Showing 45001 words to 48000 words out of 512766 words
Chapter 16 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1560
shiga Motar lokacin Haisam ya shige ya fara kokarin fidda ta dama gate d'in a bud'e yake da suka shigo, bayan sun baro gidan Abbas EE ya nufa da suka isa yace mata yana zuwa ya fita tana ta kallon shi ta glass da yake wurin akwae haske sosae har ya shige after some minutes sai gashi ya fito hannunshi ruk'e da yar jakar kwali mai d'auke da hotunan abubuwan da ake saidawa a wurin ya bud'e Motar ya shiga ya aje jakar a gefe bayan ya rufe kopar yaja suka tafi, akai akai yake d'an kallonta ta juyar da kai dama tunda suka baro gidan Abbas a haka take, lokacin da suka k'araso kopar gidansu ya parker da k'yar ta kalleshi tay mashi godiya ya bita da ido kawae duk sai ta tsargu tana niyyar juyawa ta bud'e taji yace ga abu nan nata ne ta juyo saida ta kalle shi kafin ta kai hannu ta d'auka tay mashi godiya sam bata san miye a ciki ba zata fita yace mata tay ma Amadu magana yazo ya d'aukar mata kayan baya tace mashi a'a zata iya ya d'aga kai ta juya ta fita ta rufe kopar, bayan ta fiddo kayan ta wuce har saida yaga ta shiga gidan sannan yaja ya tafi, tana shiga d'akin gwaggo ta wuce tana zaune kan abun salla bata jima da gama sallar isha ba, da sallama Fatun ta shiga ta amsa mata a gefenta ta aje ledar kayan da kuma jakar gwaggon ta kalli kayan sai kuma ta kalleta a sanyaye tace mata Ya Haisam ne ya siya mata, bud'e baki gwaggo tay da tsananin mamaki tace "kuma dae wai shi baya gajiya da hidima ne don Allah" ta k'arasa idonta kan Fatuu ta d'an ta6e mata baki ta nufi kujera ta zauna, hannu gwaggo ta kai ta fara duba kayan tana yi tana girgiza kai har ta gama sannan ta bud'e ledar kwalin ta fiddo kwalin dake ciki wanda ke nuni da na waya ne gwaggo ta bishi da ido daga inda Fatuu take zaune ta saki baki tana karanta sunan wayar har saida cikinta ya d'an yamutsa ganin iPhone 15 wayar da take taji anata zancen ta fito a social media ba wannan ne abun mamakin ba irin kud'inta da taji ana fad'a nan ta fara shakkun anya kuwa haka kud'in nata suke, suna haka sai ga Amadu ya shigo da sallama yana dariya yace "nazo a bani rabo na don naga Amar....au Hajiya Fatuu ta shigo mana da k'atuwar leda" kallon shi Fatuu tay yace "tuba nike ai dae ban k'arasa cewa Amaryar ba" d'an ta6e baki kawae tay yana niyyar duk'awa gaban kayan idanun shi suka sauka akan kwalin wayar dake hannun gwaggo wani kalar waro ido yay with mouth agape a razane yace "Wannan fa ta gasken ce ko kuwa kwalin ne kawae" ya kai hannu gwaggo ta mik'a mashi a kidi'me yace "kai wllh itace da gaske ta waye??" da kai gwaggo ta nuna mashi Fatuu ba shiri yasa hannu ya rufe baki yana fad'in "kai kai kai..." ganin yadda duk ya rud'e yasa gwaggo cewa "halan mai kud'i ce, in ce tafi waccan da ya siya mata ko?" Wani d'an murmushin Al'ajabi yay yace "mai kud'ad'e ce zaki ce gwaggo ba kud'i ba, iPhone 15 pro ce fa wayar data fito kwanan nan aketa Magana kusan miliyan d'aya take wannan in ma bata fi ba" duka hannuwanta gwaggo tasa ta rufe baki ido waje kafin a tsananin razane tace "Kai Amadu!! yanzu wannan abun ke har miliyan d'aya! ka kuwa san nawa ne miliyan!!!" Rantse mata yay haka kud'in ta suke har yana cewa in bata yarda ba bari yay mata Googling d'inta yanzu ta gani girgiza kai gwaggo ta fara yi tana fad'in gaskiya bazai yuwu ba dole tay mashi Magana wannan ai almubazzaran ci ne Amadu dake kallonta da alamun mamaki yace "kaji gwaggo da wata Magana ina ruwanki, nasan dae ba rok'onshi tay ba yaji zai iya ne miye naki na shiga Maganar, kuma da kike Maganar Almubazzaran ci ne kin dae san shi ba mai hakan bane in aikin Alkhairi ne yana yi, ba don ma bai yin yawa ba da sai ace nashi Alkhairin har yayi yawa, kawae wadata ce in Allah yasa mutum nada ita sai yay abunda ya ga dama" zugudum gwaggo tay tana bin shi da ido kawae Amadun ya juya kan Fatuu yana fad'in lalle ita mai k'ashin Arzik'i ce bin shi da ido kawae Fatuu tay jikinta duk ya mutu ita tsoron ma wayar take ganin yanayin ta yasa Amadu cewa ya yaga kaman bata farinciki kaman zatayi kuka tace mashi ita dae wllh tsoron wayar take gashi yanzu anata sare mutane wasu ma kashe su ake kan waya Amadun yace in sha Allahu ba abunda zai sameta tunda tana Addu'a da kuma Azkhar amman dae ta rink'a kiyayewa kar tay ta nuna ma Mutane a yanzu ta d'an rink'a amfani da tsohuwar tata kafin tay yawa ta d'aga mashi kai kawae yace zai koya mata yadda zata yi amfani da ita don yasan 13 sosae kuma ance bambancin su kad'an ne da wannan, sai zuba yake yana taya Fatuu murna gwaggo dae ta zuba mashi ido kawae da alama takaici ya hana ta Magana, daga baya Amadu ya tashi ya fita sukae zugudum kowa ya kasa cewa komae can gwaggo ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tace ta kwashe kayan ta kai d'akinta, bayan ta koma d'akin zaune tay a gefen gado ta zuba ma kwalin wayar ido kamar mai tsoron ta6a shi can dai ta kai hannu ta d'auka ta bud'e ta zuba ma wayar ido kirjinta na ta fad'uwa ta d'an d'auki lokaci a hakan kafin da k'yar ta mik'e don yin salla, bayan ta gama ta d'an ci Abinci sannan taje tayo wanka ta zo ta shirya cikin kayan bacci ta haye gado ta shiga duniyar tunani, ita dae tasan Haisam na mata abubuwan Alkhairi sosae amman wannan ya matuk'ar d'aure mata kai taya za'ai ace hakanan ya siya mata irin wannan wayar gaba d'aya ta rasa tunanin ma da zatayi da k'yar bacci ya kwashe ta...........
