Showing 162001 words to 165000 words out of 512766 words

Chapter 55 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1629

tsaye Haisam yay daga gaban gadon bai zauna ba ya gaishe da ita ta amsa tay mashi an tashi lafiya, kai idon ta tay kan Fatuu da ta d'an sunnar da kai da murmushi tace "Amarya an tashi lafiya ya bak'unta kuma?" a hankali tace Lafiya lou,

"Ba dai yar kunya muka fara dake ba" Hajiya ta tambaya tana murmushi hakan yasa Fatun d'agowa itama murmushin ne akan fuskar ta a hankali tace mata a'a, "Yauwa to, ni ba surukar ki bace Kakar kice a hakan zaki cigaba da kallo na muci gaba da wasa da dariya kaman da, don ma yanzu anyi hankali natsuwa tazo an rage sani nishad'i" yar dariya Fatuu tay ba tace komai ba, kallon Haisam tay "Kai kayi tsaye kaman wani Security ka samu wuri mana ka zauna, ko gadin Matar taka kake?" Fuskar shi a sake kaman zai murmushi ya kalleta ta nuna mashi Stool a gaban mirror tace ya d'aukko shi sai ya zauna, yin yadda tace yayi suka d'an yi shiru kafin ta fara magana,

"Alhamdulillah, duk abunda Allah yayi mai kyau ne, a koda yaushe muna rok'on Alkhairi so duk abunda muka ga ya faru damu in ma mai kyau ko akasin hakan Alkhairi ne, Fateema ina maki barka da shigowa wannan Family don a yanzu kin zamo wani 6angare nashi, ina fata zaki d'auke mu a matsayin dangin ki, ki rungumi kowa matsayin dan'uwan ki duk da bani da shakku akan ki nasan ki farin sani nasan baki da matsala to sai kinyi hak'uri don shi mataki ne nasara ba kamar a yadda Auren naku ya kasance, dole daga baya za'a iya fuskantan yan matsaloli bama fata in sha Allahu muna fatan Allah zai shige mana gaba, sannan ina son ki saki jikin ki kada wai ko don kiga ga yadda akai auren naki ki takura kanki Ki k'i yin walwala, duk aure aure ne duk kuwa yadda aka yi shi ki walwala ki farinciki ki Alfahari da Auren, gidan mijin ki naki ne so ba buk'atar takura kai, duk yadda bani da haufi akan mijin ki ance wai zo mu zauna zo mu sa6a, so a duk lokacin da yay maki wani abu da baki ji dad'in shi ba ki k'ok'arin yi mashi Magana kada kice zaki bar abun a ranki duk d'an Adam ajizi ne zai iya yi maki laifi ba tare da ya ankare ba, ta hanyar yi mashi magana ne zai gane har ya gyara laifin shi, in kuma bai gyaran ba wanda bana tunanin hakan ni kizo ki sanar dani kar kiji wani abu, duk yay maki wani abun da kike tunanin fad'i ma wani don neman mafita ko shawara kizo wuri na kar kice zaki kai k'ara gidan ku hakan ba komai yake jazawa ba face matsala, zai iya maki abu kije ki fad'a daga baya ku shirya ki manta ma amman su kuma abun na nan a ran su watak'il su k'ullace shi ko makamancin hakan, don haka k'opa ta a bud'e take duk in kina da wata matsala kizo gun Hajiyar Sanata ki fad'a mata ni kuma in sha Allahu zanyi k'ok'arin ganin na daidaita komai, ina Fatan zaki cigaba da yi mashi biyayyar dana san kina mashi kada don ya zama mijin ki kice zaki rage kan hakan a'a a yanzu k'arawa ya kamata kiyi don muhimmancin shi a yanzu yafi na da ya tashi daga Yayan ki Handsome ya koma Mijin ki wanda Aljannar ki ke a tafin kafar shi" d'an dakatawa tay kan Fatuu a k'asa haka Haisam d'in Fuskar shi na a gefe,

