Showing 96001 words to 99000 words out of 512766 words
Chapter 33 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1632
zancen Haisam ne za'a d'aura dashi suka nufi cikin gida da hanzari har rige rigen shiga d'akin suke lokacin su gwaggo duk suna a parlon tun bayan da suka gama sallar la'asar har saida su gwaggon suka tsorata ganin yadda suka fad'o masu Amadu na washe baki ya hau yi mata bayanin abunda ke faruwa a waje cikin d'aurewar kai ta maimaita sunan Haisam matsayin wanda za'a d'aura aure dashi yace mata eh wllh har sadaki ma an kawo Naira 500k zaro ido gwaggo tay tama kasa cewa komae Yadikko ko bata san lokacin data fara sakin murmushi ba Kamalu ne ya juya da sauri ya nufi d'akin baffan su ya sanar mashi lokacin yana kwance ya kasa fita Saboda damuwa ai yana jin zancen ya mik'e ba shiri ya nufi wajen anan aka shirya d'aura auren gobe Juma'a a Masallacin Juma'a dake Jimeta bayan gama Sallar juma'a Lokacin da Alhaji Lawal zai tafi har kud'i Abbas ya basu don su sha mai amman yak'i amsa yace da Haisam da Fatuu duk ya'yan shi ne k'arshe saidae yay ma driver d'in shi Alheri suka tafi kan sai goben, sam gwaggo ta rasa farin ciki zatai komi gaba d'aya kanta ya gama d'aurewa ta yadda akai Al'amarin ya kasance haka, sai bayan sallar isha sannan duk suka hallara a parlon Yadikko harda Abbas cike da damuwa gwaggo tace "d'ana Abbas ya akai hakan ta faru Saboda mi zaku takura kan ku har haka shi Haisam bai ganin bai dad'e da yin aure ba zai k'ara wani wanda nasan ba don yana so bane kawae k'arfin hali ne irin nashi shiyasa ya za6i cire mu a matsala shi kuma ya jefa kan shi a matsalar aure ba ba k'aramin abu bane, gaskiya ni ban goyon bayan auren nan kwata kwata shima nasan bai yi nazari yadda ya kamata ba kafin ya amince, gaskiya ban amince ba kawae a k'yaleta ta auri wanda suke so hakan zai fi nima hankali na zai fi kwanciya fiye da ace Haisam ta aura" ganin yadda duk ta damu yasa Abbas warware mata komae yace shi yana ganin hakan zai fi kan ta auri wanccan da bata so kuma shima Haisam d'in hakan yayi mashi tunda ba takura shi yay ba ta bari kawae ayi yadda suka tsaran Allah yasa haka yafi zama Alkhairi" Yadikko itama tace "nima ina ganin hakan zai fi kawai ai dama Addu'ar abunda yafi zama Alkhairi duk muke tayi to hakan shi yafi Alkhairin" Baffan Fatuu dae ya rasa ta cewa su Amadu da Kamalu ma duk suka goyi bayan yadda aka tsaran gwaggo dae tay shiru fuskarta d'auke da damuwa duk da ta ragu sakamakon jin ba auren dundundun bane nan Abbas yaba gwaggo sauran 300k d'in yace ayi abunda yakamata tace yaba Baffan dama an bashi sadakin Fatun amman saida Ardo yasa aka bashi wani abu a ciki wai ai sun riga sun gama mata komae, Yadikko ta zubo ma kowa Abinci bayan an gama ci duk akai sallama kowa ya nufi wurin kwanciya Amadu har ya fita ya dawo yace ma gwaggo yana son magana da ita ta mik'e ta fito wajen jiki sukuku acan gefe suka ke6e ganin yadda duk ta damu ya shiga kwantar mata da hankali yace shi yana jin hakan wata hikima ce ta Ubangiji nan ya kwashe komae game da son da Fatuu kema Haisam d'in har ciwon da tayi acan baya suka zata na Aljanun ta ne tsananin mamaki ne ya kama gwaggo har saida tasa hannu ta ruk'e ha6arta baki bud'e ta shiga fad'in yanzu dama duk wannan halin data shiga Saboda Haisam ne Amadun yace mata tabbas don da bakinta ta fadi mashi ya bata labarin lokacin d'aya isketa cikin mawuyacin hali tana amai a d'aki har ta sanar mashi hakan tafa hannu gwaggo ta shiga yi tana salati Amadun yace don haka ta bi su da Addu'a kawae k'ilan Allah ne ya cika mata burinta, a daren ranar kasa runtsawa gwaggo tay sosae tausayin Fatuu ya mamaye mata zuciya biri yayi kama da Mutum ashe shiyasa tak'i sake ma Fanan duk da hakan ji take ba yadda za'ai auren ya dore abunda za'ai iya su ba tare da sanin dangin shi ba ita kanta bazata so Fanan taji zancen auren nan ba Saboda yadda ta d'auke su gani take hakan zai zama tamkar cin Amana ne, Washe gari Juma'a aka fara shirye shiryen d'aurin aure tunda safe Abbas da Baffan Fatuu suka tafi kasuwa suka yo siyayyar kayan Abincin da za'ai harda tunkiya da za'a yanka bayan sun dawo dole gwaggo ta washe suka fara hidiman Abinci da soyen nama bayan sallar Juma'a Mutane masu yawa suka shaida d'aurin auren Haisam da Fatuu sosae Alhaji Lawal yay kokari don kuwa shi ya kawo take aways na abinciccikan da aka raba ma Mutane, bayan sun koma gida aka ci gaba da hidiman biki saidae yawanci yaran gidan ba kowa ne yasan da Maganar auren ba sun dae ga anyi Abinci ga nama kuma an soya Yaya ranar wuni tay a d'aki tana ciwon bakin ciki tun bayan da taji da wanda aka d'aura ma Fatuu aure to ai dama ita Hassada ga mai rabo taki ce, Washe gari ana gama sallar Asuba suka kamo hanya harda su Yadikko aka taho Katsina..........
