Showing 129001 words to 132000 words out of 512766 words

Chapter 44 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1610

bakin gadon sannan ya nufi kopar, ganin ta k'ara kwankwasa har sau ukku ba'a bud'e ba yasa ta hak'ura tana shirin juyawa ya bud'e kopar da sauri ta kai idon ta kan shi suka had'a ido, wani irin bugu kirjinta yay ta d'an zaro ido tana kallon shi shima irin kallon baka tsammaci ganin mutum ba ya bita dashi, gaba d'aya ta kame kanta ba kamar a yadda ta ganshi hannuwan ta da ta had'e sai d'an rawa suke, sakin kopar yay ya juya ba tare da ya ce mata komae ba, d'an jimm tay kaman bazata shiga ba sai kuma ta shiga ta maido kopar wani irin ni'imtaccen sanyin Ac had'i da daddad'an k'amshi mai ratsa zuciya suka tarbeta har saida ta d'an lumshe ido taja numfashi, in da kujeru suke ya nufa ya zauna kan 2 seater ta nufi can walking slowly gaba d'aya a d'arare take, a gefen wurin ta tsaya tana kallon shi ya sa duka tafukan hannayen shi ya dafe goshi alamar baccin bai ishe shi ba aka katse mashi, saida ya d'an d'auki lokaci sannan ya cire ba tare daya kalleta ba da hannu yay mata nuni da kujera alamar ta zauna jiki a sa6ule ta nufi cikin wurin ta zauna akan one seater tana facing d'in shi, gaba d'aya ta tsorata da yadda ta ganshi don bata ta6a ganin shi haka ba duk ilahirin jikin shi inda gashi ke fitowa suma ce a kwance liya liya ga farin shi gaba d'aya ya tafi bai d'aya skin d'in shi sumul da ita ba ko d'an ta6o ko bambancin kala harta gwuiwar shi ba bak'i ko tabo kamar bai yi rarrafe ba da yana yaro kawae dae skin d'in wurin jan ta ya d'an fi cizawa ga suffar k'arfin shi ta bayyana muraran gaba d'aya a murde yake, tana cikin k'are mashi kallon ya kai idon shi kanta suka had'a ido ta fara motsa baki da k'yar ta k'ak'alo Kalmar ina kwana tace mashi kaman ba zai amsa ba sai kuma ya amsa can k'asan makoshi ganin yana mata kallon da take ganin na fushi ne yasa ta sunkuyar da kanta yaci gaba da kallon ta,

"Why are u here not in School?" Bayan wasu sakanni taji cool voice d'in shi ya fad'i hakan, d'ago kanta tay ta kalle shi ta fara motsa baki tama rasa ta ina zata fara mi zata ce mashi duk ta dabarbarce ba kaman da ya kafeta da kaifafan idanuwan shi masu k'ara mashi kwarjini gathering much courage ta fara magana cikin yar rawar murya "d...dama zuwa nayi in baka hak'uri kan abunda ya faru....nasan nayi maka laifi amman ni bansan komai bane shiyasa na aikata wannan kuskuren....don Allah Ya Haisam kayi Hakuri" da k'yar ta k'arasa Saboda idon shi dake a kanta tana yi tana maida kan ta k'asa tana d'agowa, bin ta kawae yake da ido kaman ma bashi da niyyar tanka mata duk tasha jinin jikinta sai yan kame kame take,

"Ba zan yi hakurin ba!" Kaman saukar aradu haka taji Maganar da sauri ta tsaida idanunta akan shi ta zaro su don bata ta6a tunanin zata ji ya fad'i haka ba, d'agowa yay daga jinginar da yayi da kujeran a kausashe yace "da baki san komae ba banyi k'ok'arin sa ki sani ba? Tell me how many times did I call u to explain everything amman Saboda taurin kai kika k'i picking all my calls har message na tura maki warning u not to do anything amman Saboda abu ya faru bani da sauran girma da mutunci a wurin ki shiyasa bazaki bi umarni na ba, ni da kika zo nan I gave u chance kin fad'i duk abunda kike so u even shouted at me kin kira ni Azzalumi, macuci, maci Amana which I never expect to heard from u and dat's d worst thing that ever happened to me....." Dakatawa yay yana d'an girgiza kai fuskar shi d'auke da tsantsar 6acin rai ya d'an cije baki Fatuu ko tunda ya fara magana ta kid'ime don bata ta6a ganin irin yanayin da yake Maganar ba tunda suke da shi sai zare ido take tana sakin numfashi da k'arfi ta had'e hannuwan ta akan k'irji tama kasa bud'e baki tace wani abu,

