Showing 291001 words to 294000 words out of 512766 words

Chapter 98 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1609

duba ta in dai ba wata matsala gwara a sallameta su koma gida don anata faman zaryar zuwa in suka koma sai taci gaba da yin bed rest d'in a gida tace to, tambayoyi tayi ma Fatun daga baya ta fita ta nufi Office d'in Doctor, bayan sun gaisa tay mashi bayanin suna so ai discharging Fatuu tunda ba wata matsala a tattare da ita, bai da yadda zai yi dole yayi masu yadda suke so don ya gane Auntyn likita ce. Bayan sallar Magrib aka sallame ta suka dawo gida, d'akin Mom aka kaita nan fa akai ta zuwa gaishe ta ita dai sai faman murmushi take bayan an tsagaita da shigowa Mom ta tambayeta abunda take son ci tana murmushi tace mata komai aka bata zata ci itama da murmushi akan fuskar ta tace in akwae wani abu da take jin tana so ta fad'i tace mata ba komae, mik'ewa tay ta fita bada jimawa ba sai gata ta dawo ruk'e da plate mai d'an girma Fruit ne aka yayyanko wanda suke da amfani ga mai ciki ta kai mata tace ta fara shan su tay mata godiya, ganin tana k'ok'arin saukkowa daga saman gadon yasa ta tambayi zatai wani abu ne tace eh hannu zata wanko cike da kulawa tace Ok amman tabi a hankali tace to, tsaye tay har saida ta shiga ta wanko hannun ta fito bayan ta koma ta zauna sannan ta tafi, bada jimawa sosae ba sai gata ta k'ara dawowa hannunta ruk'e da babban tray, a saman Carpet ta aje tace ma Fatun ta zo ta zauna nan yadda zata ji dad'i sai ta ci tace to, bayan ta zauna da kanta ta bud'e mata plates d'in da aka rufo da wasu, d'aya tuwon semovita ne mulmule ukku sai miyar Alaiyahu data ji yan ciki a cikin bowl sai d'ayan plate d'in mai d'an zurfi farfesun kaza ne sai zabga uban k'amshi yake a ido kawai sai ya burge mutum daga gefe lemu da ruwa ne harda cup, tana murmushi tace mata ta ci ta k'oshi ta d'aga mata kai ta juya ta nufi hanyar fita daga d'akin,

tun bata saki jiki ba har dai ta saki ta shiga kwasar Abincin wasa wasa sai gashi ta cinye mulmule biyu sannan ta koma kan farfesun, Ita kanta har mamakin kanta take yanzu lokacin da ba'a san da cikin ba kwata kwata bata cin Abinci sosae yadda ta saba take ci amman yanzu sosae cin Abincin ya k'aru, shima farfesun sosae ta ci shi don ba K'aramin dad'i yayi mata ba amman ta rage, bayan ta gama ta rufe komai ta d'auki tray d'in don ta fitar, a daidai bakin k'opa suka had'e da Haisam da dawowar shi kenan daga Masallaci, hannu ya kai ya amshi tray d'in yace mata wa yasa ta d'aukko ta langa6ar mashi da kai, ruk'e tray d'in yayi da hannu guda yasa d'ayan ya bubbud'e ganin bata cinye ba yasa shi kallon ta tana ganin haka ta tura mashi baki a shagwabe tace wllh ta k'oshi sosae ta ci, d'an d'aure fuska yay yace su koma ta ida cinyewa ta yamutsa fuska kamar zatai kuka tana fad'in Allah cikinta fashewa zai yi, suna Haka Mom ta sawo kai cikin d'akin har saida Fatuu ta ji kunya da sauri ta juyar da kai, tsayawa tay gefe da murmushi ta tambayi ya akai yace mata bata cinye ba, kallon Fatuu tay tace "Daughter ya akai baki cinye ba?" Juyowa tay a kunyace tace mata Allah ta k'oshi taci sosae, hannu Mom ta mik'a ta amshi tray d'in ta duba, jinjina kai tay tace ba laifi ta ci sosae ta juya ta fita da shi, had'a ido sukai tayi mashi wani kallo ya kai hannu ya jawo ta jikinshi ta saka dariya, ganin abun na neman yin yawa ta fara k'ok'arin k'wacewa tana fad'in kada Mom ta shigo don Allah, kawai sai gani tay ya d'auketa gaba d'aya ya nufi gado da ita gaban ta sai fad'uwa yake, a saman gadon ya d'aurata shi kuma ya zauna a baki yana murmushi yace hira yazo taya ta.

