Showing 441001 words to 444000 words out of 512766 words

Chapter 148 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1612

kowa a parlon ta wuce kitchen, wanke kayan da akai amfani dasu tayi tay tunanin tayi masu girki kafin ta tafi, tana cikin aikin girkin Nameer ya shigo tun yana sawo kai ƙamshin turarenshi ya karaɗe kitchen ɗin, da alama wanka yayi yana sanye da ƙananun kaya wanda da gani sababbi ne sumar shi tasha gyara sai salƙi take haka sajen shi, daga gefen ta ya tsaya ya aje tray ɗin kayan Breakfast ɗin yana murmushi yace "sannu da aiki Yayata ta kaina" wani kallo tay mashi tana murmushi tace na daɗin baki ko,

"Amman kinsan ai tun da kika zama Yayata nike girmama ki ko" ɗan ta6e baki tay yana dariya yace yanzu ma zai ƙara girmamata tunda ta mashi aiki tay dariya kafin tace ai biya zai yi da sauri yace ta faɗi ko nawa ne zai bata in ma baida su zai samo tace bada kuɗi zai biya ba alƙawari zai yi na bazai ma Mino kishiya ba yana murmushi yace in don wannan ne dama baida wannan ra'ayin itace kaɗai matar shi har ya mutu ta ɗan harare shi tace ita zai ma daɗin baki,

"Ba daɗin baki bane am serious mizai sa in ƙara Aure inada Ameenatu, tamkar rainonta zanyi fa lokacin da zan manyanta lokacin zata ƙara cika mace to mi zai burge ni a wurin wata" murmushi Fatuu tay tace wasa ma take mashi ita ai tana da kishiyar ko yace to shi da gaske yake daga Babynshi ya gama tace Allah ya barsu tare ya basu zaman lafiya da zuriya ɗayyiba ya amsa da Amin kafin ya tambayi mi zai tayata da shi tace ba komai duk ta cimma aikin ma sauran ƙarashe yace Ok tare da yi mata godiya ya juya ya fita, farar shinkafa da miya tayi sai coleslaw tayi farfesun yan ciki saida ta wanke komai data 6ata ta zuba abincin a cikin warmers masu kyau ta kai kan Dinning table, bedroom ɗin Minon ta nufa bata yi tunanin Nameer na ciki ba saida ta shiga ta ganshi rungume da Minon suna bacci tay murmushi ta wuce inda ta aje purse ɗinta ta ɗauka kafin ta fito, parlor ta dawo ta fiddo wayarta nan taga missed call ɗin Gwaggo har biyu, sake kiranta tayi bayan ta ɗaga sun gaisa tace ta kira bata kusa ne Gwaggon tace eh tayi tunanin hakan dama zasu tafi ne taga bata ganta ba suyi sallama saida suka fito ɗanta Haisam ke faɗi mata tana gidan Mino tace eh tare da tambayar yanzu sun tafi kenan tace mata eh gasu a Mota, fatan Allah ya tsare tay tace sai tazo, kafin suyi sallama ta tambayi ya Minon tana yar dariya tace lafiya lou dama taƙi kwantar da hankalinta ne tana ta koke koke amman yanzu ta kwantar da hankalin Gwaggo na murmushi tace ina ruwan Mino a hankali zata saba sukai sallama tace tayi ma su Yaya da Safnah Allah ya tsare tace to, bayan sun gama wayar tunanin zaman mi zata zauna yi tay hakan yasa ta shiga kiran Haisam bayan ya ɗaga tace in bai komai yazo ya ɗauketa pls yace Ok, after some minutes ya kira yace mata yana a harabar gidan ta miƙe ta nufi hanyar fita, saida ta buɗe kopar gaban Motar taga ashe harda su twins yazo da yake Motar tinted ce gaba ɗaya an yi masu wanka suna sanye da kaya iri ɗaya suna ganinta Adam ya washe mata baki Abie kuma yay mata ɗan murmushi duk suka miko mata hannu suna son ta ɗaukesu suna faɗin Momy, saida ta zauna sannan ta ruƙe su gaba ɗaya ya tashi Motar suka tafi, bayan sun hau hanya take ce mashi ashe su Gwaggo sun tafi ya ɗaga mata kai tace ta kirata har sau biyu bata kusa da wayar, shiru suka ɗanyi can ya tambayeta lafiya gidan Nameer ɗin tay faffaɗan murmushi idonta akan shi tace mashi laifi yayi ne shine aka kaita rarrashi Haisam ɗin ya ɗan buɗa ido tare da ɗage gira sai kuma yay murmushi ba tare da yace komai ba, suna cikin tafiyar take tambayar shi yaushe zata je Katsina ya bata amsa da Us zasu tafi tace bazata je sallama ba yace in tana so sai taje amman yana son zasu je Adamawa su duba jikin arɗo yaji su Dad ɗinta suna faɗi ma Dad ɗinshi bai lafiya, sosae taji daɗi jin zasu je tace mashi eh bai jin daɗi yace Ok cikin next week sai suje.

