Showing 507001 words to 510000 words out of 512766 words

Chapter 170 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1558

kafin ya sake cewa likita ma yace maganin daya bata zai sa ta daina yin aman ta rinƙa cin abinci sosae in ma baiyi mata ba akwae wanda Zarah tayi amfani dashi a Us yana da kyau sosae sai yasa akawo mata cikin nuna jin daɗi tace to daga baya tayi masu sallama kamar kar ta baro Fanan ɗin don gani take kaman cikin zai iya samun matsala haka dai ta taho Fatuu da Haisam suka yo mata rakiya ta tafi, bayan sun koma ciki gaba ɗayansu a bedroom ɗin Fanan suka zauna tana kwance su Esha sun zagaye ta, hira suka shiga yi cike da farinciki daga baya Fatuu ta tambayi ko tana son wani abu ta haɗa mata da sauri ta girgiza mata kai tace ai bata daɗe data ci abinci ba a Villa Fatun tace to bari ta kawo mata fruit ba tare data jira cewarta ba ta saukko daga gadon ta nufi ƙopa, bayan fitarta bin juna sukai da kallo ita da Haisam suna sakar ma juna ƙayaaccen murmushi, saida Fanan ɗin tayi bacci sannan Fatuu ta koma ɗakinta lokacin ta kira Gwaggo ta sanar mata samun cikin ai tana ji ta shiga yin hamdala cikin tsananin farinciki ta tambayi ina Fanan ɗin ta tayata murna da sannu da jiki tace tayi bacci Gwaggon tace to in Allah ya kaimu zata kira, bayan ta gama wayar da Gwaggo Aunty Mareeya da Feenah ta kira suma ta sanar masu kowa yayi farincikin jin zancen samun cikin suna ta addu'oin Allah ya inganta, daren ranar gaba ɗaya Fatuu da Haisam saida suka yi nafila tsakar dare suka gode ma Allah tare da Addu'ar Allah ya inganta masu cikin ya sauketa lafiya. Kulawa sosae suke ba Fanan ɗin ba laifi kuma maganin da take amfani dashi yana mata aiki don tana cin abinci, bayan hutun Fatuu ya ƙare tace ma Haisam ko yayi ma Mom magana a turo Iya ta dawo nan gidan tunda ita dattijuwa ce zata taimaka ma Fanan ɗin sosae yace Ok, koda akai ma Mom magana cewa tayi lafiya lou sai ta dawo nan ɗin, ana washe gari Fatuu zata tafi Iya ɗin ta dawo nan gidan hakan ya ƙara kwantar ma da Fatuu hankali da tana ta zullumin tafiya ta barta duk da suna da masu aiki har biyu amman tafi son ace akwae wani babba na jiki a tare da ita hakanne ma yasa tayi tunanin a maido Iya ɗin nan.

