Showing 309001 words to 312000 words out of 512766 words

Chapter 104 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1589

dak'ile tace Allah ya tashe su lafiya ya juya ya tafi, d'an murmushi tay ta girgiza kai bayan ya fita ta kai hannu ta kama trolley d'in ta nufi Bedroom, lokacin data shiga Fatun na zaune a bakin gado suna had'a ido da sauri ta janye nata ta koma kallon k'asa, cikin d'akin ta nufo tazo bangaren da Fatun take zaune ta aje trolley d'in a wurin sauran akwatunan, juyowa tay ta kalleta ta tambayi taci Abinci a hankali tace mata eh bayan Magrib taci, "to yanzu kina jin yunwa" girgiza mata kai tay alamar a'a tace to ta kwanta, idasa hayewa gadon tay ta kwanta tay lamo duk tayi kalar rashin gaskiya, wucewa Hajiya tay ta nufi hanyar fita, jin fitar ta yasa Fatun d'ago kai ta kalli k'opar sai kuma ta saka dariya, wayarta ce ta fara ringing da sauri ta kai hannu ta d'agota taga Haisam ne ke kiran, picking tay tana kara wayar a kunne ta saka mashi dariya shima ita yake yi sai kuma a shagwabe tace mashi yaga abunda take ta gudu kenan yace kar ta damu ai ba wani abu bane kawae Hajiyar ce ta d'auke shi a wani abu, tambayar ta yay mi take yi tace mashi gata nan ansa ta kwanta yadda tay Maganar har saida ta bashi dariya itama ita take ta yi,

"Ina Hajiyan?" Ya tambaya, tace mashi ta fita k'ilan tana parlor ya furta Ok bari ya k'yaleta ta huta kar su k'ara wani laifin, har zai mata saida safe sai kuma ya tambayi akwae abunda take so tace mashi eh cike da kulawa yace Ok minene tace "Kai" maimaita abunda tace d'in ya yi tace "Eh Hubby, kai nike so" tana jin sautin murmushin shi yace mata ai shi ta riga ta same shi, cike da tsokana tace "to baby yace so yake ya kwana a part d'in Dad d'in shi sai kazo ka d'auke shi ko ka d'auke ta" yana dariya yace saidae yazo ya d'auki Maman Baby wanda daidai yake da tada yak'i tsakanin shi da Hajiya, labarin buga mashi sanda da tace zatai ya bata Fatun nata dariya, sai da Safe sukai ma juna cike nuna k'auna da kuma kewar juna,

Bayan su Mom sun dawo tana shiga Bedroom d'inta taga ba Fatuu bata kawo komai a ranta ba tay tunanin ko tana wurin Jidderh, bayan ta rage kayan jikinta a cikin Laundry room ta wuce toilet don yin wanka, tana cikin yin shafa Jidderh ta shigo zata fad'i mata abu nan ta tambayi Fatuu na d'akinta ne tace mata a'a ita rabon ta da ita tun kafin Magrib data shigo nan ta duba ta, bayan ta gama shiryawa cikin kayan bacci ganin har lokacin Fatun bata dawo ba yasa ta nufi k'opa, bayan ta fito daga part d'in nata part d'in Laila ta wuce tana shiga cikin parlon ta iske su zaune ita da Fanan duk suna sanye da k'ananun kaya suna kallo a Tv, maido kallon su sukai kanta jin sallamar ta suka amsa mata da murmushi, k'arasawa tay ciki ta zauna akan kujera Fanan ta gaishe da ita ta amsa Laila tace har sun dawo ta d'aga mata kai, tambayar ta tay Daughter na nan ne da alamun rashin fahimta ta tambayi wace daughter d'in tace mata Sis d'in Fanan d'an jimm tay don bata fahimci wadda take nufi ba, Fanan ce data gane tace mata Zarah take nufi, yar dariya tay tace ai cewa zatay matar big bro Mom d'in tayi d'an murmushi kawae, ce mata tay bata nan ai rabonta ma da nan part d'in tun kafin ayi D'inner, d'an jimm Mom tay duk idanunsu na akanta Laila ta tambayi Lafiya, fad'i mata tay tunda ta dawo bata iske ta a bedroom d'in ta ba kamar yarda ta barta tayi tunanin tana a wurin Jidderh kuma bata nan shine tazo nan, ce mata Laila tay to ba sai ta kirata taji ba Mom d'in tace ai bata da no d'in ta,