"Nayi tunanin koda ace hakan ya faru ne kuma ba aure tsakanin mu zaki man uzuri, for how long muna tare dake na ta6a maki wani abu makamancin wannan? duk wani dama da zan iya aikata maki hakan na samu amman ban ta6a jin ina sha'awan hakan ba kaman yadda kika fad'a man wai ina son jikin ki God forbid! ban ta6a jin hakan ga wata wadda ba halal d'ina ba, kallon da nike ma siblings d'ina shi nike maki before aure ya shiga tsakaninmu amman kin yanke man mummunan hukunci har kin nuna guy d'in da aka so aura maki yafi ni duk da halin shi da aka fad'a man Saboda shi bai cutar dake ba sai ni right?" rai 6ace yake Maganar yana jinjina kai da alama maganganun nata sun tsaya mashi a rai, a rud'e Fatuu ta taso tazo daga d'an gaban shi ta duk'a tana girgiza mashi kai ya bita da ido cikin kuka tace "Don girman Allah ya Haisam kai hak'uri nasan nayi maka ba daidai ba sharrin zuciya ne, wllh ita tasa na kasa maka uzuri duk da nasan halin ka ta raya abubuwa ba daidai ba akan ka, kuma wllh ni ban daina ganin girman ka ba kawae dai nak'i d'aga wayan ka ne Saboda ina tunanin zaka hana ni aiwatar da abunda nai niyya ni kuma ina tsoron matsalolin da zasu biyo baya don bansan da aure a tsakanin mu ba shiyasa naga yin hakan yafi kuma wllh harda k'arin don kada k'imar ka da Mutuncin ka su zube kaji na rantse maka, amman don Allah kayi hak'uri na gane kuskurena ba zan k'ara ba" ta k'arasa fuskarta jage jage da hawaye tana yi tana gogewa wasu na sake zubowa, shiru yay ya jingina da kujerar yana ta kallon ta ita kuma sai motsa baki take ta marairaice fuska can yay sigh yace "is Ok,ai ke zan ba hak'uri na aure ki bada sanin ki ba daga baya kuma na cutar dake am really for dat" da sauri tace "a'a ai ni taimako na kayi kuma ba cutar dani kayi ba don ban sani bane nace haka kuma da na saurare ka da na san komai kayi Hakuri da abunda nayi" ta k'arasa tana ta6e baki yadda ta saba kuka tun yarinta still idon shi na akan ta sai yan kame kame take taji ya sake cewa "I know kinsan girman zunubin laifin da kika aikata amman kika za6i ki aikata and kinsan had'arin da ke tattare dashi but still kika aikata kawae don gudun matsaloli, baki ji tsoron sa6a ma Ubangiji ba?" hannu ta kai tana d'an sosa gefen wuyanta tana kikkafta ido ganin ya kafe ta da nashi idon yasa tace "Sharrin zuciya ne, kuma har yanzu banda cikakken hankali tunda ban girma ba sosae amman na rok'i Allah ya yafe man" bin ta kawae yay da ido ita kuma tsakani da Allah tay Maganar ta, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yace "shikenan kawae you can go back to School nayi hak'urin" kallo ta bi shi dashi har saida yace bata ji bane sannan ta fara k'ok'arin mik'ewa tace mashi ta gode ta juya, har ta fita daga wurin idon shi na akan ta sannan ya maido su yana kallon gaban shi kaman mai tunanin wani abu lokacin yaji k'arar rufe kopar ya mik'e ya nufi hanyar corridor, bada jimawa ba ya fito sanye da jallabiya ya nufi gaban mirror ya d'auki Car key ya fice, lokacin daya fito a harabar gidan ya hangota ta tunkari gate tana tafiya tana goge fuskarta da hannu, parking space ya nufa sai lokacin ta lura da shi ya d'aga hannu yay mata alamar ta tsaya, bayan ya fiddo Motar ya nufo gate d'in a saitin inda take ya tsaya ta zagaya d'ayan side d'in ta bud'e kopar gaba ta shiga, sai da suka fito sannan ta tuna da mai Keke Napep dake ta faman jiranta sam bai ji ya gaji da jira ba don yana sa ran zai samu biya mai kyau ba kamar da ya ga gidan da ta shiga, Haisam na ganin Napep d'in tun kafin ma tayi magana ya tambaye ta tare suke tace mashi eh ya tsaya gefen shi ya kai hannu ya bud'e glove box ya k'irgo 5k ya bata yace ta kai mashi tace to ta amsa ta bud'e kopar, lokacin data ba mai Keke Napep d'in washe baki yay ya shiga yin godiya harda biyo ta bayan ta bud'e kopar ya duk'o da kai yana mashi godiya ya d'aga mashi kai kawae bayan ta shiga yaja suka tafi,