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2052*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
............. Lokacin da suka iso Katsina wannan dalilin ne yasa lokacin da Fatuu ta tambayi Abbas da gaske an fasa auranta yace mata eh amman an d'aura da shi haka da zata bi su Mino lokacin da Abbas yazo kai su suga gari ta saka fitted gown Yadikko tay magana kan rashin dacewar ta fita da rigar da d'an k'aramin gyale har gwaggo ta saka baki k'arshe dai saidae ta canza kaya haka lokacin da Haisam ya kirata vedio call da tace fushi take dashi har bacci ya kwashe ta ya kai hannu yana zagaye lips d'in ta saman screen lokacin duk matar shi ce ita, bayan an samu natsuwa su Yadikko sun koma aka fara shirin cigaba da karatun Fatuu lokacin gwaggo ta nemi Abbas yazo suka zauna a parlor bayan sun gaisa ne ta fad'i mashi dalilin kiran nashi dama kan Maganar sakin Fatuu ne don suna shirin cigaba da karatun ta kuma ga aure akan ta shiyasa take so ya tuntu6i Haisam da Maganar dama sadakin shi na nan a wurin Baffan ta za'a maido mashi amman sai yace shi yana ganin ba sai an yi mashi magana ba tunda ai yasan da auren shi a Kanta kuma dole zata cigaba da karatu don haka a k'yale shi taci gaba kawae cike da damuwa gwaggo tace "amman baka ganin akwae had'ari ace ta tafi wani gari karatu da auren da bata san dashi ba a kanta ni ina ganin d'ana Abbas gara ai mashi Magana ya saki kaman yadda aka tsaran" Abbas d'in ya nuna mata shi fatan da yake dama auren ya d'ore ba wai su rabu ba gwaggo ta hau girgiza kai tace "gaskiya ni bana son hakan duk da zan yi matuk'ar farin ciki in ta samu miji kamar shi to amman ana barin halak ai ko don kunya yanzu in matar shi tasan da Maganar auren da wane ido zan kalleta ita kanta zata ga an ci Amanar ta ba kamar yadda ta d'auke ni tamkar itama ni kakarta ce" cikin kwantar da murya Abbas yace "gwaggon mu wannan duk ba abun damuwa bane in dae Allah ya kaddaro dama zasu kasance miji da mata ai mu bamu isa mu hana ba kuma duk abunda zamu yi yanzu wllh bamu isa mu raba ba don haka mu bar ma Allah komae shi zai shige mana gaba kiga komae yazo da sauk'i" ba don taso ba tace mashi shikenan amman dae gaskiya bai kamata ta tafi wani gari karatu da aure a kanta ba shine ya kawo mata shawarar Fatuu ta fara yin School of Nursing tunda an kusa fara yin Medicine anan ko bayan ta gama ne sai tayi k'arshe gwaggon ta amince ta kuma rok'e shi kan ya taimaka mata wurin kula da Fatun yace in sha Allahu, tun daga wannan lokacin duk abu in ya shafi Fatuu sai gwaggo ta tuntu6i Abbas ko lokacin da zasu bikin Haulat Nijar sai da tay mashi magana shi kuma ya kira Haisam don neman izini lokacin yace mashi duk inda zasu suje ba sai an rink'a tambayar shi ba ya bada izini haka lokacin da taso zama a Hostel farko gwaggo tak'i amincewa tace saidae in ya kama ko zasu yi wani abun kaman yadda ta fad'a mata daga baya ta tuntu6i Abbas da Maganar yay ma Haisam Maganar shi da kan shi yace abarta in dae tana so ta zauna shiyasa gwaggon ta k'yaleta take zama saidae duk da haka tana saka ido sosae a kanta kaman wurin sa kaya da kuma tabbatar da tana a Makarantar duk da ta yarda da ita sosae.
