Showing 423001 words to 426000 words out of 512766 words

Chapter 142 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1565

da Mino ta shirya suka tafi gidan gwaggo don anjima zasu tafi siyayyar kayan ɗakin Mino kamar yadda suka tsara jiya da gwaggon da har tace ta bari sai gobe lokacin ta ƙara huta gajiya Fatun tace a'a gara su tafi ayi komai a gama don bikin nata matsowa, bayan sallar azahar Aunty mareeya ta iso dama ita suke jira ruƙe da babban kwali Kawu Amadu da Kamalu sun kamo mata suka shigo, a falo suka zauna aka shiga gaisawa ta ƙara yi ma Fatuu sannu da zuwa dama jiya tayi mata a waya, sai gashi ita lafiya lou su twins sun yarda da ita ta ɗauke su harda Abie su gwaggo sukai ta mamaki Aunty Mareeyar na dariya tace ai ita dama da wuya yara suyi mata ƙyuya Mino tace kuma dama itama fara ce ƙilan shiyasa suka yarda da ita da mamaki Aunty mareeya ta waro ido tace tsoron baƙaƙe suke ne aka ce mata eh aikuwa ta ƙyalƙyace da dariya tace bata ga laifin su ba wake son baƙi duk akai dariya, bayan an gama gaishe gaishen Gwaggo tasa Mino ta zubo mata abinci da sauri ta dakatar da ita tace wllh a ƙoshe take don daga kan abinci ta taso Fatuu tace to ai dai ko lemu tasha tace to a bata, bayan ta gama sha ne ta buɗe jakar ta ta fiddo kuɗi bandir biyar, miƙewa tay ta matsa daga gefen gwaggo ta aje bayan ta dawo ta zauna tace gashi nan gudunmawarta ce ita da Fauzy ga kuma wasu kayan Kitchen nan a haɗa ayi mata amfani dasu, gaba ɗayan su waro ido sukai suna kallonta da tsananin mamaki gwaggo ta kama baki kafin tace "Ƴata wannan gudunmawa haka ai tayi yawa gaskiya" tana dariya tace a'a ba wani yawan da tayi in so samu ne ma ai tafi haka tunda duk hidimarsu ce, Fatuu na niyyar yin magana Aunty Mareeyar ta dakatar da ita harda zare mata ido duk ta basu dariya, godiya sosae Gwaggo ta shiga yi mata tana addu'ar Allah ya bar zumunci haka Fatuu ma, tambayar yanayin yadda za'a siya kayan ɗakin Aunty Mareeya tayi Fatuu ta faɗi mata kowanne set biyu tace hakan yayi amman fa za'a sha kuɗi gaskiya don kaya yanzu sai Addu'a ko dai a siya set ɗin kujeru ɗaya masu kyau sai ayi gado biyu gwaggo tace ita da cewa tayi ma a yi kowanne seti ɗaya Auntyn tace a'a ayi dai gadon biyu sai kujeru ɗaya sai sauran kayan Kitchen da electronics suma nan ba ƙaramin kuɗi za'a kashe ba ga kuma labulaye, tambayar Fatuu tayi tasan yanayin gidan da za'a kaita ne don asan yawan labulayen da za'a siya tace a'a gaskiya Aunty tace yakamata kuma a sani ko akwae wanda zata iya tambaya, shiru ta ɗan yi kafin tace gashi Jidderh bata nan itace zata iya tambaya lafiya lau Aunty Mareeya tace ko ta kira Laila sai ta nuna mata labulaye ne ake son yi ai ba wani abu bane tace to, bayan ta kira Laila ɗin sun gaisa tayi ma Fatun an zo lafiya ta amsa itama tayi mata ya shirye shiryen hidima Laila tace Alhamdulillah Fatuu tay fatan Allah ya nuna masu ta amsa da Amin, tambayarta tay kamar yadda Aunty Mareeya tace Laila ta bata amsa da gidan bene ne ta fasalta mata yadda tsarin gidan yake Fatuu tayi mata godiya har zasu yi sallama Laila ta dakatar da ita tace amman fa saman benen Nameer yasa mashi kaya kar suce zasu yi kaya harda nan kuma duka gidan ma an sa labulayen ƙasa da sama sai dai kawai in zasu ƙara mata ne Fatun na murmushin jin daɗi tace to tare da