Bayan sallar Azahar su Aunty yan Kano suka dawo an cika su da abubuwan arzuƙi Jidderh harda kukan baro Aunty Laila duk tayi sukuku koda ana Maganar Lailar bayan sun dawo sai ta sake saka wani sabon kukan Hajiya na faɗin itama ba Auren zata yi ta tafi ba, Bayan sallar La'asar su Hajiya Maryam suka wuce lagos su Hajiya Zainab ma lokacin suka tafi harda Fauzy.

Alhamdulillah Yan Katsina sun isa lafiya sai fatan Allah ya huta gajiya, a ranar bayan sallar isha duk suna zaune a cikin parlon Gwaggo suna yin hirar bikin baka jin komai sai fullanci dake tashi su innarsu Altine sai zuzuta gidan Mino suke suna faɗin ai Aljannar duniya aka kaita, suna cikin yin firar Amadu da Kamalu suka shigo jin firar da suke ne yasashi kunna Vedio ɗin gidan Minon da yayi lokacin da suke zagayawa ya miƙa ma Yadikko ta fara gani, sakin baki tay da tsananin mamaki take kallon Vedio ɗin tana faɗin yanzu anan Minon take aka bata amsa da eh su Altine da basu je ba duk sun zagayeta sun saki baki galala suma suna kallo, ƙarshe dai kukan farinciki Yadikko ta saka ta hau gode ma Allah da kuma Gwaggo tana faɗin koda tayi aikatau a Abuja bata ta6a tunanin wani nata zai zauna a can ba balle kuma ƴarta, inna Mero matar arɗo ce tace hada halin kirkinta yaja mata yadda ta ruƙe ƴaƴan kishiyarta da Amana bata zalunce su ba ta ɗaukesu tamkar nata gashi nan hakan yayi mata rana tunda data zalunce su ba yadda za'ai Gwaggo ta ruƙa mata ɗiya har itama tayi aure gidan daula su Kakar Minon suka shiga faɗin hakane wllh Yaya kuwa duk tabi tasha jinin jikinta sai murmushin yaƙe take, suna haka wayar Kamalu ta fara ringing ya kai idon shi kan screen ɗin yaga baƙuwar lamba saida ya fito waje saboda hayaniya sannan ya ɗaga tare da yin sallama daga ɗayan bangaren zazzaƙar muryar mace ta amsa mashi tare da tambayar ya yake ya bata amsa da lafiya lou kafin ya tambayi wacece, farko shiru tayi kamar bazata tanka ba saida ya ƙara tambaya sannan tace kenan data amshi number ɗin shi tace zata kira yay saving bai yi ba kenan, jin haka yasa ya ganeta da sauri yace tayi haƙuri ya manta ne da yake lokacin jiran shi ake tace Ok kafin ta tambayi ya suka koma yace Alhamdulillah itama ya tambayeta sun koma ne ko suna Abuja tace mashi No sun koma, ɗakinsu ya nufa suka cigaba da yin wayar saidai itace ke fara yin magana sannan yayi harda tambayarshi game da karatunshi ya bata amsa da bayan ya gama Secondary acan garin su bai cigaba ba dalilin da yasa yanzu ya dawo nan kenan don ya cigaba har ma ya siya Jamb zai yi tace Ok tare da yi mashi fatan Akhairi yayi mata godiya daga baya tace mashi tana son zasu zama Friends in ba damuwa har saida ya jinjina Maganar a ran shi don baiyi zaton jin hakan daga wurinta ba jin yayi shiru tace ko bazai yi abota da ita ba, da sauri yace a'a zasu yi suka cigaba da yin wayar kafin daga baya sukai sallama ya tashi ya koma shago.