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2041*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
........Sai dae ko kafin ya kai har ta kulle kopar, knocking ya fara yi yana kiran sunanta shiru har bayan wani lokaci tak'i ta bud'e hakan yasa ya koma cikin parlon ya zauna had'i da had'e hannuwan shi ya d'aura beard d'in shi, shi dama initially hakanan zuwa binciken lafiyar bai kwanta mashi ba kawai don ta matsa ne yasanta sarai da k'wallafa rai akan abu in bai goya mata baya ba haka za tay ta damuwa yanzu kuma ga wata damuwar data fi wancan, tunanin yadda akai tana da wannan problem d'in amman ko ita bata gane ba a matsayin ta na likita ya shiga yi daga baya kuma ya tuna in Allah yaso ya 6oye Al'amari dama ba lalle a gane ba yana ta zaune can ya mik'e ya koma kan 3 seater ya d'auki wayar shi ya fara kokarin kiran Hajiya tana fara ringing ta d'auka suka gaisa ta tambayi ya Fanan jin ya d'an yi shiru dama ta ji yanayin voice d'in shi kaman yana cikin damuwa, tambayar shi tayi lafiya taji kaman yana cikin damuwa saida ya d'an nisa sannan cikin natsuwa ya fara mata bayanin komae to itama dae Hajiyar ta girgiza da jin bayanin matsalar tabbas itama haka tay ta fama da lalurar yawan 6ari wani lokacin sai cikin yayi kaman zai tsaya sai kuma ya zube ko kuma bayan ta haife ya koma saidae kuma tayi mamakin jin Fanan nada irin matsalar ba tare da an ta6a fuskantar wata babbar alama ba, cikin tashin hankali ta tambaye shi tana ina yace mata tayi locking kanta acikin d'akin tace bari ta kira wayar ta ya sanar da ita wayan na nan parlor, cike da damuwa tace dole ta shiga mawuyacin hali ba kamar yadda take da son ta haihu, ce mashi tay ya samu ya lalla6a ta ta bud'e kar wani abun ya sameta ba kamar da yake rarraunar zuciya gareta ya rarrasheta sosae itama zata kira suyi Magana ya amsa mata da Ok, mik'ewa yay walking slowly ya sake komawa bakin kopar yana knocking had'i da kiran sunanta shiru bata bud'e ba hakan yasa shi fara tunanin kar wani abu ya sameta nan take ya yanke zuwa yasa azo a 6alle kopan yana shirin juyawa yaji tana bud'e wa da sauri ya dakata ya kai idon shi jikin kopar yasa hannu ya tura, a tsaye ya ganta har saida gabanshi ya fad'i ganin yadda cikin kankanin lokaci duk ta yamutse ga hancinta duk alamun jini da alama nose bleeding tay dama yasan tana hakan tun tana k'arama in ranta ya 6aci ko ta buge sai tayi ha6o, hannunta ya kama suka koma cikin d'akin ya zaunar da ita gefen gado shima ya zauna idon shi a Kanta sai faman ajiyar zuciya take saukewa still yana ruk'e da hannunta guda slowly ya furta "Fanan" kaman bazata amsa ba sai kuma a hankali tace "Na'am" cigaba yay "Why all dis? Do you want to harm your self?" Shiru tay bata ce komae ba ya cigaba "I know how u'r feeling but kiyi hakuri muyi Addu'a Allah ya yaye matsalan yakamata ba damuwa ba tunda is curable kowane lokaci zaki iya samun lafiya" a hankali ta d'ago da rinannun idanunta ta kalle shi cikin disasshiyar murya tace "Babe ina tsoron ace bazan haihu ba bansan ya zaman mu zai kasance ba" ta k'arasa kwalla na zubo mata ya kai hannu ya jawo ta jikin shi yay mata side hug ya d'aura ha6ar shi a saman gashin ta gently yace "In sha Allah zaki haihu and nothing will change tsakanin mu ko kin haihu ko baki haihu ba ina son wife ena itama tana sona hakan ya wadatar dani" lumshe ido tay koba komae taji