yin godiya, bayan sun gama yin wayar tayi ma su Gwaggo bayani gaba ɗaya suka washe bakin farinciki Aunty Mareeya tace yauwa sunga kujeru set ɗayan sun isa tace a bata takarda da biro suyi list ɗin abubuwan da za'a siyo yadda da sun je ba tare da 6ata lokaci ba su fara yin siyayyar Fatuu ta ƙwala ma Mino kira tace ta taho da paper da biro, tare suka shiga faɗin abubuwan da za'a siya tana rubutawa, bayan ta gama suka miƙe don tafiya dama Motar Fatuu na a ƙofar gida, su ukku suka fito Aunty Mareeya na ruƙe da Adam Fatuu kuma Abie aka bar Mino a gidan, bayan sun fito ne cike da farinciki gwaggo ta sanar ma Kawu Amadu gudunmawar su Aunty Mareeya shima sosae yaji daɗi yana ta faffaɗan murmushi ya shiga yi mata godiya tana faɗin haba ba komai ai an zama ɗaya. Lokacin da suka isa wurin siyayyar babban bene ne hawa ukku gaba ɗaya manyan show rooms ne a ciki shaƙe da ƙawatattun furniture da rantsattsun kayan adon gida na gani na faɗa, cikin haba haba mai wurin wadda babbar Hajiya ce da yaranta suka tarbe su tana ta washe masu baki harda yunƙurin ɗaukar su twins suka ƙi yarda, bayan sun gama gaisawa suka yi mata bayanin kaya suke so tace gasu nan sun zo gidan kaya masu kyau da Quality ta shiga nuna masu suna jinjina kai da yabawa don ba ƙarya akwae kaya a wurin Aunty Mareeya tace ai tasan suna da kaya masu kyau shiyasa tayo masu jagora Hajiyar ta shiga yi mata godiya, ba 6ata lokaci suka shiga za6a ba tare da wani yin ruwan ido ba don kowane kaya haɗaɗaɗun kan su ne, kamar yadda suka tsara gado biyu suka za6a sai set ɗin kujeru da labulaye harda Carpet da wasu kayan ƙawata falo da ɗaki harda kitchen da kuma wasu kayan Kitchen amman banda electronics don Fatuu tace su bari suje EE inda Haisam ke zuwa gym su siya acan don suna da sauƙin kaya, kaya masu sunan kaya suka zazza6a saidai an kashe kuɗi ba kaɗan ba, bayan sun gama siyayyar suka ce ma matar ba yanzu zasu tafi dasu ba in ba matsala a cikin satin nan da za'a shiga za'a zo a ɗauka da sauri tace lafiya lou ba damuwa da ta basu receipts shikenan za'a ware masu kayan yanzu, bayan sun biya ta basu shaidar siyayyar harda ba Aunty Mareeya tukuici tana dariyar jin daɗi tayi mata godiya itama tayi masu godiyar harda cewa tana fatan suma zasu kawo mata customers suka ce in sha Allah tunda ta duba masu, bayan sun bar nan wurin siyan electronics suka wuce nan ma suka siya kayan kallo da fridge, Electric cooker harda injin wanki da sauran su, saida suka siya komai da suke buƙata sai abunda ya rage wanda sai sunje kasuwa zasu siya harda kayan gara dana abincin da za'a ci da biki, a gida suka sauke Aunty Mareeya suna ta mata godiya tana faɗin haba ba komai ta tambayi lokacin da zasu je Kasuwar Gwaggo tace ita ta fidda lokacin da take da halin zuwa, a daren ranar bayan isha Kawu Amadu ya shigo bayan ya dawo daga Masallaci nan suka shiga tattaunawa kan gyaran da za'a ma gidan Fatuu tace da da hali ma da sababbin furniture aka saka gwaggo tace a'a a gyara su kawai hidiman da yawa don ma an samu gudunmawa sosae an gode ma Allah suma kuma sunyi ƙokari ita da Kawu Amadu haka suma iyayen su Baffa da Yadikko tace ba ƙaramin ƙokari sukai ba sun bada kuɗi da yawa, suna murmushi itama gwaggon suka yaba mata tayi murmushi tare da fatan Allah ya nuna masu bikin lafiya duk suka amsa.