Kwance tashi cikin Fanan ɗin har ya fito kuma bata wani laulayi sosae don har ta koma aiki, lokacin da cikin ya kai wata takwas ne aka tabbatar da in aka bari ta haihu da kanta zata iya samun matsala don haka aka yanke yi mata Cs in ya kai wata tara, Hajiya Maryam na jin haka tace zata fitar da ita waje kawai ta haihu a can amman Fanan ɗin taƙi amincewa tace ko taje can duk abu ɗaya ne don anyi mata bayanin matsalar da ake hasashe ta kuma gamsu da hakan don saida aka yi mata duk binciken daya dace kafin a tabbatar kuma likitan da yayi mata binciken ƙwararre ne kuma shima da a ƙasar wajen yake aiki wato likitansu mai aiki Germany dole Hajiya Maryam ta ƙyale ta, bayan cikin ya shiga wata na tara kafin zuwa ranar da za'ayi su Fatuu duk cikin zullumi suke duk da Fanan ɗin lafiyarta lou, ana gobe za'ayi aikin ranar ta kama lahadi amman Fatuu bata iya ta koma Zaria ba, gaba ɗaya duk sun shiga damuwa suna ta Addu'oi a ranar kusan raba dare Fatuu da Haisam sukai suna nafilfilin roƙon Allah yasa ayi aikin lafiya itama Fanan ɗin ta yi ma kanta Addu'oin, har su twins Fatuu ta tada sukai Nafila suma sukai mata Addu'a, Washe gari Monday su Esha ƙin zuwa Makaranta sukai saboda aikin da za'ayi ma Mommynsu, misalin ƙarfe goma na safe aka shiga da ita aikin Fatuu harda ƙwallarta haka su Esha sauran yan'uwa ma duk suna a asibitin anata fatan nasara, Hajiya Maryam dai har bata iya magana saboda fargaba sai Addu'o'i take a cikin ranta, bayan an shiga da ita a Office ɗin Doctor ɗin wanda yake mai girma ne akwae kuma kujeru suka zazzauna kowa yayi jigum, bayan kamar minti arba'in da biyar da shiga aikin Doctor Taj wanda shine likitansu na Germany kuma shine yayi aikin ya shigo cikin office ɗin ai suna ganinshi duk suka mimmiƙe kusan gaba ɗaya suka haɗa baki wurin tambayarshi yadda ake ciki yana murmushi yace anyi aikin cikin nasara an fiddo mata da Baby Boy, zo kaga murna Haisam da Fatuu da Hajiya Maryam a tare suka duƙa sukai sujjada su Esha na ganin sun yi suma duk suka yi haka ma Farha da Jidderh, tura baki Esha tayi bayan ta gama yin sujjadar tace miyasa Momy ta haiho Baby Boy ita Baby Girl take so ta samu ƙanwa duk akai dariya akace tayi haƙuri in zata ƙara haihuwa in sha Allah zata haiho mata Baby Girl ɗin, Aunty ce ta kawo masu Babyn wanda ina gani na furta Ma sha Allah saboda tsananin kyaun shi sak Haisam ya biyo hakan yasa yay kama da yan biyun Fatuu sosae, sam bakunansu sun kasa rufuwa sai faman kar6a kar6ar Babyn ake, a ɗaki na musamman dake Amenity aka kwantar da Fanan din duk yan uwa sun cika shi itama Fanan ɗin idonta biyu tana amsa ya jiki da barkar da ake mata fuskarta ɗauke da murmushi, zuwa yamma duk yan'uwan da abokan arzuƙi anata zuwa dubata sai yaba Babyn ake, wuraren ƙarfe biyar Dad ɗinsu Haisam yazo tare da muƙarrabanshi suka dubata tare da yi ma Baby addu'a, kwananta biyu a Asibitin kafin aka sallameta suka koma gida, a ranar da suka koma da daddare lokacin su Esha sunyi bacci Fatuu ma ta koma part ɗinta sai Fanan ɗin tare da Iya babyn kuma na kwance cikin net yana bacci Haisam ya shigo jikinshi sanye da jallabiya, bayan sun gaisa da Iya ta miƙe don ta basu wuri, murmushi suka shiga sakar ma juna ya tambayi ya jikinta tace da sauki sosae ya jinjina kai kafin yace Allah ya ƙara mata lafiya ta amsa da Amin tay mashi godiya, juyawa yay yana kallon babyn ta cikin net ganin haka tace ko ta fiddo mashi shi ya girgiza mata kai alamar a'a, kallonta yay ya tambayi wane suna take son a saka mashi ne tace ai tayi zaton ma ya riga ya saka mashi suna ya ɗan girgiza mata kai kafin yace ya bari a sallameta sai ta za6ar mashi sunan da take so, shiru ta ɗanyi tana murmushi can tace mashi sunanshi take son a saka mashi wato Haisam, ɗan buɗa ido yay yana murmushi yace yayi tunanin zata saka mashi sunan Dad ɗinta ne tay shiru kafin tace "nafi son a saka mashi sunan ka Babe" ɗage mata gira yay ya tambayi saboda mi,