A daidai inda ya aje ta da safe ya parker tuni an koma break ba kowa a wajen ta juya ta kalle shi idon shi na kallon gaban shi a sanyaye ta furta ta gode ya d'aga mata kai ta juya zata bud'e kopar lokacin taji muryar shi yace in an tashi ta jira zai zo ya d'auketa, d'an juyawa tay suka had'a ido a hankali tace mashi to kafin ta sake juyawa ta bud'e kopar, bayan ta fita ya juya Motar ya tafi tabi bayan Motar da kallo har ta daina ganinta sannan ta juya jiki ba kwari ta nufi class, tana zuwa bakin barandar benen da ajin su yake kawae sai ta zauna a wurin ta jingina da pillar ta d'an d'age kanta sama kwalla suka fara gangaro mata wani irin dana sani take yi ta rasa ya akai ta kasa yi ma Ya Haisam uzuri kaman yadda ya fad'a yakamata ace tunda tasan halin shi bata yi mashi yadda tay mashi ba, amman tasan harda bak'in abubuwan da taga ya fara yi mata ne yasa tay tunani na daban akan shi, tuno yadda ya rink'a yi mata Magana da tsantsar 6acin rai ta shiga yi dama Fauzy tace k'ilan abun yay mashi ciwo sosae ashe hakane ta fahimci bai so ta zubar da cikin ba, girgiza kai ta fara yi a fili ta shiga fad'in "am sorry my husband nasan na aikata kuskure amman cikin rashin sani ne bazan k'ara ba..." haka tay ta sambatu k'walla na zuba, Sa'adatu ce ta fito daga cikin class d'in su zata je toilet ta hango ta saida taje ta dawo sannan ta nufi Fatun ta tsaya gefen ta ta kira sunanta har sau biyu sannan tay d'an firgigit ta sauke kai ta kalleta, ganin hawaye a fuskar ta yasa tay saurin zama a gefen ta kai hannu ta dafa Shoulder d'inta tana tambayar ta lafiya Fatun tay shiru, ta k'ara tambayar ta ko jikin nata ne sai lokacin ta d'aga mata kai alamar eh cike da tausayawa ta hau yi mata sannu ta tambayi to ta sha magani ne ko suje ta rakata Asibiti tace mata daga can take tace to ta taso su tafi aji amman sai tace taje kawae tafi jin dad'in zama anan ta ce to, ta k'ara yi mata sannu tare da mik'ewa ta nufi komawa aji, da yake akwae malami cikin class d'in hakan yasa bata fad'i ma Fauzy game da Fatun ba har saida ya fita sannan ta tashi da sauri taje seat d'in su ta fad'i ma Fauzy aikuwa tun kafin ta gama fad'i matan ta mik'e zumbur tay hanyar fita, tana hangota ta nufe ta da sauri, tana zuwa ta zauna gefenta hankali tashe ta kai hannu ta dafa Shoulder d'in ta ta hau tambayar ta miya faru, tace ta iske Ya Haisam d'in kai Fatuu ta d'aga mata alamar eh, tace to ya sukai dashi, cikin muryar kuka ta shiga fad'i mata Fauzyn nata girgiza kai itama har idanunta sun kawo kwalla bayan ta gama fad'i mata yadda sukai dashi tace "ashe abun ya mashi ciwo ne sosae kaman yadda kika ce Fauzy, ban ji dad'i ba da na kasa yi mashi uzuri har komai ya faru if I had known I would have listened to him da komai bai faru ba nayi dana sani sosae" janyo ta Fauzy tay ta rungume ta ita kanta bata ji dad'in abubuwa data fad'i ma Ya Haisam din ba wanda ta 6oye mata hak'ik'anin yadda sukai dashi lokacin data dawo, jin tana ta kuka yasa tace "shikenan kukan nan ya isa hakanan kinga ba ki idasa warwarewa sosae ba kada kuma wani ciwon ya kama ki, tunda yace ya hak'ura ai shikenan sai a kiyaye gaba" d'ago kai tay ta kalleta tace "ni gani nike kaman bai hakuran ba ya dae fad'a ne kawae tunda har yanzu yanayin da nike gani bai canza ba" Fauzyn tace "kar ki damu tunda yace ya hak'ura to ya hak'uran kin dae san ai ba zai magana biyu ba daga baya yace bai hak'ura ba wannan ai k'aranta ne, dama burin mu ya hak'uran naji dad'i sosae abunda kuma ya rasa in sha Allahu bada jimawa ba za'a biya shi wani" wani kallo Fatun ta d'aga kai tay mata Fauzy tasa dariya,