Washe gari da safe gwaggo taje wurin Hajiya tayi mata magana game da ɗaukar kayan ɗaki tace to zata kira can Abuja tayi masu magana harda cewa tana fatan badai su takura kan su ba wurin yin kayan gwaggo na murmushi tace eh. A cikin satin suka je Kasuwa ƙarasa yin siyayyar harda wasu zinarai Fatuu ta tafi dasu tasa Aunty Mareeya ta rakata inda ake saida su ciki harda wanda aka siya mata da kuɗin da Haisam ya ta6a bata da zai yi aure lokacin da kuma zasu yi aure gwaggo ta canzo mata shi da kuɗin daya bata sai gashi sosae yayi daraja harda yan'kunnan da wata ƙawar Mom ta bata da bikin su suma ta saida gaba ɗaya kuɗin taba Gwaggo tace a haɗa ayi gara dasu tace mata don me zata saida abunta duk kuɗin data bada basu isa ba tana murmushi tace to ai ƙarin zasu yi amfani kuma dama amfanin ajiye abun kuɗin kenan Aunty Mareeya na murmushi tace naka sai naka duk suka yi murmushi gwaggo tace hakane Aunty mareeyar ta ƙara faɗin "Allah ka bar mu da yan'uwanmu ka ƙara mana ƙaunar juna da abunda zamu taimaki juna" duk suka amsa da Amin. A kwana a tashi abu nata matsowa ranar Alhamis da daddare Hajiya ta kira Fatuu ta sanar mata gobe Juma'a za'a ɗauki kayan Mino sannan jibi su Aunty zasu kawo lefenta gwaggo tace to Allah ya kaimu, washe garin wurin ƙarfe sha ɗaya na safe Motar ɗaukar kayan ta iso gwaggo ta kira Aunty Mareeya tace to su haɗu can wurin da za'a ɗauki kayan, a Motar Fatuu suka tafi harda Kawu Amadu da Tk Motar kayan tabi bayan su, bayan sun je ba 6ata lokaci aka fara fiddo kayan ana shiryawa a cikin Motar wanda zasu iya fashewa aka ware su bada su za'a tafi ba aka kai ƙaton kwalin su Motar Fatuu, bayan sun gama da nan wurin ɗaukar electronics aka wuce suma aka ɗaukko su gaba ɗaya Motar ta ɗauke kayan da yake babbace sosae, Aunty mareeya ce ta tambayi gwaggo baza'a bi su ba Saboda shirya kayan in anje tace ita sam bata ma yi tunanin hakan ba, kiran Hajiya gwaggon tayi bayan ta ɗaga sun gaisa ta sanar mata an gama shirya kayan za'a sa wani ya bisu ne saboda shirya kayan Hajiyar ta bata amsa da ba dole bane masu kai kayan na gida ne in sunje zasu shigar dasu ciki shiryawar kuma ko in an kai amaryar sai ayi wannan tace to tare da yi mata godiya, daga nan su Kawu Amadu Keke Napep suka hau suka koma gida su kuma suka wuce kasuwa don yin siyayyar kayan abincin da za'a tarbi su Aunty masu kawo lefe daga can wurin Chef Ƙawar su Aunty mareeya za'a kai su ita zata yi abincin.

