Showing 459001 words to 462000 words out of 512766 words
Chapter 154 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1532
ciki lafiya lou kawai dae fatan ta ya ruƙe su amana kada tayi dana sanin yin auren bayan tsawon lokaci, yar dariya mai sauti yayi yace "Kada ki damu Amaryata, Hajjaju tasan zan ruƙe amanarki shiyasa tayi man maganar ki ni kuma ina ganin ki mashin son ki ya soke man zuciya ba shiri na faɗa tarko" Yadda yayi Maganar har saida tayi dariya don ta fahimci ɗan barkwanci ne sai ga Gwaggo an saki jiki ana shan Love😍
Bayan wata guda aka fara aikin gidan nasu gadan gadan lokacin har Baban su Umar ya samu gida an siya mashi sun tashi Tk ma an saka ranar aurenshi daidai dana Amadu wato rana ɗaya za'a ɗaura masu aure, 6angare guda aka ware masu suke zaune kafin aikin yazo inda suke. Cikin sa'a Kamalu ya rubuta Jamb ya samu point da ake buƙata don yin karatu a Jami'ar daya cike wato Umaru Musa Yar'adua University Katsina (Umyuk), bayan sun yi post Utme cikin sa'a ya samu Admission don fara karatu inda zai yi Degree akan Computer Science, a lokacin sosae suke waya da Farha sun shaƙu da juna ta kai har kuɗi ta turo mashi don ya canza waya saboda in suna yin Vedio call wani lokacin wayar shi na basu matsala, lokacin daya yi ma kawu Amadu magana kan ya rakashi su sayi wayar jin itace ta turo mashi kuɗin saida ya tambayeshi mike tsakaninsu wai dama yana lura da yawan wayar da suke, Kamalun bai 6oye mashi yadda sukai da ita ba na cewa da tayi tana son su zamo abokai, sosae kawu Amadu yayi mamakin jin hakan, bayan an siyo wayar ne suka je nuna ma Gwaggo itama dai tayi mamakin jin Farha ce ta turo mashi kuɗi ya siya saida ta tambayi yadda akai suka san juna ya faɗi mata, sam Gwaggo bata kawo komai ba a ranta tayi tunanin jinin su ne ya haɗu tayi mashi Allah ya sanya Alkhairi, lokacin daya fara karatu ita kuma ta gama Degree ɗinta a Jami'ar Lagos ta nemi da a turo ta Katsina bautar ƙasa da yake suna da hanya sai gashi an turo ta Katsinar har saida Hajiya tayi mamaki lokacin da Hajiya Maryam ta sanar da ita zancen zuwan Farhar wurinta ta zauna don yin service kuma ita ta za6i hakan, lokacin da za ta zo harda uban sababbin kayan sawa da takalma da jakuna irin wanda samari ke amfani dasu a Makaranta ta kawo ma Kamalu, ranar data zo ta kama Friday da rana tunda Tk ya ɗaukkota daga Airport tasha gayun ƙananun kaya ta tambayeshi Kamal yace bai san ko yana nan ba amman bari in sunje bakin shagonsu sai su duba, lokacin da suka iso Kawu Amadu ne kawai a ciki Tk ya tambayeshi Kamalu yace bai nan yana School Farhar harda gaishe da kawu Amadun ba laifi ya ɗan saki fuska ya amsa mata tare da yi mata sannu da zuwa, bayan ta amsa ne ta tambayi kaman zuwa ƙarfe nawa zai dawo yace mata sai anyi La'asar daga haka suka wuce, suna zuwa parlon Hajiya lokacin tana zaune Farhar ta nufeta da gudu taje ta rungumeta Hajiya ta nuna farincikin zuwan ta sosae Tk ya tambayi ina zai kai kayanta Hajiya tace ya kai su Visitor room, bayan sun gama gaisawa Hajiya tayi mata Maganar abinci tace mata bata jin yunwa sai anjima tace to taje ta huta ko, koda taje ɗakin wanda tuni an gyara