dad'in Maganar shi kuma tasan har cikin ranshi gaskiya ya fad'a mata shiru tay tana cigaba da shak'ar daddadan k'amshin da jikinshi ke fitarwa tana jin wata irin natsuwa na shigar ta, Allah ne shaida tana matuk'ar son Haisam tana jin tamkar da son shi aka halicce ta tabbas tasan rasashi babbar barazana ce ga rayuwarta tana wannan tunanin wata zuciyar ta ayyana mata wani abu da yasa gabanta fad'uwa ba shiri ta d'ago da kanta ta kalle shi shima ita yake kallo ganin kaman tana son yin Magana yasa ya tambayeta akwae wani abu ta d'aga mashi kai alamar eh yace ta fad'a mashi miye d'an jimm tay kafin tace "pls Ya Haisam I want a Favour from you" jinjina mata kai yay alamar to k'ara yin shiru tay tama rasa ta ina zata fara ya lura da ta kasa fad'i mashi Alfarmar da take son yay matan ya kai hannuwan shi ya kama duka hannuwanta yace kar ta ji komai ta fad'a mashi zai yi iyakar kokarin shi yay mata abunda take so in dai zai sakata farin ciki kuma ta daina damuwa haka, jin wannan batun nashi yasa ta samu k'warin gwuiwa ta fara magana cikin d'an rawar murya tace "I.... i want u to promise me dat you'll not marry another wife" bin ta kawai yay da ido bai ta6a zaton abunda zata fad'i ba kenan don bai ga dalilin da zata fad'i hakan ba, kaman ta san tunanin da yake ta had'iya abu kafin tace "ina nufin koda ban haihu ba don Allah ya Haisam kai man Alk'awarin bazaka k'ara aure ba tunda akwae hanyoyin da zamu iya samun yara zamu iya adopting ma in muna so" still kallon ta kawai yake hakanan ya kasa ce mata komai ganin kallon da yake Matan yasa taci gaba "isn't dat am trying to be selfish kawai ban son rasa ka ne babe in ya kasance ban haihu ba ka auro wata ta zo ta haihu zata rink'a man gori tana kirana juya k'arshe ma ta raba ni da kai hakan ya sha faruwa wllh and I can't survive without u" ta k'arasa kwalla na shararo mata taci gaba da tabbatar mashi da hakan zai faru in dae ya k'ara aure rayuwarta na cikin had'ari ya taimaketa su ci gaba da zaman su tare, gaba d'aya ya rasa mi zai ce mata bawai bazai iya yi mata alk'awarin bane amman yasan ta dama can tana da kishi ko ba don wannan matsalar ba tana yawan rok'on shi kan kada yay mata kishiya don bazata iya sharing nashi da wata ba da dai sauran maganganu, ganin yak'i yace komae yasa ta k'ara sautin kukan ta tana fad'in ya taimaketa yay mata alk'awari hakan ne kawae zai sa ta samu natsuwa a cikin zuciyarta da yanzu take mata rad'ad'i sauke ajiyar zuciya yay ya d'an yi jimm kafin calmly yace mata shikenan yayi mata alk'awarin hakan tun kan ya rufe baki ta fad'a jikin shi ta wani k'ank'ame shi tanata mashi godiya had'i da d'agowa tana yi mashi kiss a dukkan side d'in fuskar shi d'an murmushi kawai yay can yace ta tashi tay wanka zata fi jin dad'in jikinta tace to suyi tare mana yace mata zai d'an yi wani abu yanzu taje tayi yana zuwa ya fara kokarin mik'ewa yana ruk'e da hannunta ya d'agata saida ya kaita har cikin toilet d'in sannan ya fito, Bedroom d'in shi ya nufa yana shiga bayan ya rufe kopar ya nufi bakin gadon shi ya zauna, had'e dukkan hannuwan shi yay ya d'aura ha6arshi hakanan yake jin kaman bai yi daidai ba da yace yayi mata alk'awarin to amman yasan in har ba yayi mata yadda take son ba bazata ta6a natsuwa tabar damuwa ba ya d'an d'auki lokaci a haka yanata sak'e sak'e kafin can ya mik'e da k'yar don duk jin jikin shi yake ba