"Na dawo gare ka Zakee manyan dawa, ga Fateema nan Amana ce a wurin ka duk da nasan kasan da hakan amman ina fad'a maka ne don kada ya zama ba wanda ya fad'a maka hakan, ka ruk'e ta Amana dama can kai kamar guardian ne a gare ta to yanzu matsayin ka ya koma biyu don haka sai ka linka komae, kuma don ta zama taka ba yana nufin ta zama baiwar ka ba duk kyautatawar da zaka yi mata lada zaka samu haka in har kaci zarafin ta ka munana mata tabbas zaka samu zunubi don haka ta zama taka ne don ka kyautata rayuwar ta, sannan ina son jan hankalin ka kayi k'ok'arin zama adali ga matan ka nasan ba sai nayi maka bayanin yadda zaka zama adali ba kasan miye yin Adalci tsakanin mutane, idan har ka za6i yin rashin Adalci to ka bud'e ma kanka da kanka kopar matsalolin da zasu hana maka kwanciyar hankali ga kuma zunubi a wurin ubangiji, a k'arshe ina Addu'ar Allah yasa Albarka a Auren ku ya kauda duk wata fitina, yasa ya zame maku silar shiga Aljanna gaba d'ayan ku, Amin ya Rabbi" a hankali Haisam ya amsa da Amin Fatuu kuma a cikin rai ta amsa Hajiya ta kai hannu ta d'an bugi shoulder d'in ta tace ita bazata amsa ba ta d'ago tana yar dariya tace ai ta amsa,

"Oh Fateema ni wannan in nayi sakaci ban yi da gaske ba yar gaisuwar da nike samu yana zuwa ma ai sai ki hana shi ya tattara ni ya zuba a dustbin" cikin rashin Fahimta Fatun ta d'an waro ido Hajiya taci gaba "eh mana, kina irin wannan kwalliyar ina zai rink'a tunawa da wata tsohuwar matar shi..." Tun kan ta rufe baki Fatun tasa tafukan hannuwan ta ta rufe fuska Hajiyar nata dariya, a hankali Haisam ya d'ago ya kalli Fatun suka had'a ido da Hajiya ta d'an harare shi cikin wasa yay d'an guntun murmushi ya juyar da fuskar shi gefe,

"Yanzu dae ki bani cin hanci sai in yafe maki shi in kuma fad'a maki abubuwan da zasu sa ki kama shi a hannu" cire tafukan hannuwan tay tana murmushi bata ce komai ba, mik'ewa yay yace ma Hajiyar zai d'an je G.r.a tace a dawo lafiya ya nufi hanyar fita, kallon Fatuu Hajiya tay ta d'an kai mata bugu tace bazaki tashi ki raka shi ba yaran zamani duk baku san abunda ke sa ana kama miji ba, mik'ewa tay a kunyace ta nufi hanyar fita Hajiya ta bita da ido tana murmushi a ranta ta ayyana Allah kenan gwanin hikima, wasu mutanen na shigowa rayuwar mu ne in ma su amfane mu ko mu mu amfane su, wasu su tsaya wasu kuma su tafi bayan sun taka rawar da zasu taka, a fili ta furta "Allah kasa Mudace", tana fitowa har ya kusan fita daga parlon taja ta tsaya a bakin corridor, kamar yaji a jikin shi ya juyo suka had'a ido, dakatawa yay ganin haka yasa ta nufe shi walking slowly, a d'an gaban shi ta tsaya tana bin shi da kallo ganin ya kafeta da ido yasa cikin yar inda inda tace "D...dama Hajiya ce tace in rako ka" da k'yar ta kai Maganar Saboda kallon da yake bin ta dashi ba Arzik'i ta sunkuyar da kanta,

"Ok thanks, ki koma" taji yace ta d'ago, kai ta d'an d'aga mashi yana shirin juyawa tace "Sai ka dawo Allah ya tsare" dakatawa ya sake yi ganin yanayin fuskar shi kaman zai murmushi yasa itama ta d'an yi mashi, "Do you need something?" da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a ya d'aga kai ya wuce, saida taga fitar shi sannan ta juyo tana d'an sakin Murmushi ta nufi komawa Bedroom d'in Hajiya..............