"To ko dai Big Bro ya fita da ita bari a kira shi a ji don nima banda no d'in nata amman zan amsa ko don irin haka" jinjina kai Mom tay tace bata tunanin Haisam zai yi haka tunda yasan halin da take ciki, Fanan ce tace bari ta kirata sai aji, bayan ta kira layin Fatun ya shiga ta d'auka tana fara'a suka gaisa tace mata tana ina ne nan ta sanar mata tana d'akin Hajiya tace Ok sukai sallama, fad'i ma Mom inda take tay tace to ta mik'e ta nufi hanyar fita Laila na zolayarta tana fad'in duk hankalinta ya tashi kar ace ta 6atar da Amarya tana murmushi ta fuce,

part d'in Hajiya ta nufa tana shiga parlon ta isketa zaune tana kallo, ciki ta shiga ta zauna kujerar gefen ta tana murmushi ta gaishe da ita itama fuska a sake ta amsa mata, shiru ta d'an yi can tace dama ta dawo ne daga unguwa da suka je bata iske Daughter ba tun d'azu shiru ashe tana nan, d'an ta6e baki Hajiya tay tace "eh tana nan ni naje na taho da ita nan kuma bazata koma ba" da sauri Mom ta kalleta da alamun mamaki ta tambayi Lafiya ba dai wata matsala ta faru ba,

"Ba abunda ya faru saidai matsalar ake k'ok'arin janyo mata a an k'i barinta ta huta kamar yadda likita ya bada doka" fuska a kwa6e ta k'arasa Maganar, har saida gaban Mom ya d'an fad'i a ranta ta shiga tunanin to mi take ma Fatuu da zata ce haka ita a iya saninta tana hutawa yadda yakamata amman gashi tace wai an k'i barinta ta huta , tana cikin zancen zucin ta ji Hajiyar taci gaba da fad'in "in banda jarabar tsiya k'iri k'iri fa yasan halin da yarinyar nan take ciki amman yaje ya bi ya kaddadabe ta shiyasa na maido ta nan ai sai in ga ta yadda zai rink'a zuwa wurin nata balle har ya takura mata" har saida Mom ta d'an ji sanyi don ta fahimci wanda yay laifin, d'an murmushi tay ta bata hak'uri Hajiyar tace Uhm kawai, mik'ewa Mom tay tayi mata saida safe cikin sakin fuska Hajiyar ta amsa mata ta tafi,