mata shi ta kwanta a gado kasa yin baccin tayi don ba wanda take son gani irin Kamal ƙarshe sai ta ɗauki wayarta ta shiga lallatsawa, tana haka akayi la'asar ta miƙe ta nufi toilet tayo wanka, shiryawa tayi da atampa mai kyau anyi mata straight gown ta kamata sosae tayi ɗaurin kallabin Zarah Buhari a wurin Fanan taga tana yawan yin shi kuma yana mata kyau shine itama take yi kuma yana mata kyau sosae harda yar kwalliya tayi duk da ita bata cika son yin kwalliya a fuskarta ba kamar Fanan, tana cikin shiryawa Hajiya ta shigo cikin ɗakin da sallama ta juyo tana kallonta da murmushi Hajiyar tace "au ni nayi zaton ma kina nan kinata bacci naga anyi La'asar gashi baki ci komai ba nace bari in zo in tashe ki ashe ke kina nan kina ta rangaɗa kwalliya", still murmushin take yi bata ce komai ba,
"To wannan kwalliyar ta mecece daga zuwa kodai angon nawa anan yake shine zai zo yin sannu da zuwa?" dariya Farhar tayi tace mata No kawai tayi ne kuma tana son ta fita jikinta ya ɗan saki Hajiyar tace to ita ina ta sani da zata je, ɗan jimm tay kafin tace ko gidan su Zarah sai ta gaishe da Granny ɗinta, sosae Hajiya taji daɗin jin hakan don ya tabbatar mata da Farhar ta canza da gaske tace mata to tazo ta fara cin abinci kafin ta tafi suka nufi ƙopar fita harda kama Hajiyar tace wai bari ta taimaka mata taga bata yin tafiyar sosae Hajiya na dariya tace da wannan sandar tata sai tayi tafiyar da ita bata iya yi, lokacin da suka fito daga cikin corridor Saude na niyyar shiga Kitchen ganin su yasa ta dakata tana murmushi tana niyyar gaishe da Farha sai ji tayi ta rigata gaishe da ita Sauden ta amsa tare da yi mata anzo lafiya da tambayar yan'uwanta da Momynsu duk tace mata suna lafiya Hajiya ta tambayi Farhar a dining zata ci abincin tace a'a a kawo mata a parlor yadda tana ci suna hira Saude ta juya da sauri tana faɗin to bari ta kawo mata can suma suka nufo cikin parlon, a saman c-table aka shirya mata kayan abincin bayan tayi serving nata tace mata aci lafiya Farhar na ɗan murmushi tayi mata godiya, lokacin da Saude ta nufi hanyar Kitchen sosae take mamakin canzawar Farhar a ranta, ba wani sosae taci ba tace ta ƙoshi Hajiya dake yin kallo ta kalleta tace dama wannan ɗamammiyar rigar ai bazata bari taci wani abinci sosae ba basu son suna ɗinka wadatattun kaya suyi ta faman takura kai, murmushi kawai Farhar tayi itama ta maida idonta kan Tv tana kallon abunda Hajiya ke kallo can bayan wani ɗan lokaci ta miƙe ta nufi hanyar bedroom, bada daɗewa ba ta fito tana ruƙe da ƙatuwar leda mai tambarin Shopping Mall ɗin Mamanta, cikin parlon ta dawo daga bakin kujeru ta tsaya tace ma Hajiya zata je ta dawo ta ɗaga mata kai har zata juya tace mata to ina mayafi kuma ta kalleta tana ɗan yamutsa fuska tace takura mata yake gashi sai yayi ta faɗuwa saboda bata saba sakawa ba Hajiya tace mata amman bai kyautu kuma ai ta fita haka ba tana yar musulma kuma ma ba kyau fita hakan ai ta sani tunda tana zuwa islamiyya su kan su waɗannan kayan bai kamata tana saka su ba ta fita indai ba lullu6e jikinta zatayi ba komi mutum zai yi ya rinƙa tuna lahirar shi, ɗan murmushi tayi tace Ok zata