ba ai shi arzuƙi na Allah ne Maryam kema ai ba wayon ki ne ya baki ba ko, sannan Maganar anata auren su alamar suna da nagarta ne ai ko a kasuwa zaki ga ana rububin abu mai nagarta, wasu Familyn ma zaki ga basu auren bare sai yasu yasu ma don haka don anata auren su ai ba aibu bane" shiru Hajiya Maryam ɗin tayi tana goge ƙwalla,

"Ina son jan hankalin ki Maryam al'amari in dai akace na Allah ne ki daina kafiya irin haka, wannan abun daya faru yanzu tamkar ishara ne Allah ya nuna maki, nan yarinyar nan Fateema daga ta auri mijin ɗiyar ki kika ɗaga masu hankali kikai ta kumfar bakin ke ɗiyarki bazata zauna da ita matsayin kishiya ba don bata kai matsayin tayi kishi da ita ba waye waye, to yanzu ga ɗiyar ki nan ta cikin ki Allah ya ɗaura mata son Yayanta so mai tsanani itama yar jakar ubar nan harda ita aka hana Fateema zaman lafiya amma kinga soyayya ta rufe mata ido ko kunya bata ji ba tazo tace tana son Yayanta..." ta juya tana kallon Farha tare da ɗan harararta Farhar ta ɗan tura baki a hankali tace "pls Hajiya let bygones be bygones, ba kinsa mun shirya tuntuni ba",

ta6e baki Hajiya tay tace "da yake fa abunsu kike so kyace haka, shiyasa ita fitina bata da daɗi sam, yanzu da baku shirya ba kina tunani shi wanda kike son zai saurareki ne alhali kina tsangwamar yar'uwar shi, to da ya zaki da son ko sai kije ki faɗa rijiya mai kwala6e?" yar dariya Farhar tay ta sunnar da kai, maida idonta tay kan Hajiya Maryam da 6acin rai ya bayyana akan fuskarta cikin kwantar da murya tace "Wato shi Ubangiji yana yin abubuwa cikin hikima, daya halicci bayinsa sai ya kasasu wasu yayi su masu wadata wasu masu rufin asiri wasu kuma wanda basu dashi gaba ɗaya hikimar yin hakan shine don kowa ya amfana da kowa don inda yaso zai ba kowa arzuƙi amman sai bai yi hakan ba, duk wanda kika ga Allah ya ba arzuki bai bashi don ya amfana shi kaɗai ba face don ya taimaki wanda bashi dashi wanda ta silar haka zaka samu ɗunbin lada har kasamu shiga aljanna haka wanda bashi dashi in yayi haƙuri da yadda Allah yayi shi ya rungumi ƙaddarar shi bai sa6i Allah ta dalilin hakan ba shima sai kiga ya cinye jarabawar shi ta hanyar hakan har ya shiga aljanna, wasu da yawa Allah na saka arzuƙin su a hannun wasu shine zaki ga ta silar taimakon da kayi ma wani in ma aiki ka sama mashi ko kuɗi ka bashi ko auren shi kai da sauransu sai kiga hakan yayi silar arzuƙin mutumin, to dana yi nazari sai na gano kusan hakan ce Allah ya ƙaddaro tsakaninmu dasu Dije shiyasa har ya haɗamu maƙwabtaka kuma in kikai la'akari da ai basu kaɗai bane makwabtana akwae wanda muke tare tun kan suzo zaki shaida hakan, Allah yasa rabon wadatuwar su a hannun mu don haka bamu da ikon hana hakan koda kuwa ace bamu so to wllh sai rabonsu dake tattare damu ya isa gare su, don haka inason ki kwantar da hankalinki ki ɗauka mu dasu yanzu mun zama Family duk abunda ya taso tsakanin mu dasu in dai mai kyau ne to mu rungume shi hannu bibbiyu muyi fatan alkairi" shiru Hajiya Maryam tayi ta maida idonta ƙasa,

"Yanzu kin amince mata kan abunda take son?" Hajiya ta tambaya idonta akanta, ba tare data ɗago ba tace "taje Allah ya taimaka",

"Ba haka yakamata kice ba Maryam fatan alkairi zaki yi mata matsayinki na mahaifiyarta sannan ki yaƙi zuciyar ki ta rinƙa kallon abun a alkhairin" shiru tayi duk idanunsu na akanta can ta ɗago ta kalli Hajiyar tace Allah ya tabbatar da alkhairi, murmushi Hajiya tayi ta amsa da Amin Farha ta shiga yin murmushin farinciki tana washe baki tace "Thank you so much Mom, I love u" wata uwar harara ta wurga mata Hajiya tay yar dariya tace "in kina harararta fa zata ƙara 6acewa" ɗan gutsirin murmushi Hajiya Maryam ɗin tayi bata ce komai ba da sauri Farhar ta miƙe ta nufi hanyar fita daga ɗakin,