Washe gari Asabar anata shirye shiryen tarbar lefe, sai bayan Azahar suka iso da yake tafiyar Mota ce, a gidan Hajiya suka fara sauka su biyu suka zo Aunty da babbar Ƙawar Mom sai wata yar'uwar Senator da ta zo daga Daura ta jira su anan gidan Hajiya, saida suka huta bayan la'asar suka fito don zuwa kai lefen harda Hajiya dama ba'a fiddo akwatunan daga cikin Jeep ɗin da suka zo da ita ba, Mota biyu suka yi su Aunty driver daya kawo su ya jasu sai su Hajiya Tk ya jasu suka nufi gidan, gidan har anyi sabon fenti yay kyau lokacin da suka isa su Aunty mareeya da Feenah da inna zaliha sai ƙawar gwaggo da innar su Haulat ne suka tarbe su, falo aka nufa dasu bayan anzazzauna cikin sakin fuska aka gaggaisa dasu tare da yi masu an zo lafiya, su Tk da Kawu Amadu ne suka fara shigowa da akwatunan har suka gama set ukku ne masu guda biyar gaba ɗaya akwatunan guda goma sha biyar ne kowane set da kalar su sun haɗu sosae, Aunty mareeya ce da Feenah suka shiga duɗewa ba abunda kake ji daga bakunan mutanen wurin sai Ma sha Allah Gwaggo sai sakin murmushin farinciki take haka ma Fatuu don an zuba kaya ba ƙarya itama an ɗinka mata wasu da yawa ga uban ƙananun kaya da gani Nameer ɗin na son su haka su Aunty Mareeya suka faɗa, kaya dai sai son barka itama harda zinarai da sarƙar diamond mai kyaun gaske, sai faman yabawa ake Hajiya ta kalli Tk da Kawu Amadu dake tsaye suma suna kallo tace "ku baku da ma niyyar yin auren balle akai naku lefen" dariya sukai Tk yana ɗan sosa ƙeya yace "ai ni harda ma lefen ke ƙara man tsoron auren wllh, A.A ne ya yakamata yay niyya ya fiddo mata kwanan nan don nasan lefe ba matsala bace a wurin shi don ya daɗe yana tara kuɗin shago" duk akai yar dariya shima Amadun faffaɗan murmushi yay yace ai ba ƙananun kuɗi ke haɗa lefe ba balle kuma irin wannan shi in son samu ne ma a yafe mashi lefen yay Maganar idon shi akan Haulat, a hankali ta juyo zata saci kallon shi karaf suka haɗa ido da sauri ta janye ta koma kallon kayan Aunty Mareeya tace aikuwa ko ance an yafe dole sai ya fiddo tarin shagon da yake yi yayi shi don bazai ɗauki tsawon lokaci yana amshe ma yan unguwa kuɗi ba sannan yaƙi yin lefen yana dariya yace ai gini zai yi da wanda ya tara tace ya kawo Matar nan cikin gidan tunda ga ɗaki nan za'a bari in Mino ta tafi Auntynsu Haisam na dariya tace dole dai sai yayi lefen kenan itama Aunty Mareeyar dariyar take yi tace eh, bayan an gama ganin kayan aka yi addu'o'i kafin aka fara shigo masu da Abubuwan da aka shirya masu na ci farko cewa sukai a ƙoshe suke sun ci abinci a gidan Hajiya Gwaggo ta marairaice tana roƙon su ci Aunty mareeya ma tace yakamata na nan ma su ci tunda don su aka yi, ƙarshe dai yanke bin su akai dashi Mota tunda sun ƙi su ci aka ce in sunje gidan Hajiya sai su ci, anata masu godiya Gwaggo ta tambayi amman dai ba yau zasu koma ba ko taga yamma tayi Aunty tace eh sai gobe da safe in Allah ya kaimu, da daddare Nameer ya kira Mino aka shiga yin hira irinta masoya masu muradin juna anan tayi mashi godiyar lefe yace miye abun godiya don yayi abunda yake hakkin shi ne tana murmushi tace duk da haka dai yana murmushi yace mata in akwae abunda take so wanda babu a ciki karta ji komai tayi mashi magana zai siya ya aje mata da sauri tace babu komai