gyara ta aje ledar ta juya don ta ɗaukko mayafi Hajiya ta bita da kallo tana murmushi sosae take jin daɗin yadda ta canza don inda da ne tayi mata Maganar shigar da tayi yamutsa fuska zatayi kuma bazata canza ba, gyale ta yafo daya shiga da atamfar saman kafaɗa duk da baida wani girma yadda ta yafan ya rufe mata bayanta bayan ta ɗauki ledar tayi ma Hajiya sai ta dawo, ko a bakin gate saida su Officer sukai Maganar canzawarta bayan ta gaishe su ta wuce, tana zuwa saitin shagon kallo ɗaya tayi ma na ciki ta gane Kamalun ne duk da ya juya baya yana sanye da riga da wando na light blue shadda, tsayawa tayi tana murmushi cikin zazzaƙar muryata tace a bata Sweet yace wane iri saida ta wurga idonta saitin ledojin Sweet ɗin taga wani ansa mango da sauri tace mashi shi yace Ok guda nawa tana yar dariya tace pack guda, ɗaukko jakar Sweet ɗin yayi yana juyowa idanunshi suka shiga cikin nata har saida yay alamun tsorata Farhar ta saka dariya, da tsananin mamaki yace da gaske itace tana murmushi ta ɗaga mashi gira tare da furta yes,
"Amman yaushe kika zo?" still da mamaki ya tambaya tace mashi ɗazun ai tazo nan ta tambaye shi Uncle nashi yace bai dawo ba bai faɗi mashi bane yace mata lokacin daya dawo daga School ɗin shi kuma ya tafi kasuwa to basu haɗu ba shiyasa bai san data zo ba,
"Amman ko fa yau da safe munyi waya baki faɗi man yau zaki zo ba" ɗan farfar tayi da ido tace "i want to give you a surprise" yana murmushi yace aikuwa gashi ta bashi shi har tsoro ma yaji daya ganta tana yar dariya tace ai ta gani, shiru sukai ta shiga jefa mashi wani kallo shi kuma yana ɗan murmushi can tace "Ka ƙara kyau" yar dariya yay duk dimples ɗinshi suka lotsa yace "ina wani kyau kullum ina zaryar School rana yana buguna" tace duk da haka ita taga ya ƙara kyau kodai saboda ya fara zuwa University yana haɗuwa da yan'mata shiyasa yake gyara masu kanshi, tayi Maganar tana mashi wani kallo yay yar dariya yace shida bai daɗe da fara zuwa ba kuma shi karatunshi ya saka a gaba ba ruwan shi da wasu yan'mata ta ɗan yamutsa fuska tace Allah yasa gaskiya yake faɗa mata, rantse mata yay kan shi ba ruwan shi da wasu yan'mata ta ɗan yi murmushi ta furta Better gara ya maida hankali yayi karatu ya bar duk wani shiriritar yin yan'mata ya furta mata in sha Allah,
"Ka bar ni a tsaye haka ake welcoming baƙo" ta faɗa ta ɗan tura baki da sauri ya bata haƙuri yace ko zata shigo cikin shagon ga kujera ta girgiza mashi kai tace ciki zai shigar da ita zata gaisa da Grandma ɗin shi yace to, fitowa yay ya kulle ƙopar shago ta zagayo wurin shi yanata mata murmushi ganinta da kaya yace ta kawo ya ruƙe ta sakar mashi hannu guda suka kama tare suka nufi cikin gidan, faran faran Gwaggo ta tarbeta cikin sakin fuska a falo suka zauna ta gaishe da Gwaggon tana murmushi ta amsa mata tare da yi mata anzo lafiya da tambayar yan gidansu tace mata duk suna nan lafiya Kamalu yace ma Gwaggo tazo yin bautar ƙasa ne nan cikin fara'a tayi mata fatan alkhairi da fatan Allah ya bada sa'a yasa a gama lafiya ta amsa da Amin, miƙewa Gwaggo tayi ta fita daga cikin falon lokacin Farhar tace mashi kayan shi ne a cikin ledar