***** ****** *****
Suna isa Abincin Haisam ya hango Dr Habeeb a bakin main Entrance gefen shi nurses ne guda biyu suna ruk'e da gadon d'aukar mara lafiya ya nufi inda suke ya parker a gefe ko kashe Motar bai yi ba ya fito lokacin itama Hajiya ta bud'e kopar bayan ta fara K'ok'arin fitowa, d'ayan side d'in Haisam ya nufa yaima nurses d'in alamar su zo suka turo gadon zuwa inda yake bayan ya bud'e kopar ya duk'a ciki ya cicci6o Fatuu da take a kwance ba numfashi ya juya ya d'aurata akan gadon Dr Habeeb ne ya basu umarnin su nufi Amenity da ita ya juyo kan Haisam da Fuskar shi ta bayyana tashin hankali hakan yasa ko gaisawa basu yi ba ya tambaye shi abunda ke faruwa nan yay mashi bayanin cikin da ke gareta da kuma yadda ta fara zubda jini sakamakon razana da tayi saidae ya nuna mashi akwae yuwuwar tayi wani abu dama don ta zubar da cikin da sauri yace mashi su je suka nufi ciki gwaggo da Hajiya ma suka rufa masu baya, lokacin da suka isa har an shigar da ita d'aki an kwantar da ita Dr yaba d'aya daga cikin Nurses d'in umarnin abubuwan da zata kawo mashi da sauri ta amsa ta juya da d'an gudu gudu ya kalli Haisam yace su jira ya shige d'akin dama d'ayar Nurse din na ciki bada jimawa ba wadda ya aika ta dawo ta shige had'i da maida kopar ta rufe, tsaye duk sukae kowa ya jingina da bango ga seats nan na zaman jira amman duk sun kasa zaunawa Saboda fargaba da ta cika kowannan su Hajiya sai k'wafa take tana kai hannu tana ruk'e ha6arta da bakin ta gwaggo dae tayi jugum sai ido kawae ita kadae tasan halin da take ciki sai Addu'oi take a zuciyarta Haisam kuma ya d'age face d'in shi sama yana kallon ceiling yayin da hannuwan shi ke zube a cikin Aljihunan jeans d'in shi, sai bayan kusan 15 minutes Dr ya bud'e kopar ya fito da sauri Hajiya tace "Dr ya ya?" d'an murmushi yay yace mata lafiya lou in sha Allah ya juya kan Haisam da ya sauke face d'in shi yana kallon shi yace mashi bari ya gan shi a Office aikuwa a harzuk'e Hajiya tace "Dr kamar ya ka gan shi a Office baka ga yadda duk muka damu bane har ma mun fi shi shiga damuwa duk abunda zaka fad'a mashi ai mu ya cancanta ka fad'a mawa ba shi da yayi silar jefata a halin da take ciki ba saboda son zuciya har da ma wannan" ta kai Maganar tana nuna gwaggo da sandar hannunta sadda kai k'asa gwaggo tay ita kanta ta k'osa taji halin da Fatun ke ciki ganin yayi shiru yasa Hajiya cewa suna jin shi a wane hali take ciki ne gyara tsayuwar shi yay yace "ta razana sosae ne shiyasa tay doguwar suma hakan kuma ya haddasa mata bleeding d'in da take don cikin dake jikinta ya fita amman akwae yuwuwar dama anyi kokarin zubar dashi don bleeding d'in yayi yawa ace iya razanar tasata zubar da jini haka sosae amman mun samu jinin ya rage ita kuma har yanzu bata farfado ba amman dae ba wani abu zata farfado in sha Allah yanzu tana buk'atar Oxygen don level d'in nata yayi k'asa sosae sannan already an samata drip yanzu tana buk'atar jini kusan leda biyu...." Tun kan ya rufe baki Hajiya ta shiga nuna mashi Haisam da sandar hannunta tace "gashi nan ja shi ku tafi a de6i nashi in ma fiye da leda biyu ake so duk shi zai bada su" Dr dake d'an murmushi yace "ai Hajiya sai in yayi daidai...." Katse shi tay da fad'in "ko ma bai yi daidai ba ku d'iba sai kuyi ma canza ku bata wanda yay daidai da nata, amman in fad'a maka gaskiya bai dad'e daya tashi daga jinya ba don haka ku binciki jinin in ba wata cuta kar aje a d'irka mata wani abun ya faru a lik'a man sharri nima a saka ni cikin wad'anda suka cuceta" d'an ta6e baki Haisam yay yayi ma Dr alamar suje da hannu yana murmushi suka tafi nurse dake ruk'e da jinin Fatuu da aka d'iba tabi bayansu