_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2064*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*



..........tana shiga tace mata ya tafi ta d'aga mata kai kafin tace eh a hankali , a inda ta tashi ta koma ta zauna Hajiya ta fara magana "irin nuna kulawa haka yana k'ara dank'on k'auna tsakanin ma'aurata, yanzu kinga kece abu na k'arshe da ya gani kafin ya fita to zaki ga kin tsaya mashi a ran shi yana tafiya yana tunanin ki har ma kiga yana d'an murmushi kaman ta6a66e, ba kamar yadda kika ci gayun nan" Dariya Fatuu ta saki ba kaman da tace kaman ta6a66e ta bata dariya sai Maganar ta tuno mata da Maganar Aunty Mareeya, itama hajiyar Dariyar take taci gaba "naji dad'i dana gan ki haka tsaf kin sha gayu wannan ma zai taimaka wurin siye zuciyar shi don shi mutum ne mai tsananin son tsafta nasan kin san da hakan, ga son k'amshi don haka ki dage da tsafta, amman fa kuma kar tay yawan da zaki janye man hankalin shi gaba d'aya" ta d'an ta6e baki, sosae Fatuu ta saka dariya, cigaba tay bayan ta d'an murmusa,

"Komai nashi Sak kakan shi wllh, yana tuna man dashi a koda yaushe shiyasa bazan 6oye ba a duk jikokina nafi jin shi a raina kowa ma ya sani, hatta y'ay'an cikina ban jin su kaman yadda nake jin shi, Duk irin halayen shi na kakan shi ne, koda ake ganin Sojoji kaman basu da kirki basu da tausayi ba haka bane kowa da irin halin shi kaman dae a sauran mutane....." D'an dakatawa tay tana kallon hoton Gen. Adamu Zakee dake a jikin bango cikin shiga ta Alfarma, da gani akwae k'auna mai k'arfi a tsakanin su kuma rashin shi ba k'aramin ta6a mata zuciya yay ba,

"Shima haka yake da son K'amshi, ko 6ata mashi rai kikai in dae zaki je bashi hak'uri ya kasance kina sakin k'amshi to Magana ta k'are tuni zai yafe maki, koda ma ba ke kika 6ata ran ba in dae zaki rarrashe shi kina k'amshi yanzu ya saukko" idonta akan hoton take Maganar, tausayin ta ne ya kama Fatuu itama ta kai idon ta kan hoton ta d'an girgiza kai, bayan d'an wani lokaci Hajiya ta sauke idon ta tare da ajiyar zuciya, kallon ta Fatuu tay da d'an murmushi tace "Allah ubangiji ya jik'an shi da rahama yasa ya huta, Allah ya h....had'a ku a Aljanna" tana murmushi ta amsa da Amin sai kuma tace "muci gaba da soyewa acan ko?" Dariya Fatuu tay suka d'an yi shiru, can ta kalle ta tace bari taje wurin Aunty Saude ta taya ta aiki,

"to ke waya fad'a maki Amarya na wani aiki, ki zaman ki ki huta, ki k'yale ta tayi aikin ta lokacin yin aikin zai zo sai kita yi" shiru tay ta maida kanta k'asa, "in kina son zuwa kije k'yama k'ara koyon wasu abubuwan tunda Saude ba daga baya ba wurin iya girki tasan hannun ta, sai ki dage ki k'ara koya duk da ma Mijin naki ba gwanin cin Abinci bane, amman k'ilan ya rink'a cin na Matan shi" tana d'an murmushi ta mik'e zata tafi, har ta juya Hajiya ta dakatar da ita, "Yauwa na tuna, Maganar gyaran part d'in naku Tukur ne ke yi, to tun kafin ki tare yayi man magana kan zai cigaba ne ko a'a nace ya bari ki zo duk da dai shi Namiji ne ina ganin baida Matsala, amman ke ya kike so" d'an jimm Fatun tay ta rasa mi zata ce Hajiyan tace ta bud'e baki tay magana, a sanyaye tace duk yadda ta yanke yayi,