"Saboda ni a wurina sunan yafi kowane suna muhimmaci kuma shine sunan da ya cancanta a saka mashi, kayi man abubuwan alkhairi da yawa Babe, ka aure ni don ka faranta man sannan ka zauna dani tsawon lokaci ba tare dana haihu ba kuma daidai da rana ɗaya baka ta6a nuna man damuwarka ba ko kayi man wulaƙanci kaine ma kake ƙarfafa man gwuiwa kan hakan, kuma nasan ba don Allah ya ƙaddaro aure tsakaninka da Zarah ba na tabbatar zaka iya rayuwa dani a haka ba tare da ka ƙara aure ba kawai don farinciki na, kai na daban ne Babe, I know I can never repay you for everything you have done for me, amman ina son ka sani Babe ina son ka da kowanne bugun zuciyana sannan ina mai godiya a gareka mara iyaka Allah ya bar mu tare har abada, ina roƙon Allah ubangiji ya ƙara inganta rayuwar ka Babe ya dawwamar da kai a cikin farinciki ya saka maka da gidan aljanna maɗaukakiya..." ƙwallan da suka tarun mata a idanu ne suka fara zubowa tasa hannu tana gogewa, matsawa yay gabanta da yake a kishingiɗe take saboda aikin da aka mata ya kai hannu yana goge mata ƙwallan cikin cool voice ɗinshi yace mata ya isa haka shima yana matuƙar alfahari da ita sannan yana farinciki da Allah ya bata lafiya har ta haihu yayi Addu'ar Allah ya raya masu shi da sauran yaransu ta amsa da Amin ya Rabbi.

Saboda aikin da aka mata yasa aka ɗaga yin taron suna sai bayan sati biyu ita Fanan ɗin ma cewa tayi a bar taron ba sai anyi ba amman kowa ya nuna yana so, gaba ɗaya satin Fatuu bata samu komawa Zaria ba tana gida sunata zaman jego sai ranar lahadi ta tafi, hidima ba yar kaɗan ba Hajiya Maryam tayi ma jaririn don shima saida tayi mashi dozin ɗin akwatunan kaya sannan tayi ma Fanan kayan fitar suna ciki harda wata danƙareriyar sarƙar zinari ta miliyoyin kuɗi hatta Haisam da Fatuu ma saida tayi masu kayan fitar suna haka su twins ma tayi masu kayan fitar sunan sannan kowannen su ta siya mashi abunda yace yana so a Asibiti hatta Abie ta siyo mashi robobin ba yaro ruwa masu tsananin kyau yan ƙasar waje da zasu kai goma sannan Fatuu ma tasa an kawo mata Motar data bata itama mai jegon ta canza mata tsadaddiyar Mota, kowa yaji daɗin abunda tayi duk da haka kuma Haisam ma saida yayi masu kayan fitar sunan shima, waɗannan kayan fitar sunan dai ban tunanin za'a iya saka su gaba ɗaya ranar sunan don sunyi masu yawa, Ranar Alhamis Fatuu ta dawo nan suka shiga hidiman sunan da za'a yi ran Asabar a maimakon ranar litinin saboda ranar ta kama ta aiki duk mutane suna zuwa wurin aiki, Washe gari Juma'a su Gwaggo suka iso da Haulat da Husnah harda Aunty Mareeya da Feenah sosae Fanan da Fatuu suka ji daɗin zuwan nasu, a daren ranar sunan aka kira Haisam a waya cewa saƙon shanu daga Yola ya iso wanda Baffan Fatuu ne ya aiko mashi dashi a yanka ma yaro, har Fatuu bata san da aiken ba saida Haisam ya kirata a waya ya sanar mata aiko taji daɗin hakan da yayi sosae, Alhamdulillah Allah ya kawo mu ranar suna hidima ta kankama ba kama hannun yaro, a ranar da safe sai ga su Yadikko da Yaya da Mairo sun iso harda dawon furarsu mai uban yawa da kuma Nono sai zuma da ƙwai masu yawan gaske, zo kaga murna wurin su Aysha da Mino anga Mahaifiya, bayan sallar azahar gida ya fara cika da yan suna mai jego da Fatuu da kuma yaransu suna ta cin uban gayu, zuwa sallar la'asar taro yayi taro malam hidima data amsa hidiman manyan masu kuɗi ake har bansan ma ta yadda zan bayyana yadda hidiman ke wakana ba don abun na neman fin ƙarfin al'ƙalamina kawai sai na koma yar kallo, ina cikin kallon manyan Hajiyoyin Abuja dake ta zuwa kwatsam sai ga Hajiya Kubra wato Momy ta iso a Motarta harda iyalanta suma sun zo suna, ina hangota cikin Washe baki na nufeta muka gaisa nace ashe zata zo sunan cikin fara'ar ta tace man ai ita tana yin Fanan sosae dama tana cikin wanda suka damu da halin rashin haihuwarta lokacin data ji labarin haihuwar sosae tayi farinciki ta kuma yi godiya ga Allah dama ance shi maharƙuci tabbas mawadaci ne nace wannan gaskiya ne Momy Allah ya ƙara mana haƙuri da kuma dangana ta amsa da Amin kafin suka shiga ciki ni kuma naci gaba da baza idanu ina ganin danƙara ɗanƙaran, jibga jibgan Motoci masu numfashi dake ta sawo kai cikin harabar yayin da wasu kuma ke tafiya, a taƙaice dai Abuja ce ta haɗu a gidan Haisam don First lady na nan da sauran matan muƙarraban shugaban ƙasa. Alhamdulillah taro ya tashi lafiya yaro yaci sunan Haisam suna ce mashi Junior, an ci an sha anyi wadaƙa da nishaɗi sannan an raba kayan suna masu ɗauke da sunan Baby kawai ba'a saka hoton shi ba, a bangaren maijego Fanan ta samu kayan suna kai kace zata buɗe ƙaton shago ne ita kanta saida tayi mamakin kayan da aka tara mata, a daren ranar su Fatuu da Farha harda Aunty Mareeya suka shirya kayan kafin su kwanta, Washe gari Lahadi yan Katsina da Yola suka koma duk an cikasu da abubuwan arzuƙi, haka sauran yan'uwan su Haisam yan Katsina da Daura da suka sauka a Villa duk suma sun tafi, Fatuu ma taso tafiya Zaria a ranar saidai da sauran abubuwan da zatayi a gidan dole ta bari sai gobe da sassafe sai ta koma, kusan raba kayan da Fanan ta samu nata tayi taba Fatuu duk yadda taso taƙi kar6a Fanan ɗin ta kafe, har rage kayan tayi ta maida mata wasu amman taƙi kar6a ƙarshe ma sai ta nuna mata 6acin ranta sosae hakan yasa dole ta amsa tayi mata godiya da kuma Addu'oi.