"Yanzu kinga sai muji dad'in fara shirye shiryen duk da banji dad'i ba da ba wani shagali da za'ai amman mun biyo bashi koda in kika haihu ne sai mun yi shagali sosae, yanzu yaushe kike ganin zamu je ai maki k'unshi da gyaran kan?" d'agowa tay daga jikinta ta zauna sosae tace mata itama bata sani ba Fauzy tace "tun yau yakamata a fara maki gyaran jiki gobe ma a k'ara sai a gyara maki gashi jibi in Allah ya kaimu sai ayi maki k'unshi bari in aka tashi zan je gida sai in sanar ma Aunty Mareeya zuwa da la'asar sai muje wurin gyaran jikin" kai Fatun ta d'aga mata alamar to Fauzy ta kai hannu taja kumatun ta tana fad'in ta saki ranta Amarya da farinciki aka santa ta d'anyi murmushi kawai ta kama hannunta tace ta tashi su koma aji suka mik'e, Bayan an tashi Hostel suka wuce ta tattara kayan ta da suke a nan kaman yadda gwaggo ta bata umarni Fauzy nata fad'in zatai missing d'inta kad'aici zai dameta amman tana farinciki da abun Alheri ne yasa zata bar zama hostel d'in, Fatun nata murmushi itama duk wani iri take ji tasan dole ta damu da tafiyar ta, indomie Fauzy ta dafa masu harda kifi sardine suna cikin ci Haisam ya kirata yace yazo ta fad'i mashi suna cin Abinci ne amman sun kusa gamawa yace ba wani abu ta gama, bayan sun gama Fatuu tace mata to tazo ba sai a ajeta a gidan ba kawae, cike da tsokana Fauzy tace a'a wai kada ta shiga tsakanin Masoya ta hana su sakewa inta gama kimtsawa zata tafi Fatun ta harareta ta saka dariya, tare suka fito Fauzy ta kamo mata trolley d'inta dama iya shi kadae ne sauran abubuwa kaman provisions wannan ta bar ma Fauzy, lokacin da suka iso inda ya parker Motar back door ta bud'e ta saka akwatin bayan ta rufe ta bud'e kopar gaba ta shiga yana sanye da k'ananun kaya Fauzy ta lek'o ta gaishe da shi fuska a sake ya amsa yay mata ya karatu daga baya ta k'ara yi ma Fatuu sallama tace sai ta zo anjima ta rufo mata k'opar, saida ya ja Motar ta gaishe dashi ya amsa idon shi a kan hanya ta juyar da kai tana kallon gefen hanya har suka iso kopar gidan su ya parker, d'an kallon shi tay tace ta gode ya jinjina mata kai still bai kalleta ba ta juya ta bud'e kopar bayan ta fita har zata rufe sai kuma ta tuna da fitar da zasu yi anjima da Fauzy tasan in ta fad'i ma gwaggo sai tace ta tambaye shi hakan yasa ta duk'ar da kan ta ciki a sanyaye ta fad'i mashi sai lokacin ya juyo suka had'a ido, jinjina mata kai yay tay mashi godiya bayan ta janye kan ta rufo mashi kopar ta bud'e back door ta fiddo trolley din, har saida ta shige gida sannan yaja Motar, tana shiga d'akin gwaggo ta nufa ta d'aga labulan taga bata ciki ta saki ta nufi d'akinta, tana shiga ta aje trolley d'in a bakin gado ta aje jakarta saman gadon ta cire Hijab d'in itama ta d'aura ta saman gadon, tana juyawa zata nufi hanyar fita taji wayar ta tayi k'ara alamar shigowar message ta koma bakin gadon bayan ta bud'e jakar ta ta fiddo wayar ta fara dubawa, alert ne na 500k daga Haisam har saida ta d'an zaro ido dama wanccan da ya turo mata suna nan bata ta6a ko sisi ba yanzu ga wasu sun kama 1 million kenan d'an jinjina kai tay ta ayyana in gwaggo ta dawo sai ta nuna mata, har zata aje wayar wata zuciya ta raya mata yakamata tay mashi godiya d'an jimm tay tana yin wasi wasi na ta kira ko kar ta kiran, can dae ta kira saidae har ta yanke bai d'aga ba jikinta ne yay sanyi lakwas ta ji dama bata kira ba don a tunanin ta yana tare da wayar tunda yanzu ya turo mata sak'o, har zata ajeta kan gado sai gashi ya kira tabi kiran da kallo kaman bazata d'aga ba can dae tay picking ta kara a kunne bai tanka ba cikin yar inda inda tace taga sak'o ta gode sai lokacin ya furta Ok tay shiru can taji ya furta "da wani matsala ne?" da sauri tace a'a ta katse kiran, bin wayar tay da kallo a ranta ta ayyana halin Ya Haisam sai shi ta d'an ta6e baki sai kuma tay d'an murmushi ta aje wayar ta juya, d'akin Kawu Amadu ta nufa ta iske shi yana ta bacci hakan yasa ta juyo ta koma d'akin ta, a bakin gado ta zauna ta d'auki wayar tana kokarin kiran gwaggo, tana fara ringing ta d'aga bayan ta gaishe da ita ta tambayeta ta dawo ne tace mata eh ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login