Bayan Nameer ya shigo gidan daga Masallaci direct d'akin Hajiya ya wuce lokacin daya shiga parlon su gwaggo na zaune bata dad'e da gama yin salla ba suka zauna suna kallo ita da wasu yan uwan su da suke a part d'in Hajiyar, tsayawa yayi suka gaisa kafin ya wuce Bedroom, da sallama ya shiga ya hangota zaune akan prayer mat ta jingina da gado, wurinta ya nufa yana zuwa shima ya zauna a k'asa kan Carpet kusa da ita tana ta kallon shi fuskar ta a sake, ganin yayi shiru yasa ta ce mashi ya akai, gaishe da ita yay ta amsa, jimm yay sai d'an murmushi yake yama rasa ta ina zai fara, sake tambayar shi tay wai lafiya yazo ya tasata a gaba sai wani murmushi yake kaman wani zautacce, ce mata yay dama zuwa gaishe da ita yay ta d'an harare shi ya d'age gira yace ko bata so, d'an ta6e baki tay tace to ta gode sai kuma mi, saida ya d'an sosa k'eyar shi sannan ya fara Magana da yar in ina yace mata dama ya samu wacce yake so ne a wurin bikin nan kuma har sun daidaita ma to shine yake son don Allah tay ma Dad magana sai ayi magana da parents d'in ta, zuru tay tana kallon shi har ya gama tay d'an murmushi tace wacece ya ke son, fad'i mata yay k'anwar bride d'in Ya Haisam da d'an alamun mamaki tace wacce k'anwar tata yace mata Mino, d'an wara ido tay tace "Kai yaushe har kasan Ameenatun da zaka ce kana son ta kuma kun daidaita?" Fad'i mata yay anan bayan sun zo, shiru tay ta d'an jinjina kai idonta akan carpet shi kuma yanata kallonta yana jiran ya ji mi zata ce, maido idon tay kan shi tace Yanzu in aka yi magana da iyayen nata aurenta zai yi da sauri ya d'aga mata kai, d'an shiru ta k'ara yi sai kuma tace "ni da nayi tunanin kai ma yar gida za'a yi kai da yar'uwar matar yayan taka Farha" wata yar zabura yay ya bita da wani kallo na baka tsammaci jin abu ba, tana murmushi tace mashi eh ba sai a k'ara yin yar gida ba a k'ara dankon zumunci, da sauri ya girgiza mata kai yace "ni gaskiya bazan iya auren ta ba yarinyar da bata girmama mutane ko gaishe ni fa bata iya yi in ma na samu tayi man kallon arziki, d'auka na take wani tsaranta taya zamu yi aure haka, kuma ma dai ai saida soyayya ake aure ko to ni gaskiya ban mata irin wannan son" ya k'arasa Maganar ya d'an 6ata fuska, kallo kawai Hajiya ta bi shi dashi sai k'ara 6ata rai yake, jimm tay can ta tambaye shi ita Minon ya tabbatar suna son juna ba sai anyi magana ba kuma azo kuma daga baya wani cikin su ya canza ra'ayi da sauri yace mata wllh duk suna son juna sosae sun ma yima juna alk'awarin kan haka, harara Hajiya ta wurga mashi ya sunnar da kai yana dariya, ajiyar zuciya ta sauke tace Shikenan zata yi ma Baban nashi magana tana rufe baki ya matsa ya rungumeta yana fad'in shiyasa yake son ta, ture shi ta fara yi tana fad'in ba wani dad'in bakin da zai yi mata ina wani so yake yana k'ok'arin yi mata kishiya, sakin ta yay yana dariya har zai mik'e sai kuma ya dakata yace mata don Allah koda Dad zai k'i tay convincing nashi wllh yarinyar bata da matsala in ya aureta ya dace mata, hannu tasa ta ruk'e ha6a alamar mamaki ya mik'e yana dariya ya nufi k'opa yana fad'in Allah yasa yaji Alkhairi, bayan ya fita Hajiya ta d'an girgiza kai.