akwae ma saura a gida bata iya ɗaukkowa sai dai in zata koma sai su je tare ya daukko, da mamaki ya buɗe ledar ya shiga duba kayan kafin da tsananin mamaki ya ɗago ya kalleta yace ya zata yi wannan hidiman haka sosae ta yamutsa mashi fuska tare da yi mashi wani kallo tace What are Friends for abunta nashi ne so bata son yana yi mata irin haka kawai inta bashi abu ya amsa shikenan, yana murmushi yace to tayi haƙuri yayi mata godiya tare da faɗin Allah shima ya bashi ikon kyautata mata haka tace bata buƙata iya haka da ya saki jiki da ita ya wadatar, ruƙe da tray mai ɗauke da kayan abinci Gwaggo ta dawo ta daura akan table ta matsar dashi gaban Farhar tana niyyar buɗe Warmer ɗin Farhar tace wllh ta ƙoshi yanzu taci abinci Gwaggon tace ai abun marmari ne taci ko ba yawa tunda ita baƙuwar su ce, Waina ce da miya taji alaiyahu da nama sai ƙamshi take Gwaggo ta kalleta tana murmushi tace ta dai iya cin waina ko tay yar dariya tace eh ana masu shi, bada yawa tasa ta zuba mata ba ta nufi Fridge ta ɗaukko mata ruwa da lemu ta kawo mata, bayan ta koma ta zauna Kamalu ya taso da kayan ya dawo wurin Gwaggo ya nuna mata yace ita ta kawo mashi tace ma akwae saura zasu je ya ɗaukko, duba kayan gwaggo ta shiga yi kafin ta ɗago da mamaki ta kalli Farha dake cin waina a nutse tace harda hidima haka banda wadda akai ai da ta bassu kada ɗawainiyar tayi yawa idonta a ƙasa tana ɗan murmushi tace mata a'a ba komai, godiya Gwaggon tayi mata da Addu'ar Allah ya saka da alkhairi, bayan ta gama ci harda ɗaukar tray ɗin zata fitar da sauri Kamalu ya miƙe ya kar6a yaje ya kai Kitchen bayan ya dawo tashi Gwaggo tayi ta fita, tambayoyi ta shiga yi mashi kan karatun shi yana bata amsa suna haka aka shigo siyan abu sai lokacin ya tuna da ya baro shago a buɗe yace mata zai koma shago zata zauna anan tace a'a bari su fita tare, bayan sun fito Kamalun yayi ma Gwaggo magana ta leƙo sukai sallama sannan suka fito shi ya shiga cikin shagon ita kuma ta tsaya daga gaba tana kallon yadda yake sallamar yaron da yazo siyayyar tana ta murmushi, bayan ya sallami yaron ya tafi tace mashi gaskiya irin wannan business ɗin bai dace dashi ba kamata yay ace a Haɗaɗɗan Office yake A.c na hura shi har saida yayi dariyar da haƙoran shi suka fito yace shi ina zai samu irin wannan aikin abunda ma duka yanzu ya fara karatun yace ai gara ma wannan sana'ar a cikin shago yake kuma akwae fanka a garinsu kafin yazo nan rake yake saidawa akan table wani lokacin cikin rana ma ta ɗan buɗa ido alamar mamaki, ganin tana ta tsayuwa yace mata ko zata shigo tace a'a bari ta wuce yaushe zai zo amsar sauran kayan yace ko in anyi Magrib daga masallaci sai ya shigo tace ok tare da ce mashi Bye, tana niyyar tafiya ya tsaidata ya miƙo mata ledar Sweet ɗin ta ɗan girgiza mashi kai alamar a'a ya ɗan mariraice mata fuska yace please wannan ce kyauta ta farko daya ta6a mata duk da ba wata mai yawa bace ta amsa zai ji daɗi in kuma bata son irin shi sai ya canza mata wani, murmushi tayi tace ba kowane Sweet take sha bane yace ok ta faɗi mashi wadda take sha sai ya kira Uncle ɗinshi tunda yana kasuwa ya taho mata da ita tace No ba