dad'i ya nufi toilet, sosae taji dad'in jikinta da ta fito daga wankan duk da da sauran damuwa da kuma fargaba a cikin ranta na ko zata warke ta haihu ko bazata warke ba press ta nufa ta ciro wata yar riga iya gwuiwa tasa ta nufi gaban dressing mirror iya turare da roll on kawae ta sa ko mai bata shafa ba ta nufi Parlor don ta d'aukko wayarta, bayan ta dawo a bakin gadon ta zauna ta kira Momynta gaisawa suka fara yi tace ya taji muryarta ta canza bata lafiya ne aikuwa kaman tana jira ta saka mata kuka nan fa Hajiya Maryam ta rud'e ta hau tambayarta abunda ya faru cikin kuka ta shiga fad'i mata komae sosae itama ta girgiza ta hau yin salati harda ce mata ta tabbatar an yi aune aunen daidai kuwa tace mata eh kwararran likita ne suka gani sosae ta shiga damuwa amman Saboda kada ta k'ara tada ma Fanan d'in hankali sai ta hau rarrashinta tana nuna mata kada ta damu in sha Allahu zata samu lafiya tunda ana warkewa tambayar ta tay mi Haisam d'in yace da yaji zancen matsalar tace hakuri yake ta bata yana rarrashinta sam bai damu ba yama yi mata Alk'awarin koda bata haihu ba bazai k'ara aure ba zasu cigaba da zama a haka sosae Hajiya Maryam taji dad'i tace mata in sha Allahu ma zata haihu bama d'a guda ba yanzun dae ta tabbatar ta kwantar da hankalinta tunda Haisam d'in ma bai damu ba dama shine abun ji daga baya ta tambaye ta ta fad'a ma Daddy d'in su ne tace a'a Hajiya maryam d'in tace to ta bari yanzu zata kira ta sanar mashi tasan zai kirata tace to ta tambayeta su Farha da sauran yan'uwanta daga baya sukae sallama tana niyyar aje wayar kan gadon sai ga kiran Hajiya ya shigo bayan tay picking suka gaisa ta hau jajanta lamarin kafin ta shiga kwantar mata da hankali sosae tana mata nasiha daga baya sukai sallama ta aje wayar ta kwanta tana facing ceiling ba tunanin kowa take ba face Haisam ita tasan ta gama yin dacen miji ba k'aramar baiwa Allah yay mata da samun shi ba slowly ta lumshe ido wani irin son shi na ratsa zuciyarta tana haka wayarta ta sake yin ringing ta kai hannu ta d'aukko sunan Dad d'in ta ne ya bayyana kan screen d'in da sauri ta yunk'ura ta tashi zaune, bayan tay picking ta gaishe dashi shima dai rarrashin ta ya shiga yi yana kwantar mata da hankali yace kada ta damu za'ai iya bakin k'ok'ari ay treating problem din yana nan zuwa ma sosae taji dad'i harda su murmushi bayan sun gama wayar ne ta tuna da basu ci lunch ba gashi har yamma tayi sosae da sauri ta mik'e ta fita daga d'akin ta nufi Bedroom d'in Haisam tana shiga ta iske shi saman gado a kwance jikin shi sanye da jallabiya don yana fitowa ita kawae ya zura ya kwanta da alama dae wani abun na damun shi ko kuwa alk'awarin da ya daukan ne Allah masani, tana isa bakin gadon ta zauna ta kwantar da kanta a saman chest d'in shi can ta d'ago suka had'a ido ganin yanayin shi yasa da sauri ta tambaye shi mike damun shi ne slowly yace mata ba komae ya gaji ne tace tasan harda yunwa yay hak'uri bata bashi Abinci ba har yamma yayi sosai ya taso suje table ta mik'e tana kokarin d'aga shi ta hanyar kama hannun shi, baida yadda zai yi dole ya tashin ya zuro da k'afafun shi amman yafi buk'atar kwanciyar ya ji shi shiru, a daren ranar sosae Fanan ta faranta mashi duk da damuwar da take ciki da alama tukuicin Alk'awari ne aka bashi, Allah dai yasa a wanye lpy.
A daidai kopar gidansu Keke Napep d'in ta tsaya Fatuu ta fito