Wuraren k'arfe goma da yan mintuna Senator ya dawo gidan yana sanye da babbar riga da yan ciki na brown shadda kan shi sanye da hula mahad'in kayan haka agogon shi da takalman shi da alama Haisam gadon yin to match yay, ta main parlor ya shigo bai bi ta k'opar da ke kai shi part d'in shi ba kamar yadda yake yi in ya dawo da daddare, hannuwan shi ruk'e da fararen ledoji nasu d'auke da tambari a jiki ya nufi part d'in Mom, Fatuu zaune a saman gado har tayi wanka ta saka doguwar rigar bacci kanta sanye da hula su twins da Abdul da Noor zagaye da ita gaba d'aya idanun su na akan tv d'in cikin d'akin suna kallon cartoon da akai ma Fatuu dole take kallo, da Sallama ya shigo duk suka kai idanun su kan shi aikuwa da sauri su twins suka sauka daga kan gadon suka nufe shi da gudu suna fad'in "Oyoyo Daddy" bud'a masu hannuwa yay suna zuwa a tare suka fad'a ya rungume su yana dariya, d'ago kai yay ya kalli su Abdul da suma suka saukko daga kan gadon daga d'an gaban su suka tsaya suna kallon su da murmushi, ce masu yay su bazasu yi welcoming d'in shi ba Noor ta ruga itama ya rungume ta ganin haka yasa Abdul ma yaje shima aka had'a dashi aka rungume, sakin su yay yana fad'in to su shiga ciki Mubeen da Mubeena suka kai hannu suna fad'in ya kawo su ruk'e ya sakar masu leda guda d'aya yace to su je su kai ma Yayar su ta saman gado, da gudu suka juya suna zuwa suka mik'a mata ta amsa tana murmushi, nufo ciki yay ya tsaya daga gaban gadon Fatuu ta gaishe da shi Fuska a sake ya amsa yay mata ya karfin jikin tace Alhamdulillah, tambayar ta yay taci Abinci ta ce mashi eh yace sosae tana murmushi ta k'ara cewa eh,

"To ga Fura nan sai ki k'ara" kai ta jinjina a hankali tace ta gode, su twins ne suka dawo gaban shi Mubeena ta kai hannu tana k'ok'arin amsar leda guda tana fad'in suma a basu fura d'in, janye ledojin yay ya 6oye su a bayan shi yana fad'in babu na su, wani kallo Mubeen yay mashi ya turo baki yace to wannan duk na waye yace mashi d'aya na Hajiyar shi ne d'aya kuma shi zai sha, a shagwabe Mubeena tace to ya basu nashi furan, wani kallo yay masu mai kaman harara yace to shifa, har suna had'a baki wurin fad'in sai yayi hak'uri, girgiza kai yay ya d'an tura baki irin yadda suke yace "ni bazan hak'uri ba gaskiya ai don in sha na siyo ko, wai yama akai baku yi bacci ba?" dariya yadda yayi ya basu Mubeena tace rabon zasu sha furan ne yasa basu yi bacci ba yace to kuwa bazasu sha ta ba,