yayi, tambayar ta yay taga english wears dake ciki tace mashi eh yace to su yake son ta rinƙa sakawa shiyasa ma ya siyo su daga US da ɗan alamun kunya tace to, daga yadda ta bashi amsa ya gane taji kunya yace mata yana bata shawara duk ta bar wannan kunyar a gida kafin tazo in ba haka ba shi zai cire mata ita har saida ta ɗan runtse ido kafin tace to, kafin suyi sallama ya tambayi ba wani event da zasu yi ne anan tace eh tunda za'a yi Dinner da Walima anan yace amman yakamata tayi ko don Friends ɗinta tace to bari zata yi ma Adda Fatuu magana kan hakan yace Ok in sun fidda abunda zasu yi sai ta faɗi mashi tace to, bayan sun gama wayar ta iske Fatuu a ɗakin gwaggo suna tattaunawa ganin hakan yasa ta juyo da niyyar ta fito Fatun ta kirata ta komo ciki, bayan ta zauna Fatun na murmushi tace "Amaryar mu ya akai ne" Gwaggo ma kallonta take tana murmushi, faɗi mata yadda sukai da Nameer tayi ta ɗan yi shiru kafin tace to ko tayi ko Friend's Eve ne tunda tana da yan ƙawaye anan kuma tunda ba kusa za'a kaita ba ba zuwa zasuyi ba balle ayi Dinner ɗin dasu Minon tace to bari sai ta faɗa mashi zata yi shi gwaggo tace amman kada ta bari ya turo mata kuɗi masu yawa don hidimar da yawa Fatuu tace eh ko a part ɗinta ma sai suyi abun su ba sai ance a kama wuri ba Mino tace to,

"Su Mino Amaryar Nameer, na lura dai ba ƙaramin ji dake angon nan yake ba sai faman nan nan da ke yake" Fatuu ta faɗa tana dariya Minon ta rufe fuska da sauri gwaggo dake dariya itama tace to ba dole yaji da ita ba,
"Wllh gwaggo baki ji daɗin da nike ji ba da zata aureshi don shima Nameer ba daga baya ba na tabbatar zai kula da ita sosae" kai gwaggo ta jinjina kafin tace ai abun farincikine irin mazajen da suka samu tayi Addu'ar Allah ƙara masu fahimtar juna ya zaunar dasu lafiya yasa mutu ka raba Fatuu ce ta amsa da Amin,

"Yanzu ke ya za'ai da karatun ki gashi ko Ssce ba kiyi ba" Fatuu ta tambaya idonta akan Mino, shiru ta ɗan yi tana murmushi kafin tace Nameer ɗin yace zata yi jarabawar bayan an yi, tambayarta Fatuu tayi bayan an yi mi tayi shiru tana bin ta da ido ta ƙara ce mata bayan an yi wai me zata yi jarabawar, shiru tayi tana kikkafta idanu gwaggo dai murmushi kawai take don ta fahimci mi Fatun ke so ta faɗa, ganin ta kafe sai ta faɗi mata bayan an yi mi zata yi jarabawar yasa ta tura baki tana yamutsa baki tace "Wayyo Adda Fatuu ba kin gane ba" girgiza mata kai tayi alamar bata gane ba tay shiru can ta saci kallon gwaggo ganin haka yasa Gwaggon ta juyar da fuskarta, juyawa tay ta kalli Fatuu data kafeta da ido ƙasa ƙasa da murya ta furta "Auren" tana faɗin haka ta tashi da gudu ta bar ɗakin duk suka saka dariya gwaggo tace ina ruwan Mino sarkin kunya.

Washe gari da safe su Aunty suka tafi a ranar da daddare Haisam da Fanan suka iso, Washe gari Litinin Jidderh ta iso daga Dubai a ranar da yamma Haisam ya taho Katsina don gaba ɗaya a ƙagare yake da ganin Baby Fatuu ɗin sa, ko gaya mata zai zo bai yi ba saidai ta gan shi yazo sosae taji daɗi amman duk da haka saida tayi mashi shagwabar miyasa bai faɗi mata zai zo nan ba yace yana son yi mata surprise ne su twins ma sun yi murnar ganin Daddyn su, a daren ranar sun nuna yadda sukai kewar juna sosae, Washe

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login