suka nufi Lab, bayan sun je aka d'ibi jinin Haisam d'in duk aka gwada aka ga zai iya bata kuma cikin sa'a bai da ko malaria har Dr Habeeb na cewa da yake ba anan yake zaune ba shiyasa bai da yar Malariar zamani shidae d'an murmushi kawae yay sai kuma yace mashi a ka'ida leda guda yakamata ya bata Haisam d'in yace in dae za'a iya samun leda biyun a d'iba kawae Dr yace shikenan aka fara shirin d'ibar jinin baida yadda zai yi duk irin kyankyamin shi haka ya kwanta akan gadon, ana gama d'ibar leda guda wata irin juwa ta taso mashi har ya kasa jurewa saida ya kai hannu ya dafe forehead d'in shi Dr Habeeb na ganin hakan ya tambaye shi halan bai ci Abinci ba sai lokacin ya tuna da baici Abincin rana ba an dae siyo mashi bai kaiga ci ba Fatuu taje mashi da zancen cikin da ke gare ta, kai ya d'aga mashi alamar eh Dr d'in yace yana zuwa ya fita bai d'au lokaci ba ya dawo ya kawo mashi Maltina da cake yace bari aje a fara saka mata wanda aka d'iba ya d'aga mashi kai, Bayan an tafi a d'ibi jinin Haisam d'in Hajiya da gwaggo suka shiga cikin d'akin gwaggo ta tsaya daga gefen gadon idonta akan Fatuu dake kwance ido a rufe kanta ba kallabi gashinta ya tarwatse, a gefen gadon Hajiya ta zauna fuskarta cike da tausayi ta kai hannu ta shafa fuskar Fatun tana Fad'in "Baiwar Allah Fateema hakanan an d'auki alhakin ki ana neman asa ki rasa rayuwarki gashi ansa kin aikata babban laifi in ke kika zubar da cikin koda yake su Allah zai kama da laifi ba ke ba...." Haka tay ta surutai gwaggo dae tay shiru, Dr na fitowa ya nufi Amenity anan suka had'e da Abbas daya shigo ya nufe shi bayan sun gaisa fuskar shi d'auke da damuwa ya tambayi Dr d'in abunda ke faruwa don yaga Motar Haisam a waje alamar suna Asibitin nan ya kwashe komae ya fad'i mashi da tsananin mamaki Abbas ya maimaita Zarah ta samu ciki, jin yadda cikin ya zube ne yasa bai nuna farinciki ba tare da Dr suka nufi Amenity d'in, bayan sun shiga d'akin wata uwar harara Hajiya tabi shi da ita nan take yasha jinin jikin shi ya gaishe da gwaggo da ke zaune kan yar doguwar kujerar da take cikin d'akin da d'an murmushi ta amsa yace ya mai jiki kafin ta bashi amsa Hajiya ta amshe da fad'in "Mai jiki da kuka jefe halin da take ciki? to ai gata kana gani don haka sai ka ba kan ka amsa ba sai ka tambayi wani ba" hannu ya kai ya d'an sosa k'eyar shi ya gaishe da ita tay banza da shi ta kya6e baki Dr Habeeb ya wuce ya fara kokarin sama Fatuu jinin bayan ya gama zai fita Abbas na niyyar bin bayan shi Hajiya tace ya tsaya zatai magana dashi yace to, bayan fitar Dr tana mashi wani mugun kallo tace "Yanzu Abbas abunda ku kai kun kyauta, domin Allah kun kyauta ma Fateema dubi halin da kuka jefa yar mutane kiri kiri kusa yarinya tay ta yawo da aure a kanta ba tare data sani ba taya zaku aikata wannan d'anyen aiki haka??" d'an rankwafar da kai yay yace "Wllh hajjaju gaba d'aya hakan ya faru ne Saboda samun mafita gudun jefa rayuwar ta a matsala......" Nan ya kwashe yadda komai ya faru ya sanar da ita cikin fushi tace "to ai gashi nan matsalar da kuke gudan mata ku kun jefata a wata shi kuma in bada niyyar rabuwa da ita ya aure taba ai sai ya fito ya bayyana ma Mutane duk abunda zai faru ya faru yafi da ya kama baki yay shiru shi ga miskili sannan kuma yay kwance kwance ya d'irka ma yar mutane ciki ba kunya ba tsoron Allah banda fyaden da yay mata, iya cuta dae wllh an cuci Fateema kuma harda ku a cutar da ita don haka ku zauna da shirin in dae wani abu ya sameta ba fata nike ba sai an bi mata hakkinta, a ina aka ce don yarinya matar ka ce ka afka mata hakan ai bashi da maraba da fyad'e" kan Abbas na sadde k'asa haka ma gwaggo jin tayi shiru