k'ok'arin kamo ledar suka fara yi ta bayan shi yana kaucewa can ya d'age su sama yace in suka kama to zai basu, tsalle suka fara yi harda Noor da Abdul Fatuu sai dariya take sosae abunda suke ya saka ta nishad'i, ganin sun kasa kamowa don Dad d'in nasu ba gajere bane tur6une fuska su twins sukai suka hau yi mashi magiyar ya basu, suna haka Mom ta fito daga toilet tana sanye da bathrobe kanta ta nad'o towel, nufo su tay fuskarta da murmushi ta tsaya gefe, sannu da zuwa tay mashi ya amsa ta kalli su twins ta tambayi ya akai, kafin su bashi amsa Dad d'in yace fashi suke son yi mashi na furar shi kuma bada su ya siyo ba, yar dariya tayi tace a taimaka a basu tun da sun gani suka had'a baki suna rok'on shi ya basu, kwa6e fuska yay alamar zai yi kuka yana fad'in bazasu tausaya mashi ba su bar mashi furar shi, Noor da Abdul ne suka ce sun bar mashi ya sha su twins kuwa girgiza kai sukai suna bubbuga k'afa, mik'a masu leda guda yay suka saki k'arar murna Mom tace to suje Parlor su sha suka nufi hanyar fita daga d'akin suna fad'in "Thank you Daddy, We love you" yana dariya yace tunda sun raba shi da abun shi ba, wucewa Mom tay wurin mirror tana yar dariya ya kalli Fatuu ganin ta aje ledar yace ta sha yanzu Saboda ta bi jikinta cikin girmamawa tace to ta kai hannu ta fiddo robar furar ta fara bud'ewa, tambayar ta yay ko a kawo mata cup da sauri tace a'a zata sha a robar, jinjina kai yay sai kuma yace ta saki jiki duk abunda take so tayi magana sannan kada ta cika yin zirga zirga zuwa ta samu lpy sosae a hankali tace to, kai idon shi yay kan Mom dake yin shafa ta cire towel d'in kanta tana taje sumarta Tubarkallah gashin har k'ugunta gashi bak'i wuluk, maido idon shi yay kan Fatuu yayi mata sai da Safe ta amsa ya juya ya nufi hanyar fita idon ta akan shi tana murmushi.

Bayan ya fito part d'in Hajiya ya nufa don kai mata Furar ta, dama in dai tana Abuja duk dare sai ya siyo mata in yana nan in kuma bai garin sai ya sa a siyo mata, a parlor ya isketa ya gaisa da Mutanen ciki kafin suka gaisa da Hajiyar ya bata ledar, mik'ewa tay tace mashi tana son magana da shi suka nufi Bedroom, bayan sun shiga a bakin gado ta zauna shi kuma ya zauna akan carpet tana ya zauna a bakin gadon shima mana yace lafiya lou nan ma, zancen da Nameer yazo mata da shi tay mashi, farko d'an jimm yay kafin ya kalleta yace to ya take gani tunda tasan yarinyar, ce mashi tay gaskiya ita a saninta bata da wata matsala ya sake cewa to tana ganin lafiya lau a barshi ya auretan tana murmushi tace tunda yace yana so kawai ai mashi fatan Alkhairi, jinjina kai yay yace to Allah ya tabbatar da Alkhairi ta amsa da Amin, shiru suka d'an yi kafin tace mashi Kakar ita Fateema d'in ta fad'i mata gobe zasu tafi don haka sai ayi masu magana da wuri yace in sha Allah, yar hira suka d'an ta6a daga baya ya mik'e sukai sallama ya tafi. Bayan ya koma part d'in shi toilet ya nufa don yayi wanka, after some minutes ya fito jikin shi sanye da bathrobe ya hau shiryawa cikin kayan bacci riga da wando, bayan ya gama parlon shi ya fito ya zauna ya kai hannu kan table d'in dake a gefen kujerar ya d'aukko jarida ya fara dubawa, bai dad'e da zama ba Mom ta shigo itama ta shirya cikin kayan bacci masu santsi bak'ak'e da layi layin ratsin fari kanta ta yafo d'an k'aramin farin gyale sosae tay kyau farinta ya fito, nufo cikin parlon tay hannuwanta ruk'e da d'an babban tray d'auke da kayan abinci, matsar da c-table tay gaban shi sannan ta d'aura tray din, kallon shi tay suka sakar ma juna murmushi, serving nashi Abincin wanda irin tuwon data kai ma Fatuu ne ta shiga yi, bayan ta gama a kujerar gefen shi ta zauna suna d'an ta6a hira tana kallo, bayan ya gama ta d'auke kayan ta fitar da su,