Ranar Juma'a lokacin sati guda da bikinsu Nameer Jirginsu Fatuu ya tashi zuwa Yola, a yadda Haisam ya shirya masu zasu sauka a gidan wani abokin Dad ɗin shi wanda shima Senator ne mai suna Buba daga nan sai suje garin su Fatun, bayan sun sauka wurin ƙarfe goma na safe Driver ne tare da ɗan mutumin mai suna Amir wanda zai yi shekara ashirin da biyar suka je ɗaukko su, kyakkyawar tarba suka samu daga iyalan mutumin harda shi aka saukesu a part guda cikin ƙaton kuma haɗaɗɗan gidan nashi anata so a ɗauki su twins sunƙi yarda, lafiyayyun abinci da abubuwan sha aka kawo masu bayan sun ci suka huta har lokacin sallar Juma'a yayi Haisam suka tafi Masallaci tare da Senator Buba da yaran shi maza, bayan sun dawo ne ya sanar mashi zasu tafi can garin su Fatuu yace ai yayi zaton zasu kwana su ƙara hutawa ya tambayi zasu kwana acan ne Haisam ɗin yace mashi ita zai baro ta can ta kwana biyu shi zai dawo nan yace tunda hakane yana ganin kaman yanzu lokaci ya ƙure kar suyi dare ya bari gobe tunda safe sai Driver ya kaisu yadda shima zasu gaisa sosae Haisam ɗin ya amince da hakan. Washegarin wuraren ƙarfe tara da yan mintuna sukai sallama da mutanen gidan suka tafi, tafiyar Awa guda sukai suka iso tun shigowarsu bakin garin Fatuu ta fara murmushin farinciki sosae tayi kewar garin don kusan fin shekara ukku rabonta dashi da yake yanayin damuna ya fara don wasu wuraren sun fara samun ruwa ciki harda nan garin hakan yasa ganyayyaki da tsirrai sun yi kore shar shar gwanin sha'awa ga makiyaya nata koro garken shanaye da tumakai za'a tafi kiwo, Haisam dake zaune seat ɗin gaba nata kallon garin bayan sun shigo Fatuu ce ke nuna ma Driver hanya yana bi har suka ƙaraso kopar gidan tace mashi nan ne, wasu dattawan mutane da a ƙalla zasu kai biyar na zaune a ƙarƙashin ƙatuwar bishiyar dake a ƙopar gidan wasu daga cikin su yan gidan ne ciki harda Mahaifin Fatuu daya zauna yana dakon zuwan su da yake da zasu baro Yola ta kirashi ta sanar mashi sai mutum biyu a cikin su duk yayyen shi ne sauran biyun kuma abokai ne, daga can gefen su yara ne ba masu yawa ba suna ta wasa, bayan ya parker suka buɗe ƙofofin Motar suna fitowa Mutanen dake zaune suka miƙe a kusan tare suka nufo su, cikin washe baki suka shiga yi masu sannu da zuwa Baffan su Fatuu dai murmushi yake idon Fatun na akan shi itama tana murmushin farincikin ganin shi, bayan sun gama gaisawa da Haisam itama ta gaishe su suna ta fara'a suka amsa mata duk wanda yay yunƙurin ɗaukar su twins sai su ƙanƙame jikin iyayen nasu da yake kowa na ɗauke da guda ɗaya, bayan an gama yi masu sannu da zuwa Baffan tare da yayun nashi sukai ma Haisam jagora zuwa ciki, suna shiga cikin soro su Aysha suka shigo da gudu suka nufi Fatuu suka ƙanƙameta cike da farinciki suke mata sannu da zuwa da fullanci Adam dake hannunta ya fara ta6e baki zai yi kuka don sun rungumeta Aysha ta ɗago tana miƙa mashi hannu ya ƙiya sai kallonta yake kaman mai son tuna ta don da bakin su Mino ya yarda da ita Fatuu ta rinƙa faɗi mashi kowacece da fulatanci sai gashi ya tuno ta ya miƙa mata hannu cikin washe bakin jin daɗi ta ɗauke shi, ganin an amshi Adam yasa tace ma Haisam yabata Abie kafin suka idasa shiga cikin gidan mutane duk an leƙo ana masu sannu da zuwa Fatuu ke amsawa shi kuma Haisam kai yake ta jinjina masu fuskarshi a sake.......