Misalin k'arfe goma da yan mintuna Senator ya shigo part d'in har lokacin Hajiyar na zaune a parlor tana kallo, amsa mashi sallamar da yayi tay idon ta a kanshi ya k'araso cikin parlon, zama yayi akan kujera gefen tata cike da girmamawa ya d'an sunkuyar da kai ya gaishe da ita tana murmushi ta amsa tay mashi an dawo yace eh, Ledar hannun shi ya mik'a mata yace ga furar ta, amsa tayi tay mashi godiya da sa Albarka ya amsa har zai yi magana ta riga shi fad'in da yayi ta wahalar siyo mata Furar kullum mi zai hana ya rink'a siyo ta kwana biyu tunda ga fridge nan sai ta saka, yana yar dariya yace mata ai ba abun wahala bane yafi son tana shan fresh ba wadda ta kwana ba kuma ai ba shi yake siyowa ba kawai dai shi yana shigowa da ita ne, jinjina kai tay alamar gamsuwa sai kuma ya k'ara cewa shi d'in ma zai iya zuwa ya rink'a siyo mata ai tunda neman Albarka yake, dariyar jin dad'i tay tace mashi wannan kullum cikin samunta suke koda ba furar saidae kuma don samun lada tunda tana jin dad'inta yana murmushi ya jinjina mata kai, d'ayar ledar ya d'ago yace ga ta Daughter nan yaje part d'in Mom ya kai mata aka ce ta dawo nan Hajiyar ta ce eh neman hanata ake ta bi dokar likita shiyasa ta maido ta nan, jinjina kai yay yana murmushi don Mom ta fad'i mashi komai, mik'ewa yay yace bari ya d'aukko mata cup tasha ko ta bi jiki tace mashi to ai taga ma kamar bata lalata ciki, d'an fridge d'in cikin parlon ya nufa ya bud'e bayan ya d'aukko cup d'in ya dawo wurinta da kanshi ya ciro robar furar ya zuba mata, bayan ta fara sha ya d'auki d'ayar ledar yace bari ya kaima Daughter d'in Hajiyar tace Allah yasa ma bata yi bacci ba saida tace mata in zatai kallo ta fito tace a'a kwanciya zatai, Bedroom d'in ya nufa saida yay sallama sau biyu sannan k'asa k'asa ya jiyo Muryarta tana amsawa, shiga yay Fatuu data d'ago kai tana ganin shi da sauri ta tashi zaune dama a kishingid'e take suna chat da Haisam da kuma Fauzy, cikin d'akin ya shigo ya tsaya daga gaban gadon da fara'a take kallon shi ta gaishe da shi, amsa mata yay ya tambayi ya yanayin jikin nata tace mashi lafiya lou ya jinjina kai, matsawa yay ya mik'a mata ledar yace to ga furar ta sai ta sha da sauri ta kawo duka hannuwanta ta amsa tay mashi godiya, saida safe yay mata ya juya ya tafi.

Wuraren k'arfe sha d'aya da rabi Fanan ta gama shiryawa cikin had'add'iyar rigar bacci lokacin Laila tayi bacci, gaban dressing mirror ta nufa ta kwance gashinta ta fara gyara shi, bayan ta gama ta hau yan shafe shafe da feshe feshen turarurruka, press ta nufa bayan ta bud'e ta fiddo after dress cikin kayanta data jera, d'aura ta tay a saman rigar baccin tata da iyakar ta gwuiwa ta yafa veil d'in asaman kanta daga haka ta nufi hanyar k'opa, saida ta saka flat shoe dake a bakin k'opar sannan ta bud'e ta fuce, part d'in Haisam ta nufa bayan taje can ta cire rigar saman. Da Asuba bayan ya dawo daga Masallaci lokacin itama ta gama salla har ta koma ta kwanta, jikin shi sanye da farar jallabiya ya hau gadon idonta akan shi tana mashi murmushi ta gaishe da shi yay mata ta tashi lafiya ta amsa mashi, matsowa tay ta d'aura kan ta a saman chest din shi nan take mashi Maganar aikinta tace sunyi waya da Dad d'inta jiya yake tambayar yaushe zata koma don hutun data d'auka ya k'are har anyi mashi magana, shiru Haisam d'in yay kamar mai nazarin wani abu har saida ta d'aga kai ta kalle shi, ce mata yay nan da 2 weeks shima zai koma yana ganin in ba matsala ta bari sai su tafi tare tace Ok zata ma Dad d'in ta magana sai a k'ara mata hutun ya jinjina mata kai sai kuma ta k'ara mashi Maganar tafiyarta Lagos idon ta akan shi, d'age mata gira yay yace tana sauri ne tana murmushi tace a'a, ce mata yay ta bari ta k'ara ko 1 week tana murmushin jin dad'i tace to.