Dawowa tay d'auke da had'addan flask milk anyi mashi adon golden kai kace da gold akai adon harda cups d'in shi tray d'in ma duk mahad'in shi ne a saman c-table ta d'aura, bud'e Flask d'in tayi ta tsiyaya mashi ruwan shayin da ya sha kayan k'amshi da Zuma dama duk dare wadda take da kwana sai ta had'o mashi shi yau ita ke da kwana don bak'in shi wasu sun tafi d'azun da rana Saboda gobe Monday akwae aiki wasu kuma ba anan zasu kwana ba Mutum biyu yan Daura da Suka rage suna a part d'in da aka sauke su Ard'o, fuskar ta da murmushi ta mik'a mashi dama tunda ta shigo idon shi na akanta, k'ayataccen murmushi ya sakar mata ya furta "Shukran laki Ya Uwargida sarautar mata" dariya tay ta koma kujerar dake gefen shin ta zauna ta kai idon ta kan Tv shi kuma yana ci gaba da kurbar shayin nashi, jefi jefi suke yin magana a haka har ya shanye ta tambayi a k'ara mashi ya d'an d'aga mata hannu "tukunna bari inason zamu yi magana ne" kai ta jinjina ta maido hankalin ta gaba d'aya kan shi, d'an gyaran murya yay a nutse ya fara mata Maganar da sukai da Hajiya ta Nameer, shiru tay tana saurarar shi har ya gama a hankali ta maida idonta ta koma kallon Carpet d'in k'asa yanayin fuskar ta ya d'an canza, idon Senator na kanta ganin yadda tay yasa shi tambayar ko da matsala, maido kallonta tay kan shi ta fara magana "Nameer d'iyar Yaya Othman na Qatar nike son ya Aura Jahad, har nayi mashi Maganar kwanaki kuma ya nuna ma ya amince yanzu kuma ya zai zo da wannan Maganar?" sigh Senator yay ya jinjina kai kafin a nutse ya shiga kwatanta mata k'ilan dama kawai don kar yayi jayayya da ita ne yasa ya nuna mata ya amince ko kuma da gaske ya amincen yanzu kuma ya ga wannan yaji ita yake so, to shi abunda yake gani zai fi kyau ai mashi yadda yake so tunda can ba'a riga an tsaida magana ba, nuna mata yay yaran zamani yanzu ba'a cewa za'ai masu dole a 6angaren aure sun auri wadda suke so ma wasu ya aka kare bare kuma wadda basa so, shiru kawai tay still da yanayin canzawar fuskar ta,

"Ina son ki kwantar da hankalin ki nasan a koda yaushe kina masu Addu'ar mafi Alkhairi a rayuwar su don haka ki d'auka wannan d'in itace tafi Alkhairin a gare shi tunda Addu'ar mu karbabba ce a gare su, abunda ake mawa dama shine a samu asali mai kyau da kuma kyan hali Hajiya duk ta tabbatar man da wannan game da ita yarinyar hakan ne ma yasa ai tun farko ta goya ma shi Babban yayan nasu baya, kuma kinga yanzu in akace a hana shi zai ga anyi mashi ba daidai ba tunda shi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login