sai yayi haka ba tunda wannan ya bata zata sha ta miƙa mashi hannu ya bata tayi mashi godiya kafin ta ɗaga farin hannunta fatt tana mashi bye bye shima yayi mata ta tafi ya leƙo kai yana kallonta itama tana yi tana waiwayen shi tana mashi murmushi har saida ta kusa gida sannan ya maida kan shi, sai gab da Magrib Amadu ya dawo lokacin daya ga kayan da Farha ta kawo ma Kamalun shima ya jinjina abun har yana faɗin Allah yasa dai kar yazama wata matsala Gwaggo tace Amin, bayan sun gama sallar Magrib Kamalu yace mashi zai je ya amso sauran kayan kamar yadda yace mata Amadun ya tafi shi kuma ya wuce part ɗin Hajiya, a parlor ya iske Farhar tana kallo da yake ba salla take yi ba Hajiya kuma na bedroom ɗinta, sosae ta nuna jin daɗin zuwan nashi ya zauna nan suka shiga yin hira, har aka kira sallar isha suna zaune tace mashi yaje yayi salla in ya dawo sai ta ɗaukko mashi yace to, koda aka gama yin sallar ya dawo hirar suka cigaba da yi har Hajiya ta fito ta iske su suka gaisa dashi cikin fara'a ta tambayi ya karatunshi yana dai maida hankali ko yace mata sosae, ita kanta Hajiya saida ta ɗan yi mamakin ganin yadda suka saba da juna ƙarshe saida Farhar ta matsa mashi suka ci abinci tare bayan sun gama yace mata zai tafi harda ce mashi ai gobe ba School ko yace ya baro Uncle ɗin shi yana jiranshi ne sannan taje ta ɗaukko mashi tace ma Hajiya zata rakashi ta dawo tace to, tare suka kama ledar kayan suna tafe suna hira har suka iso bakin shagon yayi mata godiya ta gaishe da Amadu ya amsa mata ya ɗan saki fuska kafin tayi ma Kamalun saida safe ta tafi yana shiga cikin shagon Amadu ya wurga mashi harara tun ma kafin yayi magana yana murmushi ya bashi haƙuri yace itace ta ruƙe shi da hira, a ɗan fusace Amadun yace shi kuma da yake tsoronta yake ji da bazai ce mata zai tafi ba Kamalun nata ɗan murmushi ya ƙara bashi haƙuri yace bazai sake ba, Bayan Farha ta koma saida Hajiya ta tambayeta yadda akai tasan Kamalu har suka saba haka tace mata a Abuja wurin bikin Yaya Nameer suka san juna itama Hajiyar bata kawo komai ba a ranta tayi tunanin jininsu ne ya haɗu don shima Kamal ɗin kamar Fatuu yake yana da farin jini dama kuma yawanci Mutum mai kyau haka yake da shiga rai, bayan sun tashi daga shagon sun shiga gidane Kamalu ya haɗa duka kayan yace ma Amadun ya ɗauki wanda yake so da sauri yace mashi a'a yayi amfani da kayanshi, marairaice mashi yayi yana mashi magiya da ƙyar ya ɗauki wasu jeans da t-shirt yace sun isa ya gode duk da haka saida ya ƙara mashi da agogo da takalma, Washe gari Gwaggo ta kira Fatuu anan take sanar mata game da abubuwan da Farha ta kawo ma Kamalu sosae tayi mamaki tace banda kuɗin da akace ta turo mashi ya canza waya Gwaggon tace mata wllh kuwa kaya sosae ta kawo mashi Fatun tace ita gaskiya abubuwan da take mashi basu kwanta mata a rai ba tunda ansan halinta duk da ta canza kada daga baya abu yazo ya zama wata matsala ko tace zata yi mashi gori, Gwaggo na murmushi tace to ai dai ba roƙonta akayi ba ita taji ta gani duk da dai tana kyautata mata zaton da zuciya ɗaya take mashi Fatun tace to Allah yasa amma dai duk da haka a daina amsar mata kaya