Sam Fatuu bata wani laulayin ciki ba kamar wanccan data samu ba wannan cikin bata wani ciwo kuma komai ci take gashi sosae cin Abincin ta ya k'aru, kawai wani lokacin in taji k'amshin da bai mata ba take jin zuciyar ta ta d'an tashi sai kuma in taci Abinci wani lokacin nan ma tana jin tashin zuciyar har ta d'an yi amai shima zata iya k'irga sau nawa tayi. Gaba d'aya Hajiya ta kasa ta tsare tun abun bai damun Fatuu har ta fara shiga damuwar hakan ba kamar data ga har lokacin Fanan na a gidan kuma dai tasan dole wani abu na shiga tsakanin ta da Haisam, Haisam d'in na yawan zuwa duba ta sai dae bata wani sakewa da shi koda yazo Hajiyar bata a cikin d'akin d'an bayan lokaci take shigowa tace yazo ya wuce ya bata wuri, kullum daga kwanciya sai kallo sai latsa waya ko main parlor bata cika zuwa ba Saboda a ranakun aiki yan gidan ma ba zama suka cika yi ba a parlon. Bayan sati d'aya ranar asabar Fanan ta tafi dama Hajiya Maryam nata k'orafin ta maido mata yarinya ta hanata zuwa School, bayan tafiyar Fanan su Laila da Nameer suma suka fara shirin tafiya, ranar laraba Laila ta tafi Malaysia Nameer kuma Haisam yace ya bari su tafi tare tunda a can yake karatun dama, gaba d'aya Fatuu ta k'ara shiga takura dama dasu Fanan d'in take yin hira wani lokacin ga damuwar tafiyar da Haisam zai yi ranar Sunday zaije Lagos daga can ran Monday zasu tafi, sosae Fatuu ta shiga damuwa don in tace bata buk'atar mijinta to tayi k'arya ba kamar in ta tuna zai tafi tare da Fanan sai zuciyarta tay ta raya mata zasu je can suyi ta shan soyayyar su,

Ranar Friday da yamma gaba d'aya Fatuu tunanin yadda zata je part d'in Haisam take tana haka dubara ta fad'o mata, tana sanye da riga da skirt na lace ta nufi cikin Bedroom lokacin Hajiya na zaune tun bayan data gama sallar la'asar take tasbih, daga gefenta d'an nesa da ita ta zauna akan carpet ta shiga yin wasa da yatsunta na k'afa, bata dad'e da zama ba taji Muryar Hajiyar tana tambayarta ya kai, shiru tay ta fara motsa baki da k'yar murya na d'an rawa tace mata dama tazo tambayar ta ne Ya Haisam ne yace taje ta had'a mashi kaya tay wuri wuri da ita ta k'arasa Maganar, bin ta da ido Hajiya tay ta shiga yan kame kame,