"Shi d'in ne ya nuna yana so, tun farko ma ni ba shi naso yayi aikin ba bayan Haisam d'in ya dawo sawa nayi ya nemo wani amman ya matsa, kwanaki har zaunar dashi nayi nai mashi Magana kan hakan tunda ko ni bai bari akai kayana wurin wanki ga Karatu lokacin amman sai cewa yay wai baida abunda zai saka mana sai dai hakan kawai, nace to mu duk abunda ya ga an yi masa ai don Allah ne ba wai don ya saka mana ba, dama can Allah ya k'addaro akwae rabon shi a tare da mu" ta k'arasa tana murmushi itama Fatun shi take yi, "Yanzu tunda naga ya nuna yana so ke ki rink'a gyara Bedroom da Kitchen ala bashshi shi sai ya rink'a gyara maki parlon tunda dama yana da girma ko in kin tafi Makaranta sai ya shiga ya gyara, Wankin k'ananun kayan mijin naki kuma kyaci gaba in zai mashi na manyan kaya sai yazo nan yay amfani da injin d'in nan, koma kawae bari na mashi magana tunda ga naki sun k'aru ya bari a rink'a kaiwa dry cleaning kawai", kallon Fatun tay "lafiya lou zaki rink'a gyara Bedroom d'in da Kitchen d'in ba takura tunda naga karatu kike?" Da sauri tace mata eh, a ranta ta raya ita da ke yin fin wannan aikin a gida wannan ai ba wani aiki bane, ce mata tay taje tayi mata godiya ta juya ta fita, Kitchen ta nufa a ciki ta iske Saude na shirye shiryen d'aura girkin rana, da yar sallama ta shiga ta juyo tana murmushi ta amsa mata ta nufi gefenta gaban drawer ta jingina fuskar ta da murmushi tace "Sannu da aiki Aunty Saude",

"Yauwa Amaryar mu kun shigo" kai ta d'aga mata suka d'an yi shiru,

"Aunty Saude aiki na zo taya ki" d'an waro ido tay "aiki kuma Fateema keda kike Amarya, ki rufa man Asiri kar nayi laifi" tana murmushi tace "kai Aunty Saude daga taya aiki sai yin laifi ai na fad'i ma Hajiya zan zo in taya kin" tace "to amman ai ina iya yin laifi wurin Angon naki yaga duka daga kawo mashi Amaryar shi jiya yanzu na saka ta aiki" d'an tura mata baki tay tana murmushi "Kai Aunty Saude shi ina ruwan shi kuma ma ai ya fita bai gidan"

"Ya kamata dai kije ki huta don kina buk'atar shi ansha hidima" still tura bakin ta k'ara tana kallon ta itama Sauden kallon ta tay tana yar dariya, Fatuu tace "ni dae na huta har na gaji ma" kafewa tay kan sai ta taya ta aikin girkin tace ai ta k'ara koya ma Sauden tace shikenan tunda ta kafe,

"Mi kike so a dafa tunda ban kaiga d'aura komai ba sai ayi gaba d'aya kawai" d'an bud'a ido tay alamar mamaki tace "Aunty Saude ni zan fad'i mi za'a dafa" yar dariya tayi "Eh mana ki fad'i abunda kike so a dafa maku keda Angon naki" d'an jim tay ta maida idon ta k'asa alamar kunya, ganin ta tsaya tana kallon ta alamar amsa take jira yasa ta d'ago tana d'an far far da ido tace "Aunty Saude kiyi abunda kikai niyya kawai" tace "to ko shi ki fad'i abunda yake so sai ayi" d'an jimm ta k'ara yi sai kuma tace "to ai kin fi ni sanin abunda yake so ni dai kawai nasan bai son tuwo da miyan yauk'i"