tana fitowa ɗakin Husnah ta nufa tana niyyar shiga Husnar ta fito daga ɗayan bedroom ɗin nata cike da farinciki Farhar ta sanar mata Mom ɗinta ta amince ma soyayyarsu da Kamal ta ɗan buɗa ido kafin tana murmushi tace ta tayata murna Allah ya tabbatar da alkhairi ta amsa da Amin ta ƙarasa shigewa cikin ɗakin, gyale ta yafo saman kanta tana fitowa falo ta nufi hanyar fita, gidan Gwaggo ta nufa bayan ta fito koda tazo shagon Amadu a rufe yake ta shige gate, tana niyyar shiga entrance Amadu na sako kai dama wanka ya shigo yi yana ganinta yaja ya tsaya yana ƙare mata kallo ita kuma tana ɗan murmushi ta gaishe shi bai amsa ba da tsananin mamaki yace mata an ganta kenan tay yar dariya tace dama ba 6acewa tayi ba tana nan gidan Hajiya, da alamun rashin fahimta yace kuma shine aketa cigiyarta, nan ta kwashe komai ta faɗi mashi sosae ya jinjina abun yace lallai Hajiya ta iya shirya abu kamar Film, tare suka shiga ya nufi part ɗin Gwaggo da ita lokacin Haulat ma na can sun fara aikin abincin rana, a falo suka tsaya Amadun ya shiga ƙwala ma Gwaggo kira yana ta fito taga wani abu, tana fitowa tayi arba da Farha itama zaro ido tay cike da al'ajabi tace kamar Farha take gani Amadu na murmushi yace itace da sauri ta tambayi ina aka ganta nan Amadun ya faɗi mata ashe wai tana gidan Hajiya Gwaggon ta washe bakin farinciki tace dama sai da Haulat ta zargi hakan da suka je jaje nan ta shiga ƙwala ma Haulat kira, bayan ta fito daga cikin Kichen ɗin itama saida ta nuna mamakin ganin Farha cikin washe baki Gwaggo ta shiga faɗin zarginta ya tabbata ashe wai tana wurin Hajiya Haulat ɗin tace ita dama tunda suka je ta lura da sam Hajiyar bata cikin damuwar 6acewar tata, zama sukai kan kujeru Amadu yace ma Farhar yaga mamanta ma tazo ɗazun ta gano tana nan kenan tace mashi a'a sai bayan data zo, nan take faɗi masu ai yanzu ta amince da tarayyarsu da Kamal ɗin cike da tsokana Amadu yace ai da ta haƙura da Kamalun tabi abunda Mom ɗin nata ke so ta wani tura mashi baki tare da ɗaure fuska duk sukai dariya, tambayar shi tayi Kamal ɗin tace ko yana School yace mata ai rabon shi da School tunda yaji labarin ta gudu saboda shi yanzu haka yana ɗaki bai jin daɗi, ai tana jin haka zumbur ta miƙe ta nufi hanyar ɗakinshi tana faɗin bari taje ta faɗi mashi ba guduwa tayi ba duk suka bita da kallo, juyowa Amadu yay ya kalli Gwaggo dake murmushi yace Allah ya haɗata da suruka ƙwara ba kunya duk sukai dariya, lokacin data shiga cikin ɗakin yana kwance kan katifa idanunshi a rufe tay tsaye daga gaban ƙopa tana kallonshi da murmushi can ta kira sunan shi "Kamal" a hankali ya fara motsa idanun shi masu ɗauke da zarazaran gashin ido kafin ya buɗesu ya ƙura ma gabanshi ido duk ɗaukar shi muryarta ce ke mashi gizo, saida ta ƙara kiran nashi sannan da sauri ya ɗago kai ai koda yay arba da ita a firgice ya ƙarasa tashi zaune yana kallonta ita kuma sai murmushi take mashi ya murje idanun shi ya buɗe ganin still tana nan yasa shi nunata tare da kiran sunanta ta ɗage mashi gira tare da amsa mashi da Yes, zumbur yay ya miƙe tsaye da alamun al'ajabi yace don Allah da gaske itace yadda yay tambayar ne ya bata dariya don duk alamun tsoro ya bayyana a tattare da shi tace mashi itace mana amman tunda taga bai yi farincikin ganinta ba bari ta koma da sauri yace a'a ta tsaya pls ya nufeta, a ɗan gabanta ya tsaya har fuskar shi ta faɗa da tsananin mamaki yace mata yaushe aka ganta ne kuma miyasa zatai haka, saida ta matso gaban shi sannan tace mashi itafa ba 6acewa tayi ba dama duk shiri ne nan ta shiga faɗi mashi yadda akai, shima sosae yayi mamaki cike da farinciki ta kai duka hannuwanta ta kamo nashi tace "guess what?" da sauri ya girgiza mata kai ta sanar dashi yanzu babu wata matsala zasu yi soyayyarsu hankali kwance don Mom ɗinta ta amince masu ya ɗan buɗa ido yace don Allah da gaske tace eh mana yanzu haka Mom ɗin nasu na gidan Hajiya, ƙayataccen murmushin daɗi ya shiga saki tace yayi haƙuri ta saka shi ciwo in ba hakan akayi ba Mom ɗin nasu daba lalle ta amince masu ba, da sauri yace ba komai ai yanzu ma yaji ya warke shi dama abunda yafi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login