"Rabu dashi bazaki je ba, da da babu ke wake had'a mashi bashi ke had'a kayan shi ba, duk da abu ne mai kyau amman ai yasan halin da kike ciki ko" kallon ta Fatuu tay tana d'an kikkafta ido a hankali tace mata ai lafiyar ta lau bata jin komai, yar harararta Hajiyar tay "dama ai ba'a ce baki lafiya ba ko saidai gudun janyo ciwon ake" da sauri Fatun ta juyar da fuskar ta, d'an murmushi Hajiya tay tace mata taje taci gaba da kallonta bazata hau bene ba a halin da take ciki in dole sai ita yake so ta had'a mashi kayan tace ya kawo nan sai ta tayata su had'a mashi, jiki sukuku Fatuu ta mik'e ta nufi hanyar fita ta koma parlor, idanunta ne suka ciko da kwalla ta zauna tay shiru. Bayan sallar isha Haisam yazo dubata kaman ko yaushe lokacin tana a cikin Bedroom zaune a saman gado, ya lura da yanayin ta cike da kulawa ya tambayi mike damunta kawai sai ta saka mashi kuka tace ba shine zai tafi ba, rarrashinta ya shiga yi da k'yar ya samu tayi shiru daga baya ya tafi, bayan tafiyar shi cigaba da matse kwalla tay wani irin k'unci take ji acikin ranta, tunani ta shiga yi na ko in Hajiya tayi bacci ta tafi wurin shi don shi kan shi ta fahimci yana son hakan kawai ba yadda zai yi ne, to kuma in ta farka fa don tabbas Hajiyar na tashi da daddare wani lokacin toilet take zuwa kuma bata da nauyin bacci don sau da yawa in Fatun ta farka ko zata toilet data ji motsinta ita ke kunna lamp har ta tambaye ta lafiya, tasan muddin ta tafi da k'yar in bata farka ba taga bata a d'akin hakan kuma itama tasan zai ja masu matsala, sak'e sak'e ta ci gaba da yi bayan zuciyarta ta raya mata wanccan tunanin tana haka kawai sai wani abu yazo mata a rai lokaci guda ta hau jinjina kai alamar ta samu mafita, saida ta kai idonta kan k'opar shigowa tay d'an jimm kafin ta kai hannunta gefe da sauri ta d'auki wayarta ta shiga call log, layin Nameer ta shiga kira bugu biyu ya d'auka ya furta "Yayata ta kaina" bata ce komai ba kan hakan k'asa k'asa da murya tana yi tana kallon kopar ta tambayi yana ina, ce mata yay bai nan yana cikin gari ta tambayi yaushe zai dawo gida yace d'an anjima, jin tayi shiru yasa shi ce mata in da wani abu ta fad'i mashi ko tana son wani abu ne,

"Eh, don Allah akwae wani magani ne da nike son ka siyo man zan turo maka sunan shi saidae ni yanzu nike son shi gashi kuma kace sai d'an anjima zaka dawo" sai zare ido take tana kallon k'opa tay Maganar, da sauri yace mata ba matsala ai sai yazo ya kawo mata dama a kusa da inda yake akwae babban pharmacy, jin hakan har saida ta d'an yi murmushi tace to bari ta turo mashi, da sauri ta cire wayar daga kan kunnan ta hannunta har yar rawa yake ta fara k'ok'arin tura mashi sak'on sunan Maganin, bayan ta tura zuciyarta ta raya mata yanzu in ya kawo kuma Hajiya na zaune a parlor kuma ya bata fa gashi ansan ba kowanne magani take sha ba sannan tace mata na miye, wani irin bugu gabanta yay da sauri ta zuru da k'afafunta cikin sand'a ta nufi k'opar, a hankali ta d'an lek'a cikin parlon ta hango Hajiyar zaune da Aunty, wani irin waro ido Fatuu tay baki bud'e da sauri ta dawo cikin d'akin, can k'arshen gadon ta koma sosae hannuwanta ke rawa ta shiga sake kiran Nameer duk bugu d'aya tare yake da fad'uwar gabanta, har ta yanke bai d'auka ba a rud'e ta hau sake kiran nashi can k'asan mak'oshi take furta don Allah kayi picking Nameer, saida ta kusa yankewa sannan ya d'auka yace "Sorry Yayata ina cikin pharmacy d'in ne amman gashi nan na siyo yanzu zan kawo maki da sauri cikin rawar murya idanunta akan k'opa tsoronta kada Aunty d'in ta shigo dubata tace "N...namer..r ka gane, don Allah ban son asan da maganin kada ka bari kowa ya gani" d'an jimm yay sai kuma ya tambayeta amman to maganin miye, gabanta ne ya fad'i cikin yar in ina tace mashi maganin bacci ne saboda halin da take ciki bata samun isasshen bacci shine take so tasha ko tayi baccin amman in aka gani za'a iya hanata sha tunda ba kowanne magani take sha ba amman shi wannan baida wata illa zata iya sha, ce mata yay ta tabbatar dai bazai mata komai ba da sauri tace mashi eh wllh ai yasan dai bazata sha abun da zai mata illa ba yace Ok kada ta damu bazai

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login