"Eh bai cin tuwon masara ko dawa da miyar yauk'i sai na shinkafa da yake yana son Abinci irin haka su sakwara har teba ma yana ci" Fatuu dake kallon ta tace "to ko ayi ebar?" Dariya tay "haba Fateema ya za'a had'a ango da teba kuma" itama Fatun dariyar tay bata ma san ya akai ta furta hakan ba, "ina ganin ko ayi sakwara don gaskiya yana son ta" Saude ta fad'a, da d'an sauri ta d'aga kai tace to ayi, amsar gyalenta tayi ta kai mata d'akinta bayan ta dawo suka fara aikin Pounded Yam d'in ba 6ata lokaci, Fatuu na tsaye tana yanka su alaiyyahu da Albasa harda ganyen ugu tace "Aunty Saude wai sai yaushe zaki tare?" tana juya miya tay yar dariya "ai na riga na tare Fateema" da alamun mamaki "kin tare, amman kuma yanzu ba d'akin ki na cikin nan kika kai man gyale na ba?"

"Eh ai ban bar d'akin ba har yanzu matsayin nawa yake inna shigo ina aiki kinga ba sai nata zarya zuwa baya ba, kuma ma in ya tafi garin su wurin d'ayar matar shi a nan zan cigaba da kwana" kai Fatun ta d'aga alamar gamsuwa sai kuma tace "Amman Aunty Saude tarewa ba sanarwa balle ai mana d'an shagali" tana yar dariya ta k'arasa, itama dariyar tayi "Kai Fateema har kin bani dariya wane shagali kuma tsofe tsofe dani wannan ai sai ku, kema kawai nasan don ga yadda Al'amarin ya kasance ne da ba k'aramin shagali za'ai ba duk da haka kina iya ganin anyi daga baya" murmushi kawai Fatun tay tana fad'in ba wani tsufan da tayi wllh ai da ko yar Walima an yi masu, Sauden tace Hajiya ma taso tayi itace ta nuna bata so, cigaba da aikin sukai har Sauden na tambayar Fatuu turaren da ta shafa k'amshin yayi mata dad'i in ba tsada zata siya irin shi tace mata ai Humra ce duk da ta shafa turaren kad'an amman dai k'amshin na Humra ne, ta fad'i mata wadda ta siyo mata tace aikuwa tana so gaskiya zata bada a siyo mata Fatun tace ta bari zata d'ibo mata, nan fa suka hau yin yar jayayya Saude na fad'in a'a karta kwashe abunta ta bari a siyo mata kawai tace to ai kafin a siyo mata sai ta fara amfani da wadda zata batan tunda akwai da yawa, basu d'au wani lokaci mai tsawo ba suka gama had'a komai saura k'arashe, bayan an kwashe Fatuu tace bari ta nik'a cikin Food processor Sauden tace ta bari ta daka a turmi tafi dad'i Hajiya ma tafi son a daka, bayan ta fiddo turmin ta wanke ta fara d'akan sakwara Fatuu ta kafe kan sai itama ta daka farko Sauden ta k'i bata k'arshe da ta matsa ta bata tana faman fad'in tabi a Hankali don Allah kada tsautsayin Amarci ya gifta Fatun sai dariya take, kan kace mi daddad'an k'amshi ya karad'e Kitchen d'in har cikin Parlor, bayan an kammala hada miyan egusi da ta sha ganye ga ganda da kuma nama tayi wani irin kitif bata ko juya jikinta sai an juya ta, a tare suka nannad'a sakwarar a farar leda, bayan sun gama a wasu jigunannun luxury Warmers aka zuba tasu Fatun,

"Ban taho da Warmers d'in jiya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login