*BAYAN SHEKARU BIYAR*

Abubuwa da yawa sun faru a cikin waɗannan shekarun daga ciki abu na farko daya faru shine saukar President Ali Adamu daga kujerar mulki tuni kuma wata sabuwar gwamnatin ta hau, a lokacin daya sauka al'umma sunyi kukan rashin jajirtacce kuma nagartaccen shugaban ƙasa, bayan saukar shi Katsina suka koma da zama a gidansu dake G.r.a a lokacin tsohuwa mai ran ƙarfe wato Hajiyar sanata ta koma gidanta da zama saidai bana dundun dundun bane zo kaga murna a wurin yan unguwa karma Tk yaji, Saude da har zata dawo Hajiyar ta hana tace ai ba daɗewa zatayi ba tunda ga matar tukur nan lafiya lou tayi zamanta a ɗakin mijinta, shekara guda sukai a Katsina kafin suka koma Abuja.

Bayan saukar shi da shekara ɗaya Fatuu kuma ta gama karatunta cikin nasara har ta fara aiki bayan shekaru biyu da fara yin aikin nata ne ta ƙara haihuwar yan biyu duk mata an saka masu Khadija da kuma Fateema wato sunan Gwaggo da kuma Mom ɗin su Haisam, Esha tayi murna kamar kamar me da samun ƙanne mata, a lokacin wasu sun ƙara haihu wasu kuma nada ciki, a cikin wanda suka ƙara haihuwa harda Jidderh da kuma Fauzy ta ƙara haihuwar Namiji an saka mashi sunan mahaifin Sameer wato Bello, Aysha ma ƙanwar Mino a lokacin tayi haihuwarta ta farko ta haiho Baby girl an saka mata sunan Yadikko wato Jameela, Mino dai har lokacin bata ƙara haihuwa ba don tace ba yanzu ba bata manta kwakwar data ci ba ansamu dai ta amince zata ƙara yaronta yanzu shekararshi shidda, Farha ma ta ƙara haiho Namiji an saka mashi sunan Mahaifinsu wato Muhammad, Haulat ma ta ƙara haihuwar Namiji an saka mashi sunan mahaifinta wato ishaq, a bangaren Fanan kuwa ita bata ƙara samun cikin ba tun bayan Haisam Junior wanda yanzu shekararshi biyar da yan watanni, duk a cikin lokacin akai ma wasu aure ciki harda Yasmeen ƙanwarsu Haisam ta auri yaron Yayan Mahaifiyarta na Qatar mai suna Abdurrahman suna zaune a can ƙasar haka ƙanin Sameer wato Ashraf shi kuma ya auri Jahad itama ɗiyar yayansu ɗin na Qatar suna a Abuja zaune burin su Mom ya cika na son haɗa yaransu auren zumunci.