100


~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~


.........Bangaren da Arɗo yake aka kaisu can gefe da inda nasu Yaya yake an kewaye wurin da yar gajeruwar kanta daga cikin wurin harda siminti a ƙasa, shiga sukai cikin ɗakin wanda yana da ɗan matsakaicin girma akwae madaidaicin gado na katako yana da wardrobe mai gida biyu samantaa an ɗaura wasu tsofaffin akwatuna na fata dana ƙarfe akwae yan durowoyi na gadon sai wata yar kanta da aka ɗaura al'quranai da wasu littafan addini daga jikin bango kuma wanda ke shafe da siminti an rataye abubuwan fulani harda takubba a cikin gidajen su daga saman ɗakin anyi ceiling irin na da da ake yi da itatuwa ƙasan ɗakin kuma gaba ɗaya a rufe yake da ledar tsakar ɗaki harda ɗan madaidaicin carpet daga tsakiya wannan duk aikin Baffan su Fatuu ne don kullum cikin yi ma mahaifin nasu hidima yake dama kuma yafi duk yan uwan shi wayewa, lokacin da suka shiga Arɗon na kwance a saman gadon jikin shi sanye da riga da wando na yadi mara nauyi sai hula ha6ar kada a saman kan shi suna shiga ya fara ƙoƙarin tashi zaune bayan Baffan su Fatuu ya sanar mashi ga su Inna wuro da maigidan nata sun iso da yake yasan da Maganar zuwan nasu duba jikin shi, saida aka taimaka mashi sannan ya zauna Haisam na niyyar zama a saman carpet da sauri cikin muryarshi data disashe yace kar ya zauna nan Haisam ɗin bai ma ji abunda yace ba ya dai gane ta hanyar hannu daya ɗaga mashi hakan yasa ya dakata Arɗon ya kalli Baffan su Fatuu da fullanci yace ya ɗaukko masu darɗuman makkan shi a cikin kayan shi, Makkan da ya shekara kusan fin talatin da zuwa wasu Ƴaƴan shi ma basu san da yaje ba balle kuma su Fatuu jikoki, bayan ya ɗaukko dardumar wadda ba laifi bata ji jiki ba saboda ji yake da ita don ta shiga cikin tarihin zuwa makkan shi tana da girma, shimfiɗa masu yay a saman carpet suka ce ma Haisam ya zauna Fatuu ma ta zauna daga gefe suma Yayun Baffan dashi duk suka zauna daga gefe nan aka shiga ƙara gaisawa ya juya suka gaisa da Arɗo tare da yi mashi ya jiki a hankali yake amsawa Fatuu ma ta gaishe shi da fullanci tayi mashi ya jiki ya amsa yayi mata sunzo lafiya da tambayar ya suka baro sauran mutane duk ta amsa masu ya kalli su twins yace wannan sune Ƴaƴan nashi da bai sani ba tana murmushi tace eh ya miƙo hannu alamar a bashi su Babban ɗanshi wanda yana cikin wanda suka shigo shima ya manyanta sosae yana murmushi yace ai basu yarda da mutane duk da haka Fatuu ta miƙe da Abie tayi ma Aysha dake daga can bakin ƙopa alamar ta kawo Adam suka kai mashi su, kamar ma tsoron Arɗon suke duk sun waro fararen idanunsu tubarkallah suna bin shi da wani irin kallo daya miƙo masu hannu sai su ƙanƙame su Fatun ƙarshe saidai a hannun nasu ya gansu ya saka masu albarka harda tofin Addu'a yayi masu yace ma Fatuu kafin su koma zai bada magungunan kariya a rinƙa basu tace to, a nutse Haisam cikin cool voice ɗin shi ya tambayi an kai shi Asibiti ne don asan abunda ke damunshi Modibbo ya bashi amsa da sun kai shi Babbar Asibiti ta Jumeta anyi mashi gwaje gwaje an tabbatar ba abunda ke damunshi kawai shekarune to sun bada wasu magunguna sannan sun ce ya rinƙa samun hutu sosae to ya gama shan magungunan kuma yana samun isashshen hutun don ko zama a fadar shi ma bai yi yanzu shiyasa ma jikin nashi da sauƙi sosae, kai Haisam ya jinjina kafin yace yana ganin yakamata a kai shi Asibitin ƙwararru dake a Yola a ƙara mashi bincike sosae suka ce to shidai Baffan su Fatuu shiru yay saidai a ranshi yaji daɗin hakan da Haisam yace don ba yarda baiyi ba a kaishi can amman yayun nashi suka ce kawai 6arnar kuɗi ne tunda an tabbatar da lafiyar shi lau, nuna ma Fatuu wata yar ƙwarya dake a rufe da faifai Arɗo yay yace mata ga fura nan taba Haisam da sauri Baffanta yace mashi ya barta tashi ce yasha suma ga ta can an haɗa masu yanzu zasu je sai su sha ya ɗaga kai Modibbo yace yakamata suje an barsu ko ruwa ba'a basu ba Baffan yace to tare da miƙewa suka ce ma Haisam suje suci Abinci duk suka miƙe harda Fatuu,

Bayan sun fito bangaren su Fatuu suka nufa lokacin da suka isa Fatuu taji daɗin ganin yadda aka ƙara gyara wurin kai kace ba'a cikin gidan bane sai ma da suka shiga cikin parlor shima an ƙara gyarashi akan lokacin da tazo da za'a yi mata aure da Khalid, an sake mashi fenti na zamani haka kujerun ciki ma ba wanda ta sani bane an canza wasu manya abunda yafi burgeta shine yadda ƙasan falon aka sanya tiles daga tsakiya kuma an sa carpet haka jikin ƙopopi ma labulaye masu kyau ne harda abun maƙalesu a jikin bango ga kayan kallo harda freezer yanzu duk babu kwalliyar ƙorai da aka yi an kunna Generator fanka nata yi parlon tsaf yayi irin na yan birni, cike da farinciki Yadikko datai shiga mai kyau tana sanye da riga da zane na lace ta tarbe su tana masu maraba Fatuu ta nufeta ta ɗan rungumeta tana dariyar farincikin ganinta ta miƙo ma Abie hannu zata daukeshi yaƙi yarda Aysha ta miƙa mata Adam tana faɗin ga mai yardar nan sai gashi itama ya yarda ta ɗauke shi, bayan duk an zauna aka shiga gaisawa tare da yi masu an zo lafiya fuskar Haisam a sake yake amsawa yayi mata ya mai jiki bayan ta amsa ta tambayi mutanen gidansu duk yace mata Alhamdulillah suna gaishe su, basu daɗe da zama ba aka fara zuwa gaishe da Haisam tare da yi masu sannu da zuwa tun yana amsawa har ya koma yana ɗaga kai don sai zuwa suke Manya da yara ba alamar zasu ƙare saida Baffa yayi magana kan a bari su ci Abinci sai a zo a gaisa sosae sannan aka tsagaita da zuwa, kwanonin Abinci da ƙurai aka shiga kawo ma baƙi duk aka jere su anan tsakiyar Parlon Yadikko ta kawo masu ruwa da lemu masu sanyi da kofunan glass duk ta zuzzuba masu ta basu ta juya ta nufi cikin ƙuryar ɗaki bada jimawa ba ta dawo ruƙe da babban tray mai ɗauke da plates da cokulla da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login