A bangaren Haisam kuwa tuni Kamfaninshi ya ƙara ha6aka sosae yanzu ana ƙera wasu abubuwan ba iya kwamfutoci ba yanzu harda su Tv da kuma wayoyi, a lokacin arzuƙin shi ya ƙaru sosae don har ya ƙara buɗe wasu rassa na Kamfaninshi a Lagos, PortHarcourt, Kano da kuma Sokoto yana da kuma burin ƙara buɗewa a wasu States ɗin in Allah ya yarda, a yanzu Haisam ya zama Billionaire wanda yana ɗaya daga cikin Manyan masu kuɗin ƙasa don har private jet ya mallaka wato jirgin kanshi wanda ake hidimar iyalinshi da kuma Kamfanoninshi, daga baya aka fara yin hayar jirgin ganin akwae riba yasa Haisam ɗin yayi ma Dad dinshi Magana kan su haɗa su sayi wani jirgin na haya ya amince da hakan koda Sameer yaji zancen siyan jirgin hayar shima sai ya nuna yana ra'ayin saka hannun jari haka Hajiya Maryam ma dama duk suna da hannayen jari a Kamfanin shi na Technology, daga baya suka buɗe kamfanin sufurin jirage mai suna HaiFat Air wanda a yanzu suke da jirage guda ukku biyu manya wanda har yan Hajji ake kaiwa dasu sai ɗaya ƙarami wato private jet suma jiragen suna niyyar ƙara wasu da yardar Allah, A cikin shekaru biyar ɗin nan a duk shekara Haisam sai ya kai wasu a cikin dangi Makka, a shekarar farko daya fara kai mutane makka ne yace ma Fatuu ta bada mutum biyu cikin danginta ta bada sunan Gwaggo da kuma Kawu Amadu su Gwaggo za'a sake sauke farali sosae tayi farinciki, Hajiya na jin zancen tafiyar Amadu Hajji itama ta biya ma Tukur wato Tk Har Haisam yace ta bari shekara mai zuwa zai biya mashi tace ai shida Amadu kamar yan biyu suke bai ga ko aure tare sukai ba ya bari ta biya mashi ai duk ɗaya ne, da wata shekara ta zagayo ya sake cewa ta bada mutum biyu sai ta bada Yaya da kuma kishiyarta Mairo sannan ita kuma da kuɗinta ta biya ma Aminiyarta Haulat, da rabon dai Fatuu ita zata kai Yaya Makka a lokacin ƙurucyarta ta ta6a ce ma Haisam in ta girma tayi kuɗi zata kai kowa Makka amman banda Yaya saboda ta tsaneta har yayi mata Nasiha kan muhimmancin yafiya, Sosae su Mero sukai farincikin biya masu Makka saidai ita Yaya akwae abunda ke damunta a cikin rai shine hakkin Mahaifiyar Baffan su Fatuu dake a kanta don tun Maganar da Mero ta ta6a yi mata a Abuja kan hakan bata manta ba, ƙarshe samun Mairo tayi ɗakinta cike da damuwa tace mata ita tana tsoron taje tayi aikin Hajjin Allah yaƙi kar6a saboda hakkin A'isha dake kanta, shawara Mairo ta bata kan taje ta samu Baffansu Fatuu ta roƙe shi yafiya ta roƙeta kan ta rakata, tare suka iske Mahaifinsu Fatuu a bangarenshi wanda yanzu ya koma babban falo da Bedroom da suka sha kayan alatu

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login